Showing 21001 words to 24000 words out of 257873 words
can tace
"Dukan ki nayi ko zagin ki Halima da zaki saka mun kuka?"
"Ya yake so nayi Anty? Me zanyi Bilal ya gane irin son da nake masa?" Na faɗa cikin matsanan cin kukan dake fitowa tun daga ƙasan raina. Na yarda son Bilal jarabawa tace babu kuma wanda ze fahimci yanda nake ji har shi kansa kuwa. Kamar zata share ni ta wuce se kuma ta zagayo ya zauna gefe na tare da jana jikin ta nan kuwa na sake samun sararin yin kuka yanda nake so. Cikin tausasawa ta shiga yi mun magana tana cewa
"Halima har se ya buɗe baki yace baze aure ki ba kafin ki fahimci kurman baƙin da yake miki? Halima ko a littafin hausa kin taɓa jin labarin neman aure irin naki? Aure fa za a yi na yar mutum ba wai yar tsana ba amma ace ƙasa da wata ɗaya ba ango ba dangin sa ba babu wani ɓangare da suka nuna murna ko zumuɗin su akan abin da ze faru a ina kika taɓa ganin an yi haka?
Ki ture duk wasu al'adu ace ba dole bane basu yi ba amma Halima muhalli yana cikin sharuɗan da se sun samu kafin aure ya ƙullu, a ina ze ajiye ki? Ko kuwa dama lasisi yake nema a gidan ku zaki ci gaba da zama bayan an ɗaura muku auren ko yaya? Yau idan haya ze kama biki ƙasa da sati uku yaci ace ya samu har ya nuna guri an san me za a saka miki. Kwana nawa ina miki magana akan ki tuntuɓe shi? Yanzu da na masa magana da kaina gashi ya nuna miki zahirin da kika kasa ganewa ko kuma da be fito miki a mutum ba ba auren ki yaron nan ze yi ba ki godewa Allah da be samu galabar lalata miki rayuwa ba ki haƙura ki barwa Allah zaɓi Halima".
"Bilal yana so na kuma aure na zeyi Anty. Ta yaya za ayi ya turo iyayen sa a saka mana rana har idan ba aure zeyi ba? Kuma zancen gida na gaya miki gini yake be ƙarasa ba ni muna magana ya kuma tabbatar mun kafin ranar biki ze gama komai gajen haƙuri kawai kika yi kika masa magana gashi yanzu kin saka ransa ya ɓaci, yaƙi ya zo a waya ma sau ɗaya yake kira na kuma bata ko bari muyi doguwar magana ze kashe idan ma har ya ce ya fasa ɗin ai ke ce kika jawo ba wai a karan kansa yayi ra'ayi ba" na faɗa cikin kuka. Yanda tayi shiru tana kallo na ta tabbatar neman hanya mafi sauƙi da zata huce takaici ma takeyi ta rasa, se na miƙe ina cewa
"Ni gidan mu kawai zan tafi, dama ai so kike yi ya fasa aure na shiyasa idan ba haka ba ai ina ji har Mama se da tace ki rabu damu ai ni ce zan aure shi tun da naji na gani kowa nasa ido ne" na wuce ɗakin da nake ina ci gaba da kuka haɗi da zazzaga mata rashin kunya. Kaya na na shiga haɗa wa a akwati waya ta dake jikin caji tayi ƙara jin ringing ɗin Bilal yasa na saki kayan hannu na na wuce gurin wayar da sauri na ɗaga.
Kamar ko da yaushe a kwanakin nan muryarsa cikin sanyi ya amsa gaisuwar da nayi masa kafin yace
"Amm kina wani abu ne Halima?"
"Ba abinda nake yi, wani abu kake buƙata nayi maka? Ko abinci kake so?" Na faɗa cikin zaƙuwa. Ina jin sa ya sauke ajiyar zuciya kafin yace
"Ina so na ganki ne, akwai maganar da nake so mu tattauna me muhimmanci idan babu damuwa"
"Wace irin damuwa kuma? Yanzu zaka zo ko se da daddare?" Na amsa shi, se yayi ɗan jimm kafin yace
"Ke zaki zo ki same ni idan zaki iya amma". Shiru nayi na kusan minti ɗaya ina juya maganar a raina, abin da Anty Labiba ta faɗa mun yanzu akan na godewa Allah da be lalata mun rayuwa ba ya faɗo mun a rai se nayi saurin korar maganar daga raina ina bawa kaina tabbacin Bilal ba ze taɓa yaudara ta ba ba kuma wannan niyyar ta kawo shi guri na ba.
