Showing 60001 words to 63000 words out of 257873 words

Chapter 21 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

484

ku zamu je gaisuwa gidan wani abokin sa maman sa ta rasu a UK suke to sunyi waya yace yazo Kano amma gobe ze wuce Abuja shine muka taho yanzu fa se da muka kuje kuma ashe shi kaɗai ne yazo banda matar sa, naga zasu ɓata lokaci da hira shine fa nace ya kawo ni nan na dubaki kafin su gama mu wuce, su Halima matar Bilal, irin wannan mulmul da kika yi lallai Bilal ya iya kiwo" ta ƙarasa tana kallo na. Na rufe fuska cikin jin kunya ina cewa

"Kai Anty, kamar kin shekara baki ganni ba"
"A shekarar kaɗan ne babu ai, haɗuwa tayi wuya se dai mu gamu a hanya nan kuma ai ba wani ganin ki nakeyi sosai ba kamar yanzu ko?" Ta faɗa, nasan magana ta gaya mun dan haka nayi murmushi kawai na shiga tambayar ta su Inayah.
"Dama suna gidan Mama ɗazu shine su Amirah basu taho da su ba?" Na faɗa, se tace
"Aa, se gobe zamu je. Amir ne kawai yaje su je kallon hawa tare da su Mu'azzam". Hira muka shiga yi gwanin daɗi, har tara da rabi sannan Uncle Saleh ya kirata yace gashi nan ya taho. Se sannan ta tambaye ni Bilal, tambayar da nake ta addu'ar kar Allah ya buɗi bakinta ta mun dan ban san me zan ce mata ba sanin tun kafin muyi aure da Bilal duk wanda ya sanshi ze bada shaidar baya yawon dare. Duk in da akayi sallar isha'i ya shiga gida in dai ba guri na ze je ba.

Ce mata nayi yana can gidan su ai be jima da fita ba suka zo, kallon da ta mun yasa na fahimci bata kama zancen ba. Ta ƙare mun kallo tace
"Wannan kayan ma tun na kwalliyar safe ne da kikayi baki sake wasu ba". Zan kwaso rantsuwa ta dakatar dani tace
"Idan kika zauna shashanci kanki zakiwa sagegeduwa. Ba yanzu zaki takaicin barin sa ya koyi yawon dare ba se nan gaba dan haka tun lokaci be ƙure miki ba ki gyara. Duk irin hirar da zeje yayi a wajen ki tanade ta ki ringa yi masa a gida ya fiye miki alkhairi idan ba haka ba ke kika sani kina zaune can wasu zasu ringa cusa masa wasu ra'ayoyi na banza a lalata miki miji".

Tunani maganar ta ta jefa ni, anya babu saka hannun abokai cikin baƙin halayen Bilal da nake cin karo dasu? Waya sani kam ko a yawon da yake tafiya ake yo masa wasu karatu na banza suna gurbata masa tunani dan dai ni shaida ce ba haka Bilal ɗin dana sani yake ba tabbas. Buɗe ƙofar da akayi ya dawo dani daga tunanin da na tafi. Muka haɗa ido da Bilal ya galla mun harara ba tare da yayi ko da sallama ba ya wuce kitchen yana sakin ƙaramin tsaki. Se da naji ina ma da damar da ƙasa zata tsage na shige ciki na ɓuya ko kuma ace abin da ya farun yanzu mafarki ne zan tashi naga zuwan Anty Labiba be faru ba. Kamar me ciwon wuya daƙyar na waiga na kalli Anty Labiba dake danna wayarta se ka rantse bata ji shigowar Bilal ɗin ba. Nayi ƙasa da kai kamar munafuka ina jan yatsun hannu na, daga kitchen ɗin ya ƙwalo mun kira. Ƙafafu na sun yi sanyin da bazan iya miƙewa ba, sake kiran yayi se lokacin Anty Labiba ta ɗaga kai ta kalle ni tace

"Ba kiran ki yake yi ba?"
Ina zaton baƙuwar muryar da yaji se gashi ya fito kamar an jefo shi, yayi turus a bakin ƙofa yana raba ido kafin yayi ƙasa da kai yana shafa ƙeya kamar mara gaskiya lokaci ɗaya ya lalubo murmushi ya ɗora a fuskar sa ya nufo in da muke yana cewa
"Kune a gidan namu yau Anty"
"Mun same mu lafiya? Ya sallah?" Ta faɗa tana miƙewa saboda wayar ta data ɗauki ƙarar shigowar kira. Bata amsa gaisuwar da ya shiga yi mata ba ta nufi ƙofa tana ce mun
"Allah ya ƙara sauƙi Halima na wuce se da safe" ta fice daga falon. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na bi bayan ta. Yanzu Allah kaɗai yasan tunanin da zata yi kuma. Dubu goma Uncle Saleh ya bani barka da sallah, Anty Labiba dai tunda ta zauna a motar ko kallo na bata sake yi ba yaja suka tafi.

