Showing 30001 words to 33000 words out of 257873 words

Chapter 11 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

448

se da lokacin auren ta yayi shi yasa Abba ya kan ce Labiba ce babbar yar sa ba ni ba domin tun tana da shekaru goma a duniya take hannun sa har ya aurar da ita itama kuma kallon uba take masa b wai mijin yayarta ba.

Na gyara kwanciya ta ina sake nutsawa cikin tunanin dana tafi, irin wannan rayuwar nake so na gina, mu sha wahala tare da miji na ta yanda a duk sanda Allah yayi mana arziƙi baze manta halacci na ba. Ban yarda da irin auren da mutanen yanzu suke rububin yi ba na ready made, baki san yanda namiji yasha wahalar sa ya tara abinda yake dashi ba kin ganshi a me wadata kin aura daga ƙarshe ya ringa goranta miki cewa arziƙin sa kika hanga idan kuma me mata ne nan ma se ya fifita matar sa da suka sha wahala tare har a ringa kiran ki da yar tayin cin arziƙi shine abin da ban yarda dashi ba. Matar da aka sha wahala da ita tafi mutunchi tafi ƙima a gurin miki har ma da duk waɗanda suke zagaye dashi, haka ko da ya auro wata daga baya itan ce dai zata zama a sama haka nan yayanta se sun banbanta da wanda uwarsu ta zo rana tsaka.
A mahangar Haliman Bilal ba cewa ta ba.

Daga yana yin da naga gidan mu washe gari na gamsu dagaske an fara shirin biki. Masu aikin kayan zaƙi na gara ne suka fara baje kolin su haka nan yan uwa da ƙawayen Mama sun fara zuwa suna tsara yanda biki ze kasance hatta Goggo Habi da taga babu sarki se Allah ta saki musamman da aka aiko da yamma cewa ranar asabar da zata kama saura sati ɗaya ɗaurin aure za'a kawo lefe na wannan ya wanke mata zuciya tun da dama tace abin da idan ta tuna yake baƙanta mata rai yanda za'a ɗauki santaleliyar budurwa kamata a bayar sadaka ashe da iskanci ne yasa yaƙi yin abin da ya kamata yanzu da yaga ana nema a ƙwace masa goruba daga hannu ai ya motsa a tunanin ta kamar yanda Abba ya gaya mata sun kira waliyyan sa ne sun ce musu sun fasa shine suka bayar da haƙuri akan wani al'amari ne ya janye shirun da sukayi amma yanzu komai ya yaye.

A cikin sati ɗaya aka gama aikin gidan Bilal, gida ya fito yayi kyau masha Allah tamkar na wani hamshaƙin me kuɗi. Ranar alhamis su Anty Labiba suka je suka ga gidan a lokacin ana fenti kowa ya dawo yana santin gida amma saboda rashin tsoron Allah irin nata da dai ba zata taɓa son Bilal ba se cewa tayi ita bata yarda gidan sa bane, idan kuma har yana da halin yin gini irin wannan to kuwa ba ƙaramin rainawa Halima hankali yayi ba. Ni kaina da naga video gidan se da nayi mamakin yanda finishing ya sake fito da ainihin kyau da tsarin gurin, har ƙofofi naga an canza a sanda muka je na ƙarfe ne har so nayi na masa magana akan me ze haka a saka dai na zamani amma na kasa ze gashi an canza saman ma da da yace ceiling ze yi bashi da sararin yin pop yanzu se gashi anyi ga tiles me kama da marbles an malale ko ina haka kitchen yasha cabinet irin yanda nake mafarki.

A maimakon Asabar da suka fara ambata zasu kawo lefe ranar da aka je ganin gida suka bada uzurin se ranar Alhamis me zuwa ranar da zamuyi kamu kenan saboda akwai yan uwan Bilal ɗin da zasu zo daga guri me nisa be kamata a taso su kawo lefe ranar asabar ba kuma ace za'a fara biki ranar alhamis gara kawai a haɗe ayi komai lokaci ɗaya, babu wani abu da muke jira na amfani a cikin lefen dan haka aka ce musu babu komai a cikin satin kuma aka yi mun jere na yar gata. Ɗakuna na biyu na part ɗina da ɗaya na part ɗin Bilal duk se da Abba ya saka mun gado ga kujeru suma saiti biyu. Yanda Anty Labiba ta zage darje ni da kayan kitchen ya bani mamaki ita da tace duk abinda suka siya Amirah da Inayah zasu aje ma, babu ce akwai ba'a saka mun a gida na ba. Saboda tsabar zumuɗi irin na Bilal tun ranar da aka fara jere ya koma kwana a gidan, haka ze ishe ni da tura hotuna da videos, Halims kin ga kaza da aka saka mana? Kin ga gadonki kuwa? Waya mutu waze tashi se da ya zama har bana so ya kira ni saboda gaba ɗaya zancen gida ya kwance masa kai.