"Karki takura kanki idan ba zaki iya ba babu damuwa dama magana ce akan abinda ya shafe mu mu biyu da nake ganin ya kamata mu tattauna amma zamu iya barin ta kawai idan baki da lokaci" ya katse mun shirun da nayi. Ban san sanda harshe na ya furta
"A ina zan zo na same ka toh?"
"Ina shagon Sani" ya bani amsa. Se na sauke ajiyar zuciya jin ba wani guri daban ya ce na same shi ba har na tsinewa shaiɗan ɗin daya fara kawo mun wasi wasi akan Bilal ɗin. Aje wayar nayi na shiga toilet da sauri na canza pad ɗin jiki na tare da wanke fuskata na fito na canza kaya. Dogon Hijab na saka da niƙab saboda munafukan unguwan mu. Dana fito ban tarar da Anty Labiba a falo ba se Amir ne ya tare ni yana tambayata me ya samu Momy ya shiga ɗakin ta ya tarar da ita tana kuka nace masa ban sani ba sauri nakeyi kuma ana jira na ne yaje ya bata haƙuri.
A bayan gidan mu Chemist ɗin Abokin sa Sani yake, haka na ringa gyara niƙab ɗin fuskata harda canza tafiya dan kar a gane ni ce, na tarar da shi da Bilal zaune suna hira. Kallo ɗaya na masa na hango ramar da yayi idanunsa sun sake fitowa haka dogon hancin sa ya ƙara tsayi hatta da lips ɗin sa se naga sun bushe sun ƙara jaa alamar yana cikin damuwa ko bashi da lafiya. A taƙaice muka gaisa da Sani kafin ya fita ya bamu guri. Na sauke kaina ƙasa saboda yanda Bilal ya kafe ni da nasa idon da nake jin sun ƙara kaifi yau, sama da minti biyar muna zaune kafin a hankali ya fara magana yace
"Kiyi haƙuri Halims be kamata ace na ɗauki fushi akan abin da ya faru ba. Bayan na dawo gida na nutsu na gane kun fini gaskiya se dai ina cikin wani yanayi da ni kaɗai na san wane hali nake ciki duk kuma wanda zan yiwa bayani be zama lallai ya fuskan ce ni ba". Kallon sa nayi jin yayi shiru se yayi murmushi ya ci gaba da cewa
"Tun farko shiyasa ban so aka saka bikin nan wata shida ba kuma kema na gaya miki, dalilin da ya saka bana ɓoye miki komai da nake ciki kenan Halims saboya tunani na duk abin da ya taso za kiyi mun uzuri" se na ɗaga kai na kalle shi yayi saurin cewa
"Ban ce baki mun ba, wlh na sani kin yi ƙoƙari. Kin mun abin da ba kowacce mace ba kuma na yaba and i will for ever be grateful for that Halima. Ke ɗin kin nunawa duniya true love still exist, se dai har yanzu ban kai ba Halima. Nayi tunanin a wata shidan nan zan iya yin ƙoƙarin ganin ban baki kunya ba amma se yanzu na fahimci wautar da nayi gashi kuma lokaci ya ƙure mun balle na juya da baya".
Gaba na ya yanke ya faɗi baki ja har yana rawa na kalle shi nace
"Ban gane ba, what are you trying to tell me Bilal what do you mean by lokaci ya ƙure balle ka juya baya?"
"Relax Halima ba wani abu nake nufi ba" ya faɗa yana kama hannu na, se na fizge ina kallon sa se dai na kasa ci gaba da magana saboda yanda zuciya ta take wani irin bugu kamar zata huda ƙirjina ta fito. Wayar sa ya ciro daga aljihun sa yayi danne danne kafin ya miƙa mun, hannuna na rawa na karɓa na kalli screen ɗin. Video gidan daya kai ni a matsayin nasa wanda zamu zauna a ciki ne yake playing, seda na kalla daga farko har ƙarshe kafin na kalle shi muka haɗa ido dan shima ni yake kallo se ya karɓi wayar ya mayar da ita aljihunsa kafin ya haɗe hannu biyu ya dafe haɓarsa ya furzar da iska daga bakin sa kafin yace
"Bayan da aka saka ranar auren mu munyi magana da Baba Liman ya kuma kira gidan su yaron da ze auri Fadila akan suyi haƙuri a ƙara ranar auren su zuwa wata goma amma suka ƙi yarda akan in dai ba wata shidan da suka yanke ba se dai a mayar musu da kuɗin su kawai ya haƙura ya fasa auren ta. Na gaya miki Halima ni zan yi mata komai na aure, babu abin da baki sani ba a kaina tun da mahaifin mu ya rasu duk wata ragama ta yan ɗakin mu ta dawo kaina. Yayyenmu tun da muka samu saɓani dasu lokacin rabon gado shike nan suka zare hannun su daga komai daya shafe mu ko sanda nace babu damuwa a bar zancen auren mu a wata shidan na ɗauka su Yaya Alhaji ze yiwa Fadila kayan ɗaki ne se da kuma biki ya taho da Hajja tayi musu magana suka ce ai an raba gado an bawa kowa nasa dan haka ba abin da zasu mana.."
