Showing 135001 words to 138000 words out of 257873 words

Chapter 46 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

503

nakeyi suka tsaya, zuciyata ta shiga bugawa da ƙarfi mamakin ƙarfin halinsa da kalaman da yake furtawa suka sumar dani a gurin da nake zaune. Ban san sanda na ce

"Ashe har kana da bakin da zaka iya kare kanka Bilal? Bilal da idona fa na gani na kuma saurari irin fasiƙancin da kakeyi sannan har ka iya buɗe baki kace wai da ina da tunani bazan bari abun ya dameni ba Normal ne, Zina ce ta zama Normal a gurinka? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un Bilal ina iliminka ina saninka na addini da har ka bari duniya ta rufe maka ido kake kiran Zina da Normal abu?" Na ƙarasa ina sakkowa ƙasa kan guiwoyina. Sai ya miƙe cikin fusata ya ce

"Halima idan kika sake dangantani da Zina wlh sai kin sha mamaki na"
"Ka faɗa mun abinda ya kamata na danganta dashi toh Bilal idan ban kiraka da Mazin...." Marin da ya kai mun ya hanani karasa maganar dana fara, sai da na wuntsila gefe saboda yanda marin ya shige ni na fasa kuka mai tafe da ƙara lokaci ɗaya Sharifa ma ta farka ta fasa mata kukan. Ko a jikin sa ya shiga cewa

"So kike sai kin ƙure haƙuri na, da zaki ringa ce mun Mazinaci da uwarki nayi Zinar?"
Tamkar dukan guduma haka naji maganar a kunnuwa, yau Bilal ne yake wannan zagin na rashin mutunchi? Ban dawo daga shock ɗin farko ba yaci gaba da cewa
"Ki ɗauki duk matakin da kike ganin yayi miki Halima idan kinga dama ki tafi gidan Radio ki siyi fili ki faɗawa duniya kinga ina Sex Chat da mace, amma kafin nan ki sani kanki zaki zubarwa da mutunchi bani ba. Duk inda kika ɗauki laifina kika kai kafin a saurareki sai an miki dariya ko kin manta kin zaɓeni akan kowa da komai naki? Duk kuma aje a dawo ba zaki taɓa iya rayuwa babu ni ba dan haka zaɓi ya rage naki ko kiyi haƙuri da abinda kika gani mu cigaba da zamanmu cikin rufin asiri ko kuma ki tafi ki zubar mana da mutunchi kuma ki dawo ɗin mu zauna, zaɓi ya rage naki" ya ƙarasa yana watsa hannaye alamar matsalata ce ba tashi ba kafin yasa kai ya fice daga ɗakin.

Ban taɓa riskar dare mai tsayi irin na ranar ba, na ringaji inama ina da ikon janyo safiya ko kuma na fito da masu abin hawa domin na samu wanda zai kaini gida? A cikin dare na haɗa mana kaya na fitar dasu barander na ajiye dan na ƙudurce ko da jinin jaka Bilal ya tsafance ni da yardar Allah sai na karya asirin yau na bar masa gidan sa koda kuwa hakan yana nufin tsayawar numfashi na a doron ƙasa. Ƙarfe shida na goya Sharifa daƙyar dan tun cikin dare ciwon kai da zafin ƙirji ya sake dawo mun, na riƙe hannun Al'amin dake tafiya daƙyar dan ko farkawa baiyi daga bacci ba ni na ɗaga shi na aje shi kan ƙafafunsa. Muna fitowa falo naji ƙarar buɗe Get, wani dunƙule ya taso daga cikina ya tsaya mun a maƙogaro.

Haka na ringa jansa muka fito daga falon lokacin har ya fita da mota ya dawo yana zuge Get ɗin na kalli kan Barander inda na aje kaya basa nan sai ji nayi ya ce
"Gasu can a mota muje na kaiku tunda kin san babu yanda za'a yi ku fita da sassafen nan da kaya duk yan unguwa suna kallonki".

