Showing 120001 words to 123000 words out of 257873 words
yake so, ko da ba zan ɗauki kuɗi na bashi ba yana so na wahalata masa shine farashin soyayya ta a gare shi.
**********************
Daƙyar na iya buɗe ido na da suka mun nauyi dalilin kukan Al'amin da na jiyo. Na yunƙura daƙyar na tashi ina dafe kaina da yake mun ciwo matuƙa. Waya ta na janyo na duba, biyu saura kwata lallai na daɗe a kwance ashe. So nake na fita na ji dalilin kukan nasa tun kafin ya tashi Sharifah wadda a garin lallaɓa ta ne bacci ya kwashe ni nima. Ajiyar zuciya na sauke saboda jiyo muryar Bilal a falon yana tambayar me akayi masa, dukda cikin faɗa da hargagi yake maganar amma shirun da Al'amin ɗin ya yi ya saka na samu nutsuwa har na miƙe daƙyar na shiga banɗaki.
Ina fitowa ya shigo ɗakin yana jan rai kamar numfashin sa zai ɗauke. Na janyo shi jiki na a hankali na ce
"Kasan idan ka bari kukan nan ya fita Dady ya ji muryarka zai dake ka ko? Wai me ma aka yi maka? Wa ya ɗakko ka daga makaranta?" Bai bani amsa ba sai rungumeni da yayi, na ringa shafa bayan sa har saida ya daina ajiyar numfashin bacci ya ɗauke shi daga tsayen da yake kafin na kwantar da shi na zare masa takalman ƙafar sa sannan na miƙe daƙyar ina dafe kaina na fita falo.
Bilal na zaune kan 2 sitter kunnuwan sa saƙale da air pods yana danna wayar dake hannun sa fuskar sa ɗauke da murmushi, lunch box da school bag ɗin Al'amin dake ajiye a ƙasa na ɗauke, motsi na ya saka ya ɗago ido ya kalle ni nayi kamar ban ganshi ba na yi wucewa ta kitchen. Ina jin motsin alamar ya biyo ni nayi maza na kullo kofar kitchen ɗin. Ina jin sa ya zabga tsaki ya ce
"Halima so kike ki ƙure haƙuri na ko? Tun jiya nake binki akan ki zauna muyi magana amma kinƙi wai me yasa kike haka?"
Kwanukan da ban samu na wanke ba na shiga wankewa ba tare da na bi ta kansa ba. Jin har na gama bai fita daga falon yasa na nemi kujera na zauna haɗi da jingina da cabinet dan gaba ɗaya bana jin daɗin jiki na.
Sai da na jiyo kukan Sharifa kafin na fito daga kitchen ɗin na tarar da ita a hannun Bilal yana gani na ya nufo ni yana cewa
"Jikin ta ya yi zafi sosai, kuma kiji numfashinta yanda yake yi". Karɓar ta nayi ta wuce ɗaki ba tare da na amsa shi ba, na sake fitowa na wuce kitchen na ɗakko sauran kunun dana dama mata. Sauran madarar da na ajiye akan dining na nema ban ganta, na ɗaga kai na kalli Bilal dake tsaye shima yana kallo na ya ce
"Am, bari na karɓo a shago nayi amfani da ita". Banza na masa na shiga shayar da ita shi kuma ya fita. Daƙyar take shan nonon saboda hancinta da yake a toshe ta baki take numfashin.
Wata irin mura take yi me zafin gaske. Tunda ya kwashe su ya kai su gidan Hajja ranar Juma'a ko cikakkiyar awa biyu basu yi da tafiya ba sai ganin su na yi jage jage cikin ruwan sama Salima yar Anty Amina ta kawo su wai kuka take tayi shine Hajja ta ce a maido da ita. Tun ranar ta fara mura duk da na basu loratidine da paracetamol, ta Al'amin kwana biyu ta warke ita kuwa kamar ana ƙara murar ga tari da amai dukda na sake kai ta chemist an bata wani maganin amma a banza ganin abun na nema ya wuce hankali ya saka dole na tattara kuɗin dake hannu na na kaita asibiti bayan an yi mata test suka tabbatar mun infection ne, magungunan da aka rubuta mata antibiotics a pharmacy dubu ashirin da huɗu.
Bani da su ba kuma ni da ƙarfin halin da zan kira wani cikin yan uwana na roƙe shi kuɗi a yanzu.
Haka na koma gida na bashi takardar kai tsaye kuma ya ce mun bashi da kuɗi.
"Kina sane kika kaita wannan asibitin ai bayan kin san shegiyar tsada ce da su. Ni bani da wasu kuɗi da zan baki ki siya mata magani yanzu sai dai ki jira zuwa jibi mu gani akwai abinda nake saka rai idan na samu sai a siyo. Banda ma jaye jayen abu normal mura ce fa kin sani amma kinje sai an jawowa yarinya wani ciwon daban" ya faɗa yana danna wayar sa da ta zama abokiyar hirar sa a yanzu ko da yaushe tana hannun sa yana kallo yana murmushi.