A kan kujera na tarar da Bilal ya dafe kai da hannu biyu yana jin motsi na ya miƙe fuska ba yabo ba fallasa yana kallo na yace
"Me yasa baki kira ni kin ce mun ta zo ba?"
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 15*
Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce ɗakina na kwanta, nayi mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci kafin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa
"Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya ɗauke ni. Washe gari nayi zaton ze cigaba da fushin amma naga akasin haka dan tun asuba daya tashi be zauna ba seda ya share gidan tas yayi mopping ya wanke banɗakuna harda na tsakar gida.

Ina kwance a falo kan carpet in da nayi sallah ya shigo bayan ya gama gyara tsakar gidan, zazzaɓi ne a jiki na sosai, na lulluɓe har kaina ga iskar hadari dake kaɗawa tasa har karkarwar sanyi nake yi. Sama sama nake jin sa yana kiran suna na, jin ban amsa ba yasa ya ƙaraso in da nake ya duƙa yana kirana tare da ɗan bubbuga gefen pillow da nake kwance.
"Dame zaki karya?" Ya tambaye ni, nayi shiru dan baki na yayi mun nauyi kuma kusancin da mukayi ƙamshin turaren sa dake bugun hanci na duk se ya sake hautsinamun kai baki na har ya fara tara yawu alamar amai na son taso mun. Miƙewa yayi yana cewa

"Shikenan ai, tun jiya nake binki kina mun wulaƙanci. Fitina kike nema ni kuma ba zakiyi da ni ba" ya shige kitchen. Se maganar sa ta ma bani dariya, wai yana bina ina masa wulaƙanci Bilal kenan me abin mamaki. Ƙarfe tara na farka daga baccin da ban san sanda ya ɗauke ni ba, zazzaɓin ya saukar mun dan haka na miƙe ina kallon falon dake ta tashin ƙamshin turaren wuta da roomfreshener. Zancen gaskiya iya gyaran gidan Bilal ba duk mace ba. Haka nan idan ya bushi iska har canza jeren kujeru ya keyi. Se da nayi wanka nayi kwalliya cikin sababbin ɗinkin sallar da nayi kafin na shiga kitchen neman abinci. Doya ya dafa da sauce ɗin ƙwai. Dake akwai wuta se nayi microwaving na haɗa baƙin shayi na dawo falo na zauna kan carpet na shiga karyawa. Bilal ya shigo falon da sallama, kan kujerar dake kallo na ya zauna yana murmushi yace

"Ranki ya daɗe an tashi kenan". Kallon sa nayi ba yabo ba fallasa na gaishe shi. Surutu ya fara mun ina bin sa da eh da aa har na ƙare cin abincin na yunƙura zan maida kwanon kitchen ya karɓa se gashi ya dawo harda ruwa me sanyi ya ajiye mun.
"Yanzu Hajja ta kira ni kin ji kuma wai taron suna suke so suyi, na zata tun da aka wuce satin ga kuma daga ita har yaron ba wata lafiya ta ishe su ba ai se su haƙura ko?" Ya faɗa yana kallo na. Na gyara kwanciya ta nace
"Eh, dama Fadilan tace mun zatayi taron suna ai, kuma haihuwar fari ai ya kamata tayi dama kuma yawanci in dai C's ne se sati biyu akeyin taro ba ranar kwana bakwai ba"

"Amma dai ƙarawa mutane ɗawainiya ne, baki ga jiya nayi dare ba? Wai fa ɗan iskan mijin nan nata se jiya sannan suka zo da yayyen sa biyu wai bada haƙuri suka kawo wasu shegun kayan su a leda wai na barka. Wlh badan Hajja tace nayi shiru ba niyya nayi nace su tafi da tsiyar su tunda da basu kawo ba ɗin ma babu abin da aka fasa yi mata da ɗan nasu har suna cewa a musu lissafin abin da aka kashe na asibiti zasu biya kamar gaske" ya sake faɗa. Tun da ya fara maganar na zuba masa ido ina kallon sa, so nake nace masa kawo kaya a leda ai ba kansu aka fara ba ƙarewar kayan barka naga har lefe sun kai a leda me yasa dan an musu yanzu abin ze yi musu zafi amma na kasa faɗa saboda nasan ƙarshe ze iya juyawa maganar manufa yace na masa gori ko wani abu se kawai na datse zancen da cewa
"Allah ya rufa asiri kawai".

