Showing 165001 words to 168000 words out of 257873 words

Chapter 56 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

496

ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 42*

A yayinda muke shirin kammala wannan littafi idan har kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina 🙏🏽🙏🏽


Cike da ƙaguwa da zancen ya ce
"Yanzu dai Umma wanne ake so a ciki? Lefen ko kuma kuɗin za'a bayar ko ayi mata kayan yanda tace?"

"To ai ni ba na ce ba, kaga ita Nuratu dai kayan tace tana so to ita ya kamata ka tambaya itama kaji wanne tafi so" ta bashi amsa sai ya girgiza kai ya ce
"Ai na gaya miki yanda mukayi da ita, dama kuma ni na ɗauka ma kunyi shawarane shiyasa ban tuntuɓe ki ba dan har na bayar da aikinma, kawai ki faɗi wanda za'ayi a ciki tunda kince tariyar Nuratu nan da sati biyu kamata yayi duka a haɗa ai ba wai ayi daban daban ba"

"Toh inaga a bayar da kuɗin ko dan naji Nuratu nata ƙorafi kayan duk masu duhu aka aka saka mata inaga ya manta bai faɗawa musu haɗo kayan baƙa bace" ta faɗa tana yar dariya, wayarsa ya zaro yana cewa
"Toh idan akwai account ɗin wanda za'a turawa kuɗin a kusa a kawo idan babu kuma sai ta tura mun in fara saka mata wani abu kafin ƙarshen sati na cika dan na rigada na bayar da kuɗin kayan Wallahi yanzu kuma ko nace musu na fasa ba zasu dawowa mun da kuɗin ba sai dai na nemi wani ya siya tunda kamfani ne"

"Ai ka tura mata a Opay ɗin ta kawai tunda tareda Habiba ƙanwata zasuje kasuwar dama" cewar Umman, sai yayi murmushi yace
"Ai kuɗin da yaww Umma idan aka saka mata a opay rufewa zasuyi account ɗin nata ba zai ɗauki kuɗi da yawa ba"
"Ai kuwa yana ɗauka kwanaki can naji tace anyi buɗa mata shi har maliyoyi ma za'a iya sakawa a ciki yanzu amma bari dai tazo muji kar ayi gwari" Umman ta sake faɗa kafin ta shiga ƙwalawa Zulaiha dake laɓe tsakar gida duk tana sauraronsu kira. Sum sum ta shigo ta tsugunna daga bakin ƙofa, Umman ta ce

"Wai akawun ɗinki nace kamar naji kwanaki kince an buɗa miki shi zai iya ɗaukar kuɗi da yawa?" Da kai ta amsa ganin Bilal ɗin yana kallonta, danne danne yayi a waya ya ɗago ya cewa Umman
"Na tura da miliyan biyu, idan na samu yanda nake so zuwa ƙarshen sati zan ƙara mata miliyan ɗaya idan kuma bata samu ba zan saka ɗari biyar amma fa duka da kuɗin lefe dana sallamar amarya". Yanda kasan Umman zata kwanta tsabar murna ne ko meye oho haka ta baza hijabi ta shiga masa godiya ƙarshe ta fashe da kuka tana jera masa addu'a. Sai da ya sake ajiye mata cash na dubu ashirin daya ruƙo dama zai mata ihisani kafin suka fita tareda Zulaiha zata rakashi.

Rungumeta yayi da suka isa soro ta janye tana wani ɓata fuska, bai haƙura ba ya sake kamota yana dariya ta kuma janyewa tana cewa
"Ni dai bana so ni da kacewa yar iska daga gwada abinda aka ce idan ina maka zaka ƙara so na"
Ya ruƙo hannunta ya ce
"Banda sharri mana baby a yaushe nace miki haka? Kuma ai gaskiya aka faɗa idan kina mun hakan zan ƙara sonki kawai na jiye miki tsoro ne kar na kasa riƙe kaina na haɗa Umma da gashin amarya" ya ƙarasa yana kashe mata ido ɗaya, rufe fuska tayi da hijabinta cikin jin kunya tana dariya ya saketa yayi waje tabi bayansa, sai da suka isa gurin mota ta sake haɗe fuska. Da mamaki yace

"Wai menene haka kuma? Minti kaɗan kina fara'a anjima ki haɗe rai ko dai dagaske ne da Umma tace tana zargin iskoki suna taɓa ki?"
Baki ta tunzura tace
"Ni ba wasu iskoki kaine kayi mun laifi" sai ya tattara hankalinsa kanta ya ce
"Ni kuma? Yaushe?"

