Showing 240001 words to 243000 words out of 257873 words
shi a masifa? Ni wlh tun ganina da ita dama hankali na bai kwanta ba, kawai dan shi ɗin yace ba komai ne amma dama matan Habuja tun duniya na kwance ma makiraine, mutanen da suke kashe mazajensu dan suci dukiya balle kuma yanzu da duniya ta tashi tsaye makirci ai sai wanda aka gani ni dai Allah ya isa tsakanina da ita wlh" Hajja ta sake faɗa cikin kuka.
"Daga baya kenan, yanzu dai ki gwada duka layukansa da kike dasu ki faɗa masa ya dawo ayi komai a mutunche idan kuma ya zaɓi asirinsa ya tonu kowa ya san halin da ake ciki shikenan" Abubakar ya faɗa yana ficewa.
Anty Amina ce ta shiga kiran wayar Bilal amma layukansa biyu da take da duk aka ce a kashe suke, ta kalli Hajja dake sharɓar kuka kamar yar yarinya tace
"Hajja baki da wani layin nasa ni na kira wanda nake dasu duka a kashe"
"Guda biyu ne MTN da Airtel nima su ɗin ne" ta bata amsa tana fyace majina. Anty Habiba ce tace
"Toh kin tambayi ita matar tasa ko ta san inda ya tafi?"
"Tace dai bata sani ba amma ban sani ba ko ƙarya takeyi" Hajja ta bata amsa dai-dai nan Abubakar ya dawo falon ya zauna yana cewa
"Kun same shi?"
"Aa duka layukansa a kashe suke" Anty Amina ta bashi amsa a sanyaye, ya ce
"Ku kira Anty Halima ko zaku samu wata number".
Su ukun suka haɗa baki gurin cewa
"Halima?"
"Eh, akwai wani layi da ya ɗan yi amfani dashi can da daɗewa, na duba shi naga banyi saving ba amma ƙila a samu a gurinta ita" ya sake faɗa.
"Ga matarsa wacce Halima za'a samu number sa a gurinta?" Anty Habiba ta faɗa, ya kalleta ya ce
"Kada kiyi mamakin ta san inda yake yanzu haka"
"Sai ta yuwu dan zata rufa masa asiri ko mutum ya kashe" Hajja ta faɗa a sanyaye, ya miƙe yana cewa
"Kuma da Kinsan da haka kika goya masa baya ya rabu da ita, matar da duniya ma ta shaida abokiyar rufin asirice. Ai dai wlh ya tafka asara, gashi nan ya ƙare da yan balaja'u a gida da waje".
"Ni dai ba zan kirata ba wlh" Anty Amina tayi saurin faɗa ganin Hajja na kallonta, sai ta ɗauki wayarta tana cewa
"Buɗo mun lambar ni na kira".
HALIMA
Ajiye cokalin hannuna nayi ina ɓata fuska nace
"Ni dai ka daina kallona idan ba so kakeyi na ƙware ba"
Ɓata fuska yayi ya ce
"Na gaya miki ba zan iya daina kallonki ba Leemah". Sai da na lumshe ido kafin na buɗe su akansa ina cewa
"Toh na ƙoshi" yayi saurin tashi daga kan kujerar sa ya nufo ni yana cewa
"Ai kuwa baki isa ba, harfa kakarin amai kikeyi saboda yunwa kuma ko spoons biyar bakiyi ba kice kin ƙoshi? Ashe zan yi miki ɗura kuwa" ya ƙarasa yana naɗe sleeve ɗin farar rigar jikinsa. Ji nayi kamar in tashi na taka rawa amma na kanne na ɓata fuska nace
"Allah Uncle Salman na ƙoshi, ka fa bani tea ko ka manta?"
Ƙarar da wayata dake aje kan table tayi ya saka duk muka kalli gurin, sunan Hajja na gani yana yawo, na ɗago wayar ina buɗe ido dan na tabbatar da ita ɗin ce ko kuma idanuwane suke gizo? Ganin kiran na neman katsewa ba tareda na amsa ba Dr Salman dake tsaye kaina ya zare wayar daga hannuna ya amsa tareda sakata a speaker.
