Showing 171001 words to 174000 words out of 257873 words

Chapter 58 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

473

dai dai sanda na sakeyin wani mugun ganin, ɗan kunne, agogo harda zobe na mace akan center table. Da baya na ringa tafiya ina jin kamar ana zare mun laka, kaina ya cushe ta yanda na gagara tuna komai da ya kamata nayi a lokacin.

"Bilal ya ƙara aure" maganar Hafiz ta shiga dawo mun. Yaraf na zube kan kujera na dafe kaina da naji ya mun wani yammm kamar an barbaɗa mun yaji.

Ban san tsayin lokacin da na ɗauka a zaune ba, nesa nake jiyo muryar Mu'azzam yana mun magana amma ban fahimci komai ba sai bin sa da na ringayi da kallo, can kuma kamar an tsikareni na miƙe na fice daga falon da sauri ya biyo ni yana kiran sunana amma ban tsaya na sai da na dangana da falon Bilal.

Taimakon da ubangiji yayi mun tsayuwar Mu'azzam ɗin bayana na tabbata ba dan haka ba yanda na tafi idan da ace na samu nasarar kaiwa ƙasa tabbas a wannan karon babu lallai in warke domin da wahala idan ban samu paralyze ba. Dukda yanda nake jin jikina tamkar an saka mun shocking haka na fizge daga riƙon da Mu'azzam ya mun na juya baya domin na hana idanuwana cigaba da arangama da mummunan ganin da nayi.

Bai sakeni ba sai rungumeni da yayi lokaci ɗaya na fashe da kukan da komai dakewar zuciyar mai sauraro sai ya tausaya mun. Idanuwana a rufe suke amma hoton mugun abinda na gani yana nan tar tamkar a lokacin nake kallo, Bilal kwance kan cinyar wata mace da ban san matsayinta gare shi ba tana shayar dashi tamkar jariri.

A yanda nake a jikin Mu'azzam ya ringa tafiya da ni har ya sakani a mota, yanayin sa kaɗai ya bayyanar da shima ya shiga shock da abunda muka gani. Sama da minti goma muna zaune a motar ni ina kuka ahi kuma ya riƙe haɓarsa ya zurawa gaban motar ido.

BILAL
Bacci rabi da rabi yayi saboda alarm ɗin daya saita tun ƙarfe huɗu domin baya son wani dalili da zai janyo har tsautsayi ya gifta gari yayi haske bai fitar da Jalilah daga unguwar ba. Tun kiran farko yayi wanka ya zauna yana jira a kira sallah, ana fara kira kuwa ya shiga ɗakin ya fara tashinta amma tayi masa banza sai ma gyara kwanciya da tayi, cikin ƙufula da halinta ya ce

"Dan Allah ki tashi, kin san dai yanzu zakiga gari yayi haske idan kuma ba so kikeyi ki makara ba". Bata amsa ba ya gaji da tsayuwa yana mitar ta tashi jin har an tayar da sallah ya sa ya fita yana sakin ƙwafa, shi yanzu ya ke tunanin kamar ma da biyu tace sai a nan zata kwana saboda taja masa wani bala'in a unguwa. Hawa uku ya murzawa Get muƙulli kafin ya tafi, yana idar da sallah kuwa bai zauna ba ya fito da sauri ya koma yana tafiya yana satar kallon mutane gaba ɗaya ya tsargi kansa gani yake kamar kowa ya san mace ta kwana a gidansa a haka ya shige ya sakw kullo ƙofar ta ciki.

Duk yanda yayi da Jalilah akan ta tashi tayi sallah ta shirya su tafi taƙi ƙarshe ta balbaleshi da masifa akan ya fita ya bata guri saboda tazo gidansa ne zai uzzura mata ya hanata bacci ai ta san da tafiyar babu kuma sisinsa cikin kuɗin data biya balle yace idan ta rasa jirgi zata ja masa asara.

