Showing 51001 words to 54000 words out of 257873 words
try harda ruwa na wuce ɗakin nasa. Ban same shi a falo ba, se na aje kayan na wuce cikin ɗakin ƙarar saukar ruwa da kayan daya cire dake kan gado yasa na gane wanka yake yi dan haka na koma falon na zauna. Kusan minti goma ya fito ya shirya cikin jallabiyya yana ta zuba ƙamshi. Bilal ba dai tsafta da gayu ba, komai sanyi ko ruwa baze kwanta ba tare da yayi wanka ba. Na kan tuna Anty Labiba da take cewa duk buge ne gayun nasa waya sani ma ko tsaka tsami yakeyi ya fesa turare gashi dana zauna dashi na tabbatar da tsaftar tasa ta gaske ce in dai ɓangaren tsafta ne na sarawa Bilal abinda kuma yake ƙarawa abin armashi bashi da son jiki. Yanda baya son ƙazanta baya taɓa bari in da yake wani abu ya kasance da datti ba kuma ya jiran wani ya masa da ya ga guri be masa yanda yake so ba ze tashi ya gyara.
Kamar ma be lura da ni ba ya zauna kan kujera yana wani cin magani, nayi murmushi na matsa in da na ajiye kayan abincin ina cewa
"Ga abinci". Ban damu da shirun da yayi ba dan idan ba ze ci ba nasan ze ce Aa, na buɗe miyar na tura masa try ɗin gaban sa, kwanon miyar ya ɗauka ya kalla kafin ya watsa mun wani kallo yana cewa
"Shikenan naman da yayi saura?"
"Pieces biyu ya rage na saka maka ɗaya na aje ɗaya zan ci da safe" na bashi amsa ina tsiyaya masa shayi a kofi. Ko da ban ɗaga kai na kalle shi ba jiki na ya bani kallo na yake yi ko ma na ce harara ta. Ina jin sa yayi ƙwafa, se lokacin na ɗaga kai na kalle shi duk kuma yanda naso da in share kar na tanka masa na kasa, tsautsayi yasa na furta
"Ko in ɗakko maka ne naji kaja ƙwafa karma naci nayi amai tunda ba'a bani ba".
Ban san Bilal ya ƙware a iya sharri ba se da ya dire kwanon miyar hannun sa ya miƙe tsaye yana nuna kansa yace
"Ni kika cewa maye Halima?"
Ban san sanda na miƙe ba nima na dafe ƙirji tare da fito da idanu nace
"Yaushe? Ni nace maka maye Bilal a ina mukayi haka?"
Be amsa mun ba illah kallo na da yakeyi kamar me neman gurin da ze fi masa sauƙin hallaka ni a jiki na kafin ya juya ya shige ɗaki yana cewa nanata
"Ni kika cewa maye ko? Zaki san ni kika alaƙanta da maita Halima". Gaba ɗaya se hankali na ya dugunzuma, babu alamar cewa wasa yakeyi akan fuskar sa ko furucin sa duk ma ba wannan ba tsakani da Allah a yaushe na alaƙan ta shi da maita? Idan ma kuma nayi hakan ai ya sani wasa ne be kamata ace ya fusata ba balle ma kuma duk yanda nake wasa da koma wane akwai irin kalaman da bana taɓa kuskuren furta su.
Bin bayan sa nayi, yana kwance kan gado ya daga kansa da hannayen sa biyu yana kallon ceiling na shiga da ƙaramar sallama kamar mara gaskiya. Daga bakin gadon na tsugunna kaina a ƙasa na rasa me zance masa. In dai ba dama da wani abu a ran Bilal ba be kamata ace ɗan ƙaramin abu haka ya kawo yamutsi a cikin daren nan ba. Murya ba amo na kira sunan sa, be amsa ba na sake maimaitawa har sau uku still yayi banza da ni se kawai na kife kaina a kan gadon na fashe da kukan ƙarya, Anty Labiba tana gaya mun da yawan maza basa son kuka kuma yana daga cikin abin da yafi saurin karya lagon su yawancin maza basa iya jure ganin matar su tana kuka ko da kuwa ace na rashin gaskiya ne. Na rigada nasan ni nawa kukan bashi da tasiri a gurin Bilal gwaji kawai na sakeyi ko Allah ze saka yau hakan yayi tasiri ilai kuwa se ji nayi ya ja tsaki me ƙarfi da har se da na dakata daga dramar da nakeyi, ina kallon sa ya fice daga ɗakin da bargo a hannun sa ya barni a durƙushe ban san lokacin da kukan gaske ya ƙwace mun ba.
