Showing 243001 words to 246000 words out of 257873 words

Chapter 82 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

514

ji ban kuma san dalilin haka ba.

Ban sani ba ko kulawar da yake bani ce ta saka zuciyata ƙoƙarin kware masa, yanda yake mun idan yana tareda ni yana sakani ina jina tamkar sarauniya, abu ɗaya ne cikas ɗin, baya mun kalaman soyayya irin waɗanda kunnuwana suke da muradin sauraro, amma dukda hakan zan gwada.

HAJJA.

Cikin yanayin damuwa ta kalli su Anty Amina tace
"Kunji wai bata da lambar sai dai a tambayi Nasir"

"Toh ki kira Nasir ɗin aji, ni bari na wuce duk yanda zake ciki sai muyi waya" Amina ta sake faɗa tana miƙewa daga haka tayi musu sallama Anty Habiba ma ta miƙe suka bar Hajjan ita kaɗai.

Abubakar ta kira tace ya kirawo mata Nasir ɗin a waya,
"Kana kallo duk sunyi tafiyarsu kamar ma halin da ɗanuwanku yake ciki bai damesu ba" ta faɗawa Abubakar. Yana danna waya ya ce mata

"Toh Hajja me kike so suyi? Shi fa ya jefa kansa a koma menene idan sun zauna mai hakan zai canza?"

"Amma ai sa ɗebe mun kewa su kwantar mun da hankali ko?" Ta sake faɗa, ya miƙa mata waya ganin Nasir ya amsa kiran ya fice ba tareda ya sake cewa komai ba. Nasir ɗin ma kamar Halima ce mata yayi ya kwana biyu rabonsa da Bilal yana ta kiran layukansa kuma baya samu sai da yaje can gidan matarsa tace ai yayi tafiya. Ya ce mata

"Na san dai kin san mai yake faruwa Hajja, ki faɗa masa duk ma inda ya tafi ya dawo dan wannan ba mafita bace gara yazo kawai ayi abunda za'ayi asiri ya rufu".

"Wai har dubu nawa ne kuɗin da zai saka ya gudu?" Hajja ta tambayi Abubakar bayan data gama wayar, ya watsa hannu kafin ya ce
"Ni ban sani ba Hajja idan ya dawo sai ki tambayeshi"

"Ai shikenan" Hajjan ta faɗa kamar abar tausayi, har ya miƙe sai kuma ya koma ya zauna ganin tayi tagumi lokaci ɗaya fuskarta harta wani rame damuwa ta cikata.

WASHE GARI
HALIMA
Ƙarar waya ta ce ta tayar dani daga baccin da ban jima da komawa ba dan tun asuba bayan na idar da sallah Dr Salman ya kirani bai kuma barni ba har sai da aka fara sanarwar jirginsu zai tashi zuwa Abuja wayar sama da awa biyu kunnuwana har ciwo naji suna neman kamawa daga ƙarshe a speaker na sakata na kwanta ina amsa shi da Eh da Aa. Ban jima da komawa baccin ba aka sake kira, na tashi zaune daƙyar, har wani yaji-yaji kaina yake mun, na ɗaga nayi sallama cikin muryar bacci, sai daya amsa sannan na fahimci wanene mai kiran dan banga sunan da kyau ba.

"Na tashe ki daga bacci Anty Halima na ɗauka ai kina gurin aiki ma" ya faɗa, nace
"Yau banida aiki shiyasa" daga haka muka gaisa ya ɗan yi jimm kafin ya ce

"Jiya Hajja ta kiraki ko?"
"Eh ta kira tana tambayar ko ina da wata number Abbansu Al'amin" na bashi amsa, ya sakeyin shiru kafin ya ce

"Na san ko ba zai kira kowa ba zai kiraki ta yuwu ma ya faɗa miki in da yake, dan Allah ki bani number da ake samunsa Anty Halima idan kuma ba haka ba nazo ki kirashi sai ki haɗa mu a wayarki"

"Ni bamuyi magana dashi ba amma akwai wata number sa da nake tunanin zaka iya samunsa a ita bari na tura maka". Sallama mukayi na aika masa da number kafin na kashe wayata na koma bacci.

Abubakar kuwa tana tura masa number ya dannawa Bilal kira, sau uku ya kira bai amsa ba sai ya tura masa message cewar Hajja tana kwance a Asibiti kuma tace a kirawo mata shi dan jikin yayi tsanani ya zo idan ba yana so ya mutu da nadamar ƙin zuwan ba.