Muryar Hajja ta cika kunnuwanmu ta rafka sallama kafin tace
"Hello Halima kina ji na?"
"Ina jin ki Hajja ina wuni?*" Na faɗa bayan dana amsa mata sallamar, ta amsa da
"Lafiya lau, ya su Aminu da Sharifa? Duk suna lafiya ko?"
Sai naji wani banbarakwai, ashe sun san da yayansu a hannuna? Shiru nayi ban amsa mata ba ta cigaba da cewa
"Dama lambar Bilal nake so ki tura mun, banda Mtn ɗin sa da Airtel idan kina da wata daban su duk ba'a samunsa a su"
"Ai ni banida kowacce number sa ma yanzu Hajja" na bata amsa a dake, tayi shiru kafin tace
"Abubakar yace ba zaki rasa ba, ki taimaka wata matsala ce ta taso kuma ana ta nemansa a waya ba'a samunsa idan kuma kin san inda yake kawai ki faɗa mana aje a same shi"
Na saci kallon Dr Salman daya koma kujerarsa ya kafeni da ƙananun idanuwansa kamar farin shigar maita kafin nayi ƙasa da kai nace
"Sai dai ki kira Yaya Nasir ba zai rasa sanin inda yake ba ko ya baku number" sai tayi jumm kafin tace
"Shikenan, kya gaida Mamarku sai anjima" daga haka ta katse wayar.
"Tashi mu tafi toh" Dr Salman ya faɗa yana miƙewa tsaye. Na kalleshi, fuskarsa ta canza, yar fara'ar da yakeyi tunda na shiga office ɗin duk ta gudu ya dawo boss ɗin sa ga ƙananun idanuwan sun sake ƙanƙancewa. Ganin banida niyyar tashi ya saka ya wuce yana cewa
"Ki sameni a mota" ya fita ya barni.
Kada wadda ta tambayeni mai yake faruwa ko yaushe aka fara? Nima ban sani ba kuma daga nan zamu tashi 😂😂😂😂
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*Zanyi amfani da damar nan in roƙe ku, Dan girman Allah kada wacce ta haɗa mun Document. Ban taɓa yin Allah ya isa ba ko wata mummunar addu'a akan fitar mun da rubutu ba tareda izinina ba amma Allah ya sani ba zan yafewa duk wacce ta haɗa mun Document ba. Dukkanmu musulmi ne mun kuma san girman haƙƙi dan haka mu kiyaye.*
*PAGE 59 (SECOND TO THE LAST PAGE)
Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace
"Ina kika tafi tun ɗazu?"
Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa
"Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita.
A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce
"Get in".
"Amma cewa nayi ki sameni a mota ko?" Ya faɗa bayan dana zauna, na kalli gefe na ce
"Ni fa gaskiya bana son abunda kakeyi, yanzu wane kallo kake so a ringa yi mun kawai a wani ringa ganinmu tare?"
"Ko?" Ya faɗa yana ɗage gira ɗaya, na tura baki cike da shagwaɓar dana daɗe da daina yinta tun lokacin da Bilal yace haushi nake bashi idan ina abu kamar wata sakaltacciyar yarinyar idan ma kuma nayi ko a jikinsa, sai yanzu da naga alamar idan nayi zan samu kulawa na ɓata fuska na ce
"Ni dai dan Allah ya zama sirri bana so kowa ya sani"
"Hakan yana nufin kin amsa tayi na kenan?" Ya faɗa yana mun wani kallo da najishi har cikin jini da ɓargona. Nayi ƙasa da kai ina sakin murmushi ba tareda nace komai ba,
"Leemahh.." ya kira na ɗaga kai kamar mai ciwon wuya na saci kallonsa, yanda ya kwanta cikin kujera yana mun wani lalataccen kallo ya saka nayi saurin sauke kaina ƙasa ya sake maimaita kiran sunan da sautin daya fi na farko taushi kafin ya ce
"Kin karɓi soyayyata dagaske?"
