Showing 63001 words to 66000 words out of 257873 words

Chapter 22 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

489

center table naga leda da mangwaro harda yalo fari da kore a ciki se farar takarda a ninke na buɗe ta 'i might be late, amma karkiyi bacci ki jira ni please' abin da aka rubuta kenan.

Murmushi na saki wani daɗi ya ratsani dan nasan daren yau kam ze zama na daban ne, kasala da zazzaɓin da nake ji ma duk se na neme su na rasa na tashi ina idar da sallah na shiga shiri dukda bansan da me ze zo ba.

Washe gari cikin annashuwa da farin ciki muka fita, gidan mu ya sauke ni, a cike na tarar da gidan su Anty Labiba da sauran ƙannen Mama da suka zo yinin sallah dan tun bayan da mahaifiyar su ta rasu kasancewar Mama Fauziyya da take babbar su ba'a nan suke zaune ba se Mama ta ƙwace girma ya zama duk wani haɗuwar su a nan gidan mu sukeyi. Se yamma lis muka leƙa gidan su Bilal suna dukda ni tun azahar na zabara zan tafi Anty Mimi cousin ɗin su Mama kuma matar Uncle Mudassir ce ta hanani. A bakin get muka ci karo zata shigo ni kuma zan fita ana yayyafi dan anyi ruwa be ƙarasa ɗaukewa ba tun farko ma saukar ruwan ce ta hanani tafiya dan niyyata kamar sha ɗaya haka na tafi tunda tara bata ƙarasa bama ya kaini gida naga kuma da naje zanje ɗin babu wanda yace Aa Anty Labiba cewa ma tayi ya kamata ai dana haƙura ma da zuwa gidan yau na tafi can tunda muna da suna wai ashe baƙar magana ta faɗa mun.

"Karki kuskura ki ɗauki wannan salon gaba ya dame ki, ba'a ce kar kiyi sabga da dangin mijin ki ba amma komai ya zama da iyaka babu cusa kai babu wulaƙanci biki suna ba zancen ki tafi tun wurwuri ki zauna gara ki shiga a marmarce a gama ki kama gabanki da kina da yara ne ma wannan tun safe kya iya turasu su shiga cikin yan uwansu idan yaso kya je daga baya amma gari ko gama tsanewa beyi ba kin zari mayafi zaki tafi kyaje ki rasa gurin zama yanda baki da aikin nan se kwanciya".

Ɗaki na shige jin sun mun caa ashe wai duk shiru kawai sukayi kowa da magana a bakin ta. Ni dai na kasa nutsuwa gani nake ban kyauta ba ace ana sunan ƙanwar miji na a matsayi na na matar wanta da suka ɗaki ɗaya nasan yanzu duk faccaloli na wanda mazajen su suka haɗa uba da su Bilal ai sunje se ni kaɗai ce bazanje da wuri ba. Haushin dalilin daya sa ban fara tsayawa acan ba naji yanda kasan wadda tayi laifi haka na kasa tsaye na kasa zaune daga ƙarshe ban wa kowa sallama ba na bi ta ƙofar kitchen na fice surutu ne dai zasuyi su gama kuma duk da zasu ce kar naje naga kowa idan sabgar dangin mijin ta ya tashi sune a gaba har ma su gayya ce mu shine ne za'a koya mun na wulaƙan ta nawa na kuma kashe wayata dan karma su kira ni.

Aiko abin da na guda ina zuwa yan gidan su Bilal suka mun caaa wai se yanzu harda Hajjan kuwa da yan uwanta, abin takaici gurin zama me kyau ma na rada duk da gidan ba'a cike yake ba iya su ne yan ɗakin su se yan uwan Hajjan da yayan su ko waɗan da suke uba ɗayan mutum ɗaya na gani Farisa sauran sun ce ruwa ya hana su fito. Haka na ringa raɓe raɓe daga wannan bangon zuwa wancan ga babu fuska hatta mejegon wani gani gani naga ta mun ba abun na koma gida ba na tarar da surutan su Anty Labiba a daddafe na jira akayi la'asar suma ban musu sallama ba na kama hanyar gida na.