Tunda ni na damu da lafiyar ta haka na siyar da zobe na guda ɗaya na siya mata magungunan da abincin ta na yiwa Al'amin shopping ɗin abin tafiya makaranta dan cewa ya yi na ringa zuba masa duk abinda muka karya dashi shi ba ze ɗaukar wa kansa ƙaryar da bazai iya ba.
Dama akan saka shi a makaranta ma sai da raina ya ɓaci cewa ya yi bashi da kuɗi yanzu sai dai a jira zuwa second term.
"Kawai tsurfa ce irin taki, shekara uku ne zaki wani damu a saka shi a makaranta ni banyi lissafi da kuɗin makaranta ba gaskiya a watannan watan da na gaba, sai dai ki jira second term se a kaishi idan kuma na zaki iya jira ba ki saka shi tunda ke kike so" amsar da ya bani a lokacin har kuma aka cinye first term aka shiga hutu bai tayar da maganar ba ƙarshe ni ɗin da na damu ni na nemi kuɗi na kaishi makaranta kuma ya dawo zai yi mun haukan ƙarya akan me zan kaishi ko ce mun ya yi ba zai saka shi? Kuma shi ba wacce na kai shi ya yi niyya ba sai a cire shi a mayar da shi wacce yake so.
Peak ya siyo leda biyu, na haɗa kunun na bata tana gama sha kuma ta koma bacci bayan na bata magungunan ta na zuƙe mata majinar da hanata sukuni lokacin Al'amin ya tashi na masa wanka sannan na zuba masa abinci. Ina zaune ina kallon sa yana cin abincin, a zahiri kallon sa nake yi amma a baɗini nayi nisa cikin tunanin neman hanyar da zan ringa samun kuɗi tunda sune tikitin farin ciki na a cikin gidan. Na sauke ajiyar zuciya jin Al'amin yana girgiza ni, ya gama cin abincin muka tafi kitchen na wanke masa hannu sannan na bashi ruwa ya sha muna fitowa Ummi yarinyar Maman Yusuf da suke tafiya Islamiyya tare ta shigo da suka fita.
Sai lokacin nima na ɗebi abinci kaɗan na ci. A mudubin banɗaki da na shiga alwala na tsaya na ƙarewa kaina kallo, ni dama jiki ba auki ba damuwa duk ta sake tsotseni nayi baƙi kamar mara lafiya. Na ɗauro alwala ina fitowa na ji Bilal yana kirana. Hijab na saka na fita ina ɓata rai ganin Abubakar da wani da ban sani ba ya saka na ɗan saki fuska na zauna kan hannun kujera muka gaisa a gurguje suka tafi.
Ledar dake kan center table ya nuna mun ya ce
"Ga magungunan nan".
"Kai da ka ce baka da kuɗi?" Na faɗa ina tsareshi da ido.
Tsareni yayi da ido shima yana wani murmushi dana tabbatar akwai wata manufa a ƙasan zuciyar sa, na ɗauke kaina gefe saboda bana fatan nan kusa ya ci galaba akaina na sakko, ina fatan ya fahimci fushi na kuma canza zuwa yanda nake fatan ya kasance.
"Na samu na siyo toh. Kina ta fushi wai kina zaton da gangan zan ƙi siya mata magani ne ahalin ina da kuɗin siyan?" Ya faɗa yana wani karya harshe. Tsakin da ban zata ba ya ƙwace mun na miƙe tsaye ina cewa
"Na tabbata ko maganin dubu ɗari ne Nasir ba zai ƙi yi maka lamuni ba, amma saboda baka damu da ta rayu ko ta mutu ba faɗa kayi akan me zan kaita asibitin kuɗi a rubuta mata magani mai tsada. Ni da na haifeta ina son abata kuma na nemi kuɗi tuntuni na siya mata magani dan haka ka mayar ka karɓo kuɗin ka mungode" na wuce ɗaki saboda kukan da ya taho mun. Ina shiga na mayar da ƙofa na rufe na jingina a jiki na fashe da kuka.
Bayan na idar da sallar la'asar ina lazumi na tuna da Oil ɗin da nake mata sirace da shi ya ƙare, goyata na yi na ɗakko jakar da na zuba sauran kuɗin suka ce na ɗauke su in da na ajiye. Sai da na duba duk jakunkunana da inda nake ajiyar kuɗi amma ban gansu ba, na koma na zauna gefen gado na zabga tagumi hawaye suka fara tarar mun a kwarmin ido na. Waye ze ɗauka kuɗin gida daga ni sai yara.