"Bilal ka faɗa mun kai tsaye me kake nufi ko me kake so ayi yanzu dan Allah tun baka janyo zuciya ta ta buga ba" na katse dogon sharhin daya ɗakko wanda babu abin da nake fahimta a ciki. Shiru yayi ina kallon yan da abin wuyan sa ke sama da ƙasa alamar magana na cikin sa ya kasa furtata kafin ya sake riƙe hannaye na biyu duk yanda naso na ƙwace be bani dama ba haka ya kafe idon sa cikin nawa yana murza zoben dake hannu na yace
"Ina son ki Halima bana fatan na rasa ki amma a yanzu bani da halin auren ki".
"Dagaske Bilal dama yaudara ta kake yi ba aure na zaka yi ba?" Na faɗa cikin karyewar sauti. Se ya ƙara ƙarfin ruƙon da yayiwa hannaye na yace
"Allah shine shaida ina son ki Halima dai dai da rana ɗaya ban taɓa niyyar yaudarar ki ba"
"Amma da bakin ka yanzu kace ba zaka iya aure na ba, me yasa tun farko baka faɗa mun ba se da ka bari auren mu ya rage sati biyu?" Na faɗa ina fashe wa da kuka.
"Nayi zaton zan iya Halima, na ɗauka zan samu yanda nake so kafin lokacin amma hakan yaci tura. Ta yaya kike zaton iyayenki zasu bani ke bayan ba ni da ko muhallin da zan ajiye ki?" Ya faɗa tamkar shi ma ze fashe da kukan. Kamar zan shiɗe nace
"Shi kuma wannan gidan fa? Ko dama ba naka bane ƙarya kayi mun kace na ka ne?"
"Gida na ne Halima amma wannan shi da kango ai basu da maraba ta yaya mutum ze shiga ya zauna a gurin da ko daɓe babu? Ki aje maganar wannan gidan a gefe kawai dan dashi da babu banbancin su kaɗan ne. Da ace ina da sararin da zan kama miki haya ma da wlh bazan damu ba amam bani dashi, a yanzu bani da wasu kuɗi a tare dani se wanda za a siyawa Fadila kujera su kansu basu gama haɗuwa ba dama sadakin ta ne na cika kuma na ranci wani abu ciki dashi na ƙarasa aikin fulasta ai kin gani sanda muka je iya waje ne da fulasta ba ayi a waje ba ko? Zaɓi biyu ne kaɗai ya rage mana Halima, ko dai a ɗaga auren mu wanda bana zaton iyayenki zasu amince tun da har sun ambata dama akwai wanda suke so su haɗa ki dashi a familyn ku kenan se dai na haƙura dake tun da bani da halin auren ki shikenan rayuwa ta tazo ƙarshe ban san wace alƙibla zan kalla ba idan babu ke a tare da ni".
[5/18, 13:09] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 7*
Page 7
Na fi minti goma tsaye a ƙofar gidan mu ni ban shiga ba kuma ban bar gurin ba. Maganganun da mu kayi da Bilal ne suke mun amsa kuwwa a kunnuwa na da ƙwaƙwalwata bana kin ko wanne sauti dake zagaye dani banda muryar sa.
"Ba ni da kuɗin da zan ƙarasa gini Halima, ba kuma ni da sararin da zan kama haya a yanzu. Abu biyu ya rage, ko dai iyayen ki su ɗaga auren mu ko kuma mu haƙura gaba ɗaya, ƙila a gaba idan muna da rabon kasancewa tare se muyi aure. Ina son ki Halima amma bani da halin mallakar ki a yanzu" kalaman ƙarshe daya gaya mun kenan. Bana ko gani sosai na shiga bubbuga ƙofa, se da na buga sau uku kafin aka buɗe. Musa ne, jikan Goggo Habi Ƙanwar Mahaifin Mamanmu. Ɗan ta ɗaya Baba Sulaiman kuma shine mahaifin Musan accident suka yi dashi da matar sa duk suka rasu. A Birnin gwari take da zama dama naji Anty Labiba tana faɗar tace tun biki na saura sati biyu zata zo ashe har ta zo ɗin kuwa.