Nayi murmushin da yafi kuka ciwo, wato maganar yan unguwa yake gudu amma baya kunyar ubangijin sa yake kiran Zina da Normal abu. Ina buƙatar na isa gidan da wuri na san kuma tafiyar tawa bata dame shi ba zai ma fi farin ciki da hakan shiyasa na yarda na shiga motar muka tafi. Har muka isa gidan babu wanda ya cw uffan a tsakaninmu har muka isa ƙofar gidanmu. Ina ƙoƙarin buɗe motar naji ya ce
"Ina sake jaddada miki dariyar da za'a miki sai tafi laifina da zasu gani yawa, infact sai kin tsani kanki Halima muddin aibu na ya fita daga bakinki" sai na waiwaya na kalle shi na ce
"Barazana kake yi mun kenan?" Ya ɗage kafaɗa n ƙarasa ɓalle murfin motar na fita ban ko lura da Abba dake tsaye bakin Get da maƙwafcinmu Alhaji Bala suna magana ba na shige ciki.

A tsakiyar falo na kwance goyon Sharifa dan ji nake kamar zan faɗi na mutu a gurin kai tsaye kuma na shige tsohon ɗaki na sama sama ina jiyo kamar muryar Amirah tana kiran sunana amma ban tsaya ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 35*

Amirah ta ɗaga Sharifa data saka kuka daidai lokacin da Mama ta fito daga kitchen lokacin kuma Al'amin shima ya shigo Suraj na biye dashi da akwatin mu.
"Ku kuma daga ina haka da sassafe?" Mama ta tambaya, Suraj ya ajiye kayan yana cewa
"Tareda Babansu suke" ya juya ya fita sai Amirah tace
"Yaya Haliman tana ciki itama". Tsaye Mama tayi kafin tace
"Toh lafiya dai?"
"Gaskiya ba lafiya ba kinga fa jefar da Sharifa tayi ta wuce ina mata magana ko saurarona ma batayi ba" Amirah ta amsa mata. Jumm tayi tana kallon Al'amin daya haye kan kujera ya kwanta alamar baccin sa zai cigaba, sai ta juya kitchen ba tareda tace komai ba amma zuciyarta cike da saƙe saƙe.

Kan gado na faɗa bayan dana shiga ɗakin dafe da ƙirjina da nake ji tamkar an ɗaure ni da igiya, daƙyar nake fuzgar numfashi, na ringa juyi a kan gado ni kaɗai tsayin lokaci kafin ubangiji ya kawo mun rangwamen abinda nakeji ta hanyar rabani da numfashina na wani lokaci.

A waya Mama ta kira Abba, tambayar sa tayi ko Bilal yace masa wani abu ne tunda ance tare muka zo sai ya ce mata
"Bai tsaya ba yana sauke musu kayan su ya juya ko gaisawa bamuyi ba"
"Ikon Allah, to mai ya faru?" Ta sake tambaya cikin jimami. Daga can yace
"Ni kam ina zan sani ne Amina? Ba gata nan a cikin gidan ki tambayeta mana", jin kamar ya fara fusata ua saka tace
"Toh shikenan sai ka dawo" ba tareda ya bata amsa ba ya katse wayar dan ransa y sosu matuƙa da ko in kulan da Bilal ya musu. Sosai yaji ba daɗi sanda Alhaji Bala da suke tsaye yace masa
"Wannan ba Mijin Halima bane naga yaja mota bai ko tsaya ya gaida mu ba? Koda yake yanda ta shige itama kamar dai akwai matsala dan na lura bata ma ga tsayuwarmu ba, amma shi ai idan ɗan arziƙi ne yaci ko matsala suka samu ya tsaya nan ya maka bayani ba yaja mota ya tafi ba".
Wannan maganar ta dame shi har ta saka ya fasa komawa cikin gidan da yayi niyya ya sallami Alhaji Balan kawai ya wuce inda zashi ya a tafe kuma yana tunanin dalilin zuwan Halima da sassafen nan.