"Aikin banza kawai saboda na zo wannan akurkin gidan naka shine zaka ringa mun ihu akai in tashi to ba zan tafi ba idan kana da ƙarfi ka ɗauke ni a wuya ka fita dani kuma wlh idan ka ishe ni sai in tashi na fita ƙofar gida ka san ni sarai tijara zan maka nace ka kawoni kwanan gida ka hanani kuɗi na idan ya so sai naga ƙaryar iskanci" ta faɗa tana balla masa harara.

Tsaf ya zuge bakinsa domin baya shakku zata aikata abinda ta faɗa ɗin haka ya wuce yana waigenta tamkar zaiyi kuka ya koma falo ya zauna yana kallon agogo. Har ƙarfe bakwai ta gota bata fito ba ita da tace jirginsu ƙarfe takwas, shahada yayi ya sake komawa ɗakin ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallonta ta tashi tana zaune tsakiyar gadon waya kare a kunnenta.

Murmushi ta sakar masa hakan ya bashi ƙwarin guiwar matsawa kusa da ita, da Mamanta take waya sai bayan ta kammala ta buɗe masa hannu alamar ya zo, haka ya ƙarasa ya rungume ta ta ɗora kanta a ƙirjinsa tana cewa

"Jikina duk yayi tsami kazo kayi mun wanka".
"Jalilah bakwai ta wuce fa kada ki makara" ya faɗa yana ƙoƙarin janyewa sai ta sake shige masa tana cewa
"8pm ne fa flight ɗin ba morning ba". Yanda kasan ya kurma ihu saboda takaici, duk yanda ya so ya cigaba da pretending sai da fuskarsa ta nuna ya zameta daga jikinsa yana cewa

"Amma tsakani da Allah me yasa zaki mun haka?"

Kallon banza ta watsa masa kafin ta miƙe tana banƙarewa ta sigar miƙa ya yi saurin ɗauke idonsa daga kanta, toilet ta wuce abinta tana wata tafiyar iyashege. Ya zauna gefen gadon yana cika yana batsewa a ransa yana ayyana yanda zai yi da ita su rabu ƙalau dan ya lura a shirye take data yanka masa nata rashin mutunchin.

Tashi yayi ya matsa bakin ƙofar toilet ɗin jin tana kiransa, ƙaramin kit ɗin ta tace ta miƙe mata ya wuce ya ɗakko shi yana buɗe ƙofar da niyyar ya bata ta ja shi ciki duk kuma yanda ya so da ya noƙe ko a jikinta sai da ya mata abinda take so kafin ta barshi ya fito tayi wankanta. Haka take kamar mayya in dai ta so abu to fa sai ta same shi ko ta daɗin rai ko aka sin haka.

Falo ya koma ya zauna bayan yayi wanka a ɗayan ɗakin ya dafe kansa da yaji kamar yana so ya masa ciwo. Allah ya sani tun sanda Halima ta bankaɗo sirrin sa komai ya fita a ransa kuma yayi alƙawarin dainawa amma kuma ya rasa yanda zai yi da Jalilah dukda ya fara janye mata kuma lokaci kaɗan yake jira dama wannan tafiyar da zasuyi ce target ɗin sa na ƙarshe da zarar sun shigo da kayyakin an buɗe company zai yi duk mai yuwuwa ayi rubutu ta yanda zai mallaki kaso mai tsoka cikin shares ɗin kamar yanda tayi masa alƙawari idan ya so ko sun rabu ya san ya tsira da abinda zai cigaba da riƙe shi.

Kusan yanzu duk wasu kuɗaɗe da yake da su a hannu sun ƙare sai canji ga hidima kuma a gabansa dan bayan ya gama da Zulaiha yana so ya yiwa Hajja gyaran gida dan har ya saka an fara duba masa gidan haya da zata koma shekara ɗaya kafin a gama aikin gidan sannan idan ya samu yanda yake so duk a shekarar nan yake so ya biya musu shi da ita aikin Hajji. Waɗannan burikan da sauransu ya saka ko ya ji yana so ya kawo ƙarshen mu'amalarsu da Jalilah nan kusa sai ya sake ƙara mata lokaci.

