Showing 177001 words to 180000 words out of 257873 words

Chapter 60 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

497

ɗauki jakarta ta fita tana jin Ladi da Habiba na faɗa mata maganganu amma bata tamka ba.

A hankali ba tareda ya haɗa ido da kowa ba ya bi bayan Anty Aminan yana ko Hadiza tana cewa
"Ina zaka je kuma munafukin Allah ko an sallameka ne?"

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 45*

ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi.

"Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya.

Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida.

Kallonsa ta ringayi har ya kai aya kafin ta harare shi ta ce
"Kaine shaiɗan ɗin ai ba wani ba zancen Hajja kuma ko da da gaske da saka hannunta ai kai ba mahaukaci bane; da zaka ringa biye mata idan dama ba gangara kake nema ba ai ka san ta yanda zaka lallaɓata ka zauna da matarka lafiya. Karma ka raina mun wayau na san kana sane yanzun ma Allah kaɗai ya san abinda yake ƙasan ranka da kake so ka sake janyota ka cigaba da gasa mata aya a hannu, to ni dai babu ruwana; yanda sanda ka koreta bakayi shawara da kowa ba yanzu ma sai ka san ta yanda zaka bi idan itama bata gaji da uƙubar da kake mata ba sai ta dawo" ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe motarta.

Riƙe murfin yayi tamkar zai fashe mata da kuka harda rage tsayi ya ce
"Na rantse da Allah bani na ce ta tafi ba haka kawai ta haɗa kayanta kuma babu yanda banyi da tayi haƙuri mu zauna mu sasanta koma menene ba amma ta ce ita tafiya zatayi".

"Lallai Bilal, wato har yanzu bakayi laushi ba ka iya kallon tsabar ido na ka shirga mun ƙarya har kana rantsuwa da Allah ko?
Ka san ko jikina kunnuwa ne ba zan taɓa yarda haka nan Halima ta sa ƙafa ta bar gidanka ba domin a baya ka mata abubuwan daya kamata ta tafin amma ta shanye sai yanzu zaka ce haka nan ta tafi?

To bari kaji, babu ruwana; yanda baka godewa ni'imar da Allah yayi maka ta aurenta ba yanzu sai ka godewa azabar sakacin da kayi har ka rasata" ta faɗa tana fizge murfin motarta. Ƙasa ya zube ya kama ƙafarta yana cewa

"Dan girman Allah Anty karki ce haka; ke kaɗai nake saka ran zaki fahimce ni kuma ki mun uzuri na kuma san itama ba zata ƙi sauraronki ba. Dagaske laifi nayi mata amma wannan tsakaninmu ne kuma na san yanzu ta haƙura. Dan Allah ki tayani rarrashinta wlh na miki alƙawarin har idan ta dawo ba za'a sake jin kanmu ba".

Ganin masu giftawa sun fara tsayawa suna kallon su ya saka ta daka maza tsawa ta ce
"Dallah tashi karka tara mun mutane" ya miƙe tareda riƙe hannunta, ta balla masa harara sai ya saketa ya zare key ɗin motar dGa hannunta yana cewa

"Muje na kaiki dan Allah"
"Ka kaini ina? Kaga Bilal ka bani key ɗin motara na tafi; tunda kake shuka mata tsiya banje na tayata ƙwatar yancinta ba sai yanzu da ta tasarwa kanta kake so naje saboda goyon bayan rashin gaskiya na ce ta dawo taci gaba da zama da kai? To ba haka nake ba" ta faɗa cikin muryar dake nuna ba wasa take ba.

Hannu biyu ya dafe kansa kafin ya juya ya kalli ɗai ɗaikun yan unguwa dake satar kallon su ya ce
"Idan na faɗa miki laifin da na mata zaki tayani bata haƙuri?"