Yana turawa ya kashe wayarsa ya tafi uzurinsa, ya sani Bilal ɗin yana girmama lamarin Hajja da wahala kuma ya share alhalin an ce tana kwance a gadon Asibiti.

Tunaninsa kuwa ya zama gaskiya dan lokacin daya kirashi yana zaune yana karyawa ne kuma cikin shiri yake dan yana so yaje gurin Yusuf da yake ta kira tun daren jiya baya ɗauka bayan sunyi magana ya gaya masa an sauke kaya ya sauraresu a kowanne lokaci zai iya jin alert tunda sun karɓi details ɗin sa da komai dama, yana ganin kiran Abubakar ya san tabbas Halima ce ta bashi number.

Niyyar kashe wayar yayi gaba ɗaya ganin yana ta kira sai ga saƙonsa ya shigo take kuwa hankalinsa ya tashi ba shiri ya kama hanyar Kano. Yana tafe a hanya yana sake gwada kiran Yusuf ɗin shiru har sannan tana ringing amma ba'a ɗauka, yana guraren Yankaba ya same shi, haƙuri ya bashi wai wayar ce yara suka saka masa a silent bai lura ba sai yanzu daya ɗakkota yaga tarin missed calls yace ya sameshi a office yanzu dan haka ya karya akalar motar daga hanyar asibitin da suke zuwa in da yayi tunanin an kai Hajja zuwa gurin Yusuf ɗin.

Ji ya ringayi kamar ana jijjigashi tsakanin sama da ƙasa, dukda sanyin Ac daya cika office ɗin amma zufa ta shiga keto masa ya ringa kallon Yusuf ɗin yana sake kallon Tablet ɗin daya kunna masa video.

"Kayi haƙuri Alhaji Bilal, shiyasa na ringa maka magana akan ka rage yawan kuɗin nan amma kaƙi ji, yanzu ka shiga harkar nan mu mun daɗe da yin wayo a cikinta. Yanda ake samun riba kamar hauka haka idan Allah ya juyo abun asara ta afku nan ma sai kaji kamar zaka haukace amma kuma idan ka tuna a baya Allah ya baka dan ya jarabceka yanzu dole kayi haƙuri. Toh yanzu ma haƙurin zakayi mu kumayi addu'ar Allah ya kawo ninkinsu a gaba, amma gaskiya nafi zargin canza kayan nan sukayi dan irin packing ɗin da akayi da wahala ace wai ruwa ne ya tarar dasu har yayi wannan ɓarnar sai dai idan dama can lalatattun ne" Alhaji Yusuf ya faɗa yana dafa kafaɗarsa.

Cike da ƙarfin hali kawai Bilal yake ɗaga masa kai, gaba ɗaya basu fi buhu goma sha zuwa ashirin bane aka buɗe su lafiya lau sauran komai ya lalace ba ga Zoɓon ba ba cittar ba sun yi funfuna cittar kuwa da yawan buhunhunan har ta siƙe kamar yanda sukace ta zama kamar ƙurar katako.

"Kaga lissafin iya abinda aka samu nan, sai ka sake turawa da Abu Amar details ɗin sai ku ƙarasa magana, yanzu bari naje ana jirana idan kuma yanzu zaka wuce sai mu tafi tare ka saukeni dan ba da mota na fito ba" Alhaji Yusuf ɗin ya sake faɗa, yanda yake magana ba zaka ɗauka da wanda ya tafka asarar Miliyoyin kuɗaɗe yakeyi ba kamar ma ba komai. Da laluben bango Bilal ya fita daga office ɗin, Yusuf ɗin ne yaja motar dan ce masa yayi baya gani sosai ya taimaka ya kaishi gida kawai.

"Haba Alhajin Allah kada ka bada maza mana, ni idan na faɗa maka irin ibtila'in daya ringa saukar mun bi da bi sai kayi mamaki amma dana mayar da komai gurin Allah ba gashi ya wuce ba? Ita rayuwa dama akwai samu akwai rashi ai, kuma sau tari jarabta tana zama matakin nasara idan kayi haƙuri sai kaga Allah ya maido maka da dubunsu" Alhaji Yusuf ɗin ya faɗa Bilal sai jin sa kawai yakeyi ba dan yana gane komai ba.

