Showing 252001 words to 255000 words out of 257873 words

Chapter 85 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

466

sonka tsakani da Allah ne"

"Haba Abubakar ai babu zancen godiya tsakaninmu duk abinda nayi saboda Allah ne ba dan a gode mun ko wani abu ba. Ni dai fatana ya kiyaye Allah kuma ya sake tsare mu baki ɗaya" Nasir ya faɗa daga haka yaja motarsa ya wuce su kuma suka shige ciki ganin unguwa da yara sun fara taruwa suna kallonsu.

Falon Hajjan cike da yayanta da yan uwanta da suke jiran dawowarsu, gida ya sakw cika da murna da kuma jaje. A ƙofar ɗakin da Abubakar yake ya hangi Zulaiha tsaye yana masa murmushi, bai ganta ɗazu a kotu ba, ko kuma bai lura bane oho haka dai suka shige falon Hajja bayan ya ɗaga mata hannu. Abubakar ne yace yaje ya huta suma matan kowa ta wuce gidanta haka kuma abun ya isa.

A tsakar gida ya kalli Abubakar ya ce
"Ka samo mana Adaidaita na gaji wlh kamar zan faɗi nakeji"

"Ga ruwa can ai naga ta kai maka ka samu kayi wanka bari naje na samo maka abu mai ɗan ruwa ko yoghurt ne, ga magungunan da Yaya Nasir ya taho maka dasu yace idan kasha zaka samu sauƙin ciwon jikin kafin safiya sai muje Asibiti" Abubakar ya bashi amsa yana nuna masa Zulaiha dake tsaye ƙofar banɗakin tsakar gida, ya kalleta ya kalli Abubakar ɗin, bai dai yi magana ba ya wuce ɗakin da ta shiga zuciyarsa cike da tambayoyi.

Ɗakin na nan yanda yake Katifa ce Gado huta a ciki sai ƙaramin carpet a tsakiyar ɗakin daga gefe kuma ga alwatuna da yake zaton kayansa ne dana Zulaihan a ciki. Towel ɗin data fitar ta bashi ya cire kaya ya ɗaura ya yafa wani ƙarami kafin ya fita yana sunkuyar da kai ya shiga wankan. Bokiti uku ta ajiye masa sai da ya gamsu dan kansa da wankan da yayi kafin ya fito yana jinsa kamar wanda aka sake haihuwa. Bai san inda zai tsoma ransa ba da ta tabbata zai yi zaman kurkuku na shekarun da yaji ana ambatowa. Ko a ina aka samu kuɗaɗen da aka ce an biya masa bashin ma sai Allah domin dai bashi da su bai kuma bawa wani ajiya ba.

Kaɗan ya ci abincin da Zulaiha ta shirya masa bayan yayi sallar magriba da aka kira yana wanka. Yana jingine da bango yayi shiru Abubakar ya ƙwanƙwasa ƙofa ya bashi izinin shiga dan Zulaiha bata ɗakin. Ledar Rufaida yoghurt ya ajiye masa da magunguna yana masa sannu.

"Na san dai da takura amma ba yanda za'ayi da nayi tunanin ko nemi haya toh ga wani sabon lissafin kuma ya sake tasowa. A haka ma Allah ya rufa asiri kaga gidajen da aka siyar duka sunyi daraja sosai shiyasa har aka samu aka rage kuɗaɗen" Abubakar ya faɗa. Bilal dake kallonsa ya ce

"Wai a ina aka samu kuɗaɗen da aka biyasu kuwa?"
"Shine maganar da nake yi maka, an siyar da gidanka na Goran dutse da kuma wancan na Rijiyar Zaki sai filaye guda biyu, takardun uku na gani amma biyu ne suka siyu ɗayan dillalan sunce hanya ce kaima kayi ganganci daka siya".

Shiru yayi kafin a hankali abin tausayi yace
"Toh yanzu saura nawa a gama biyanta ita?"

"Miliyan goma aka bata" ya bashi amsa, ya ɗago kamar a firgice ya zaro ido ya ce
"Goma? Saura Ashirin fa kenan, a ina zan nemo miliyan ashirin banda yanzu waccen tarar? Na shiga uku da wahala dai idan ban yi zaman kurkuku ba dan ban san in da zan samo kuɗin nan ba" ya faɗa gwanin tausayi kamar zai fashe da kuka.