Ta kafe shi da ido kamar mai nazari kafin ta ce
"Idan ka cancanci yafiya zan ga abinda zan iya". Saida ta zagaya ta zauna a kujerar mai zaman banza ya rufe mata ƙofar kafin ya koma mazaunin direba ya tada motar suka bar layin, can gefen titi ya samu guri yayi parking, sun fi minti biyar yana saƙa abinda zai gaya mata da zata yarda ita kuma tana danna wayarta kafin yayi ƙarfin halin cewa

"Wayata ta ɗauka ta bincika shi ne ta ga chats ɗina da Zulaiha da kuma Jalilah. Ba tareda ta buƙaci wani ƙarin bayani ba kawai ta hau zagina tana gayamun baƙaƙen maganganu; na faɗa mata ba abinda take tunani bane duk su biyun auren su zanyi amma taƙi fahimta ta ringa zagina har da kama mun wuyan riga wai na saketa ni kuma na zuciya na mareta shikenan ta haɗa kayanta ta tafi gida".

Yanda yayi maganar sai ka rantse da Allah gaskiya ya faɗa, Anty Amina da tayi shiru tana kallon sa ta ce
"Ka faɗa mun abinda hankali zai ɗauka in kuma ba haka ba ka daina ɓata mun lokaci ka rabu da ni na tafi".

Wata rantsuwar ya sake kwasowa ya dire yana tabbatar mata da iya gaskiyar abinda ya faru kenan.

"Gaskiya ƙarya kakeyi, Halimar dana sani b zata zageka ba balle har ta kama ka da kokawa" ta sake faɗa, ya marairaice fuska ya ce

"Amma Anty kin san dai ƙarya ba hali na bace kuma ke macece akan lamarin kishi kin san ba abinda ba zaku iya yi ba. Ni kaina wlh idan wani ya ce mun Halima zata aikata hakan zan ƙaryata amma ya faru na san kuma ba lallai duk wanda zan faɗawa ya yarda ba shiyasa kawai nayi shiru na bar maganar ina so mu sasanta a tsakaninmu amma kuma hakan yana nema ya faskara. Wlh ina son matata kuma ni bana so ace Zulaiha ta tare bata nan balle hakan ya buɗe hanyar da zata fara rainata shiyasa ma nayi shiru ko Nasir ban faɗawa ba balle maganar ta fita har taje kunnen yan uwan Zulaihan".

Hararar sa Anty Amina tayi ta ce
"Na nawa kuma? Kaf dangi da yan unguwa wanene bai san bata gidanka ba?"

"Ai dai su can basu sani ba" ya bata amsa, kafin tayi magana ya ruƙo hannunta ya sake cewa
"Na san ina da laifuka a gurinta amma yanzu a shirye nake da na gyara komai ba iya alaƙata da Halima ba da kowa ma duk wasu kuskure nawa ina so na gyarasu amma dawowarta rayuwata shi zai jagoranci komai dan Allah Anty ki taimaka mun".

Yanda yayi sai da ta ji zuciyarta ta sosu amma ta dake bata nuna masa ba ta ce
"Ni dai na gaya maka ba zan shiga ba dan yarinyar nan na ganin mutunchi na haka kawai ban ma san gaskiya ka faɗa ko ƙarya ba a xe ma gaskiya ne in shiga ta haƙura ta dawo ka cigaba daga inda ka tsaya ai kaga nima ka mayar da ni mutuniyar banza a idonta"

"Yanzu baki yarda nayi nadama dagaske ba?" Ya faɗa kamar zai fasa kuka. Tayi gajeran tsaki ta ce

"Zan maka abu ɗaya, zan kira Yaya Aminu na faɗa masa, ko zata dawo gara ayi komai da shaidu ta yanda ko ka cigaba da halinka ka san shi ba sa'an wasan ka bane".