Har ƙofar gida ya kaishi kafin ya masa sallama ya wuce yana sake jaddada masa kada fa ya sakawa kansa damuwar da zata haifar masa da wata rashin lafiyar yayi biyu babu, dukiya dai ta tafi ba dawowa zatayi ba, a waya ya shiga kiran Zulaiha dan baya jin zai iya fita daga motar da kansa. Ƙirjinsa ya masa nauyi haka kansa sara masa yakeyi sosai tamkar wanda ale kiɗan gangi a cikinsa.

Ya kira Zulaihan yafi sau biyar bata amsa ba daga ƙarshe haka ya lallaɓa baya ko ganin gabansa ya fita daƙyar bai ko kashe motar ba balle ya kulleta ya fita yana bin bango har ya tsaya jikin get ɗin kafin ya shiga bugawa da duka ƙarfin daya rage masa.

ZULAIHA

Tana kwance tana baccin huce gajiyar da Ahlan ya tara mata a haɗuwar da sukayi jiya. Tunda suka fara mu'amala babu wani abu daya taɓa shiga tsakaninsu, zai ɗauketa su fita yawo gari ko suje Hotel amma ba abinda yake mata sai dai suyi hira duk shaye-shayen da yake ƙoƙarin koya mata sai jiyan tukunna ta kasa riƙe kanta dan tunda Bilal ɗin ya tafi ita kaɗai ta san a halin da take ko da ba wani samun yanda take so takeyi sosai a gurin nasa ba amma yafi babu, yanzun da baya nan ga hirarraki da wasannin banzan da sukeyi da Ahlan ɗin kullum idan ta koma gida har kuka takeyi kafin ta samu tayi bacci, jiyan ji tayi kamar ya zuba mata wani abu a lemon da suka sha dan sai bayan komai ya lafa kuma ta shiga jin haushin kanta haɗi da nadamar abinda ya faru ƙarshe bata ko jira shi ba ta hawo Adaidaita sahu ta koma gida.

Tun bayan tafiyar Bilal ta samu free get, gari na wayewa zata yi wanka ta fice sai dare zata dawo, hankalinta kwance take al'amuranta. Ɗaki Ahlan ɗin ya kama musu ko bai kirata ba zata tafi tayi kwanciyarta ta wuni a can irin yanda ta saba a lokacin da take gida sau da yawa zata fita da sunan makaranta amma hotel zata wuce can zata wuni sai magriba ta koma gida abunta.

Duk yawon makarantar data ringayi asar kuɗi kawai ta ringa yiwa Bilal amma ba karatun takeyi ba, canjin department ɗin ta na uku kenan yanzu ita daya kamata ace tayi graduation kamar yanda Bilal ɗin yake zato amma maganar gaskiya 200L take shima da taimakon wani saurayinta da yake HOD a wani department shi ya shiga ya fita idan ba dan haka da tuni an koreta tareda su Suwaiba. Toh yanzun ma dai bata da banbanci da korarriyar dan tuni semester tayi nisa har ana shirin fara exams amma bata san ta yanda zata fara sanarwa da Bilal ɗin zata koma makatanta ba.

Ƙarar bugun da yakeyi tamkar zai ɓalle ƙofar ya farkar da ita, a gigice ta rarumi zani ta ɗaura ta fita tana murza ido, sai data tareshi ganin yana shirin faɗowa. Jiki na rawa ta kamashi suka shiga ciki ya zube akan carpet yana sauke numfashi kamar mai cutar Asthma. Yanayin da yake ciki ya saka ta wartsake babu shiri ta rarumo wayarta ta shiga kiran layin Hajja.

Hajja na zaune tareda Anty Ladidi tana bata labarin halin da ake ciki, Ladidin tayi tagumi tana cewa
"Tun jiya Yaya Habiba ta kirani ai ta gaya mun harda yanda suka tarar da Fadila itama. Ashe ɗan abu ta kazan uba mijin nata mayaudari ne, ya zo ya yiwa mutane lamɓo an bashi yarinya yaje yana gana mata azaba kamar wanda dama yayi auren ɗaukar fansa? Ai nace mai yasa suka barota a gidan basu tasota a gaba sun taho ba? Ko sai ya kasheta tukunna sai ya bugo waya yace azo a ɗauki gawarta ko me?"