Zuciya ta ta ringa raya mun Bilal ne kawai zai ɗauki kuɗin amma da wacce shaida zan kama shi? Tunda muke bai taɓa ɗaukar mun kuɗi ba ba tare da sanina ba sai dai na ɗauka da hannu na na bashi amma kuma idan ba shi ba waye ya ɗauki kuɗin??
Kuka na zauna na sha na godewa Allah. Yanzu idan na masa magana ko da ace shi ya ɗauka na san tashin hankali zan janyowa kaina da sai na gwammace ban yi maganar ba idan kuma nayi shiru zan cutu dan su kaɗai ne kuɗin da suka rage mun su nake so na lallaɓa a hannu na zuwa wani lokacin.
Kwanciya nayi na cigaba da saƙa da warwarar yanda zan ɓullowa al'amari na, Abban dai bani da kamar sa shi kaɗai ya fahimce ni shi ne kuma ba zai gajiya da ni ba. Tashi nayi na ciro wayata daga caji, sau uku ina danna layin Abba sai na katse dan ban san me zance masa ba.
A tsakanin shekara ɗaya sau biyu ya bani jari wanda da ace da gaske kasuwancin na yi da yanzu sun haɓaka amma muka taru da ni da Bilal muka cinye su. Miliyan ɗaya ya bani da farko akan na je na kama wani abun idan ya ga kamun ludayin sana'ar sai ya ƙara mun wani abu. A raina a lokacin Anty Labiba nayi niyyar bawa kuɗin, tana siyar da kayan kitchen da kayan irin PAT PAT ɗin nan, na san ko a cikin unguwar da nake zanyi cinikin su tunda kusan kowanne gida akwai yara ƙanana tsautsayi farin ciki ya saka na bawa Bilal labari shi kuma ya kawo mun shawarar gwada Exportation.
Kamar yanda ya ce shima yanzu abinda yake so yayi kenan wani abokin sa yana harkar fitar da riɗi da citta. Lissafin da ya mun dukda kuɗin basu da yawa acewar sa a zuwa ɗaya za'a iya samun ribar dubu ɗari biyu zuwa sama kuma a ƙalla duk wata suna tura kaya sau biyu dan haka na bayar da kuɗin ya haɗa da nasa sai mu ringa raba ribar haka na bashi ba tareda nayi shawara da kowa ba har yau kuma babu kuɗin babu riba, da na masa magana bayan an shafe wata biyu bai ce mun komai ba sai cewa yayi wai motar da ta ɗakko kayan daga ƙauyen da aka siyo su yan kidnapping sun ƙwace ta shikenan maganar ta wuce.
Haka na sake komawa a karo na biyu akan a ƙara mun jarin sai Abba ya bani zaɓi saboda ya ce kuɗin da ya ware a lokacin wanda zai biya mun aikin Hajji ne. Idan na yarda ya bani rance a ciki tunda akwai sauran lokaci da Sharaɗin zan maido da su kuma na karɓa tunda na san zance ne kawai yake yi in dai Allah ya nufa tunda yayi niyya zai biya mun na je na san kuma ko da na mayar da kuɗin ba zai karɓa ba. Wannan karon Anty Labiban na bawa aka kawo mun kayan yaran kuma Allah ya buɗa mun kasuwar kafin kace me suka ƙare sai dai kafin na haɗa kuɗin na sake bata a kawo wasu na cinye rabi, da aka sake kawowa dab da sallah ƙarshe ya saka na bawa yaran yayyen sa akan zai siya har yau kuma bai bani kuɗin ba shikenan jarin ya karye ido da kunya kuma na sake komawa.
Sai da Abba ya kira sau biyu kafin nayi ƙarfin halin ɗagawa. Muak gaisa kafin ya ce
"Ina kan hanya ne sai da ma sauka yanzu naga kiran ki, kuma ɗazu na shigo unguwar taku wata gaisuwa kamar na leƙo naga wannan maƙuyaciyar matar tawa da ake mun rowar ta sai kuma na wuce"
"Lah Abba da ka zo ai bata da lafiya ma shiyasa kwana biyu kuka ji mu shiru" na faɗa. Ya tambaye ni mai ya sameta na gaya masa harda sunan magungunan da aka rubuta mata kafin ya mata addu'ar samun sauƙi. Jin yana ƙoƙarin kashe wayar ya saka na ce
"Dama Abba likitan ya rubuta mana wani test ne yace idan ta sha maganin na kwana uku bata samu sauƙi ba muyi kuma yau kwana ukun da sauƙi jikin amma ba yanda na zata ba shine nake tunanin ko zan mayar da ita ayi"
"Ya kamata dai ayi test ɗin na ɗauka ma ai sai da sukayi kafin aka bata maganin, amma dai ba Dr Bashir kuka gani ba dan na san shi baya rubuta magani kai tsaye in dai symptoms yana buƙatar ayi test sai ya tabbatar da abunda yake damun mutum kafin nan" cewar Abba. Shiru nayi ya sake cewa
"Ki tabbata gobe kun koma anyi test ɗin Allah ya sa ba Pneumonia ba ce ba"
"Ai kuɗi ne bani da shi ma shiyasa da yau ɗin zan mayar da ita" nayi ƙarfin halin faɗa. Ya ɗan yi shiru kafin ya ce
"Babanta baya nan ne?"