Wayar sa ya zaro daga aljihu, tun daren jiyan ya kasheta saboda kada a samu tsautsayi Zulaiha ta kira shi baya kusa a sake maimaita abinda ya faru tsakaninsa da Halima. Kunna wayar yayi, tana gama booting kuwa messages ɗin Zulaihan biyu suka diro na farko ƙorafi tayi ta kira wayar sa a kashe sai kuma wanda da alama yanzu da safen ta turo tana roƙon idan ya ga saƙon ya kirata ko hankalinta zai kwanta.

Kiranta yayi, ringing biyu ta ɗaga cikin muryar bacci.
"Ban lura na sam a ƙoƙarin na rage volume ashe wayar na kashe gaba ɗaya" ya fada mata bayan da suka gaisa. Motsin buɗe ƙofar da ya ji alamar Jalilah zata fito ya saka shi saurin yi mata sallama dan dama ya ce mata har ya fita office ma yau yana da uzurin sassafe. Sake latse wayar yayi ya kasheta ya turata ƙasan pillow ganin ta nufo shi tana murmushi.

Ya kasa ɗauke idonsa daga kallon adonta, Jalilah ta iya kwalliya duk kuma kamewar namiji in dai ta giftashi sai ya ƙara mata kallo ɗaya, Allah ya mata wannan baiwar ba namiji ba ko mace da wahala ta mata kallo ɗaya ta ɗauke kai dan bayan kyau na zahiri da take dashi tana da kwarjini da jan hankali.

Kan ƙafarta ta zaune tareda saƙale hannayenta a wuyansa babu ɓata lokaci ta haɗe bakinsu guri guda shima kuma bai yi mata musu ba sai da ta sake shi dan kanta kafin ta narke fuska tana shafa cikinta ya fahimci yaren yunwa take ji dan haka ya tashi suka shiga kitchen tana zaune tana masa hira har ya gama haɗa musu abin kari suka dawo falon suka ci.

Bai san me ya saka duk motsin da tayi a falon sai Halima ta faɗo masa ba ko dan gurin ya daɗe babu mace a ciki ne oho?

Zama sukayi ya kunna Tv ta kwanta haɗi da yin matashi da cinyarsa suna kallo abun su yanda kasan wasu sababbin aure, Mamanta ta sake kiranta sai da suka gama magana tayi ɗan danne danne a waya kafin ta kalle shi ta ce

"Wai ina wayarka ne?"
"Tana can ɗaki na" ya bata amsa ba tareda ya kalleta ba, ajiye tata wayar tayi ta gyara kwanciya ta fuskance shi ta ce
"Mom ce ta tura mun da kuɗi yanzu kaima na aika maka da 5m". Yanda kasan wanda ta ce ta xdxdqq ko nawa ne.

Haɗuwar sa da Jalilah ta buɗe masa ido har ya fara raina abinda Hafiz yake masa wanda a baya yake ganin kamar yanke talauchi yake bashi. Ganin fara cire ɗan kunnenta ya saka ya fahimci abinda take nufi, ɗazun ya gama raya ba zai sake biye mata ba amma kuma abinda ta masa dole itama ya bata tukuici me zafi.

Har ta fara cire undies ɗin ta sai kuma ya dakatar da ita ya ce su koma can part ɗin sa. Ashe ƙaddara da rabon ayi ne suke tafe, suna tsaka da masha'arsu yayi nisa gurin yiwa Jalilan abinda ya san zai faranta mata rai yana tsaka da tsotson ƙirjinta kawai yaji ta ce
"Wace ce wannan kuma?" Ya ɗaga kansa yayi mummunan gani Halima tsaye a kansu a wannan lokacin ta kuma same shi cikin yanayin da ko shi yafi kowa iya lauya zance a duniya bai isa ya kare kansa ba.

Da saurin gaske ya tashi zaune tareda jan rigar sa ya jefawa Jalilan akan jikinta, ya sake kallon in da Halima take tsaye saɓanin ɗazu da take kallonsu ta juya baya sai kuma a lokacin ya lura ba ita kaɗai bace harda Mu'azzam.