Cike da mamaki Hajja ta ce
"Wace Fadilar kike magana akai?"
"Auta mana ko muna da wata Fadilar ne bayan ita?" Ladidin ta bata amsa, kafin ta sake magana wayarta dake kan cinyarta tana jiran kiran Bilal tunda Abubakar ya gaya mata ya tura masa saƙo ta shiga ringing, ɗagawa tayi kawai ganin number daga can muryar Zulaiha ta cika mata kunne cikin tashin hankali take sanar mata ga Bilal ya zo ita dai bata gane kansa ba gashi nan numfashinsa yana sarƙewa.

Miƙewa Hajjan tayi da sauri kafin kuma ta koma kamar wacce aka ja tayi zaman yan bori, cikin tsananin azabar data ziyarci bayanta zuwa ƙugunta ta saki wayar hannunta tana wayyo Allah dai-dai nan Abubakar ya shigo, ganin yanayin Hajjan bai ko tsaya jin ba'asi ba ya kinkimeta daƙyar, tare suke da Abokinsa Isma'l ya shigo ya gayawa Hajja abokin zai shiga su gaisa kenan dan haka ya sakata a motar Isma'l ɗin suka wuce Asibiti da sauri.

A hanya yake tambayar Anty Ladidi mai ya faru tace masa bata sani ba an dai kirata a waya ne ta miƙe tsaye kuma ta koma ta zauna gashi sun baro wayar a gida balle subi ba'asin kiran ko na menene?

Aminu Kano suka kaita sun ci sa'a babu ɓata lokaci aka karɓeta emergency, a ransa ya ringa jin babu daɗi, ƙaryar da yayi saboda Bilal ya zo gashi Allah ya tabbatar da abun. Layin Bilal ɗin ya shiga kira cikin sa'a Zulaiha dake ta sake gwada layin Hajja taji ƙarar waya a jikinsa ta zaroshi ganin Brother ya saka ta ɗaga da sauri kafin ma yayi magana ta shiga karanto masa halin da ake ciki.

Salati ya shiga yi jin wata sabuwa kuma take kuma ya fahimci dalilin faɗuwar Hajjan, ya balbaleta da masifa yana cewa
"Ke mahaukaciyar ina ce da zaki kirata? Mai yasa baki nemi wani daga cikinmu ba?"

"Da Allah Malam dakata mun, ina da number ku ne ko ya aka soma? Toh ban kira ɗin ba idan kaga dama ka tsaya masifa kada Allah ya sa kazo ka taimaka masa" ta bashi amsa haɗi da yin tsaki kafin ta kashe wayar.

Tashi tayi ta wuce ɗaki ta sako doguwar riga kafin ta fita waje ta nemo wanda zasu kama matashi kawai ta kaishi Asibitin, ta manta da mota shiyasa ma har ta tsaya neman taimako zai zo yana nema ya faɗa mata magana.

Mamaki ya kamata ganin babu mota a ƙofar gidan, amma kuma data tuna a yanayin daya shigo sai mamakin ya gushe tunda dai ba zai iya tuƙi a hakan ba ta yuwu wani ne ya kawo shi. Ganin motar Alhaji Zakariyya mai gidan dake jikinsu tana tahowa ta shiga ɗaga masa hannu, bayan ya tsaya ta faɗa masa abinda yake faruwa, shi ya kira masu gadin kan layin suka shiga suka ɗakko Bilal ɗin suka sakashi a mota kamar matacce kafin ta shiga suka wuce Asibiti.

Wani private Asibiti ya kaisu dukda ta gaya amsa Aminu Kano suke zuwa amma yace gara aje mafi kusa, idan yanayinsa ya dai-daita ya fita daga hatsari sai a mayar dashi ko ma inane. Suna tare da Alhaji Zakariyyan yana ta kwantar mata da hankali Bilal kuma yana ciki tareda likitoci har sanda Abubakar da ɗaya daga cikin masu gadin ya gayawa Asibitin da Alhaji Zakariyyan yace zasuje ya isa. Ya ballawa Zulaiha harara kafin ko ya ɗauke ido itama ta maka masa tata, yayi ƙwafa ya wuce suka gaisa da Alhajin yana amsa godiya sai lokacin ya wuce bayan ya musu fatan Allah ya bashi lafiya.

