Showing 159001 words to 162000 words out of 257873 words
yake turo mun sunfi kama da wanda yake jaddada mun cewar ya san ba zan iya rayuwa babu shi ba dan haka dole nayi haƙuri na koma masa kuma ko kusa bai ma nemi cewar na bashi dama mu zauna ko zai wanke kansa ba aa kawai cewa yakeyi nazo mu koma gida tabbacin ko a jikinsa ma shi ya manta da duk abinda ya faru.
Ba tareda kowa ya bani shawara ba na yankewa kaina shawarar ɗibar masa lokaci, zanyi ta jansa in ga iya gudun ruwansa. Shin zai fahimci kuskuren sa ya biyo ta sigar daya kamata ko kuwa zai cigaba da yi mun kallon ba zan iya rayuwa babu shi bane?
Na kwanaki huɗuya jera kullum yaje gidanmu daga zarar kuma yayi mun kira ɗaya ba zan bari yayi na biyu ba zan kashe wayar. Na zuba ido naga gudun ruwansa tunda har aka kwana huɗun dai salo ɗaya yake maimaitawa na kirana haɗi da tura mun text yana tunasar dani yanda yake a raina ba wai yanda ni nake a nasa ran ba in dubi wannan nazo mu koma gida. Nasan Mama ta san yana zuwa amma ko da wasa ɓata ce mun komai ba nima kuma ban ce mata ba a haka muka kwana huɗun a yini na biyar shiru tun Magriba nake tsammacin naga kiransa amma har sha biyun dare ta gota shiru babu shi babu labarinsa tils na cire rai sai kuma damuwa da ƙuncin da ban tsammata ba suka lulluɓe ni.
Washe gari haka na tashi sam babu walwala ba fara'a, komai ma baya mun daɗi dan ko abinci ɗan kaɗan na tsakura na ture saboda yanda nakejin komai yana mun ɗaci a bakina. Bini bini zan ɗauki waya in duba ko zan ga saƙon sa ko makamancin haka amma shiru har azahar tayi, bayan na idar da sallah ina zaune kan sallaya ina lazumi wayata ta shiga ƙara, tun da gari ya waye ko message bai shigo mun ba ina jin ƙarar wayar kuwa na zabura zuciyata tana raya mun Bilal ne dai dai lokacin kuma Mama ta shigo ɗakin. Wayar na duba ganin baƙuwar number ya saka zumuɗi na raguwa dukda haka bam cire tsammanin shi bane sai bayan dana kai wayar kunnena bayan na amsa naji murya daban ba tashi ba.
Zare wayar nayi na kashe ba tareda na amsa sallamar da wanda ya kira yayi ba, na saci kallon Mama jin tana cewa
"Iska dai tana wahalar da mai kayan kara" kafin tayi ƙaramin tsaki ta nufi ƙofa tana cewa
"Ga Mudassir can a falo yana jiranki". Jiki ba ƙwari na biyo bayanta, bayan mun gaisa da Uncle Mudassir ya tambayeni jiki na ya ce
"Na ɗauka kin karɓo posting letter ki Halima tuntuni ashe baki je ba". Ɗan ya mutsa fuska nayi na ce
"Uncle ba fa ni da lafiya, kuma ni ban ma san an fito daga camp ɗin ba". Daƙuwa yayi mun yana cewa
"Dan gidanku ni kike gayawa baki da lafiya tun yaushe kika samu sauƙi yau kwananki nawa da aka sallamoki daga Asibiti? Naga alamar har yanzu baki san inda yake miki ciwo ba Halima, satinki nawa a gidan nan? Ke ko ji bakiyi zaman ya isheki ba kina buƙatar samun abun da zai ɗebe miki kewa ko kuwa dai saboda kanki aka fara mutuwar aure shikenan sai ki zauna ki lalata rayuwarki a banza ba zaki gyara gobenki ba?"