Abubakar ya kalle shi cike da tausayawa ya ce
"Alhaji Hafiz ya biya duka tarar, yanzu ina hanya Barr Sajid ya kirani yake cewa ya kirashi yace ya tura da account number da za'a saka kuɗin, ya tura masa na san kuma ya saka dukda bai sake kirana ba".

Cike da rashin yarda Bilal ya ce
"Hafiz? Hafiz dai dana sani ko wani daban?"

"Shi dai Hafiz abokinka. Badan shi ba ai da wahala wannan yarinyar ta haƙura. Na fahimci ba wai kuɗin ne a gabanta ba burinta ta wulaƙanta ka dan shi kansa Alhaji Lawan ɗin ita ta ringa zugashi sai da Hafiz ɗin ya shiga maganar kafin suka haƙura."

Shiru sukayi na kusan minti biyar kafin a hankali Bilal ya ce
" Ɗazu naga Halima amma kafin mu fito ta tafi ita da wani Namiji"

"Eh taje nima bamuyi sallama ba gaskiya ta wuce" Abubakar daya miƙe ya bashi amsa. Sai ya sake karyar da murya ya ce
"Shi wanene wanda na gansu tare toh?"

"Wanda zata aura ne" ya bashi amsa cikin halin ko in kula. Yanda ka san dirar mashi haka yaji maganar, ya gwale ido yana kallon Abubakar ya ce
"Wanda zata aura?"
"Haka tace mun" Abubakar ya sake bashi amsa. Sai ya koma laƙwas ba tareda ya sake cewa komai ba Abubakar kuma ya fice daga ɗakin.

Kwana yayi a zaune, dukda ya tsammaci rasa sauran abubuwan daya mallaka domin dai babu mai biya masa bashin daya ci wa kansa amma kuma bai zaci abin zai dame shi haka ba. Shikenan yanzu ko gidan da zai zauna bashi da shi ya dawo ɗakin ƙaninsa da zama dan asalin nasa ɗakin samartaka a soro yake shi aka shigowa Hajja dashi aka ƙara mata a falo bayan da aka raba asalin ɗakin ya koma ciki da rumfa sannan aka mata banɗaki da sauran a cikin ɗaki. Shi gashi yanzu ɗakin ma falle ɗaya suka samu banɗaki sai sun fita tsakar gida, hatta da kayan gadon sa da na Zulaihan duka dasu akayi gwanjon gidan kayan kitchen ɗinta da sauran abubuwanta kawai ta fita dasu.

Abu ɗaya da ya saka ya ɗan ji dama-dama yanda bai ga damuwa sosai akan canjin muhallin a tattare da Zulaiha ba. Ba yabo ba fallasa take sabgoginta, daya gama cin abinci ta tattare kwanuka ta fita dasu ta dawo ta tambaye shi ko akwai abinda yake buƙata yace babu shikenan tayi kwanciyarta.

A haka ya kwashe kwana uku yana jinyar malaria daya kwaso a prison, ba inda yake fita yana ɗaki ko falon Hajja sai ta fito tana ta ƙwala masa kira musamman idan yan jaje da yace munafunci suke zuwa suka zo kafin zai shiga yafi ganewa ya zauna a ɗaki kawai yayi shiru yana Istigfari da tunanin duniya.

Ranar daya kwana huɗu da yamma yana kwance a ɗaki ranar an samu sauƙin yan jaje dan tun safe babu wanda yayi sallama, yana kwancen yana jiyo Hajja nata sababi wanda kuma ya san ba zai wuce da Zulaiha take ba. Tun washe garin daya dawo ya fahimci za'a samu gagarunar matsala tsakanin Hajja da Zulaihan a zamansu.

Hajja tamkar shi take, gurinta ya gado shegiyar tsafta da rashin son ganin shirgi a guri. Idan ka shiga gidanta kamar ba na tsohuwa ba shiyasa sanda Fadila take zawarci Hajjan take gwammace ta tafi gidan Anty Habiba saboda tace ɓata mata gida takeyi, da ciwon ƙafar da komai haka zatayi shara ta wuni tana kaye-kaye ko leda iska ta kwaso mata idan bata ɗauke ba bata jin daɗi toh yanzu ga Zulaiha kuma da shegiyar ƙazanta.