Kansa ya dafe da hannu biyu a fili ya shiga furta
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shikenan na shiga uku"

"Ka shiga uku da me? Wai su waye ma waɗannan da zasu shigowa mutane kai tsaye haka ba tareda an basu izini ba? Kuma baka rufe gidan ba ko a ciki suke dama?" Jalilah ta faɗa cikin yanayin da babu wata damuwar ko tashin hankalin halin da aka tarar dasu a ciki.

"Halima ce" ya bata amsa yana kallon Halima da Mu'azzam suka bar falon, sai ta taɓe baki irin ko a jikinta ta ce
"Kuma sai ta faɗowa mutane haka nan don tana taƙamar gidan ta ne ko me?"

"Dallah Malama ki rufewa mutane baki, ke wace irin mace ce? Baki ganin abinda kika sakamu a ciki har kina da bakin cewa ta shigo ba izini ke bakiji kunyar abinda ta kamamu muna aikatawa ba ma kenan?" Ya taso mata. Hannu ta ɗaga masa kafin tace

"Ko da wasa kada ka sake tunanin ɗaga mun murya domin ni ba tsarar ka bace, kunya kuma kai ka aikata abin kunya ba ni ba dan kai ta sani" ta ja tsaki kafin ta miƙe ta jefa masa rigarsa daya rufa mata a yanda take ɗin kuma ƙirjinta a buɗen ta fice daga falon.

Kasa motsawa yayi daga in da yake ya dafe kai da hannu biyu ya tafi laluben ya zaiyi? Yau da ace iya Halima ce kaɗai ma zai iya cewa da dama dama domin ya san yanda ta iya riƙe wancan sirrin wannan ma ba zata taɓa tonawa ba amma yanzu harda wannan ƙanin nata da ya fi kowa tsanar sa da tsanar zamansa tareda Halimar.

Wai har tun yaushe ma suka shigo gidan har suka shigo falon bai sani ba? Shi da kunnen sa yake kamar na maciji ko yaya motsi yake zai ji amma ya akayi har aka buɗe gidan aka shigo bai sani ba duk bai ji ba?

"Ta ina zakaji bayan tunaninka da nutuswarka sun yi nisa a cikin aikata saɓon ubangiji?" Zuciyarsa ta tuna sar dashi.

Hannu biyu ya zura yana barbaza gashin kansa a fili cikin sauti kamar zai fasa kuka ya ce
"Na kwafsa, tun farko ma mai ya sa na biyewa Jalilah gashi ta kaini ta baro waya sani ma ko ita ta shirya komai ta kira Haliman?" Shiru yayi saboda tunanin daya ɗarsu a ransa, haka kawai Halima ba zata zo gidan ba ya sani dole wani ne ya gaya mata ko dai Jalilan da kanta ko kuma wani a yan unguwar ya ganshi yayi mata waya ya gaya mata.

Ta shi yayi da sauri ya mayar da rigarsa ya fito dukda bashi da tabbacin sun tafi ko suna nan, cikin sa'a yana buɗe ƙofar kuwa yaga mota a tsaye. Sai da ya tattaro duka ƙarfin halin da yayi masa saura ƙafin ya shiga ƙwanƙwasa window gefen da take zaune.

HALIMA
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 44*

Kafin na kai ga buɗewa Mu'azzam ya ɓalle murfin motar ya fita da sauri, gefe suka matsa, ina kallon su amma ban san mai ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga ya kama baki da hannu biyu cikin alamar ninkuwar tashin hankalin da ya fito dashi akan fuskarsa kafin Mu'azzam ɗin ya nufo mota shi kuma ya biyo shi sai dai bai ko sake kallon sa ba ya shiga motar ya tayar.