Wace irin rayuwa ce haka ace abinda be taka kara ya karya bane ze ringa zama na tashin hankali a gurin Bilal? Sannan wannan halin ko in kular da yake gwada mun idan yana cikin fushi ban taɓa hasashen fuskantar sa daga gurin sa ba. Baya cikin alƙawarin daya ɗaukar mun. Ya gaya mun gidan sa ze zame mun dausayi ne na farin ciki ba akasin haka ba, shikenan nan da laifi na da ba nawa ba se dai shi yayi fushi na bishi da rarrashi ni baze taɓa dubana ya fahimci tawa damuwar ya kwantar mun da hankali ba?"
Ban san tsawon lokacin dana ɗauka ina kukan ba har bacci ya kwashe ni a gurin. Mun yi dashi akan washe garin gidan mu zan tafi na wuni dan haka ko da na tashi naga be sauka daga fushin sa ba ban damu sosai ba tun da gidan zan bari naje in da zan samu farin ciki na gabatar da shagalin sallah ta cikin nutsuwa. Ni kam idin farko a gidan Habibi ya zo mun da mishkila. Ruwan shayi kawai na tun da akwai sauran sinasir muna kuma d bread. A yanda yake a 360 ɗin nan nasan idan na dafa wani abun zamu sake haurawa ne ban ma kuma ji sha'awar cin komai ɗin ba dan haka kafin ƙarfe goma na gama shiri na tsaf. Ban zaci ze ci abin karin dana ajiye masa ba se da na fito naga ya cinye harda sauran kazar dana ɗumama na aje masa da wadda beci ba jiyan da wadda na aje wa kaina, na tattare kwanukan na ɗauraye, a waya na kira shi bayan dana duba babu mashin ɗin sa, se da na masa missed calls uku be amsa ba na huɗun na shiga yayi rejecting se ga text message ya biyo baya yana tambayata menene baze iya amsa waya a in da yake ba?
Sanar masa nayi da na shirya zan tafi gida ya maido mun amsa da
"Ban yarda ba". Na nanata karan ta rubutun yafi sau uku kafin na ajiye wayar lokaci ɗaya hawaye ya cika mun ido. Idan nace zan kira Mama a waya na gaya mata na fasa zuwa nasan kukan da nake dannewa ze fi ƙarfi na dan haka na tura mata da text kawai ina ƙoƙarin kashe wayata dan karma ta kirani kuwa se ga kiran Abba dole na amsa bayan mun gaisa yake tambaya me yasa bazan zo ba? Se da ma toshe baki na dan kar kuka ya ƙwace mun kafin na sharara musu ƙaryar ciki na ne ya kama ciwo. Murya cike da alhini ya shiga tambayar me ya same ni? Munje asibiti toh? Nace masa nasha magani kawai se ya bawa Mama wayar dake nayi mata ƙorafin ciwon mara da nake yawan yi se tace mun na kwanta na huta ƙila aikin da nayi jiya ne na jijjiga jiki na idan kuma ciwon ya wuce misali to mu tafi asibi kawai nace mata irin wanda na sabayi ne kuma nasha maganin da aka bani. Suka ringa jera mun sannu, har mun kashe waya ta sake kira tace ga Amirah nan zasu zo su taya ni zama toh ko da zan buƙaci wani abu.
Sosai nayi kuka, sallah guda yayi mun wannan rashin mutunchin ya hanani zuwa gidan mu bayan duk sun saka ran zan je. Gurin sha biyu su Amirah suka zo, Mu'azzam ne ya kawo su amma be shigo ba ya wuce. Mama ta haɗo su da abinci shinkafa da tuwo se miya stew da Amirah tace yanzu Maman tayi mun ga soyayyen nama na sa da na kaji tuli harda zoɓo da kunun aya Abba kuma ya basu dubu goma a envelope su kawo mun barka da sallah. Ban san sanda na fashe da kuka ba. Ranar wunin ɗaki nayi se dai bini bini Amirah ta leƙa ta tambaye ni ko akwai abin da nake so? Da Abubakar ƙanin Bilal suka zo ma ce mata nayi kawai ta zuba musu abinci tace musu bacci nake yi. Dab da magriba Mu'azzam yazo ɗaukar su har sannan kuma banga idon Bilal ba. Bayan na rakasu na dawo na kwanta a falo sun gyara mun ko ina har abincin da zamu ci da daren ta zuba a kuloli ta ajiye sauran kuma nace su bawa almajirai abin da ze ajiyu kuma ta saka mun a fridge. Ina kwance wayata tayi ƙara, na zata Bilal ne se da na ɗaga ta naga Anty Labiba ce.
Yau ɗin har gidan ta naso naje, ina jin muryar ta bayan dana amsa wayar kawai kuka ya ƙwace mun. Tayi shiru kusan minti biyar ina mata kukan kafin tace mun
"Menene?"