"Yanzu ba zamu iya sirri tsakaninmu ba sai an sako wani a ciki?" Ya faɗa ta ce

"Shi Yaya Aminun ne wani? Lallai baka canza ba Bilal yaudara ta kawai kake so kayi"

"Haba kin san ba haka nake nufi ba kawai ina tunanin Hajja ne idan ta ji kin san dai ta hana saka su cikin sabgogin mu" ya sake faɗa. Taso masa tayi da masifa ta ce

"Fitar mun daga mota mutumin banza kawai, dama na san ba zaka taɓa canzawa ba. To ai sai kaje Hajjan ta dawo maka da Halimar kar ka sake sakoni a shirmenka wlh tunda ba zakayi hankali ba". Duk yanda ya so ya shawo kanta ta ƙi sauraro, fata fata ta masa ya fita daga motar kamar zai fashe da kuka ya samu gefen titi ya zauna ya dafe kai. Yafi minti ashirin a gurin yana jin wayarsa nata ringing amma bai ɗaga ba sai da ya gaji ya zama kafin ya tashi ya tare Adaidaita ya wuce.

Hankalin sa ya ɗan kwanta da yaga duk missed calls ɗin Hajja ne da na Zulaiha Jalilah bata kira shi ba, sai da ya siyo mata abincin kafin ya wuce gida ya tarar da ita a falo da kayanta cikin shiri tana waya sai da ta gama fuska a sake ta kalle shi ta ce

"Yanzu Abdul ya kirani ƙarfe uku zamu tashi"
"Ƙarfe uku kuma?" Ya faɗa yana zaro wayarsa da kira ya shigo, ta ɗauki takeaway ɗin ta buɗe tana cewa

"Haka ya ce, zaka ajiye ni ko na yi order bolt?"

Ɗaki ya shiga bayan da ya ce zai kaita airport ɗin duk ya sha jinin jikinsa a ransa ya ringa raya anya ba wani sharrin ta sake ƙulla masa ba yanda ta ware tamkar babua abinda ya faru ɗazu.

Yanda ka san wanda ya ɗakko gawa haka ya ringa zare ido yana haɗa zufa sanda suka fita sai da ya hau babban titi kafin hankalinsa ya ɗan kwanta. Bai zauna ba yana sauketa ya wuce dan suna hanya yaji tana waya da Hafiz akan zasu haɗu a airport ɗin dan haka a parking lot suka rabu itama kuma bata matsa da ya tsaya ɗin ba sukayi sallama ta shige.

Sai lokacin ya ji kamar an zare masa ƙaya a maƙoshi, guri ya samu ya tsaya yayi wa Zulaiha transfer na sauran kuɗin da ya mata alƙawari dan ta masa kira ya fi ashirin daga sanda ya kunna wayarsa zuwa yanzu wayar da sukayi ɗazu ma cikin fushi take har tana cewa idan ya san ba zai bata ba ya faɗa mata ta cire rai ba wai ya ringa raina mata wayau ba.

Halin da yake ciki ya saka bai mayar da hankali akan maganar tata ba, jiya jiya fa ya bata 2m amma ko 24hrs ba'a yi ba ta addabe shi da waya akan cikon kuɗi.

Shi yanzu lamarin Halima ne ya tsaya masa a rai sam ya kasa samun ƙwarin guiwar kiranta balle ya taka ya bita to mai zai ce mata? Duk wata ƙarya da zaiyi dan ya kare kansa na zai fita ba da ace ita kaɗai ce ma da sauƙi ƙila ya iya manipulating nata amma yanzu wannan shegen ƙanin nata da dama can ba ƙaunar sa yakeyi ba shi kaɗai ya isa ya lalata komai.

Gashi Anty Aminar da yayi tunanin zata iya taimaka masa itama ta botsare, tada motar yayi ya nufi gidan Nasir. Yayi mamakin yanda ko da wasa bai masa zancen Halima ba dukda ya san Nasir ɗin yana sane da basa tare amma bai san dalilin da ya saka ya masa shiru ba.