Sai gurin ƙarfe tara Mama tace Amirah ta shiga ta kirawo Halima ta karya lokacin har tayiwa su Al'amin wanka sun ƙoshi sun shiga sabgogin su, ihun da Amirah ta fasa bayan shigar ta ɗakin ya saka Maman tashi da sauri tamkar zata hantsila ta shiga ɗakin, gabanta ya yanke ya faɗi ganin Amirah tsugunne kan Halima tana girgiza ta haditda kiran sunanta amma ko gezau bata motsa ba, cikin tashin hankali ta isa gaban gadon ta ɗagota jikinta ta shiga jijjigata da ƙarfi amma bata koyi alamar zata farka ba.

"Ta mutu innalillahi mun shiga uku Yaya Halima ta mutu" Amirah ta faɗa hannu biyu akai cikin matsanancin kuka Mama dake rungume da Halima ta ɗaga mata hannu tana cewa
"Bata mutu ba fita ki kira Mu'azzam, kiyi sauri dan Allah yazo mu kaita asibiti" ta ƙarasa tana ƙoƙarin buɗe idanun Haliman. Da gudu Amirah ta nufi ƙofa sai kuma ta juyo cikin kuka tace
"Kin manta ya tafi makaranta tun ɗazu yana da exam yau?"

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Amirah ki fita kowa kika gani ki kira mu kaita Asibiti" Mama ta faɗa tana fashewa da kuka itama. Tareda Samari biyu Amirah ta dawo wanda a waje ta taresu sun taho a mota su suka ɗauki Haliman suka fito da ita daga Mama har Amiran babu wanda ya tsaya neman koda Takalmi suka biyo su Zainab na kuka riƙe da Sharifa haka Al'amin dukda ba wai sanin mai yake faruwa yayi ba kawai ganin sunayi ya saka shima ya kama. Suna ƙoƙarin sakata a motarsu Suraj ya iso ƙofar gidan dan dama tare suka fita da Abba ya kaishi Airport zai tafi Lagos, motar sa Mama tace su sakata suka shiga ita da Amirah ya ja motar da gudun gaske suka nufi asibiti.

Bayan tsayin lokacin dana ɗauka tsakanin mutuwa da rayuwa na farka, na buɗe idanuwana da naji tamkar an manne mun su da super glue daƙyar na iya buɗe su na kalli in da nake saidai ban fahimci komai ba hakan ya saka na sake mayar da idanuwan nawa na kulle ina jin sautuka sama sama kamar daga can nesa. Mama dake zaune kan kujerar dake kusa dani ta miƙe da sauri saboda ƙafata dana motsa, ta kira sunana, dukda ba wai na fahimci mai ta faɗa ba sautin da naji ya saka na sake buɗe idona na sauke akan fuskarta. Ta kama hannuna hawaye na ziraro mata tace

"Kin farka Halima?" A hankali tamkar mai koyon magana na kira sunanta a rarrabe "Ma..ma" haɗi da matsa hannunta data riƙe nawa dashi. Cikin kuka mai haɗe da dariya ta amsa da
"Na'am Halima kin farka? Alhamdulillah". Ji nayi maganganunta suna hau mun kai sai na sake mayar da idona na rufe tayi azamar kamo fuskata tana cewa
"Ki tashi dan Allah kada ki sake komawa Halima dan Allah ki buɗe idonki ko hankalina zai kwanta" ta ƙarasa cikin kuka. Na sake buɗe idona na kalleta, tabbas naga ƙauna mai tsanani haɗi da tausayi cikin ƙwayar idanunta dake tsiyayar da hawaye, kalaman Bilal da ya ce "Da uwarki nayi zina" suka dirar mun tamkar saukar mashi take wani abu ya taso ya sake tokare mun maƙogaro, ban iya yin abinda ta buƙata ba na sake mayar da idanuna ruf na rufe su sai ta saki hannuna ta nufi ƙofa kusan da gudu ta fice daga ɗakin ba jimawa suka dawo tareda likita da Nurses biyu. Sai da ya gama dubani kafin ya kalleta cikin kalaman kwantar da hankali yace

"Kiyi haƙuri Hajiya na faɗa miki jikinta yana da buƙatar hutu sosai zata farka idan lokacin hakan yayi in sha Allahu ki daina damuwa zata samu lafiya da yardar Allah"