Da sauri na kalle shi jin abinda ya faɗa na ce
"Ni fa Uncle aure na bai mutu ba". Ina kallo Mama ta jijjiga kai irin na zallar takaici shi kuma ya ce
"Oh har kina da bakin cewa aurenki bai mutu ba? Toh zaman uban me takeyi kusan wata biyu a gida?" Ya ƙarasa yana kallon Mama. Hannu biyu ta watsa ta ce
"Gaka gata ƙila kai tunda tana ganin kanka da gashi ta gaya maka zaman me takeyi tunda mu da ta raina ba yanda bamuyi ta girma da laluma ta faɗa mana mai ya faru ta taho gidan ba amma tace babu komai"
"Aa wannan kuma laifinku ne Anty, ai ƙarya ne wlh yarinya ta taho gida sama da wata ba wani ƙwaƙƙwaran dalili ni duk ɗauka ta ya saketa ne kuma abinda yasa kika ga ban ko yi miki maganar ba saboda naga babu amfani ne ko yanzun LGI ɗin ne ya kirani dan tuni an turo da relocation list har anyi posting nasu dake nayi masa maganar ta da in da nake so a kaita ya kirani akan bafa ta je ba har yanzu shiyasa ma kika ganni yanzu. Kuma shi Yaya Aminun ya zuba muku ido take ta zama bai ce komai ba?"
"Toh mai zai ce Mudan? Ita me auren an tambayeta tace babu komai shi kuma bai biyo baya ba haka babu wani nasa da yazo toh ta ina zamu san meya faru?" Mama ta sake faɗa, ni dai kaina yana ƙasa ina jinza ya kira sunana na sake sadda kai ƙasa sai da ya buga mun tsawa kafin na ɗago da sauri ya nuna ni yana cewa
"Kar kiga kin girma ko kin haihu wlh dukan tsiya zan miki Halima kuma banga uban da zai ce dan me ya saka ba, tun muna shaida juna dake ki faɗa mun mai ya saka kika taho gida yanzu ba sai anjima ba". Kuka na fashe dashi bayan da naja baya daga kusa dashi dan na san dukan daya ambata zai mun tsaf zai aikata dan zuciya ce dashi kamar kuturu duk cikin ƙannen su Mama yafi su zafi ba kuma ya wasa damu dama shiyasa muke shakkar sa sosai. Tsawa ya sake bugamun bayan daya miƙe tsaye da alama neman madoki yakeyi, dai dai nan Anty Labiba da Mama Fauziyya sukayi sallama da gudu kuwa na nufi Mama Fauziyya na rungume ta ina sake fashewa da kuka ta ɓoye ni a bayanta tana tambayar mai ya faru nan kuwa ya fara zazzaga faɗa akan me zan zo gida tsayin lokacin nan na sakina akayi ba kuma naƙi faɗar zuwan me nayi wlh zai mun dukan tsiya idan ban buɗe baki nayi magana ba.
"Kai daɗi na da kai saurin hasala Mudassir banda haka duk maganar ai bata wuce ayita a zaune ba" Mama Fauziyya ta faɗa, Mama ta ce
"Ai kuwa magana ta wuce ta sulhu dan tuntuni nake bin yarinyar nan akan ta faɗa mun mai ya faru tun hankalina yana tashe da lamarin har na haƙura na fawwalawa Allah tunda naga alamar zan ɗorawa kaina damuwa ne a banza alhalin wacce nakeyi akanta ita bata damu ba toh wlh nima yanzu na gaji, cikin biyu dole ayi ɗaya. Ko dai idan sakinta yayi ta faɗa mu san zaman me takeyi ko kuma ta tattara ta koma amma na gaji da zama da ita a haka kullum ina kallonta ina jin ɓacin rai".