Sunyi saɓani dan yana zuwa matarsa tace yanzun nan shi kuma ya fita ya kira wayarsa bata shiga ba dole ya tafi a ransa yana raya Nasir ɗin ne kaɗai yake jin zai iya gayawa gaskiyar abinda ya faru dan ya san zai rufa masa asiri. Wata zuciyar ta ce ya gayawa Hafiz mana,

Halima na ganin girmansa ya san idan ya saka baki zata haƙura amma kuma ko giyar wake ya sha ba zai taɓa faɗawa Hafiz gaskiyar abinda ya haɗa su ba; ko da ace ba da Jalilah bane domin a duk sanda zasu zauna lokuta ɗai ɗai ne baya tunasar dashi akan duk rintsi kada ya yarda shaiɗan ya kwaɗaita masa biye biyen mata har ya kan ji kamar Hafiz ɗin na da masaniya akan alaƙar sa da Jalilah.

Yanzu mai zai ce masa ya haɗa shi da Halima ya yarda? Dan dai ya san duk ƙaryar da zai masa zai gane gaskiya ce kaɗai zata ƙwace shi a hannun Hafiz ɗin.

Haka ya ƙarar da yinin ranar daga nan yayi can kansa cike da tunanin ta ina zai fara tunkarar Halima? Suna ƙare magana da Jalilah bayan sun sauka take yayi blocking nata a duk wata hanya da zata iya samun sa ya kuma saka duka numbobinta a blacklist. Ya gama da shafinta ya haƙura da zancen shago da kayan da zata zuba, tunda takardun gurin suna hannun sa hakan ma ya ishe shi zai siyar da gurin kamar yanda ya siyar da gidanta idan ya so ya haɗa kuɗin ya kama wani business ɗin.

HALIMA

Farkawa nayi na tsinci kaina a gadon asibiti; cikin abinda bai gaza seconds uku ba kuma komai ya dawo mun na abinda yayi silar zuwana asibitin. Na sake runtse ido na hotunan su suna gilmamun, ban lura da mutane a ɗakin ba sai da na ji muryar Mama Fauziyya ta na cewa

"Wai yanzu haka za'a zubawa yarinyar nan ido ta salwantar da rayuwarta akan wani banza da bai san darajarta ba?". Mama ta ja tsakin da naji har tsakiyar kaina ta ce

"To Anty ya za'a mata? Halima dai ba yarinya bace da za'a kama a doka; iya bakin ƙoƙari lallami da nasiha har ma da faɗan an mata tunda abinda ta zaɓa kenan ai sai mu zuba mata ido kawai. Ni wlh na gaji, na ma faɗawa Abbansu daga nan gidanta zata wuce taje can tunda dama ba wani ya ce ta taho ba haka kawai ba zata kasheni da fargaba kafin lokaci na yayi ba".

"Ke kika so ai; tuntuni na ce ki tattara lamarinta ki aje a gefe kiyi rayuwarki amma kika ƙi sai kace ita kaɗai kika haifa. Ni fa shiyasa tuntuni na kama bakina, ga labari yana ta ci na a zuci amma sanin idan na faɗa ƙarshe tare zaku raba jinyar ya saka nayi shiru".

Haɗa baki Mama da Mama Fauziyya sukayi gurin cewa "labarin me?"

A jikina naji ta kalle ni dan ta tabbatar da har lokacin bacci nake kafin ta ce
"Auren da mijinta ya ƙara mana". Suka sake haɗe baki gurin cewa
"Me? Wane irin aure kuma? Yaushe?"

Ji naji kamar ta soka mun mashi a zuciya, na sake runtse ido hawaye masu zafi suka ziraro ta gefen ido na amma nayi ƙoƙarin saita kaina gudun yin motsin da zai ankarar dasu. Ina buƙatar jin ƙarshen zancen ko babu komai zan samu amsar wacece na tarar a ɗakin Mijina tareda shi cikin yanayin da nake fatan in manta saboda abinda tuna shi yake haifar mun a gangar jiki da zuciyata.