Daga yanayin yanda Bilal ya shigo gidan na gane ba lafiya ba, be dai ce mun komai ba har na dafa masa Indomin daya buƙata. Ina shafa mai bayan na fito daga wanka ya shigo ɗakin ya zauna kan bedside drawer yana kallo na yace
"Ƙarfe nawa kika je gidan sunan ne?"
Se naji gaba na ya faɗi dukda cikin sanyi yayi maganar, a hankali ni ma nace
"Kasan anyi ruwa ga zazzaɓi kuma a jiki na se da akayi sallar azahar ruwan ya tsaya sannan na tafi". Kai ya gyaɗa kawai jin yayi shiru se na cigaba da shiri na ina satar kallon sa, har na kammala na shimfiɗa sallaya zanyi shafa'i da wutri ya sake cewa
"Ke kaɗai kika je kenan?"
"Eh ni kaɗai na tafi, sun ce na jira mu tafi naga lokaci na ƙurewa shine na tafi"
"Hajja tayi zaton tare zaku je da su Mama ai ta zaunar da mutane akan su gaisa kuma basu je ba shine wai taji babu daɗi" ya sake faɗa. Yanayin yanda yake maganar se naga kamar yana so yayi faɗa ne se dai kuma rashin hujja ko dalilin yin faɗan yasa yake fadar maganganun a sanyaye. Ban bashi amsa ba na tayar da sallaha ta dan jikina duk ciwo yake mun dan ma nayi wanka, washe gari da la'asar salaliya kuwa se ga Farisa dake akwai ƙanwar mijinta bayan layin mu itama ta haihu yau ne sunan shine ta ratso.

"Ai in gaya miki jiya karki so kiga tijarar da Hajja ta dasa a gida mara dalili. Bafa ayi girki ba banda na safe har se sanda kika zo ɗin nan fa kikaga ana kiciniyar ɗorawa ga guri ya jiƙe ni dai ana kiran sallar magriba na tafi lokacin abinci ya sauka jama'a dai sunyi wunin yunwa a gidan suna".
Farisa data gama kora zoɓo me sanyi ta faɗa. Ƙanwar Bilal ce da suke una ɗaya ita kaɗai mamanta ta haifa a gidan dan haka ta zama bakin ganga bata ɓangaren su Bilal ɗin bata gefen yan ɗaya ɗakin. Tana da kirki matsalar ta na lura ta fiya gulma da tsegumi ta ɗakko zancen wancan ta kai can aikin ta kenan.

Tun aure na da Bilal take so mu ƙulla mu'amala da na fara sake mata dana fuskanci halin ta se na janye ko a whatsapp ta mun magana se na ja kwanaki ban amsa ba dukda haka bata haƙura duk sanda tazo gidan ƙanwar mijin ta dana fahimci suna shiri se ta ratso ko ita ƙanwar mijin nata ma taso ta haɗa mu zuwan ta uku ban je mata ko sau ɗaya ba dake me hankali ce se ta janye ta rabu da ni.

Shiru nayi ban tanka mata ba ta sake cewa
"Ban da son zuciya dai irin na Babar mu, ashe ke ake ta jira zaku kawo abinci, kin san haihuwar ƙarshe da Ummi tayi bikin ku saura sati biyu Anty Murya Amaryar Yaya Khamis ce ta ɗauki nauyin abincin da aka ci a gidan sunan nan se kinga abu, shine suka saka rai kema zaku musu haka. Se gashi da kika tashi zuwa sungup ance ko abin barka baki bayar ba. Ni dai nace ko ita Ummin da kuɗin Yayanta aka mata ba wai a aljihun ta ita Anty Murjar ta zare tayi ba wlh. Haka dai aka watsa taro yan fadar Hajja marasa tsoron Allah sun tafi dake a baki har ana cewa arziƙi beyi rana ba wai ana wa Yaya Bilal murna ua samo yar masu hannu da shuni ashe duk ƙaryar banza ce babu abin".
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 16*

*Nayi kuskuren rubutu a page 13, ajizanci ne, abinda ke raina daban abinda alƙalamina ya rubuta daban. Ina fatan zaku mun uzuri*

Na ringa juya zancen Farisa a raina bayan ta tafi har sanda Bilal ya dawo sau biyu ina buɗe baki da niyyar tambayar sa gaskiyar abin da ta faɗa mun se na kasa daga ƙarshe na tattara zancen na watsar har ina ganin baike na dana yarda da maganar tata har na saka a raina. Ta ya ma haka zata yuwu? Kawai dai haɗa guri ne irin na Farisa amma kuma idan tayi ƙarya ta ƙulla abu mara daɗi tsakani na da dangin Bilal ribar me zata ci?
Ganin ba ni da wani takamaiman wanda zan tambaya na ji gargar ɗin maganar yasa na barta a bata faru ba naci gaba da sabgogina.

An gama bikin sallah ta wuce ta bar wawa da bashi kamar yanda hausawa suke faɗa, ranar data kama kwana bakwai dai dai da yin sallah tun da safe Bilal yace mun zamu fita da yamma. Yanda yake ta zirgilli da rawar ƙafa akan fitar yasa na ringa mamakin in da zamuje dan be gaya mun ba. Ana la'asar ya shiga azazzalata da na shirya mu tafi ni kuma gaba ɗaya naji jiki na ya mun nauyi, ina ta so na koma asibiti ma amma shauni da shiririta ya hanani. Haka dai na ƙoƙarta na shirya, atamfa na saka Holland riga da zani dan kayana sun fara matse ni da alama dai cikin kiɓa ze saka ni, ina tsaka da ɗaura ɗankwali na ya shiga ɗakin yanda kasan me shirin tafiya dinner haka ya sha kwalliya da sabuwar shadda cream color se ƙyalli take yi.