Bubbuga ƙafa ta shigayi kamar yarinya tana cewa
"Ba kaine kawai ka tashi ka haɗa kuɗin kayan lefe da na sallamar amarya ba? Yanzu wlh sai iya abinda suka ga sama suka bani ni dai da kayi shawara dani Allah ba haka za'ayi ba".

Ajiyar zuciya ya sauke dan ji yayi hankalinsa ya tashi da tace wai ya mat laifi, shi fa baya son ɓacin ranta Allah ma ya sani. Hannayenta ya kamo cikin kwantar da murya ya ce
"Shikenan kuma sai ki ɗaga mun hankali kice wai nayi miki laifi akan ɗan wannan maganar?"
"Oh yar magana ce ma a gurinka kenan?" Ta faɗa tana taɓe baki kamar me Shirin yin kuka. Zagaywa yayi da ita ya buɗe mata sit ɗin mai zaman banza kafin ya dawo ya shiga driver sit ya tayar da motar suka fita daga layin. Gadon ƙaya sukaje ya siyo mata shawarmar daya san tana so a hanya suka sasanta bayan da suka daddale akan sai dai fa ya bayar da 3M ɗin nan idan ya so ta ɗauki 500k na hidimarta dan ta san duk kashe kuɗin zasuyi ba za'a bata komai ba. Sauketa yayi ya juya yana tafe a ransa yana mamakin dama Zulaiha ta san kuɗi haka?

A sanin sa da ita ko kyautar 20k ya mata a dunƙule sai tace sunyi yawa ya rage shiyasa idan ya tashi kawai yake siya mata duk wani abu da yasan zata siya da kuɗi idan ya bata idan ta kama zai bata kuɗin kuma baya wuce 5k tunda tun tana 200L ya samar mata mai Adaidaita da yake kaita makaranta ya kuma ɗakko kuma yana saka mata Airtime da Data kusan duk sati dan haka ba wani abu zatayi da kuɗi ba amma ita ce yau suke ja'inja har tana cewa 500k ɗin ma manaji zatayi dan ba isarta zatayi ba. Kamar ya biya gidan Hajja sai kuma ya fasa dan ɗazu da safe da yaje ko arziƙin amsa sallamar sa ba tayi ba daga ƙarshe ma ɗaki ta shige ta barshi fushi take bilhaƙƙi dashi amma ya san zata sakko nan ba da daɗewa ba dan Hajjan bata iya dogon fushi dashi.

Halima ta faɗo masa a rai yayi ƙaramin tsaki a fili, idan so samu ne ta dawo kafin Zulaiha ta tare amma kuma yaga tana nema ta kawo masa wasa itama sannan ga Hajja yanda take akan tsini yanzu bata huce daga wannan fushin ba amma kuma gara tayi lokaci ɗaya ta gama a wuce gurin tunda dai gaskiya a wannan karon sai dai tayi haƙuri amma ba zai iya sakin Halima ba ya san kuma har a gurin Allah baiyi laifi ba tunda dai Haliman nan babu abinda tayi mata. Shi yanzu duk kewar yaransa ce ma take addabarsa dan tun ranar daya kaisu gidan bai sake ganinsu ba, Al'amin ma a bakin malamin makarantarsu yaji wai anzo an karɓar masa transfer sai ƙarya ya gilla masa ya ce eh ya koma can gidan kakanninsa ne da zama.