Bata mata aikin komai, dai-dai da kwanukan abinci idan aka kai masa dan ita bata wani ci sai kayan kwaɗayi yanayinta ma sai yake ganin kamar tana da shigar ciki dukda bai tabbatar ba amma haka zata haɗo na rana da dare ta fito dasu ƙofar ɗaki da safe sai dai Safiyya yar Anty Ladidi ta ɗauke ta wanke. Tun bayan da aka sallamo Hajjan daga Asibiti ta dawo gidan da zama saboda yanzu ko tafiya sai da sanduna biyu take yinta Safiyyan ce take mata komai haka su ma hatta sharar cikin ɗakin ita take shiga ta musu.

Yau ɗin Safiyyar ta tafi rubuya Jamb tun safe kafin ta fita kuma sai da ta yiwa Hajjan komai har abin karyawa, tun sha ɗaya yana ji tana kiran Zulaiha ta fito ta ɗora abincin rana tunda Safiyya bata dawo ba amma tayi kunnen uwar shegu tana danna waya shima ya maimaita mata amma bata ko kalle shi ba yayi shiru ya zura mata ido ana kiran Azahar ta ɗaura zani ta fita ta juye ruwan zafin da Hajjan ta ɗora a kurfoti ta shige wanka shine yanzu ta fito ta gani take sababi.

Tashi yayi ya saka riga saboda jiyo tashin muryar Zulaihan da yayi kamar tana amsawa Hajja maganar da takeyi, yana fita kuwa ya jita tana cewa
"Ai na faɗa miki ni ba yar aiki bace zaman aure nakeyi idan ma zan girkawa wani abinci toh mijina ne tunda kuma kince ke zaki ringa bashi abinci sai kiyi tayi ku dafa ko karku dafa matsalarku ce ko kinga ina cin abincinku ne?"

"Ni kike faɗawa haka" Hajja ta faɗa tana kallonta, Zulaiha ta ɗauke kai gefe ganin Bilal ɗin ya fito ba tareda tace komai ba shirun da sukayi kuma ya saka suka ji sallamar da ake ta dokawa tun farkon fara muhawarar tasu. Duka su ukun suka kalli ƙofa, Halima dake tsaye riƙe da hannun Sharifa Al'amin da Inaayah na tsaye kusa da ita hannayensu riƙe da ledoji ta sake maimaita sallama.

Ba Bilal da Hajja ba hatta Zulaiha sai da taji wani iri da zuwan Haliman da sauri ta shige ɗaki ta bar Bilal da Hajja da suka ƙame a tsaye aka rasa wanda zai amsa musu.

HALIMA
Ganin duk suna kallonmu sun kasa magana ya saka na shiga ina faɗaɗa fuskata, tabarmar da na gani shimfiɗe kan barandar ɗakin Hajja muka zauna tareda yaran sai lokacin sukayi firgigit kamar waɗanda aka watsawa ruwan sanyi Hajja cikin murmushin da kana gani kasan na yaƙe ne haɗi da kunya mai tsanani ta shiga yi mana sannu da zuwa tana cewa mu tashi mu shiga ciki.

"Nan ma yayi Hajja" na faɗa ta ce
"Aa ku tashi dan Allah" ta kamo Al'amin tana cewa
"Ku tashi ku shiga ciki kunji kai da ɗakin matarka ace ku zauna a tabarma".

A raina nace "ikon Allah" kafin na miƙe nabi bayanta. Kallon falon na ringayi, tunda naje gidan Bilal nake masa nacin ya kamata ya gyarawa Hajja ɗakinta ƙarshe cewa yayi nima idan nayi mata ai ba laifi bane shi in rabu dashi a lokacin har na niyyata zanyi ɗin da surutu na faɗawa Mama tace kar taji karta gani na fishi sanin ya kamata ne ko kuwa da zance zan gyarawa Babarsa ɗaki gashi yanzu Allah ya nufa an mata shi ɗin ne ko Abubakar ne sai Allah.

Al'amin ta cewa ya buɗe fridge ya ɗebo mana ruwa da lemo nace mata a barshi daga gida muke ma mungode"

"Kai tashi ka ɗebo, rashin ƙafa ya saka har aka fara ganin damata ana maida mun magana" Hajjan ta faɗa sai na kama bakina nayi shiru kawai ina duba wayata da tayi ƙara dai-dai nan Bilal ya shigo falon da ƙaramar sallama kamar Almajirin dake jin yunwa.