Na sanya tafukan hannayena biyu na rufe fuska ina sakin murmushi kamar wata wawuya, ina jin nasa sautin murmushin kafin ya tayar da mota muka bar gurin. Har muka isa gida babu wanda ya sake cewa komai a tsakaninmu, lokaci-lokaci muna haɗa ido tareda sakarwa juna murmushi. A hankali na ce
"Gobe bani da aiki" ina ƙoƙarin buɗe motar amma najita a kulle, ganin kuma bai yi yunƙurin buɗewa ba ya saka na koma na zauna ina kallonsa.
"Wanene Bilal?" Ya faɗa ba tareda ya kalleni ba, nayi shiru ina kallonsa, ganin ya juyo ya sa nayi saurin sauke kai ƙasa ina jin idanuwansa na yawo a kaina. Kusan minti uku bai sake cewa komai ba alamar amsata yake jira kafin a hankali nace
"Babansu Al'amin ne".
Wani shirun ya sakw ratsawa kafin ya mula yace
"Ina da kishi sosai Leemah, bana tunanin akwai wani abu da yayi saura a tsakaninku; idan ma kuma akwai ina so ki gaggauta datse shi ko kuma ni ki datse ni"
Da sauri na kalleshi jin abinda ya faɗa, ya mun kallon dake tabbatar da gaskiyar maganarsa kafin ya cigaba da cewa
"Har idan mahaifiyarsa zata kiraki tana tambayarsa kenan kuna tare"
"Wlh bama tare, ni rabona dashi tun ranar daya sakeni ko yanzun ban san dalilin daya saka ta kirani ba" nayi saurin faɗa har muryata tana rawa.
Murmushi mai kyau Salman ya saki kafin yace
"Na yarda". Na saki ajiyar zuciya ina dafe goshina take kuma haushin kaina ya rufeni, to rikicewar da nayi mata mecece? Sai kace wacce Alƙali ya rutsa. Wata jakar takarda ya ɗakko a kujerar baya ya ɗora mun a cinya yana cewa
"Gobe zan koma Abuja, ya kamata idan na tafi a ƙalla na ɗauki tsayin wata biyu ko sama kafin na waiwayo Kano amma babu hali tunda na ajiye mutum"
Nayi murmushi jin wai ya ajiye mutum kafin a hankali nayi masa godiyar abinda ban san ko menene ba, da kansa ya fita ya buɗe mun ƙofa na fita ina jina kamar wata sarauniya, sai da na shiga gida kafin ya ja motar ya wuce nima na shige ciki.
Anty Labiba na zaune a kan kujera tana waya dan haka na wuce ciki kawai bayan na mata sannu da gida, kayan jikina na shiga ragewa na tafi tunanin da Dr Salman ya hanani yi.
Mai ya faru ake neman Bilal har Hajja zata kirani? Na zauna gefen gado, saƙon daya turamun ranar nan ya faɗo mun a rai sai naji hankalina yana so ya tashi. Wayata na ɗauka na shiga Whatsapp na lalubo chat ɗin, bai sake mun magana ba tun waccen ranar. Na shiga sake biya saƙon, matsalar mecece? Na shiga tambayar kaina amma bani da amsa dan haka na ajiye wayar na shiga wanka ina jin yanayi na gaba ɗaya ya canza daga farincikin dana shigo dashi zuwa damuwa.
Haka na ƙarasa yinin ranar sukuku sai bayan Magriba da Faisal ya zo ne ma na zauna muka ɗan yi hira amma ina kwanciya na sake shiga tunanin, kasa bacci nayi daga ƙarshe na bi abinda zuciyata take ta saƙamun. Sai da na murza key a ƙofa kafin na shige banɗaki na lalubo number na kira. Ringing biyu aka ɗaga, daga can ya kira sunana ya ce
"Haleems! Dama na san ba zaki rabu dani ba dole zaki nemeni".
"Kana ina? Mai yake faruwa" Na faɗa, ya marairaice murya yana cewa
"Maganar ba zata yuwu a waya ba My Haleems muna buƙatar mu zauna idan kin amince zaki zo zan turo a ɗauki gobe".