Daya isa gida falon Halima ya shiga, gurin tsaf tamkar tana ciki dan duk bayan kwana biyu sai ya share ya goge ko ina ya kuma kunna turaren wuta dake winduna a rufe suke kuma babu zurga zurga sai turaren ya sake kama gurin sosai. Ɗakinsa na nan ya shiga ya cire bedsheet ɗin kan Gadon ya canza wani dan yau ɗin kawai yaji a nan yake son kwanciya, wanka ya shiga yana Allah Allah ya fito ya kirata yana wankan yana shirya maganganun da zai faɗa mata a ransa, yana jiyo wayarsa na ƙara ya san ba zai wuce Zulaiha ce take kira ba, sai da ya gama shiryawa kafin ya ɗauki wayar ya tarar da missed calls uku na Zulaiha ɗaya sai na Jalilah guda biyu.

Murmushi yayi yabi bayan kiran Jalilan, dole ce kawai zata raba shi da ita ba dan yana so ba amma Jalilan hannunsa ce ta kowanne ɓangare kuma da ce yana da tabbacin shi kaɗai take kulawa da zai iya danne zuciyarsa ya aureta dukda ya san ba zai taɓa samun nutsuwa ba saboda kullum zuciyarsa zata ringa saƙa masa ko da auren nasa zata iya bin wani a waje amma kuma wasu ɓangarorin da yake morarta ya saka yake jin kamar zai iya haƙuri ya zauna da ita a hakan.

Muryar da take masa magana kaɗai a yan sakanni take hargitsa masa lissafi balle aje ga sauran lamura daga Haliman balle Zulaiha da take nan bagidajiya (a ganinsa 🤣🤣🤣) babu wacce ta kamo ƙafarta a iya kyau, iya kwalliya, gayu uwa uba kuma iya kula da namiji ta wannan fannin kam dole ma a karya mata ɗan kwali. Yana can zancen zuci ta ɗaga wayar tana ta Hello Hello harta gaji ta kashe ta kira ya zare wayar da sauri daga kunnensa saboda ƙara.

"Ina ka shige duk yau baka kirani ba" ta faɗa bayan daya amsa wayar. Kwanciya yayi akan gado ya kashe murya shima ya ce
"Kema baki kira ni ba"
"Yaushe muka fara haka? Idan ban kiraka ba kenan ba zaka kirani ba kake nufi?" Ta faɗa sai ya tashi zaune dan yaji sautin muryarta ba yanda ya zata ba ya kuma san halin kayarsa idan tana sama abu kaɗan zai tuzurata shi da yake so ya karɓi kuɗaɗe a hannunta kuma ina zai bari suyi faɗa?

Cikin kwantar da murya ya ce
"Ba haka nake nufi ba honey tsokanarki naso nayi ban san kuma baki cikin yanayi me daɗi ba, yanzu dai mai ya samu baby na?" Ya ƙarasa cikin sautin da ya san zai iya samun kanta. Tayi ƙaramin tsaki ta ce
"Ban san me yake damunka kwana biyu ba Bee kawai shiru nakeyi amma gaba ɗaya ka canza, kayi cancelling tafiyarka a die minute sannan kana sane yau ya kamata na tafi amma baka ko kirani ba balle kaji yaya nake ciki anya kuwa babu wani abu da kake ɓoye mun?"

Sai da yaji hanjin cikin sa ya kaɗa, duk ƙoƙarin da yakeyi na kada ya kuskure har ya bada ƙofar da zata zargi wani shiri ashe ya bar baya ba zani, da sauri ya ce
"Kiyi haƙuri Honey pot kin san na gaya miki yanda nake ciki da gurin aiki na gaba ɗaya sun taso ni a gaba gashi gida ma duk sai a hankali na gaya miki Halima ta tayar da rigima tunda taga chat ɗin mu yanzu haka ma kusan 1 week fa tana gidansu kin san mutanen mu kuma family kowa ya ɗora mun laifi ana ta cewa na fara wulaƙantata saboda zan kawo wata".