Rana bata ƙarya aka ce sedai uwar ɗiya taji kunya, tun ranar talata muka fara shagalin bikin aure na da Bilal wanda aka fara da Ball da abokanan sa suka shirya masa. Washe gari laraba mukayi ƙauyawa day a gidan Anty Labiba ranar Alhamis kuma Mama tayi mother's eve. Wannan ranar tana cikin ranakun da bazan manta dasu a tarihin rayuwata da Bilal ba. Munyi kyau na bugawa a shafin farko na jarida dangina sun nuna mun gata har na ringa ƙaryata cewar da kowa yake baya farin ciki da auran mu. Ana kiran sallar magriba aka tashi kai tsaye kuma muka fara wucewa gidan mu in da za'ayi mun kamu kafin mu koma gidan Anty Labiba in da ni da ƙawaye na muke kwana.
Ƙarfe tara yan uwan Bilal suka iso lokacin har ƙawayen Mama da wasu daga cikin yan uwa da suka zauna jiran karɓar lefe da kamu sun gaji sun tafi se tsirari suka rage, ina tsakiyar ƙawaye na a ɗaki na ana hira suna tsokana ta babu kunya ina maida musu martanin duk abin da suka faɗa.

Anty Labiba ta shiga ɗakin ta kalle ni kawai ta fashe da wata dariyar da kana gani kasan ta zallar mugunta ce, muka ringa kallon ta se da tayi me isarta har tana riƙe ciki kafin ta kalle ni tace
"Ke dai Halima kin haɗu da yan bura'uba matsiyata. Ni dai da wannan kayan takaicin salin alin gara yace a yafe masa kawai ya ƙarasa ɗaukar ki a sadaka yanda aka faro da dai wannan kayan zubar da mutunchin, Ko da yake Allah ya ƙara ranar baƙin naci kenan, yammata ku taso ga lefe can an kawo" ta juya ta fita tana cigaba da dariya ta barni da fassarar maganganunta. Gaba ɗaya suka fice suka tafi kallon lefe aka bar ni ni kaɗai, Hansa'u ce ta fara dawowa a sanyaye ta zauna a kusa dani tayi tagumi ba tare da tace komai ba.

"Meya faru?" Na tambaye ta, se da taja fasali kafin tace
"Amma Bilal be kyauta ba Halima, tsakani da Allah da wannan shaddar daya ɗinka da designer takalmin daya saka da uban liƙin daya ringa miki ba gara ya haɗa kuɗin ya siyi akwati ko me guda biyu da kit bane? Ke ko aro ne ai gara ya yiwo da wannan rashin mutunchin wlh"

"Ban gane ba? Me lefen yayi?" Na sake tambayar ta, se da ta zabga tsaki kafin tace
"A ledoji suka kawo, wlh tallahi in da yasan wannan abun tsiyar zasuyi gara ma ta bakin Anty Labibar ya ce ayi haƙuri kawai idan yaso ya aje miki kayan acan gidan idan kin je kya ɗinka abin ki. Harka duk da tsiya da ƙaranta, Allah ka raba mu da irin wannan abun kunyar".

Ta shi nayi na yafa mayafi na Hansa'u na tambaya ta ina zanje na mata banza, buɗe ƙofa nayi na tsaya, daga in da nake ina hango ledojin kantin El-samad dana Alpen stores zube a tsakira falo ga muryar Anty Labiba a sama tana tijara wani abu ya taso ya tsaya mun a wuya ban san sanda na juya da baya na faɗa kan gado na fashe da kukan takaici irin wanda ban taɓa ji ba akan Bilal.
"Karki damu Halims zan baki mamaki. Yanda kuka gwangwaje ni da kayan ɗaki masu kyau bake ba kowa se yayi mamakin lefen da nayi miki ke dai ki kwantar da hankalin ki kawai" maganar daya gaya mun kenan ɗazu da muke dawowa daga gurin kamu ashe irin mamakin daya shirya mun kenan.

Ana wata ga wata.
Domin cigaba da karanta littafin KURA A RUMBU a biya 800 a
1840175439
Access bank
Maryam Farouk. Se a tura shaidar biya zuwa
07061838488
Nagode
[5/18, 13:09] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 9*
Ina ji wayata na ƙara na san kuma Bilal ne amma naƙi amsawa, Allah ya sani har raina naji haushin anin da ya mun. Wane irin tozarci ne lefe a leda? Idan bashi da kuɗin akwati ya ara mana ko kuma ya bar lefen gaba ɗaya tun da ni dama ban saka rai da zeyi mun ba. Shine kuma saboda rainin hankali har yana cewa ze bani mamaki da irin lefen da ze mun aiko ga mamaki nan ya bar mun abin faɗa a cikin dangi da unguwa. Kusan minti talatin ina kuka ina jiyo hayaniya sama sama daga falo, Anty Labiba ce ta tasa dangin Bilal da rashin arziƙi ita da Anty Ummi ƙanwar su Abba. Da alama kuma manyan dake gurin abin da yake ransu kenan shiyasa basu tsawatar musu ba basu dai saka baki ba dan kar ace sun taru sun zaka ɗaya.