"Hmmm mu dai anayi muna jin daɗi" Anty Labiba ta faɗa tana zama akan kujera irin ba abinda ya shafeta ɗin nan, banda kuka ba abinda nakeyi, sai da Uncle Mudassir ya mun tatas kafin ya tafi akan kada na kuskura ya sakw dawowa bai tarar da ɗayan biyu ba, ko dai in koma ko kuma ya samu tabbacin zaman yanci nakeyi. Ba abinda ya sake ɗaga mun hankali irin yanda Mama take nanata ita ta gaji Mama Fauziyyar da take kareni sai in tattara na bita amma ba zata cigaba da zama dani alhalin bata san ina ma saka gaba ba. Duk sai suka sake jagula mun lissafi ga danuwar da na tashi da ita ga kuma wata sabuwa data ɓullo na ringa jin inama ban biyewa huɗubar Hansa'u ba na saurari Bilal ƙila da na bashi dama zai zayyana mun nadamar sa ya kuma nemi yafiyar tawa idan yaso sai in yanke hukuncin da nake ganin ya fi mun yanzu gashi nan a garin jan aji ya tsinke gidan ma kuma zasu tasoni a gaba in rasa ina zan tsoma raina.
Ɗaki na koma na cigaba da kuka sai da nayi mai isata kafin na haƙura na wanko fuskata na koma na zaune bayan na ɗauki wayata zuciyata na ayyana mun na kirashi, tarin missed calls na gani da number da aka kirani da ita ɗazu zai text guda ɗaya,
"Hafiz ne abokin Mijinki Bilal, idan kin samu lokaci ki kirani akwai abinda nake so mu tattauna" abinda saƙon ya ƙunsa kenan. Na natata karanta saƙon yafi sau biyar a raina ina mamakin wace magana ce Hafiz zai tattauna dani kuma mai muhimmanci kamar yanda ya ce?
Tunani na shigayi a zuwan Matarsa ko akwai wani abu dana faɗa mata da bai kamata taji ba amma ban tuna ba, ajiye wayar nayi kawai ba tareda na kira shi ɗin ba kamar yanda ya buƙata dan ni banga dalilin hakan ba. Bacci ne ya kwashe ni ina tsaka da tunanin neman mafita, sanda na farka gari har yayi duhu alamar magriba ma ta wuce na ringa salati in mamakin wane irin bacci nayi haka tun azahar kuma ace babu wanda ya tashe ni da akayi la'asar da ga magriba ma lallai dagaske da Mama tace ta gaji da zamana ba wasa takeyi ba tunda gashi ko a jikinta bata ma ko yi tunanin mutuwa nayi ba ba wanda ya leƙo ni. Hawaye suka ɓalle mun ina wanka ina kuka har na gama sannan nayo alwala ina jin cikina kamar zai haɗe da bayana tsabar yanda yunwa ta gama rarakeni, daƙyar nayi sallolin da suka wuce ni kafin na fito kai tsaye na faɗa kitchen neman abinda zanci.
Mama da Zainab na aikin ƙarasa abincin dare ko kallo na batayi ba sai Zainace ta ce
"Kin tashi Yaya Halima? Tun ɗazu nake leƙo ki naga kina jin daɗin baccin shiyasa ban tashe ki ba". Ban amsa ta ba na ɗebi abinda na gani na fita, bayan mun gama ci tareda Sharifa ina shirin na koma ɗaki tun kafin Mama ta fito falon Mu'azzam ya shigo, ba yabo ba fallasa ya ce mun
"Kina da baƙo yana falon Abba".
Kallon za nayi kafin cikin ɗaga murya na ce
"Wane irin hauka ne haka ni zaka cewa ina da baƙo ko ka manta matar aure ce ni?"
"Wai matar aure" ya faɗa yana nuna ni kafin ya tuntsure da dariya harda buga ƙafa ya wuce yana cewa
"Idan zaki tashi kije Malama ki wuce kar ki ɓata masa lokaci".
Miƙewa nayi da zummar na bishi in ji ba'asin akan me da mutunchi na da kuma aure na har wani zai zo gurina a shigo dashi har falo saiga Abban ya shigo, ba yabo ba fallasa shima ya kalleni ya ce
"Ibrahim bai gaya miki kina sa baƙo ba ne?"