Kallo na ya tsaya yi saboda niƙab ɗin dake fuska na raɓe shi na wuce ina haɗa hanya, motar Abba da na gani a ajiye yasa na gane yana gida dan haka kai tsaye na wuce falon sa. Tare da Aminin sa Baba Hashim na same su suna magana daga kuma yana yin fuskokin su na fahimci ko ma me suke tattauna ba magana me daɗi bace. A tare suka amsa sallama ta suna kallo na, ka ƙarasa gaban Abba, tamkar wadda tazo isar da saƙon rasuwa haka na fashe da kuka irin me gigitar nan har jiki na yana jijjiga. Abba ya miƙe hankali tashe ya ruƙo ni yana cewa
"Lafiya Halima? Me ya samu su Labibar?" Haka Baba Hashimu ma cikin kaɗuwa suka ringa tambaya ta me nene amma na ƙi cewa komai har se da nayi kuka iya kar yi na se da naga Baba Hashimu ya nufi ƙofa yana cewa
"Bari na kira Amina" se lokacin na buɗe baki daƙyar nace
"Ba se ka kira ta ba". Se da na sake kwashe kusan minti biyar ina kokawa da kukan dake taho mun da zarar na buɗe baki kafin daƙyar na iya cewa
"Abba Bilal ne"
"Me ya same shi?" Abban ya tambaye ni. Ina kuka tamkar raina ze fita na tsara musu duk yanda mukayi da Bilal da abin da ya gaya mun ban rage komai ba. Su kayi shiru kamar ruwa ya cinye su banda sautin kuka na da ƙarar fanka baka jin komai har kusan minti goma da alama duk su biyun bakin su ya mutu sun rasa abin da zasu faɗa ne. Daƙyar Baba Hashimu ya katse shirun yace mun
"Ki bar kukan haka Halima kiyi shiru muyi magana". Se da na sake shafe wasu mintunan kafin na iya tsagaitawa da kukan, yace
"Zaman nan da muka yi zancen ki muke yi Halima. Mahaifinki ya kira ni yana cike da damuwa akan lamarin auran ki. Yau saura kwana goma sha huɗu amma babu wata magana me ƙarfi daga gidan maza su basu zo akan suna sane da lokaci ba kuma basu ce wani abu dangane da shirun da suka yi ba. Yanzu Alhaji Salahu muke ji yazo mu ji ta bakin sa akan abin da ya kama muyi se kuma gashi kin zo da wannan maganar. Ina ganin ai ba abin kuka da tayar da hankali bane ba, dama kullum cikin yi muku addu'a muke akan Allah ya zaɓa muku mazaje na gari. Irin haka babu daɗi, amma sha'anin aure da ace ayi azo ana dana sani daga baya gara a haƙura se kiga ubangiji ya musanya miki da wanda ya fishi zama alkhairi a gare ki".
Kukan dana sake fashewa dashi se ka rantse da Allah irin marin nan na shammata ya zabga mun, ko da yake ai gara ya dake ni naji zafin a kan fata ta da ciwon da yake neman haifar wa zuciya ta. Na rabu da Bilal fa yake cewa. Daga shi har Abban Kallo na suka ringa yi cikin mamaki za a ko ace ɗimuwa tamkar dai basu fahimci dalilin sabon kukan dana dasa ba. Ban ji nauyin Baba Hashim ba domin dama Abba babu batun jin kunya tsakani na dashi nace
"Wallahi ina son sa Abba, idan na rasa Bilal ban san ya zanyi da rayuwa ta ba ni dai a nemi wata mafitar amma kar ma a fara cewa in rabu dashi" na haɗe kai na da kujera na ci gaba da rera kuka. Baba Hashim ya ringa salati yana tafa hannu Abba dai yayi shiru ya tallafe haɓar sa da hannu biyu yana kallo na. A haka Baba Salahu ya shigo ya same mu, a taƙaice Baba Hashim ya yi masa bayanin abin da nazo musu dashi yayi shiru kawai yana jimanta abun a ransa yana kallo na, jin kukan nawa bana ƙare bane yasa ya fara magana cikin lallashi yana cewa
"Yi shiru Halimatu kwantar da hankalin ki babu wanda ze raba ku amma ki fara amsa mun tambayar nan tsakani da Allah kar ki mun ƙarya ni kuma zan yi iya ƙoƙari na ganin na samar miki muradin ki". Na tsagaita kukan ina share hawaye haɗi da face maji na da hijabi na, shiry ya ɗan yi cikin jin nauyin maganar da take bakin sa kafin daƙyar ya iya cewa
"Halimatu, kar kiji nauyi ko kunyar mu ki gaya mun tsakanin ki da Allah wani abu na rashin dacewa ya taɓa shiga tsakanin ki da Bilal ne?"
Da sauri Abba ya kalle shi se Baba Hashim ya masa alama da ido akan kar yace komai ni kuwa a yanayin da nake ciki ban ma ji tambayar tasa a