"Aa yana nan Abba, cewa yayi na bari cikin wanin satin ayi salary tukunna"
"Wace irin magana ce ita rashin lafiyar yarinyar za'a ce a jira har wani lokaci? Zan tura miki kuɗi yanzu ki kama hanya ki mayar da ita Asibiti duk kuma yanda akayi ki sanar da ni" Abban ya faɗa kamar cikin fushi dai dai lokacin Bilal ya shigo ɗakin nayi masa kallo ɗaya na cigaba da yiwa Abba godiya.
"Halimatu" Abba ya sake kira sunana, kafin na amsa ya cigaba da cewa
"Ya kamata kiyi ƙoƙari ki samu certificate ɗin NYSC a nema miki aiki idan ya so ki haɗa da business ɗin gaba daya zai fi, duk da dai na ce ba zan sake magana akan hakan ba amma hakan ya kamata ayi".
"Shikenan Abba zan masa magana duk shawarar da ya yanke sai na faɗa maka" na faɗa murya ta na karyewa, ya ce
"Ba zancen shawara bane Halima umarni nake baki, ya isa haka ya kamata ki san in da kika dosa a rayuwa zuwa yanzu". Haka nan naji zuciya ta ta karye kuka ya taho mun amma na daure na ce
"In sha Allah Abba".
"Ko akwai wata matsala ne Halima?" Na toshe baki na da hannu dan kar sautin kukan da ya taho mun lokaci ɗaya ya isa kunnuwan sa daƙyar na iya saita kaina na ce
"Babu komai Abba, nima dama zama hakan ya isheni dama ina so na fara aikin na haɗa da business ɗin duka"
"Ya dai fi kam, Allah yayi miki albarka ki gaida maigidan naki" ya sake faɗa na amsa da " Amin" kafin na kashe wayar na kife kaina akan pillow na fashe da kukan tausayin kaina.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 31*
Nayi mamakin yanda Bilal bai musa ba lokacin da nayi masa maganar service. Nayi sa'a a lokacin ana dab da fara registration dama, ranar da aka buɗe kuwa banyi wasa ba na je na yi a matsayin mara aure saboda ko da na gaya masan ya ce toh nayi zaton zai je ya fitar da certificate of marriage da domicile letter waɗanda zan buƙata amma har ranar ta zo bai ce mun komai ba nima kuma banyi masa magana ba dan ina gudun kada ya canza ra'ayi.
Posting ya fito aka kaini, ban wani damu ba tunda ba nesa bane nasan zan iya zuwa nayi registration a ranar na dawo ba daga nan na nemi relocation dan ba zai yuwu nayi service ɗin a can ba. Sai ana gobe shiga camp ɗin sannan na faɗa masa Jigawa fa aka turani kuma gobe zan je.
"To me kike so na ce yanzu? Ai ba yau kika san Jigawa aka kaiki ba ko da yake yanzu sai kin gama yanke shawarar ki kike gaya mun kinga wata magana tawa bata da amfani sai ki je ai" amsar da ya bani kenan. Washe gari kuwa na kama hanyar Jigawa da sassafe, saboda ban san sanda zan dawo ba Al'amin bai je makaranta ba na kaishi gidan Mama. Cikin sa'a dake ranar farko ce kuwa kafin ƙarfe uku na gama komai na karɓi exit, a Kano shida ta mun dan ma mota ta ɗan tsaya mana a hanya na wuce gida kawai ba tare da na ɗakko Al'amin ba dan na gaji kuma goben Juma'a ce ya ƙara hutawa Monday sai ya koma makarantar.
Ina tayar da sallar magriba wayata ta fara ƙara, yanda kira ya ringa shigowa daga wani ya katse ya ɗaga mun hankali, daƙyar na kammala ina yin sallama na ɗauki wayar gaba na ya yanke ya faɗi ganin Bilal ne. Ina shirin bin bayan kiran wani ya sake shigowa na ɗaga, cikin muryar dake nuna yana cikin tashin hankali ya ce
"Halima kina ina?"
"Ina gida na dawo mai ya faru?" Na faɗa cikin sauri.
"Hajja ce sukayi accident gamu nan a Emergency na Aminu Kano" ya faɗa lokaci ɗaya kuma ya kashe wayar.
A fili na shiga nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Hajja kuma