Zuciya ta tana raya mun na gaya mata abin da nake ta dakon sa a zuciya ta ni kaɗai se dai ɗaya ɓangaren na gargaɗi na da kar nayi hakan. Zata mun dariya tace dama se da ta faɗa be zama lallai ma ta fahimci damuwata har ra bani mafita ba kawai zata fassara abun ne da hasashen ta na farko akan Bilal, wannan tunanin yasa na fasa faɗa mata ainihin abin da nayi niyya kawai nace mata bani da lafiya ne.
"Kuma saboda baki sa lafiya se ki ringa irin wannan kukan Halima? Baki san shi kansa kukan bashi da kyau ga me ciki ba so kike ki saka abin da yake cikin ki a damuwa shima? Bana son sakarci, ya kamata dai yanzu ace kin girma tunda nan da ɗan lokaci uwa kike shirin zama kina wa yar rashin lafiya kuka yanzu idan ranar haihuwa tazo kuma se yaya kenan?" Ta faɗa. Se na tsagaita da kukan taci gaba da cewa
"Yanzu da su Amir suka dawo yace mun baki da lafiya, toh kun je asibiti dai ko?"
"Eh mun je ba wani abu bane dama marata ce kawai take ciwo kuma nasha magani ta rage" na bata amsa, se ta ɗan yi shiru kamar bata yarda ba kafin tace
"Shikenan Allah ya ƙara lafiya. Ki ringa kula da kanki duk abin da kika san ze jigata ki kar kiyi, na ma yiwa Mama magana tuntuni ko za'a sama miki me aiki tace a bari tunda baki nema ba amma ya kamata gaskiya saboda ba laifi aikin gidan naki da ɗan yawa kuma yanzu hutu kike buƙata musamman tunda cikin yazo miki da ciwon mara".
"Aa fa yau ne kawai shima nasan saboda aikin da nayi jiya ne amma ba wani abu nake yi da yawa ba duk su shara da mopping shi yakeyi da kansa" na faɗa dan na taɓa yiwa Bilal zancen yar aiki yace baya so, yanzu idan ta kawo ta ya koreta sabuwar gaba ce zata ƙullu tsakanin su. Shiru ta sake yi kafin tace
"Shikenan, Allah y sauwaƙe ya bata lafiya me amfani" daga haka mukayi sallama. Jin an fara kiran sallah yasa na koma ɗaki nayi, se da na idar da isha'i na sake fitowa har sannan kuma Bilal be dawo ba. Ina tsaka da cin abincin dana saka kaɗan naji ana buga get. Bilal ya fita da key dan haka nasan bashi bane, nayi mamakin ganin Anty Labiba da Uncle Saleh bayan dana buɗe ƙofar, ban san sanda na rungume ta ina dariya ba. Rabon ta da gidan tun ranar da aka kawo mun gara, Uncle Saleh be shiga ba a wajen muka gaisa yace ze je ya dawo muka shiga tare da Anty. Na rasa me ma zan bata, har ga Allah naji daɗin zuwan ta over ma. Ganin ina ta kwaso ruwa da lemo na kinkimo kular abinci yasa ta dakatar dani tana cewa
"Ke bafa zama zanyi ba. Nan bayan ku zamu je gaisuwa gidan wani abokin sa maman sa ta rasu a UK suke to sunyi waya yace yazo Kano amma gobe ze wuce Abuja shine muka taho yanzu fa se da muka kuje kuma ashe shi kaɗai ne yazo banda matar sa, naga zasu ɓata lokaci da hira shine fa nace ya kawo ni nan na dubaki kafin su gama mu wuce, su Halima matar Bilal, irin wannan mulmul da kika yi lallai Bilal ya iya kiwo" ta ƙarasa tana kallo na. Na rufe fuska cikin jin kunya ina cewa
"Kai Anty, kamar kin shekara baki ganni ba"
"A shekarar kaɗan ne babu ai, haɗuwa tayi wuya se dai mu gamu a hanya nan kuma ai ba wani ganin ki nakeyi sosai ba kamar yanzu ko?" Ta faɗa, nasan magana ta gaya mun dan haka nayi murmushi kawai na shiga tambayar ta su Inayah.
"Dama suna gidan Mama ɗazu shine su Amirah basu taho da su ba?" Na faɗa, se tace
"Aa, se gobe zamu je. Amir ne kawai yaje su je kallon hawa tare da su Mu'azzam". Hira muka shiga yi gwanin daɗi, har tara da rabi sannan Uncle Saleh ya kirata yace gashi nan ya taho. Se sannan ta tambaye ni Bilal, tambayar da nake ta addu'ar kar Allah ya buɗi bakinta ta mun dan ban san me zan ce mata ba sanin tun kafin muyi aure da Bilal duk wanda ya sanshi ze bada shaidar baya yawon dare. Duk in da akayi sallar isha'i ya shiga gida in dai ba guri na ze je ba.