"Likita ta farka fa, ta buɗe idonta har magana tayi mun kafin ta sake komawa dan Allah likita kayi wani abun yarinya ta ta farka kaifa kace mun awanni kaɗan amma gashi kwana biyu kenan bata farka ba". Kwana biyun data ambata ya saka na sake buɗe idona na kalle su, hannu biyu ta ɗaga tana cewa
"Alhamdulillah, ka gani ko idonta biyu". Ganin tana ƙoƙarin ɗago ni ya saka ya dakatar da ita, a hankali ya kira sunana na kalle shi yace

"Kina jina Halima?" Nayi shiru badan bana jin sa ba sai dan bansan ta yanda zan amsa masa ba. Bakina yayi mun nauyi tamkar an ɗaure mun harshe. Cikin taushi ya sake kiran sunana da maimaita tambaya ina jinsa amma na kasa amsawa. Mama ta fashe da kuka tana cewa

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Dr mai ya samu yarinyata dan Allah kayi mun bayani ni Musulma ce koma menene zanyi haƙuri na karɓi ƙaddarar data samemu".

"Dan Allah Hajiya ki nutsu, idan ba zaki iya shiru ba kuma ki fita waje. An gaya miki babu abinda ya sameta kawai tana buƙatar lokaci ne babu yanda za'ayi mutum ya tashi daga dogon suma irin haka kiyi tsammanin nan take tunanin sa zai dawo tamkar yanda yake a da sannan wannan hayaniyar da kukan da kikeyi shima kina ƙara mata wata damuwar ne cikin wadda take" ɗaya ɗaga cikin Nurses ɗin ta faɗa a hasale, sai ta juya cikin kuka ta nufi ƙofa na bita da kallo ina so in tsayar da ita amma kuma banida ikon yin hakan.

Wata yar fitila likitan ya kunna ya shiga haska idanuwana bayan ya gama ya zaro biro daga aljihun rigarsa yace
"Idan kina jina ina so ki ringa bin biron nan da idonki duk inda nayi dashi kinji?" Na lumshe idona kafin na buɗe nayi abinda ya ce. Ya mayar da biron aljihu yana cewa

"Yawwa Halima, yanzu ki motsa ƙafar ki na gani" nayi yanda yace sannan ya kama hannuna yace in matsa hannun sa nan ma nayi sannan ya sakeni, cewa yayi na tashi na zauna. Nayi jimm dan kwata kwata banajin alamar ƙashi ko tsoka a jikina ji nake tamkar a iska nace, sai da ya sake maimaitawa kafin na yunƙura a hankali naja jikina Nurse tayi saurin saka mun pillow a bayana na jingina ina mayar da numfashi tamkar wadda tayi tseren gudu. Hamdala yayi kafin ya karɓi folder dake hannun Nurse yayi rubutu ya bata yace taje pharmacy ta karɓo abinda ya rubuta sannan idan ta fita ta turo masa Mama.

Tare suka shigo da Abba, Mu'azzam, Anty Labiba da Mijinta sai Mama Fauziyya. Gaba ɗayan su kallo ɗaya zaka musu ka karanci hashin hankalin da suke ciki, Abba ya matso ya dafa kaina nayi karfin halin tattaro kalmomi na haɗa na kira sunansa, "Abba" ya amsa yana shafa kaina
"Na'am Halimana kin tashi?" Sai na gyaɗa masa kai lokaci ɗaya kuka ya kwace mun Abba ya rungume ni yana cewa

"Kuka kuma Halima menene? Kiyi shiru dan Allah kinga halin da kike ciki babu abinda zai faru ki dena kuka kinji?"

"Ina ganin kuyi haƙuri ku koma waje ƙila ganinku ne ya dawo mata da wani abun kuma a yanayin da take ciki yanzu bama son duk wani abu da zai sosa mata rai balle ya sake ƙara mata wata damuwar" likita ya faɗa. Duka suka fita banda Abba dake rungume dani idanuwansa sunyi jajir tamkar shima zai yi kukan yana ta bubbuga bayana da cewa nayi shiru, Nurse ɗin da Dr ya aika ta dawo da allurai da da drip ya karɓa ya fara haɗawa, zai zare ruwan dake hannuna Abba ya dakatar dashi yace

"Dan Allah kada ka saka mata abinda zai sake mayar da ita wannan baccin"
"Amma Alhaji saboda lafiyarta ne" cewar Dr, sai Abba ya girgiza masa kai yace
"Na sani amma ka ɗanyi haƙuri ku bamu guri zanyi magana da ita". Tsayawa yayi kamar ba zai fita ba kafin ya juya, Nurse ɗin da ta yiwa Mama magana ɗazun ta buɗe baki zata sake magana yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa su fita.