Ko a ƙauye ban taɓa jin an kai lefe a leda ba ai wlh gara ku zubo su kwalla ko fanteka kunyi gargajiya akan dai wannan nuna tsiyar" Anty Labiba ta faɗa cikin jin haushi. Su kansu kayan ba wai wasu na arziƙi bane, Atamfofi ne guda bakwai da lace biyu se shadda biyu da material ɗaya se kuma dogayen riguna kala huɗu da mayafai huɗu haka jaka da takalma duk saiti hurhuɗu. Tsiyar zubo su a leda ce ta rinjayi ta kayan, ko da yake iya ƙarfin sa yayi ba'a kushe masa ba. Tankawa da yayar Bilal tayi yasa abin ya sake tsamari aka shiga faɗi in faɗa kamar dai za'a kaure da faɗa se da Baba Abubakar ƙanin su Abba ya shigo gidan ya tsawatar musu. Dake Abban ma yana gida tare da su Baba Salahu take ya kira shi a waya suka zo Baba Salahu ya ringa faɗa akan me yasa su Anty Labiba za suyi haka su dai yan kawo lefe guiwa babu ƙwari suka miƙe. Baba Salamatu da neman ayi ta cewa Mama Fauziyya ina kayan snacks da aka musu da tukuici? Nan fa baga dangin Maman ba ba ga nata yan uwan ba suka hayayyaƙo mata baiwar Allah har hawaye se da tayi ƙarshe ma tace ba zata kwana gidan ba tafiya zatayi ba za'a ƙarasa biki da ita ba daƙyar aka bata haƙuri ta zauna.

Ƙarfe goma da rabi bayan na gama shan kuka na na ƙoshi ina kwance Hansa'u tace mun in zo in ji Abba ya kira na, na zumbula hijab fuska a kumbure muka fita se naga ta nufi hanyar waje na kalle ta kafin nayi magana tace
"Suna ƙofar dasu Baban Galadanci". Ban yarda ba amma na bita, ina saka ƙafata a waje muka haɗa ido da Bilal na juya da sauri kafin na ida komawa ciki ya riƙe hijabi na yana cewa
"Dan girman Allah ki tsaya ki saurare ni Halima".

Tsaye nayi na kasa ci gaba da tafiya amma ban juya na kalle shi ba, se ya zagayo yana fuskanta ta tamkar ze durƙusa mun yace
"Na fiki baƙin ciki da takaicin abin da yan uwana suka aikata mun domin ba ke suka wulaƙan ta ba ni suka yi wa, ga Nasir ne shine shaida, dubu hamsin na nawa Yaya Saratu su siyo akwati amma suka aikata wannan abun amma babu komai kowa yayi me kyau dan kan sa" ya ƙarasa kamar ze yi kuka. Se kuma naji tausayin sa ya tsurga mun, dama zuciya ta tana ta raya mun babu sanin sa amma na danne yazun kuma da yake gaba na se naji na yarda dashi amma duk da haka ban nuna ba cikin dake wa nace
"Dama ai kace zaka shayar dani mamaki ga shi kuwa ka bar mun abun faɗa a cikin dangi da ƙawaye ka ja mun abun gori har jikokinmu" na rufe ido da hijabi na na fara kuka take hankalin sa ya sake tashi. Ya ringa rantse rantse har yana durƙusawa ya riƙe ƙafafuna ganin zan bar gurin.

Murna fal zuciyata, se da na wana shi iya yanda naji ya mun kafin cikin shagwaɓa nace na haƙura.
"Nagode Halims kuma alƙawari, ba dai akwatin lefe bane? To ki biyo ni bashi in sha Allahu zan biyaki da dozen ma ran da kika haifar mun Bilal junior ko little Halims" se na rufe ido na cikin kunya jin Nasir na cewa
"Daga gobe ne ai zamu fara irgen lokaci" ganin zasu fara shaƙiyancin yasa Hansa'u da takaici ya hanata cewa komai tun tsaiwar mu tace dare yayi mu shiga gida. Haka muka raba dare muna waya da Bilal yana faɗa mun irin murnar da yake ciki da yanda ya tsara goben mu zata kasan ce. Na ringa juyi a gado ina jin kamar goben tayi mun nisa.