"Abba ya za'ayi da aure na ace wai wani yazo gurina in fita?" Na faɗa ina rau rau da ido kamar zan fasa kuka, sama sama yace
"Bana son sakarci Halima ki wuce kuma tun kafin ranki ya ɓaci". Sum sum na wuce domin na fi kowa sanin fushi ba ɗabi'ar Abba bace har kuma idan ransa ya ɓaci to fa baya yi da sauƙi.
Turus nayi a bakin ƙofa ganin baƙon, Hafiz ne abokin Bilal. Na ƙarasa ciki da ƙaramar sallama na samu kujera can nesa na zauna kafin ma shiga gaishe shi ya amsa cikin kulawa yana tambayata yara na gaya masa Al'amin yana can gidan Anty Labiba Sharifa kuma tana ciki.
"Kiyi haƙuri Halima kin ganni ba tareda kinyi mun izini ba, na yi ta jiran martaninki toh amma gaskiya ina da ɗan uzuri ne wanda kuma ina son mu tattauna kafin na wuce dan ban san ko har zan dawo ba tareda lokacin buƙatar hakan ya wuce ba" ya faɗa, ni dai kaina yana ƙasa ya cigaba da cewa
"Kiyi haƙuri Halima, na san zaki iya cewa menene nawa da shiga cikin maganarki da Bilal amma ki sani ina da dalilin yin hakan, na san kin fi kowa sanin kusancin da yake tsakanina da Bilal. Allah ne ya haɗa jinina da shi kuma Allah shine shaida ina jin sa a raina tamkar wanda alaƙar jini ta haɗa mu shiyasa ban taɓa ƙyashin nayi masa wani abu ba, a zaman da nayi da Bilal na karanci wasu halayensa waɗanda na ɗauka a matsayin tawaya da kowanne ɗan adam yake dashi dole idan ya zamo ya cika ta wani ɓangaren ta wani gefen kuma za'a same shi da kuskure dan haka na karɓe shi a yanda yake ina kuma yi masa uzuri a duk in da ya kuskure domin nima na sani dole akwai ta inda nake da giɓi sai dai ko kusa ban taɓa tsammanin Bilal zai aikata irin abin nan ba.
Kiyi haƙuri Halima ni ne silar da har Bilal ya san Jalilah sai dai bani da wata masaniya ta ƙulluwar wata alaƙa a tsakanin su domin daga shi har ita sun rufeni akan haka. Jalilah Ex ɗina ce kuma dalilin da ya kawo ruɗani tsakaninki da Bilal shine silar rabuwar mu da ita har na fasa aurenta bayan har an yi mana baiko. Yanda kike son Bilal haka Jalilah take so na, albarkacin wannan soyayyar ta saka kuma duk yanda na so na yakice ta daga rayuwata taƙi fita na raga mata har muka cigaba da mu'amalar gaisawa.
Ban ɓoyewa Bilal komai akan Jalilah ba tun a sanda ya fara ganinta har yake tuhunata akan me yasa naƙi aurenta bayan a nasa ganin tafi Suhaila komai na ya mace, na ɗauka abinda na gaya masa akanta zai saka ya hankalta dukda ban taɓa kawo cewar wata mu'amala zata iya shiga tsakaninsu ba sai dai abin takaici hakan ya faru kuma ya rufeni har ta kai a silar ta yana shirin rusa rayuwarsa ta hanyar rabuwa da abubuwa masu muhimmanci ciki harda ke da kuma aikin sa.
Bazan cika ki da surutu ba amma Halima ina so ki san da cewa duk wani abu da kike tunani akan Bilal da Jalilah na sani, na daɗe ina masa addu'ar gane gaskiya tun kafin ubangiji ya kawo irin wannan lokacin da asirinsa zai fasu, kada kiyi tunanin shirun da kikayi yana nufin kin rufa masa asiri domin shi da kansa ya ɗaurawa kansa ƙararrawar da zata yayata sirrinsa har ya isa ga kunnuwan kowa. Jalilah ba zata taɓa yarda da cin amanar da yayi mata ba bayan ta gama ɓata lokacinta ta kuma kashe kuɗinta akansa da tunanin zai aureta sannan ya zagaya yayi amfani da kuɗin ta ya auri wata hakan ba zai taɓa yuwuwa ace ta ƙyale shi ba".