Kallon sa na ringa yi kamar yanda shima yake kallona hanci a ɗage kafin cikin faɗa faɗa yace
"Meye Halims? Wane irin kaya ne wannan kika saka kamar wadda zata je cin kasuwar ƙauye?"

Kallon kaina nayi sama da ƙasa ko zan ga abinda yayi kama da shirin tafiya ƙauye a jiki na amma ban gani ba dan haka na mayar da kallona kan sa nace
"Ban gane ba, me shigar tawa tayi?"
Ba amsa ni ba ya wuce gaban wardrobe ɗina ya buɗe ya shiga birkito kayan ciki yana cewa
"Malama ki cire wannan kin san in da zamuje da zakiyi wannan shigar salon ki zubar mun da mutunchi?
Hannu na harɗe kawai a ƙirji ina kallon ikon Allah. Lace ɗin da nayi kwalliyar kamun bikin mu ya janyo daga ƙasan kaya ya ware shi kafin ya watsa kan gado ya buɗe in da mayafai na suke yana cewa
"Wannan zaki saka". Se ma ya bani dariya, na matsa gefen gado ina cewa
"Wai ina zamuje Bilal?"
"Siyar da ke zanyi, malama ki yi abin da nace kawai kar ki ɓata rai da lokaci" ya faɗa yana aje mayafin daya ɗakko kan kayan. Se na ɗaga rigar nace
"Kasan dai yanzu wannan kayan baze shige ni ba, ka faɗa mun in da zamu je se na duba wanda zasu dace da fitar na saka"
"Walima zamu je" ya bani amsa a daƙile". Har na buɗe baki zan sake tambayar sa tame? Koma waye ya gayyace mu se dai yanda ya haɗe girar sama data ƙasa yasa na kama kaina na shiga lalubo wasu kayan tunda ya kushe atamar dana saka.

A motar Nasir daya karɓo muka fita, se da muka fara tsayawa a kantin Baby dream. A mota ya bar ni ya shiga bayan wasu mintuna ya fito hannu biyu riƙe da ledoji shaƙe da kayan jarirai ya ajiye su a back sit. Mamaki fal rai na baki na cike da magana amma babu fuska dole na haɗiye na zubawa sarautar Allah ido. Can cikin nasarawa gra ya kaimu wani gida. Daga get ɗin farko ma zuwa cikin gidan tafiya ce ta misali, yanda ya gaisa da masu gadin get ɗin na gane akwai sanayya a tsakanin su amma dukda haka a tsorace na ringa kalle kalle har muka isa in da ake ajiye motoci.

Kamar mara gaskiya na ringa bin bayan sa har muka isa entrance ɗin gidan ya dannan door bell, mun kusa minti bakwai a tsaye kafin aka zo aka buɗe, yanda kasan gidan su haka Bilal ya ringa jefa ƙafa ni kuma ina bin sa a baya, se da muka zauna kan wasu kujeru masu azabar kyau da laushi kafin na fahimci gidan Abokin sa Hafiz muka dalilin hoton su shida matar sa dake kafe jikin bango. A raina na raya ashe dai ba ƙarya Bilal yake ba idan yana santin irin arziƙin da Hafiz ɗin suke dashi, na ayyana yana da kuɗi haka ko me ya kaishi aikin gomnati kuma bama wani shahararre ba irin su CBN ko Oil ko porth authority naga can aka fi samun yayan manyan ƙasar a ciki.

Tun zuwan da suka mana ni na manta ma da babin su har idan ba shi ya ɗakko zancen su ba, matar ma da mukayi exchanging number sau ɗaya ta taɓa kirana tace sisters ɗin ta sun ji ƙamshin turaren wutar dana bata suna so na haɗa ta da me siyarwar (08033950747, kina neman turaren wuta me asalin ƙamshi da kama guri wanda duk wanda ya shaƙa seya tambayi in da kika samo shi? Ki tuntuɓe ta) shikenan bamu sake magana ba. Da ina ɗan ganin ta a whatsapp daga baya kuma na dena ganin ta ma na zata yanda ta sake dani sanda suka zo zamu yi doguwar mu'amala kamar yanda Bilal yake fata toh kuma hakan bata kasance ba.