Ba jimawa Likita ya fito, Zulaiha ta tashi d sauri haka Abubakar ya kallesu yana cewa
"Kune yan uwan mara lafiyar da aka kawo ɗazu?"

"Eh ni matarsa ce" ta bashi amsa da sauri Abubakar ya sake hararta kafin ya ce
"Ya jikin ɗan uwana likita? Mai ya same shi dan Allah?"

Office yace su bishi, a taƙaice yayi musu bayanin jinin Bilal ɗin ne yayi mugun hawa sakamakon wata damuwa ko tashin hankali daya fuskata a bazata.
"Mun bashi duk wani taimako da yake buƙata a yanzu ya kuma samu bacci zamu jira zuwa ya farka kafin kuma mu san mataki na gaba" Likitan ya faɗa. Godiya suka masa suka fita Abubakar ya wuce gurin biyan kuɗi ya bada abinda aka buƙata. Yana gurin Anty Amina ta sake kiransa dan suna hanyar kai Hajja Asibiti ya kirasu duka ya faɗa musu harda Fadila da ya samu number ta cikin sa'a, suna gama waya da Zulaihan kuma ya sake kira ya sanar musu halin da Bilal ɗin yake ciki, akayi sa'a kuma Anty Amina tana ta gurin Asibitin Malam ɗin dan haka tana zuwa tace ya tafi gurin Bilal ita da Ladidi zasu tsaya da Hajja kafin su Habiba su ƙaraso.

Kira tayi tana sake tambayarsa jikin Bilal ɗin yace musu da sauƙi da kuma abinda aka ce yana damunsa.
"Itama Hajjan sunce jininta ne ya hau" ta faɗa masa, yayi ajiyar numfashi ya ce
"Nayi tunanin haka dama, amma dai babu wani abu bayan wannan ko?" Ya tambayeta. Tace

"Haka muke fata amma dai basu ce komai ba yanzu sun ce sai ta farka an gani"

"Shikenan, bari na tambaya nan ɗin naji idan zai yuwu mu ɗauke shi kawai a dawo dashi nan ɗin dan nan Asibitin bai yi mun ba gaskiya" Daga haka sukayi sallama.

Gurin likitan ya koma ya faɗa masa buƙatar sa sai likitan yace suyi haƙuri dai zuwa ya farka idan ma zasu kaishi wani gurin.

"Ka raina kulawarmu kenan Alhaji" Likitan ya faɗa yana murmushi, Abubakar ya ce
"Ba haka bane, mahaifiyarmu ce itama babu lafiya tana can AKTH ɗin, idan aka haɗe su guri guda hankalinmu zai fi nutsuwa guri ɗaya shine dalili"

"Haka ne gaskiya, Allah ya bata lafiya babu damuwa kuma da zarar naga yanayin jikin nasa yayi yanda za'a iya motsashi zuwa wani guri sai ayi hakan" cewar Likitan.

Zulaiha ya bari ya koma can gurinsu Hajja, itama ya tarar tana bacci. Su Anty Habiba harda wasu daga cikin yan uwan Hajjan suna gurin Fadila ce kaɗai babu suka wuce gida tareda Anty Amina ta ɗebowa Hajjan abubuwan da zata buƙata daga can suka biya gurin Bilal suka tarar da yan uwan Zulaihan Ummanta da ƙanwar Umman Anty Habi sai Nuratu da Mijinta. Har sannan bai farka ba. A nan ya bar Anty Amina ya wuce ya kai kayan Hajjan, haka sukayi ta jigila tsakanin Asibitoci biyu har dare kafin yan dubiya suka wuce gidajensu sai masu jinya aka bari.

Abinda ya saka ya ɗan da sakewa Zulaiha fuska jin tace zata kwana da Bilal ɗin daya ce ta wuce gida shi zai zauna tace Aa har kaya ma taje ta ɗakko shima ta haɗo masa abinda zai iya buƙata idan ya farka. Sai lokacin ya tambayeta motar Bilal ɗin fa? Tace masa ita dai data fita nemo wanda zasu taimaka mata bata ganta a wajen ba.

Washe gari da Asuba Bilal ya farka gaba ɗaya dan ya farka da yammacin jiyan amma suka sake mayar dashi bacci saboda jinin bai sauka yanda suke buƙata ba. Jikin yayi kyau sosai dan da kansa ya tashi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login