Washe gari aka tashi da shirin ɗaurin aure, yini da kai amarya duka a ranar za'ayi. Da wuri muka koma gidan su Hansa'u ni da ƙawaye na da muka kwana tare har sanda muka fita kuma ledojin lefe ma na zube a falo na dai ji Goggo Habi na cewa Anty Labiba a kwashe waɗannan kayan tsiyar kafin mutane su fara shigowa a samu na yayatawa a gari. Sanarwar ɗauruwar aure a tsakanina da Bilal yana cikin abubuwa ma fiya daɗi da kunnuwa na suka taɓa sauraro tsayin rayuwa ta. Tsabar farin ciki bayan da nayi sujudushshukur se kawai na zauna na fashe da kukan murna. Ƙarfe biyar muka tafi Galadanci in da aka haɗa mu da sauran cousins ɗina biyu iyayenmu maza suka mana nasiha daga can kuma bayan magriba aka ɗauki kowa zuwa gidan mijinta.

Kwata kwata na kasa yarda wai yau nice na zama matar Bilal? Da su Anty Labiba zasu tafi ta riƙe hannu na tana cewa
"Buri ya cika kin zama matar Bilal Halima, se kiyi haƙuri domin yanzu wata rayuwa ta daban zaku shiga ba wacce kuka saba da ita a waje ba. Yanzu ne za kuyi zaman gaskiya da gskiya halin kowa ya fito, zaki iya tarar da Bilal a yanda kika tsammaci samun sa koma fiye da haka ki na kuma iya tarar da akasin hasashen ki ma'ana yazo miki da wasu halaye na daban da basu kika sani a tare dashi ba. Fatan mu yanda kika masa halacci ya maida miki, kiyi haƙuri da duk abin da zaki ji ko ki gani duk wani gidan aure da kike gani da kalar ƙalubalen sa haƙurin da ma'aurata suke yi shi yake lulluɓe komai kiga tamkar ba'a saɓawa. Mace ita take mayar da gidan ta dausayi ko ta mayar dashi filin yaƙi. Yanda kika ɗora mijin ki haka ze miƙe. Idan kin tafi dashi ta laluma zakiji daɗin sa in kika koya masa hargagi da masifa har tsufa hara ze ringa miki dan haka ki koyi ta yanda zaki ringa bayyana fushi idan ranki ya ɓaci. Ina miki nasiha da kiyi koyi da halin Mama, na tabba har kike riƙi halayanta na gari badai a kawo ƙarar ki ba. Ina sake maimaita miki da kiyi haƙuri Halima, kiyi haƙuri kiyi haƙuri ki ƙara da haƙuri Sadiyayye. Yanzu ba zaki gane haƙurin me nake nanata miki ba. Allah ya albarkaci rayuwar auren ki, Allah ya mallaka miki Bilal ya hane shi da yi miki butulci irin na maza" se ta fashe da kuka muka rungume juna daƙyar aka raba mu suka tafi ya rage saura ni da ƙawaye na.

Dubu hamsin abokanan Bilal suka bada kuɗin siyan baki ga ruwa da lemo katan katan da kayan shayi, a cikin kuɗin Hansa'u ta cire dubu goma ta saka mun a jakata, itama se da muka sha kuka kafin muka rabu ya rage daga ni se Habibi na cikin gidan mu. Faɗar irin tarairayar dana samu a gurin Bilal ɓata baki ne, tamkar ƙwai haka ya ringa riritani yana shayar dani madarar soyayya har ya samu nasarar maida ni cikakkiyar mace jikin mu ya ƙara sa zama abu ɗaya kamar yanda zukatan mu suka daɗe a tare. Washe gari haka ya wuni tare dani duk da yan uwanmu da suka fara zuwa tun safe da nashi dangin be fita ba se da yamma tayi aka zo kawo gara sannan ya fita ana idar da sallar isha'i kuwa ya dawo.

Haka rayuwa ta fara miƙawa, tsakanina da Bilal a kullum so da shaƙuwar mu ƙara karfi yakeyi. A sati guda da auren mu ina jin da ace wani kuskure ya gifta har ya zamana ban auri Bilal ba da bazan taɓa yafewa kaina ba. Bilal ƙarshe ne gurin iya tattalin mace, ya iya soyayya. Irin soyayyar nan me tsayawa a rai da kake wuni cikin shauƙi da tunani ita Bilal yake gwada mun. Se da muka kwashi sati biyu ban da sallah babu abin da yake fitar dashi daga gida tun da komai muna dashi babu ce kaɗai ba'a sako mun a cikin garata ba har da soyayyen nama da dafaffen kayan miya da ɗanye se dai idan zan yi girki kawai na ɗiba. Baƙi yan ganin ɗaki ma sun haƙura saboda yanda baya kunyar idon kowa haka ze zauna a cikin su ko kuma ya riƙe ni a ɗaki se dai su gaji da jira su tafi. Dake dama dangin sa ne masu zaryar ni nawa tun da aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login