"Wallahi kawai in na tuna zumunchin da Fadila ta mun shiyasa nake tsaye akan sabgoginta. Yarinyar nan bata ji ƙyashin bani rabon ta na gado nayi sabgogin karatu ba shiyasa ko miliyan nawa zan samu a rayuwa ta nima ba zan ji takaicin kashe mata ba dan ta mun abinda kowa be mun ba cikin yan uwana" Bilal ya sake faɗa, a raina na raya
"Ashe dai kasan me maka" yawan zancen Fadila da irin yanda ya ɗaukaki halaccin da ta masa yasa a kullum nake kyautata masa zaton baze taɓa wofantar dani ko ya manta tawa sadaukarwar a rayuwar sa ba kamar yanda da yawa suke tunanin ze bani kunya.

"Kinga a duniya bayan Hajja, ke da Fadila kune mata biyu da suke da ƙima da daraja a ido na. Har gaban abada ba zan manta hallacin ku ba a kullum kuma ina roƙon Allah daya hore mun abin da zan kamanta muku dan nasan bazan biya ku ba" ya sake faɗa yana matso ni jikin sa. Kaina ya fasu, ban san sanda na fara murmushi ba kamar gaula. Ban taɓa wa Bilal wani abu da fatan ya biya ni wata rana ba. Komai ina masa ne saboda son sa da nakeyi tsakani da Allah amma bazanyi ƙarya ba ina jin matuƙar daɗi a duk sanda ya nuna mun jin daɗin sa kan wani abu da nake masa irin wannan tunasarwar kuma tana sakawa na cire kokonton dake damun zuciya ta na Bilal ya canza daga bigiren dana san shi saboda sababbin ɗabi'un da yake gwada mun a yanzu.

Tuni na watsar da ƙudurin motsa kambu na nuna masa ɓacin raina akan rikicin gangan ɗin da yake mun na biye masa muka shiga filin baje kolin ƙauna. Bayan la'asar ina kwance a falo zazzaɓi na namen dawo mun, Bilal ya shigo daga masallaci gani na a kwance yace
"Ya haka kuma ke da nace ki shirya da an idar da sallah zamu tafi?"

Na yunƙura na zauna ina dafe kaina dake sara mun nace
"Gaskiya ba yau ba, jiya fa cewa Mama nayi bani da lafiya shiyasa muka fasa zuwa kaga ma ƙaryar da nayi ciwon gaske na neman kwantar dani". Zama yayi a gefe na ya ɗora hannun sa a wuya na yace
"Jikin ki yayi zafi, dubaki Anty Labiba tazo yi jiya kenan? Dama nayi mamakin ganin ta haka kawai ita da tun da mukayi aure bata taɓa zuwa ba"

"Allah ne be kawo dalilin zuwan bane ba" na faɗa ina gyara zamana. Ya ɗan ɓata fuska yace
"Ba wani nan nine bata so kika aura ba shiyasa ba zata zo gida na ba" se nayi saurin katse shi da cewa
"Kaima da kake hanani zuwa gidan ta saboda baka son ta ne kenan?"

Ya mun kallo me kama da harara kafin yace
"Ya zanyi nace bana son ƙanwar mahaifiyar ki? Kawai bana jin daɗin yanda bata mun kara ƙarara take nuna bata ra'ayin kasancewar mu tare tun ina neman auren ki. Sannan nasan har yanzu bata yada makamanta ba, zuga ki zata cigaba dayi idan kika je gidan".

"Lallai Bilal, ita kuma Anty Labiba saboda bata da abinyi se ta zauna tana zugani. To ta zugani na kashe aure na ko me? Ribar me zata ci?"
"Ita kuwa zata ci riba tun da wannan soloɓiyon ƙanin mijin nata na sonki kinga burin ta se ya cika ki aure shi" ya faɗa yana wani zare ido. Kallon sa kawai nayi na koma na kwanta dan maganar ta fara hawar mun kai. Beyi shiru ba yaci gaba da cewa
"Yanzu Allah kaɗai yasan me zata je ta faɗa jiya, tun da na gaishe ta naga bata amsa ba nasan ta ƙudurce wani abun ne a ranta". Jin na masa banza ban tanka yasa ya miƙe yana cewa
"Ni bari na tafi toh dan na kira Nasir nace ya shirya ze raka ni mu gaida su Mama zuwa gobe idan kinga zaki iya daga gidan sunan se kije".