Se da mukayi jiran kusan wasu minti goman har seda Bilal ya kira maigidan a waya kafin suka fito yana saɓe da baby tana bin sa a baya. Na ringa hasaso sanda suka je mana ni dai bangan ta da ciki ba ko kuma lura ne banyi ba oho dai gashi nan ta haihu. Farat farat kamar karon farko muka gaisa, tace mun
"Baki da kirki Halima, na rasa number ki ke kuma ko sau ɗaya baki ce kinji ni shiru bari ki taɓo ni kiji ya nake ba ko dai zumunchin ne bakya so muyi?"
Kafin na bata amsa Bilal yayi caraf yace
"Ai itama wayar ta ta lalace ne, tuntuni kuma tace na karɓo mata number gurin yallaɓai se in manta" Hafiz yace
"Kai dai kace zaka kare ta kawai amma zuwan ka nawa gidan nan kuna haɗuwa ai ko ka manta ya kamata ace idan ka ganta ko sau ɗaya ka tuna saƙon da aka baka". Ni dai sakin baki da hanci kawai nayi ina kallon Bilal jin wannan gingimemiyar ƙarya daya shirga an kuma kama shi. Na sha mamakin jin wai yana zuwa gidan ashe, lallai se a bar Bilal. Ashe shi yasa ba'a ko tambaye mu daga ina ba aka bar mu muka shigo, ko me yake zuwa yi se Allah.

Mita Suhaila taci gaba dayi ni dai na bita da ban haƙuri ina riƙe da kyakykyawan babyn ta me suna Muhammad Sani sunan babanta suna kiran sa Na'im. Duk tarin kayan ciye ciyen da aka cika mu dasu ruwa kaɗai na iya sha a ciki, se da muka shiga ɗakin ta ta dame ni da se na faɗi abin da nake ra'ayi an mun tunda ta lura ba ni kaɗai bace baze yuwu na zo gidan banci komai ba. Dankali nace a soya mun dan na kwana biyu ban ci ba tun azumi. Se bayan sallar Isha'i muka tafi gida shaƙe da kayan arziƙi harda naman suna kusan cikin ƙaramin bokiti a haka ma tace wai ya ƙare ne haihuwar kusan kwana talatin ni dai nace an gaida masu kuɗi ko raguna nawa suka yanka se Allah ko kuma dan basu da yan uwa da yawa a Kano ne tunda mu na gidan su Bilal ma ko hanji ban gani ba cewa akayi mutane sunyi yawa akan naman ya ƙare dama kuma dabbar ƙarama ce batayi auki ba.

"Ki san a Egypt ta haihu se ranar idi suka dawo yace baya so azo ayi ta jagwalgwala masa yaro shiya sa suka yi zaman su se da ya ɗan yi ƙwari. Yan gidan su can a Kaduna sukayi suna na zata ma da suka dawo gida zata wuce wai su basa haka ashe ba'a zuwa wankan gida" Bilal ya faɗa bayan da muka hau titi. Na gyaɗa kai tare da cewa
"Allah sarki, zuwa wankan gida dama ai ra'ayi ne kuma ma yanzu duk an dena ai kowa a gidan ta take zama tayi jegon ta"

"Wanda suka de na dai sun dena mu kuwa a dangin mu kwana sittin ma akeyi ba arba'in ba" ya sake faɗa, se da juya na kalleshi da mamaki nace
"Wato kwana sittin ma? Kai yanzu idan na haihu se ka yarda na tafi gida nayi har kwana sittin bana tare da kai?"

Ido ɗaya ya kashe mun kafin yace
"Nasan dai zan azabtu da missing ɗin ki amma ya zanyi da abin da al'ada ta gindaya. Kwana sittin ɗin ma fa bayan an haihu ne wannan lissafin naga matan su Yaya Suleiman da haihuwar fari da cikin su ya shiga wata tara suke tafiya gida. Kinga kamar Anty Mariya da take ba yar gari ba ina ga se da tayi wata uku ma ita sannan ta dawo ai to ke tun da a kusa kike da kafin haihuwar zuwa bayan haihuwar se kije kiyi arba'in biyu kawai, wai ma wata nawa ne cikin yanzu?" Ya ƙarasa yana ɗora hannun sa akan cikina.

Al'ajabi da mamaki suka sa na kasa cewa komai se bin sa da ido dana ringayi ya kuma yi mirsisi abin sa yaci gaba da tuƙi yana soko mun wata hirar. Mamakin nawa biyu ya kasu, na farko wai ashe ma ya tabbatar ina da ciki amma ko da wasa ban ga wata murna ko zumuɗi a tattare dashi ba sannan kuma yanzu lissafi yake idan na tashi haihuwa gidan mu zan yafi nayi arba'in har biyu wato lallai bani da wani muhimmanci a gurin Bilal. Ji nayi raina ya ɓaci take hawaye ya fara cika mun ido, jin nayi shiru bana amsa hirar da yakeyi yasa ya kamo hannu na yana cewa
"Bacci kika yi ne ina ta magana kinyi shiru?" Aiko kamar ina jira se

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login