Ƙasa da murya tayi ta ce
"Ranar da kuka zo duba Inaayah har kika ganshi ai gurin yarinyar zai je, a nan ƙasan layinmu suke kusa da gidan Zinaru mai yi mun kitso basu ma daɗe da tarewa ba dan basu shekara ba shi ya siya musu gida a gurin.

Tunda ya fara zuwa Zinaru ta faɗa mun tana ganin Mijin Halima a gidan ni farko ma na ɗauka ko yan uwansu ne amma da naji Haliman ba tayi zancen ba sai kuma Zinaru ta faɗa mun ai yarinyar gidan yake so, mun kuma sha haɗuwa yanda yakeyi bai ganni ba nima in ɗauke kai to kuma sai ji mukayi an ɗaura aure".

Ajiyar zuciya Mama ta sauke kafin ta ce
"Ai dama duk wanda ya siyi rariya ya san zata zubda ruwa, to waya sani ko zancen auren ta ji yanzun?"

"Dagaske kenan dama saboda zaiyi aure tayo yaji ashe?" Mama Fauziyya ta faɗa, Mama ta girgiza kai Anty Labiba kuma ta ce
"Ita ta sani, idan ma dan hakan ne dai ba abinda ya canza tunda gashi yayi auren sa in da kuma yana sonta yana son zama da ita ko bai fasa aurenba ba zai mata wannan wulaƙancin ba. To ba ji take ba balle ka ɓata lokacin ka ka mata magana ni shiyasa na sallamata bana iya kayan takaici ba".

Maganar suka cigaba da tattaunawa, na samu na gyara kwanciya cikin dabara na basu baya dan in samu damar yin kuka dakyau, ita bata san abinda ke damuna ya zarce maganar auren Bilal ba wannan ai tsohon zance ne tuntuni na samu labari. Sai da aka kira la'asar suka fita duk su ukun kafin na tashi zaune sosai na fashe da kuka harda shassheƙa.

Ina tsaka da kukan wata Nurse ta shigo dubani, babbace dan ta haifeni ai kuwa ta rufeni da faɗa yanda kasan zata dokeni tana cewa wai ni muguwa ce bani da imani na san a halin da iyayena suka kawoni kuwa shine zan tashi na cigaba da kuka saboda na ƙara tayar musu da hankali?

A daren aka bani sallama Dr ya ce ba abinda zasu mun kawai na koma gida na cigaba da shan magunguna na. Sai na ringaji na kamar marainiya wacce bata da sauran gata da muka koma gida a falo aka barni kamar baƙuwa kowa ya kama sabgarsa saida na gaji da zama dan kaina na lallaɓa na shige ɗaki na kwanta na shiga tunani.

Idan wacce Bilal ya aura yar unguwar su Anty Labiba ce kenan tana nufin gidan da ya kaini nayi musu gaisuwa; in kuwa haka ne ba Jalilah da na tarar a ɗaki na ya aura ba, wancan mugun abunda na gani suna aikatawa a waya ne ya cigaba har ta kai ya ɗakkota ya kawota gida shi tafiyata yanci ya samu mai lasisi na kawo mata.

Na haɗa kai da guiwa ina hawayen tausayin kaina. Sam ba wannan ne Bilal ɗin da na faɗa soyayyar sa ba, Bilal ɗina ba haka yake ba. Amma wai a yaushe ya canza Ina tareda shi ban taɓa fahimtar komai ba? Ya akayi na bari soyayya ta rufe mun ido har na kasa fahimtar canzawarsa ina zaune da manemin mata amma yardar da nayi dashi ko da wasa ban taɓa hasaso zai kasance haka ba.

Tabbas Bilal ya cuceni kuma ya yaudareni sannan ya ci amanar ƙauna. Wlh da ace Zulaihan ita ce na kama shi yana chat da ita ba Jalilah ba zan iya yafe masa ko dan aurenta da yayi zai shafe komai amma ƙazantar tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login