Sai sa suka rufo ƙofar kafin Abba ya ɗago kaina daga kafaɗar sa yace
"Kukan ya isa haka Halima kiyi shiru kinji"
"Tsoro nakeji Abba" na faɗa daƙyar kafin na kama hannunsa na ɗora saitin zuciyata da nakejin ciwo tamkar an hura mun wuta nace
"Zuciyata zafi takeyi Abba mutuwa zanyi"

"Ba zaki mutu ba Halima har sai lokacin da ubangiji ya rubuta faruwar hakan, duk wani tsanani a rayuwa yana tareda sauƙi kiyita nanata Hasbunallahu wani'imal wakeel a zuciyarki in sha Allahu zaki samu salama kinji?"
Kai na ɗaga masa alamar naji take kuma na kama na shiga nanata Hasbunallahu a hankali a hankali na fara jin abinda ya tokare mun maƙoshi yana zagwanyewa, zafin da zuciyata take mun ma ya fara raguwa inayi Abba ma na biyawa a fili sannu sannu har bacci ya ɗauke ni. Ajiyar zuciya ya sauke ganin nayi bacci, sai da ya ɗauke ƙwallar data zubo masa kafin ya gyara mun kwanciya akan gadon ya lulluɓa mun bargo sannan ya koma kan kujerar dake gaban gadon ya zauna yana kallona.

Har ya sauka Lagos zuciyarsa babu daɗi gaba ɗaya hankalin sa na ga son sanin dalilin zuwan Halima gida da sassafe haka da kuma yanayin daya ganta a ciki. Yana so ya kira Mama yaji ko ta faɗa mata wani abu amma kuma baya son yaji abinda zai ɗaga masa hankali ya hanshi nutsuwar yin abinda zajeyi Lagos ɗin. Da zai shiga meeting ya saka wayarsa a Flight mood dan haka sai bayan Magriba lokacin sun tashi gaba ɗaya ya shiga hotel room ɗin sa kafin ya buɗe wayar yana so ya kira wani Abokinsa, Network na daidaita kuma saƙon Mama ya faɗo tana gaya masa Halina na Asibiti sun sameta a sume a ɗaki har lokacin kuma dukda bai san ƙarfe nawa ta tura saƙon ba bata farka ba kuma likita yaƙi ce musu komai yace dashi zai yi magana.

Cikin tsananin tashin hankali ya shiga neman layin Maman amma bai samu ba dan haka ya mayar da akalar kiran kan Mu'azzam wanda bugu ɗaya ya ɗauka kuma yanda ya jishi da bayanin da ya masa akan yanayin Haliman ya saka yaji ba zai iya ƙara koda awa ɗaya a Lagos ɗin ba duk kuwa da bai kammala uzurin da yaje yi ba, sai dai yayi rashin sa'ar rasa jirgi, haka ya kwana a zaune tamkar yanda suma a Kano suka kwana cikin tashin hankali da zullumin halin da Halima take ciki da gari ya waye kuwa ko wanka bai tsaya yiba ya hawo jirgi ya taho musamman yanda Mama ta kira tana rusa masa kuka akan yayiwa likita magana ita dai ayi mata bayanin halin da yarta take ciki idan ma mutuwa tayi a gaya mata kawai saboda tunda aka kawota take nan kwance kan gado bata motsa ba gara ta sani in mutuwa tayi ta ɗauki dangana a basu gawarta su wuce gida su mata sutura.

Koda yazo ma babu wani gamsasshen bayani daya samu daga bakin likitan, abinda ya gaya masa kawai zuciyar Haliman ta kumbura kuma jininta yayi hau sosai wanda yayi sanadiyyar samun partial

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login