Cikin kaushin murya nace
"Babu wani abu da yayi saura tsakanina da kai Bilal, Hajja ta kirani tana neman number ka daga yanayinta kuma na fahimci akwai wani abu da yake faruwa shiyasa kawai na kiraka".
Murmushi yayi kafin ya ce
"Ni dama na san ba zaki daina so na ba Haleems, kada ki biyewa su Anty Labiba kin sani dama tun usuli bata taɓa son tarayyata dake ba. Ina sonki, kuma nayi nadamar duk wasu abubuwa sa suka faru a baya and nayi miki alƙawarin soyayya da farinciki mara yankewa har idan kika dawo gareni kiyi haƙuri kinji My Haleems".
Zare wayar nayi daga kunnena, har zan kashe sai kuma na fasa naja numfashi na ce
"Ba zan iya zuwa in da kake ba, amma ka faɗa mun abinda yake faruwa idan ina da halin taimaka maka zanyi"
"Wata yar matsala ce ta faru, wasu kuɗi Jalilah ta bani nake juyawa kuma tsautsayi ya faɗa musu suka narke shine ta makani a kotu akan na biyata kuɗin sannan akwai gidanta da yake hannuna shima da aka siyar ban sani ba ashe gidan takaddun bogi yake dasu yanzu kuma ta zagaya ta sake siyarwa da wani daban ta haɗani rigima da wanda ya siya a hannuna" ya faɗa tamkar zai fashe da kuka.
Tunda ya ambaci sunan Jalilah wani abu mai ɗaci ya taso ya tsaya mun a maƙogaro, ba abinda nake gani sai hotonsu ganin da nayi masa na ƙarshe yana kwance akan cinyarta, daƙyar na buɗe baki na ce
"Ashe baka rabu da wannan matar ba Bilal?"
"Wlh na rabu da ita Halima shiyasa nace miki ina so mu haɗu akwai maganganu da yawa da nake so na faɗa miki wanda ba zasu yiwu a waya ba" yayi saurin tarata, na ja hanci saboda hawayen da suke neman ƙwace mun na ce
"Ya kamata tuntuni ka san cewa alaƙarka da ita ba zata taɓa kasancewa mai riba ba, ka biye mata ka kaucewa haryar Allah da tarbiyyar addininka, da aurenka Bilal ka zaɓi bibiyar macen banza a waje mai ya sa? Dame na rageka?" Na ƙarasa ina sakin kukan dana kasa riƙewa.
Shiru yayi kafin a hankali ya ce
"Kiyi haƙuri Halima, tabbas na zalinceki kuma nayi nadamar duk abubuwan da suka faru a baya, dagaske nakeyi ki yafe mun nayi miki alƙawari abinda ya faru a baya ba zai maimaita kansa ba"
"Yanzu kana ina?" Na faɗa bayan dana tsagaita kukan, ya ɗan yi jumm kafin ya ce
"Ina Minjibir zaki zo?"
"Hajja tana nemanka kuma hankalinta a tashe yake ya kamata ka kirata ta san kana lafiya" na faɗa ina jin yana ƙoƙarin sake yin magana amma na katse wayar take kuma nayi blocking layin. Kwanciya nayi lamo cikin yanayin da ni kaina bazan iya fasaltawa ba ina sauraron bugun da zuciyata takeyi. Na rasa yanda zanyi in daina jin sa a zuciyata, ina jin haushinsa da zafin abinda ya aikata mun amma kuma zuciyata ta kasa daina sonsa.
Vibration wayar ta shigayi na ɗagota na duba, nayi zaton shi ya canza layi ya sake kira amma sai naga Dr Salman ne. Sai da na duba agogo sha biyu saura kwata kafin na tashi zaune dakyau na amsa murya can ƙasa kamar wadda ta farka daga bacci nayi sallama.
"Bacci kikeyi?" ya faɗa bayan daya amsa sallamar na bashi amsa da
"Eh" mukayi shiru, kusan minti ɗaya kafin yaja iska yace
"Baki kirani kinji ya na isa gida ba anya dagaske na samu karɓuwa kuwa Leemah?"