Tsaki ta sakeyi kafin tace
"Ta hutar da kanta ai sai ka aika mata da takardarta kawai dan dama ko bata tafi yanzu ba zata tafi idan na zo dan ka san dai ba zan zauna da kishiya ba"

"Amma Babe munyi maganar nan kin ce kin haƙura ke da ba gidan ku ɗaya ba dan Allah menene damuwar ki da ita kuma?" Ya faɗa kamar zai yi kuka, daga can tace
"Babu dole fa Bee, idan ita ka zaɓa sai kuyi zamanku ai ba cewa nayi ka saki matarka dole ka aureni ba. Ni dan Allah duk ba wannan ba kazo ka ɗauke ni, kawai sai yau Salis ya sake tura mun da flight ticket ɗin wai ashe ta Kano ya mun booking na zo kuma anyi shifting flight ɗin sai 8 na safe, duk raina a ɓace yake wlh kazo ka ɗauke ni na samu nayi wanka ko zan ɗan samu nutsuwa".

Idan da ya san dalilin kiran kenan da ba abinda zai zaka yabi bayan kiranta kai da kashe wayarsa ma zaiyi gaba ɗaya. A hankali ya ce
"Ayya sorry Babe shine baki kirani tun ɗazu ba kuma?"
"Ai gashi yanzu na kiraka dan Allah idan ba zaka zo ba na nemi taxi zaka cikani da surutunka da baya ƙarewa" ta faɗa a hasale. Kamar ya ce ta nemi taxi ɗin sai dai ya ce

"Toh mai zai hana ki kama lodge mana anan kawai tunda da safe ne kar kuma kiyi nisa sosai"
"Tun yaushe ka fara shirya mun abinda ya kamata nayi da wanda ba zanyi ba Bilal?" Ta faɗa kamar wata uwarsa, da sauri ya ce
"Kiyi haƙuri gani nan zuwa" tayi tsaki ta kashe wayar.

Tashi yayi ransa duk ba daɗi, kamar ya kirata yace ta hau taxi kawai sai dai kuma baya so ya ɓata rawarsa da tsalla gara dai su rabu lafiya idan buƙatarsa ta gama cika daga nan shima zai buɗe mata shafin nasa rashin mutunchin. Haka nan badan ya so ba ya kama hanyar Airport ɗin sha ɗaya harta gota bai yi nisa ba sai ga kiran Hafiz, sai da ya gangare gefen titi ya kashe motar kafin ya amsa cikin muryar bacci.

"Afuwan na tashe ka daga bacci" Hafiz ɗin ya faɗa, ya sake maƙale murya ya ce
"Ina zaune ne banma san baccin ya ɗauke ni ba". Daga can Hafiz ɗin ya ce
"Dama Jalilah ce ta shigo Kano, ka santa da hayyata ta kirani wai anyi shifting flight ɗin ta zuwa safiya in samo mata mai Taxi da na sani dare yayi tana jin tsoro ita bata san Kano sosai ba shine na kiraka ko zaka ma Abokinka me Uber ɗin nan magana idan bai tashi ba dan Allah yaje ya ɗauke ta ya sama mata hotel nan kusa da Airport ɗin".

"Wai Ammar? Ai ya samu aiki Lagos yana can kusan wata shida kenan ya dena Uber, amma bari akwai wani da ya ɗauke ni kwanaki nay saving number sa kuma ɗan nan kusa damu ne bari naji idan bai tashi ba ka tura mun number ta" cewar Bilal ɗin, yana aje wayar kuwa Hafiz ɗin ya turo masa number ya wani taɓe baki bayan daya kunna motar ya cigaba da tafiya. Rai ɓace ta zauna a motar bayan daya isa, haɗe fuska yayi shima yana kallonta ya ce

"Na ce miki ina hanya shine kuma kika wani kira Hafiz ya nemo miki Taxi ko?"
Harara ta balla masa tace
"Ai naga alamar wuyanka ya fara kauri ne har in ce kazo ka ɗauke ni ka ce wani na kwana a nan shiyasa na kirashi dan nasan ƙarshe kai ɗin dai zai turo ka ɗauke ni". Kallonta kawai yayi kafin ya ɗauke kai gefe yayi ƙwafa sannan ya ce

"Yanzu ina zan kaiki?"
"Gida na" ta bashi amsa tana danna kiran layin Hafiz. Fuzge wayar yayi da sauri ya katse kafin ya ce
"Me zaki gaya masa kuma?"
"Zan gaya masa kazo ne mana" ta bashi amsa tana karɓar wayar, ya zare ido ya ce
"Kinyi hauka amma? Karfe sha biyun zaki ce masa nazo ɗaukar ki me kike so yayi tunani?"
"Oho" ta bashi amsa kafin ya sake magana yaji muryar Hafiz ɗin a speaker yana cewa

"Jalilah sa'arki ɗaya matata bata gari amma ko dan gaba kada ki sake mun irin haka ya zaki ringa kirana tsakiyar dare?"
"Allah ya baka haƙuri dama ce maka zanyi me Taxi ɗin ya zo"
"Shikenan mu kwana lafiya ki kula da kanki" ya bata amsa bai jira tace wani abu ba ya katse kiran.