Ce mata nayi yana can gidan su ai be jima da fita ba suka zo, kallon da ta mun yasa na fahimci bata kama zancen ba. Ta ƙare mun kallo tace
"Wannan kayan ma tun na kwalliyar safe ne da kikayi baki sake wasu ba". Zan kwaso rantsuwa ta dakatar dani tace
"Idan kika zauna shashanci kanki zakiwa sagegeduwa. Ba yanzu zaki takaicin barin sa ya koyi yawon dare ba se nan gaba dan haka tun lokaci be ƙure miki ba ki gyara. Duk irin hirar da zeje yayi a wajen ki tanade ta ki ringa yi masa a gida ya fiye miki alkhairi idan ba haka ba ke kika sani kina zaune can wasu zasu ringa cusa masa wasu ra'ayoyi na banza a lalata miki miji".
Tunani maganar ta ta jefa ni, anya babu saka hannun abokai cikin baƙin halayen Bilal da nake cin karo dasu? Waya sani kam ko a yawon da yake tafiya ake yo masa wasu karatu na banza suna gurbata masa tunani dan dai ni shaida ce ba haka Bilal ɗin dana sani yake ba tabbas. Buɗe ƙofar da akayi ya dawo dani daga tunanin da na tafi. Muka haɗa ido da Bilal ya galla mun harara ba tare da yayi ko da sallama ba ya wuce kitchen yana sakin ƙaramin tsaki. Se da naji ina ma da damar da ƙasa zata tsage na shige ciki na ɓuya ko kuma ace abin da ya farun yanzu mafarki ne zan tashi naga zuwan Anty Labiba be faru ba. Kamar me ciwon wuya daƙyar na waiga na kalli Anty Labiba dake danna wayarta se ka rantse bata ji shigowar Bilal ɗin ba. Nayi ƙasa da kai kamar munafuka ina jan yatsun hannu na, daga kitchen ɗin ya ƙwalo mun kira. Ƙafafu na sun yi sanyin da bazan iya miƙewa ba, sake kiran yayi se lokacin Anty Labiba ta ɗaga kai ta kalle ni tace
"Ba kiran ki yake yi ba?"
Ina zaton baƙuwar muryar da yaji se gashi ya fito kamar an jefo shi, yayi turus a bakin ƙofa yana raba ido kafin yayi ƙasa da kai yana shafa ƙeya kamar mara gaskiya lokaci ɗaya ya lalubo murmushi ya ɗora a fuskar sa ya nufo in da muke yana cewa
"Kune a gidan namu yau Anty"
"Mun same mu lafiya? Ya sallah?" Ta faɗa tana miƙewa saboda wayar ta data ɗauki ƙarar shigowar kira. Bata amsa gaisuwar da ya shiga yi mata ba ta nufi ƙofa tana ce mun
"Allah ya ƙara sauƙi Halima na wuce se da safe" ta fice daga falon. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na bi bayan ta. Yanzu Allah kaɗai yasan tunanin da zata yi kuma. Dubu goma Uncle Saleh ya bani barka da sallah, Anty Labiba dai tunda ta zauna a motar ko kallo na bata sake yi ba yaja suka tafi.
A kan kujera na tarar da Bilal ya dafe kai da hannu biyu yana jin motsi na ya miƙe fuska ba yabo ba fallasa yana kallo na yace
"Me yasa baki kira ni kin ce mun ta zo ba?"
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*Page 13*
Kasaƙe nayi ina kallon sa har ya fice daga kitchen ɗin lokaci ɗaya jiki na yayi sanyi lanƙwas kamar an watsa mun ruwan sanyi. A hankali na ajiye bowl ɗin hannu na na dafe drawer baya na da hannu biyu jin jiri na neman ɗiba ta. "Sam wannan ba Bilal bane, ba halin sa bane akwai wani abu da yake damun sa tabbas" abin da na furta a fili kenan cikin son ƙarfafawa kaina guiwa da kuma bawa kaina tabbacin ba cikin sani Bilal yayi mun wannan tozarcin ba. Nafi minti biyar kafin na tattara ƙarfin daya rage mun na bi bayansa zuciyata na ƙarfafa ni da naje naji me ya same shi? A bakin ƙofar ɗakin na ci burki na kasa shiga saboda yanda zuciya ta take bugawa fat fat. Ba zan iya jurewa ya sake gaya mun wasu maganganun ba zuciya ta zata iya bugawa amma kuma ina da buƙatar sanin me yake damun sa? Waye ya tunzuro shi haka ko ma im ce wasu shaiɗanu ne suka shafe shi?.
Ina kama hannun ƙofar aka buɗe daga ciki, mukayi ido huɗu ya jefe ni