Kunya naji a hankali nace
"Kayi haƙuri mantawa nayi"
"Mantawa kikayi?" Ya faɗa cike da mamaki, nayi saurin rufe baki na kamar yana gabana nace
"Aa ba haka zan faɗa ba cewa zanyi inata aiki ne ban san dare yayi haka ba so nakeyi idan na gama sai na kiraka"
"Amma kika ce bacci kikeyi? Ko dai Bilal ne ya ɗauke miki hankali?" Ya jefo mun wata tambayar, nayi narai-narai da fuska kamar ina gabansa kafin nace
"Aa wlh dagaske zan kiraka aiki ne ya ɗauke mun hankali"
"Shikenan na yarda, toh ya kike ya dare?" Ya faɗa daga haka muka shiga hira wacce zancen tafiyarsa gobe ne. Dama shi hirarsa kenan aiki da sabgoginsa na rayuwar yau da kullum ni kuma sai dai nayita binsa da Eh ko Aa dan a gurina wannan ba hira bace, a matsayinsa na mai neman gurin zama a ganina ya kamata hirar sa ta kasance ta ƙoƙarin kafa kansa a gurina amma shi sam ba haka yake ba. Sha biyu na bugawa yayi mun sallama, kashe wayar nayi gaba ɗaya dan tun muna magana nake ta jin shigowar kiran Bilal.
Tunanin fara maganarmu da Dr Salman na tafi, washe garin ranar da muka haɗu dashi a gidan Uncle Mudassir mun fita tareda su Al'amin da yamma siyo Popsicles muka haɗu dashi a gurin. Har ga Allah ban so kulashi ba dukda mun haɗa ido musamman da na ganshi tareda wata mace da wani abokinsa ina tsaye gurin biyan kuɗi ya tarar dani sai jin muryarsa nayi a bayana yana cewa
"Barka da yamma Malama Leemah". Da farko dukda naga tsayuwarsa ban ɗauka dani yake ba musamman sunan daya kira wai Leemah dan haka ban amsa ba, sai da ya sake matsoni sosai yana kallona ya maimaita maganar kafin kuma kunya ta kamani na shiga gaishe shi kai a ƙasa. Shi ya biya kuɗin abinda muka siya ya rakamu har mota kawai ya miƙa mun wayarsa wai na saka masa number na. Haka na koma gida cike da mamakinsa bai kirani ba sai washe gari Monday lokacin mun fita break, tsarin number dama gani kawai jikina ya bani shine, ilai kuwa bayan na amsa yace naje na sameshi a office, tareda Uncle Mudassir na tarar dasu babu kuma jeka ka dawo a gaban Uncle Mudassir ɗin ya ce wai nayi masa tun ranar daya fara ganina a lokacin ma bai san nice Niece ɗin Mudassir ba kawai yaji yana so na dagaske kuma idan na amince aurena yake so yayi.
Uncle Mudassir yace masa babu ruwansa shima yace bai sakashi a ciki ba abinda ya saka ya faɗa a gabansa kawai saboda ya san dagaske yakeyi koda yaji labarin wani zai masa shige ya faɗa cewar yana ciki, ni dai na tafi na barsu kawai, shikenan ya fara kirana a waya, ban kuma ɓoye masa ba na faɗa masa na taɓa aure har ina da yara biyu, nayi mamakin jin wai bai sani ba dan na faɗa masa ne saboda ya ji daga bakina dukda ina da yaƙinin ya sani Uncle Mudassir ba zai ƙi ya gaya masa ba amma yace mun bai sani ba.
"Bakiyi kama da wacce ta taɓa aure ba har kuma ace kin haifi yara biyu amma ke nake so, aure ko haihuwa ba zasu canza hakan ba" abinda ya faɗa mun kenan. Soyayyar sa a bayyane take kuma da zafi yake yinta.
Dukda cewar baya faɗarta da baki amma a bayyane take a duk ayyukansa ba kuma ya shakka ko jin nauyin wani ya sani kamar yanda nake jin tsoron fallasuwar alaƙarmu a office ɗin, ya mutane zasu kalli abun ace daga zuwansa kawai soyayya ta ƙullu tsakaninmu? Ba yan office ba hatta da mutanen gidanmu bana bana so maganar ta fita su