Kusan daga iya in da na dena fahimtar duk wasu maganganu daya cigaba da faɗa kenan, da farko na cika da mamakin yanda yace ya san komai dake tsakanin Bilal da Jalilah sai kuma maganar da na tsinta ta ƙarshe ta goge mun hadda ta kuma jefani a ɗimuwa ko in ce gushewar hankali na wucin gadi cewar da yayi Bilal yayi amfani da kuɗin Jalila ya auro wata?
Har idan dagaske ta silar sa Bilal ya san Jalilah kenan sai bayan ya aureni hakan ta faru tunda ina gidan Bilal suka haɗu da Hafiz hakan yana nufin bani ce wacce aka auro da kuɗin Jalilah ba kenan to me yake nufi? Aure Bilal ya ƙara ko me?
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 41*
A yayinda muke shirin kammala wannan littafi, idan kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina. Account details suna sama 🙏🏽🙏🏽
A hankali na buɗe ido na jin saukar abu mai sanyi a goshi na, ganin na buɗe idon ya saka Mama janye hannunta, ganin da tayi ina shirin sake komawa baccin ya saka ta ce
"Da dai kin tashi haka nan kuma ki ƙarfafa jikinki tunda dai zazzaɓin ya sauka". Na yunƙura na zauna ina cije baki saboda kaina daya sara, dukda zazzaɓin da rafke ni ya sauka amma har yanzun bana jin ƙwarin jikina. Banɗaki ta shiga bata jima ba ta fito tana cewa
"Ga ruwa can na tara miki kiyi wankan Zainab zata kawo miki abinci" daga haka ta juya ta fita na rakata da ido ƙauna da kuma tausayinta suna sake ratsani. Allah sarki iyaye masu daɗi duk inda akaje aka dawo su ɗin dai ko sun yi fushi a hakan zasuyi haƙuri su karɓe ka. Jiya ta gama nanata ta gaji da zaman da nake gabanta amma hankalinta yafi na kowa tashi da yanayin da na shigo gidan bayan da na baro Hafiz.
Na runtse ido na saboda yanda tuna Hafiz ɗin ya dawo mun da zantukansa da sukayi matuƙar kiɗimani haɗi da hargitsamun tunani, hawaye suka ɓalle mun, dukda har yanzun na kasa gasgata maganarsa wai Bilal yayi aure amma tunanin hakan kaɗai da nakeyi ace da gaske ne ji nake zuciyata kamar zata ƙone saboda zafin da takeyi mun, ba zan taɓa iya jurar ganin wannan baƙin cikin ba wata mace a rayuwar Bilal sai kawai na haɗe kai da guiwa tareda fashewa da kuka mai sauti harda shassheƙa.
Ƙarar ruwa dake ta zuba ya saka na tashi daƙyar bayan da na haɗiye kukan nayo wanka haɗi da alwala na fito, kan gado na sake komawa na zauna, gaba ɗaya komai ya sake jagulemun na sake komawa yanayin da nasha wahala kafin na samu kaina daga cikin sa. Saƙe saƙe kala kala zuciya ta ringa kawo mun, daga ƙarshe na yaƙi kaina ta hanyar tashi na ɗora dogon hijabi kan towel ɗin dake ɗaure jikina na shiga jera nafila duk da cewar bayan la'asar ne magriba ma ta gabato lokacin.
Bayan sallar isha'i ina kwance a ƙasa, duk yanda naso na mayar da hankali na kan lazumin da nakeyi na kasa gaba ɗaya tunani na ya tafi akan son sanin haƙiƙanin gaskiyar abinda Hafiz ya faɗa mun. Idan har da gasken ne Bilal yayi aure toh wa ya aura? Ko Jalilan da suka gama