Ban amsa ba na da naji shiru ma na zata ya fita duk da banji motsin buɗe ƙofa ba,
"Halims" ya kira ni, na juya ba tare da na amsa ba. Irin kallon daya yaudare ni dashi nayi kaca kaca a ƙaunar sa ya watso mun kafin ya tsugunna gaba na ya ruƙo hannu na yace
"In nemi wata alfarma mana"
"Ta me?" Na faɗa a ƙasan maƙoshi saboda kallon da yake mun duk yasa naji wani iri se yace
"Kin san rigimar Hajja, wai dubu hamsin take nema a hannu na daga yanzu zuwa dare ni kuma wlh account ɗina kaf babu dubu ashirin ma balle ashirin. Gurin Nasir kaɗai nake iya zuwa rancen kuɗi shima kuma cikin buƙatar su yake. Nace mata bani da kuɗi amma bata yarda ba har tana cewa wai bayarwa ne kawai bazanyi ba bata ko dubi kuɗin dana kashe na aikin Fadila ba amma dan nace bani da dubu ashirin take nema tayi fushi"ya ƙarasa kamar zeyi kuka dan har idon sa ya canza.

Har raina naji tausayin sa, na karanci halin Hajjan su maganar Allah mace ce me son abin duniya kuma bata da uzuri akan babu tafi so a duk sanda a buƙaci abu kawai ayi kusan yana daga abun da yasa nake ɗagawa Bilal ƙafa dan nasan yana da nauyin daya fi samun sa akansa.
"Ki agaza mun ki samo mun aron dubu hamsin zuwa ƙarshen wata ayi albashi, akwai ma kuɗin da na rantawa Abubakar satin da za'a shiga ze fitar da kajin sa idan ya bani se ki mayar musu" ya sake faɗa yana matsa hannu na. Kallon sa nayi nace
"Ni yanzu a gurin wa zan ranto maka kuɗi?"
"Haba Halims mutane da yawa mana ga yan uwanki ga ƙawayen ki ko gurin Hansa'u ai ba zaki rasa" se na harare shi nace

"Kuma kawai se na tafi cikin yan uwana ko ƙawaye neman rancen kuɗi kaga ma se a samu nayi dani ace wahala nake sha a gidan ka har na fara yawon neman rance". Se yayi shiru kamar me nazari kafin yace
"Kuma haka ne. Wlh kaina ya kulle sam na rasa mafita shi yasa ma wannan tunanin be zo mun ba. Ni kaina akwai gurin waɗan da idan na tambaya zan samu amma kin san bana son raini ba kowa ne ze fahimci buƙatar matsuwa ta saka ka neman taimako ba se a samu abin gulmar ka a unguwa. Barshi kawai bari naje na bata abin da nake dashi idan yaso su Yaya Amina sa cika mata sauran tun da dama su suka ƙirƙiro bidi'ar yin sunan ba wani ba" ya ƙarasa yana miƙewa tsaye.

Kamar wani maraya ya fara tafiya yana waige na, na koma na kwanta ina danne zuciya ta kar tausayin sa yayi tasiri ya sakani yin abinda banyi niyya na amma ina na kasa. Har ya kai bakin ƙofa na tashi zaune na kira sunan sa, tsayawa yayi. Na yamutsa fuska. Dubu goman da Abba ya bayar aka kawo mun sa wadda Uncle Saleh ya bani jiya har ga Allah na gama lissafin me zanyi dasu wasu kayan jarirai irin na turkey Hansa'u ta turo mun har na zaɓi waɗanda nake ao jira nakeyi na fita na samu wanda zan bawa kuɗin ya tura mun a account na aika mata ga wata lalukar ta faɗo musu dukda a zahiri abin be shafe ni ba amma bazan so ran miji na ya ɓaci akan abin da nake da halin fitar dashi ba. Ba dai zan tambayi kowa ba amma zan masa komai da abinda nake dashi.

Ina dafe kai na shiga ɗaki na fito da rafar sababbin yan ɗari da yan hamsin biyu na haɗa na miƙa masa, karɓa yayi yana kallo na da sigar neman ƙarin baya ni. Na yamutsa fuska nace
"Jiya Abba ya aiko mun da barka da sallah wannan kuma Uncle Saleh ne ya bani, kayi maneji dasu dan gaskiya ni babu wanda zan iya tambaya wasu kuɗi yanzu"

"Allah sarki My Halims da kin barsu ma kawai zanje nace mata ban samu ba faɗa ne kawai zata tayi amma dole ta haƙura tun da dai bazanyi sata na basu ba" ya faɗa yana dawo mun da kuɗin. Ban karɓa ba na juya na zauna ina cewa
"Ka taho mun da mangwaro ko guava idan zaka dawo"
"Allah ya maida miki da dubun su Halims, bari naje ba daɗewa ma zanyi ba zan dawo naji ba'asin wannan ƙyallin goshin da faɗin kwankwason da kika ƙara kwana biyu. Yana yinki dai kamar akwai wani abu da kike ɓoye mun" ya faɗa yana kashe mun ido ɗaya. Murmushi nayi tare da zamewa na kwanta ina ɗaga masa hannu. Yana fita bacci ya kwashe ni ban farka ba kuma se da aka fara kiraye kirayen sallar magriba. A kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login