Bilal dake kallonta ya sauke ajiyar zuciya jin bata ambaci sunansa ba can cikin ransa kuma kishi ne ya taso masa jin yanda take yiwa Hafiz ɗin magana a nutse cikin ladabi kamar me tsoron sa shi kuma yana wani bata amsa a tsaye, ɗauke kai yayi ganin ta juyo ta kalle shi ta ɗan yi murmushi ta ce
"Akan Hafiz har Malamai na shiga amma shegen guy ɗin nan yanda kasan aljani na kasa samunsa"

"Bafa zan ɗauki wannan wulaƙancin ba ta yaya a gabana zaki ringa gaya mun kina son wani daban a hakan kike so na aureki?" Ya taso mata, wani shegen kallo ta masa tace
"In aureka dai, ai nice mijin kaine matar ko kai a haka da kake kana zaton ka isa ka aureni?
Banda ma so banzan abu ne Bee ai ka san ni ba tsararka bace ko shi ubangidan naka nafi ƙarfinsa kawai dai zuciya da baka da iko da ita tayi ta kwaso maka tarkace tana saka ka son su" ta ƙarasa tana soka earpiece a kunneta. Ya kusa minti biyar yana kallonta yama rasa mai zaiyi ko mai zaice, tunda yake ba'a taɓa masa zagi irin wanan ba, wato shine tarkace? Lallai Jalilah taga gadon baccin sa.

Haɗiye zuciya yayi ya tada motar, sai da suka fita daga Airport ɗin kafin a ƙufule ya sake tambayarta in da zai kaita
"Nace maka gidana ko kunnuwanka sun toshe ne kuma baka ji da kyau?" Ta bashi amsa, wlh ba dan ba sai ya gaggaya mata maganganu kuma ta fice masa a mota amma kuma yanzun dai bai isa ba amma lokaci na zuwa, daya tuna abinda ya shuka dole ya sauke fushi ya gyara murya ya ce

"Kin manta ana aiki a gidan ne?"
"Aikin da akeyi a waje meya shafi ciki kuma ina kace an gama fentin cikin tun last week?" Ta tambaya tana tsare shi da ido, titi ya mayar da idonsa kafin ya ce
"An gama amma ai kin san an kwashe kayan ni kuma da naji kince sababbi za'a zuba shiyasa ba'a mayar ba dan wasu abubuwan ma na kyautar dasu"
"Su kuma kayana ka kaimun su ina?" Ta faɗa tana tsare shi da ido, kashe mata ido ɗaya yayi ya ce

"Na kaiwa Matata ta ringa sakawa kinga se na ringa ganinta kamar ke"
"Har ta mutu ba zatayi kyauna ba" ta faɗa tana juya ido, ya ruƙo hannunta yace
"Ni shaida ne yar balarabiyata, yanzu dai ina zamuje kinga idanuwanki sun nuna a gajiye kike ki samu ki huta kar kiyi missing flight kuma goben"
"Muje gidanka toh tunda kace can babu gurin kwanciya" ta faɗa tana kallonsa.

"Gida na kuma?" Ya faɗa da sauri har yana sakin stirring, ta taɓe baki tace
"Eh mana ko ba zaka kaini ba?"
"Zan so in kaiki mana amma kin manta na gaya miki matar gidan bata nan kuma kinga dai unguwarmu ba kamar in da can gidan yake bane akwai yan sa ido yanzu a ganni na shiga gida da Mace ai na shiga uku a garin nan bama unguwar ba"

"Ai kuwa ko dubu zaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login