Na waiwaya ina kallon Bilal da ya bi motar da kallo cikin tashin hankali kafin na rufe ido na hoton ganin da na musu tar tamkar a lokacin abun yake faruwa take na sake fashewa da kuka har muryata na sarƙewa. Ci kanki Mu'azzam bai ce mun ba sai gudu da yake fellawa a titi kamar zamu bar gari hakan kaɗai kuma ya isa ya sanar mun da ransa a ɓace yake.

Na ɗauka a yanayin da nake zaiyi tunanin mayar da ni gida ne amma akasin haka sai naga ya ɗauki hanyar Jambulo, daƙyar na iya ce masa

"Ka mayar dani gida" ai kuwa kamar yana jira ya taso mun yana cewa
"Iya abinda kika gani yanzu ya isa idan har ba dusace a cikin kanki ba ki gane ya kamata ki nemawa rayuwarki ma'ana ko dan saboda gobenki" ya ja tsaki mai ƙarfi kafin ya mayar da hankalinsa kan tuƙi.

Ban sake cewa komai ba na mayar da kaina tsakanin cinyoyina ina jin wani abu na mun yawo tsakanin maƙoshi ga amai dake taso mun haka kaina yanda kasan ana kiɗan ƙwarya a ciki kai gaba ɗaya duniyar ma juyamun takeyi. Da muka isa ban ko yi yunƙurin motsawa ba dan bana jin akwai sauran ƙarfin da zai iya riƙe ni a tattare da jikina.

Uncle Mudassir ya kira a waya, ban san mai ya ce masa ba ya fita ya shiga gurin shi kaɗai ya ɗan jima kafin suka fito tareda wani mutum babba. Ƙofar ɓangaren da nake ya buɗe na ɗaga kai daƙyar na kalle su, mutumin ya ce
"Subhanallah, mai yasa zaku fito tana jin jiki haka? ai da ya kirani kawai ya gaya mun idan ya so daga baya sai ta zo".

Baki Mu'azzam ya taɓe ya ce
"A hanya rashin lafiyar ta sameta ai"
"Ikon Allah, toh Allah ya bada lafiya amma ya kamata ku wuce asibiti daga nan gaskiya" mutumin ya sake faɗa kafin ya juya ciki tareda Mu'azzam ɗin. Bai jima ba ya fito, a jikina ya watsa mun posting letter da state ID card ɗina suka zube nan ƙasa ban ko bi ta kansu ba nima dan ta kaina nakeyi. Har muka je gidan bai sake ce mun komai ba, sai da ya gama daidaita parking kafin na kalle shi daƙyar hawaye na ziraro mun na ce

"In roƙe ka alfarma?"
"Idan ma ɗaukar ki zaki ce nayi wlh ba zan ba" ya faɗa na girgiza kai lokaci ɗaya ina fashewa da sabon kuka na ce
"Dan girman Allah kada ka faɗawa kowa abinda ya faru".

Buɗe baki yayi yana kallo na cike da mamaki, na kamo hannunsa ina cigaba da kukan na ce
"Dan Allah ka rufa mun asiri, kada ka duba ni ko shi ka duba Al'amin da Sharifa kada ka janyo...." Fizge hannun sa yayi da ƙarfi ya buɗe motar ya fita, ban san ta inda na samu ƙarfin da na fita na bishi da sauri ina kiran sunansa ba amma ko tsayawa bai yi ba. Dab da zan shiga falo na taka step na farko ina ɗaga ƙafa zan taka na biyu juya ta ɗebe ni lokaci ɗaya wani duhu ya mamaye idanuwana ji da ganina suka ɗauke a lokaci ɗaya daga nan ban sake sanin mai ya faru ba kawai na farka na ganni a gadon asibiti.

BILAL
Ya fi minti biyar a tsaye yana kallon hanya dukda tuni motar su ta ɓacewa ganinsa. Yanda kasan wanda yake gaban tandar waina haka zufa take keto masa saboda sabon tashin hankalin da ya riska bayan wanda yake ciki.

"Shawara ɗaya zan baka shine ka fita daga rayuwar yar uwata, idan kuma ba haka ba ka kuka da kanka domin ina da hoto da kuma video abinda muka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login