A kujerar dake bakin ƙofa ya zauna, sai da na kalli Inaayah da Al'amin da suke kallonsa kamar sunga wani baƙo kafin suka gaishe shi, ya miƙawa Sharifa hannu ta sake lafewa a jikina dan tunda Hajja tace taje da a zaune take a kujerar ta tashi ta haye jikina.

"Au kaima ubanta kenan, toh bari na shafawa kaina lafiya" Hajja ta faɗa, na kalleshi kafin na gaishe shi haɗi dayi masa jaje ya amsa yana mun kallon ƙurilla kamar wanda ke neman wani abu a jikina. Falon yayi shiru, ƙarar da wayata tayi ya saka na miƙe ina cewa
"Dama kawo su nayi su dubaku bari muje ana jiranmu a waje"

"Sai kace wanda ake korarku Halima gashi ko ruwan ma baki sha ba balle ki barsu suma su sha sai kace wanda suka zo baƙon guri ko baki gaya musu nan ɗin tushensu bane? Mu jininsu ne basu da sama damu?" Hajja ta faɗa. Kamar inyi shiru sai kuma nayi murmushi na kalleta nace

"Ina fa zasu manta tushensu Hajja? Ai idan ita Sharifa bata sanku ba shi Al'amin daya bar gidan da wayonsa ai ba zai mantaku ba. Ita ɗin ma da ace tana ganinku ba zata muku ƙiwa ba in da zataga Abubakar yanzu zaki san da gaske ta san jininta" ina rufe baki Abubakar ɗin yayi sallama tun kafin kuma na san su biyu ne ƙamshin turaren Dr Salman ya isarmun da saƙon.

Da gudu kuwa Al'amin ɗin ya nufi Kawunsa itama Sharifan ta zame tana kiran "Uncle" ya ɗaga su duka su biyun yana juyi dasu suna dariya. Sai na rasa jikin wanda ya fi wani yin sanyi tsakanin Bilal da Hajja musamman da Dr Salman ya ƙaraso ya zauna gefena. Suna gama gaisawa na miƙe ina nuna mata ledojin da muka shiga dasu shi kuma ya ajiye musu rafar 1k guda biyu na fita yana biye dani a baya dan Abubakar ya fita da yaran.

Amarya na tsakar gida ta shimfiɗa sallaya a inda rana bata tarar ba tana shan rake, na ce mata "Sannu" ta amsa mun da "Ina wuni" muga gaisa daga tsayen na mata jajen abinda ya samu Mijinta kafin nayi waje.

A soro Bilal ya tsayar dani, kamar wani mai jin tsoron kada a jishi kai a ƙasa ya ce
"Na san abubuwa da yawa sun faru a baya da ban samu damar wanke kaina ba Halima. Dawo da maganar bashida amfani amma ina so ki sani na gane kuskure na kuma yarda cewar na zalunceki a zamantakewatarmu. Dagaske nake miki wannan maganar tun daga ƙasan zuciyata ina mai neman gafararki Halima kiyi haƙuri ki yafe mun duk wani abu dana miki daga ranar da kika fara sanina har zuwa yanzu da muke tsaye. Ko ba'a faɗa mun ba na san abubuwa da suke faruwa harda haƙƙinki Halima. Na sakaki kuka sau babu adadi a sanda kike taredani tun bayan rabuwata dake nayi kuka sau babu adadi nim. A hankali abubuwa da yawa suna ta faruwa da suke ankarar dani girman laifukan dana ringa aikata miki wanda nake kallo a matsayin ba komai ba a wancan lokacin dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mun" ya ƙarasa kamar zai durƙusa mun.

Murmushi nayi na ce
"Na daɗe da yafe maka Bilal, sau da yawa mu kanyi baƙin ciki idan wani al'amari ya samemu wanda kuma daga baya hakan sai kaga ya zame mana alkhairi amma bama fahimtar hakan da sauri har sai munyi haƙuri tukunna. Tsakanina da kai idan akwai mai laifi nice dana cusa maka kaina ta ƙarfi dukda ka yi iya ƙoƙarin ka gurin nuna mun baka muradin hakan. Kayi haƙuri ka zauna dani tsayin lokaci. A yanzu na fahimci ba'a yiwa so dole, sannan Soyayyar da kake so ake sonka ita ce soyayya"

Na nuna masa Salman dake zaune cikin mota nace
"Da baka barni ba da ban haɗu dashi ba hakan yana nufin da nayi asarar ingantacciya kuma nagartacciyar soyayya wacce babu algus a cikinta. Saurayine bai taɓa aure ba amma ya zaɓeni mai yaya biyu akan tarin yammatan da suke karakaina akansa, wannan kaɗai nasarace na kuma godewa Allah" daga haka na sa kai na fice na barshi tsaye yana bi na da kallo.

A hanya Dr ya kalleni ya ce
"Amma kika ce kinfi jin daɗi da Abbansu baya zuwa dubasu". Ba tareda na kalleshi ba nace
"Eh mana nafi son hakan"
"Ba gaskiya bane, idan kinfi son haka mai yasa kika nuna jin zafin rashin kulawar tasa kuma ɗazu a gabansa?"

"Ni kuma nayi me?" Na faɗa ina buɗe masa ido, shima buɗe idon yayi kafin ya ce
"Wai sai yaushe zaki daina sonsa kwata-kwata? Dame ya fini Halima? Ina zaune a mota ina kallonki kina ta washe masa baki har kina nunoni Allah kaɗai ya san mai kike gaya masa a kaina ƙila cewa kike ni maye ne na nace miki ko?"

"Ni dama na san kana kallonmu" na faɗa da sigar zolaya. Ya haɗe fuska kamar gaske yana cewa
"Wlh na raina ajinki ma dana ganshi sam ashe ma baki ga taste. Kalleshi ba sai kace wani sahorami fuska kamar mace. Dama ta yaya wancan zai san darajar mace kamarki? Da kike ta wahalar dani kike garani kamar wani ball na ɗauka zanga wani namijin gaske wanda ya fini banda girman idanuwa da tsinin hanci baya ga haka na kereshi a komai har ma abinda baki rigada kin sani ba duk na san zan fishi wlh dan daga ganinsa ba wani ƙoƙari zai yi na azo a gani ba".

Baya na fara kallo naga hankalin yaran gaba ɗaya yana kan Tab ɗin da suke kallo ko da ma ƙasa ƙasa yayi maganar na toshe kunnuwana biyu da hannu ina cewa
"Kai dai kaji tsoron Allah kuma ni a yaushe nace maka har yanzu ina sonsa?"

"Idan bakya sonsa akan me tunda aka ce an kamashi hankalinki yaƙi kwanciya? Kin ganshi a kotu amma dukda haka baki haƙura ba kika wani fake da yara saboda kizo ki ganshi yanzu dai hankalinki ya kwanta ko?" Yayi maganar yana kallona. Shagwaɓe fuska nayi ina kallonsa nace

"Amma dai ka san asirin da kayi mun ya ci dan bana iya cikakkiyar awa ɗaya ba tareda nayi tunanin ka ba" ya saki murmushinsa mai kyau kafin yace
"Ni dai kika asirce ina nan kuma ina addu'a Allah ya ɗorani a kanki kada ki mayar dani bita zai-zai dan tunda har Hajiya tace ta lura ina sonki dagaske na tabbata gaskiya duk inda kika kai sunana ba'a ci miki kuɗi a banza ba".

Tare mukayi dariya nace
"Haka fa yan office suke cewa wai daga zuwa na asirceka duk ga mata nan da suka kwashe shekaru a gurin babu wacce kake yiwa kallo biyu sai ni gani ɗaya zaka fara so na?"

"Sai ki ce musu dama ke nake jira shiyasa bana iya yiwa kowacce mace kallo biyu sai a kanki na fara". Ji nayi kaina ya fasu, yanda yayi maganar haɗi da mun wani kallo yana lumshe ido da yake tabbatar da gaskiyar abinda ya faɗa ya saka naji kamar in fasa ihun murna. Gidan Mama muka koma ina tsaye muna sallama Abba ya fito dan haka na shige gida na barsu suna gaisawa dariya ta kamani ganin Salman kamar zai kwanta a ƙasa ana gaida suruki.

"Kin je hankalinki ya kwanta dai ko?" Anty Labiba ta faɗa ina shiga, Mama Fauziyya ta tare mun tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login