Showing 75001 words to 78000 words out of 257873 words
19*
Ba zan iya cewa ga ta yanda muka fita daga gidan ba ni dai kawai na san munje gidan mu; muna sauka daga Adaidaita sahu Amirah ta sake ni na dafe gini saboda jirin dake kokawar kayar dani ita kuma ta tura ƙofar get ta shiga tana rushewa da kuka tamkar wadda tazo isar da saƙon mutuwa. Daƙyar na cira ƙafata na rufa mata baya ina yi ina dakatawa saboda ciwon marar dake taso mun, na dafe ƙofar shiga falon na tsaya ina kallon mazauna ciki da suka rufu kan Amiran cikin tashin hankali suna tambayar ta ba'asin kukanta; tabbas idan na canka dai dai kowannen su abu guda yake ayyanawa shine wani mugun abun ne ya same ni.
Ƙarasawa nayi ciki ina cije leɓe, Abba ne ya fara gani na; "Alhamdulillah" ya furta a fili yana nufo ni hakan ya ankarar da Mama da Anty Labiba suka waiwayo. A ƙasa na zauna duk suma suka zauna suna kallon Amirah da har sannan take kuka ni ɗin ma ita nake kallo ina mamakin wannan dirama tata. Abba ne yayi mata tsawa; cikin hasalar da sam ba ɗabi'ar sa bace ya nuna ta yana cewa
"Ga dai yar uwarki lafiyarta ƙalau, tun banyi loosing temper ba Sauda ki faɗa mun me akayi miki kike wannan kukan" ya ambaceta da ainihin sunanta wanda kuma sunan Mahaifiyar su Mama ne.
"Ai wlh dab nake da kai mata duka; duk a zato na wani abu ne ya samu Haliman se gata da ƙafafun ta ta shigo amma dan iskanci shine ta shigo tana irin wannan kukan me tsinka zuciya" Mama ta faɗa, ba tareda Amirah ta dakata da kukanta ba gaba ɗaya tace
"Ai Allah ne kawai ya kiyaye da ba lallai ta dawo da ƙafarta ba se dai a shigo muku da gawarta; Bilal ne ya rufe mu da duka, Allah ne kawai ya ƙwace mu a hannun sa da ƙila duk mu biyun ma ze kashe muku" ta ƙarasa tana sake rushewa da wani kukan daya fi na farko. Duk su ukun ni suka zubawa ido in da ni kuma na kafe nawa kallon kan Amirah mamakinta na neman dakatar mun da numfashi.
"Ai dan kar in magana ne ace na faɗi abinda ba shikenan ba amma dama ina ganin su nasan Bilal ne; ai kuwa billahillazi ya dakarwa kansa masifa da bala'i yau" Anty Labiba ta faɗa tana miƙewa tsaye. Hannu Abba ya ɗaga mata yana kallo yace
"Dakata Labiba, Halima gaya mun meya faru, gaskiya ne abinda ƙanwar ki ta faɗa?"
Ajiyar zuciya me nauyi na sauke haɗi da maida kallo na ƙasa; cikin muryata da firgicin abinda ya faru a can gidan ya dasa mun na ce
"Ba gaskiya ta faɗa ba Abba, babu abinda Bilal ya mana kawai dai..."
"Wallahi ƙarya takeyi Abba dukan mu yayi kuma ya ringa zaginmu yana ce mana yayan matsiyata marasa tarbiyya sannan yace mu bar masa gida kafin ya dawo idan ba haka ba se yayi mana abinda za'a ɗaure shi" Amirah ta katse ni.
Jikin Anty Labiba kamar wadda ta taɓa wayar wuta har wata girgiza take tace
"Shi Bilal ɗin?" Se ta nufi ƙofa. A tsawace Abba ya kira sunan ta yana nuna mata kujera, na tabbatar tsananin yanda take ganin mutunchin sa yasa ta dawo ta zauna, yanda take kaɗa ƙafa yasa na ja jikina na matsa gefe domin kada mutanen ta su kawo ziyara ta fara ta kaina. Kallon Amirah Abba yayi da yanayi na ɓacin rai ya nuna ta da yatsa yace
"Ita yayar taki kike ƙaryatawa ko? In sake jin bakin ki a nan gurin har idan ba ni na nemi kiyi magana ba". Se ya sake juyowa kaina yace
"Ina jinki".
Muryata na rawa ba tare da na kalli kowa a cikin su ba na shiga cewa
"Amirah ce, ban san meya haɗa su ba tayi masa rashin kunya har tana ce masa matsiyaci, shine yace ta bar masa gida". Falon yayi shiru hatta da Amirah dake kuka ta dakata ina kuma jin dirin idanunsu a kaina amma ban yarda na ɗaga kai na ba,
"Me ya haɗa ki da Mijin Yayarki har kika zage shi Amirah?" Abba ya tambayeta.
"Wallahi Abba babu abinda nayi masa, kawai ina bacci ta tashe ni tace na zuba masa abinci zatayi sallah; shikenan daga na ajiye masa abincin yayi bal da farantin Allah ne ma ya rufamun asirin ban yanke ba dan fashewa yayi ƙwalaben duk suka bazu a falon shikenan fa ya fara masifa yana zage zage wai mu yayan matsiyata ne mun dafa masa taliya fara da manja bayan kuma be siyo kayan miyan ba balle a dafa masa da miya. Ya ringa zaginka shine ni kuma na gaji nace ba dai ubana ba; shine y ɗakko belt lokacin Yaya Halima ta fito daga ɗaki ya hau dukana yana zagi na data zo zata kare ni shine ya ture ta ta faɗi ya haɗa dani da ita rufe mu da duka yana cewa wai ze koya mana tarbiyyar da ba'a bamu a gida ba" ta ƙarasa tana fashewa da sabon kuka.
Mama dai kamar bata gurin Anty Labiba ko banda kaɗa ƙafa ba abinda takeyi.
"Kiji tsoron Allah Amirah; yaushe akayi haka?" Na faɗa ina kallonta kafin na juya kan Abba nace
"Wallahi ƙarya takeyi Abba be doke ta ba kuma ni banji sanda ya zageta ba kawai nasan yayi mata hargagi yace ta taho gida kuma ita ta zage shi ta masa rashin kunya".
"Kinyi asara Halima, namiji ya zagi iyayenki har ya kira ki mara tarbiyya sannan kizo kina kare shi wallahi kinji ɓutur, namiji dai kika ɗauka uba ko? Zako ki mutu marainiya. In dai Bilal ne gaki gashi nan ko yau be dake ki ba muna nan ranar zata zo Halima zaki san ki fifita son miji akan mutunchin iyayenki" Anty Labiba ta faɗa tana miƙewa, saboda fushi babbar rigar Abba ta shiga fizga a zaton mayafin ta ne dake ajiye kusa da shi dan duk zaburar data ringa yi ɗazu zata fita babu gyale akanta. Gyalen Abban ya miƙa mata ta fizge ta fita tana sake nanata
"Halima kinyi asara, Halima zaki gane baki da wayo a hannun namiji".
Se lokacin Mama ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta bita ba tare da tace komai ba, Abba ya kalle ni yace
"Ina ita kaɗai yace t taho gida ko harda ke?" Se na fashe da kuka nace
"Abba ransa ya ɓaci sosai, ina tsoron na zauna kuma ma ni bani da lafiya, marata ciwo take mun".
"Tashi mu tafi Asibiti" ya faɗa yana miƙewa tsaye, sunan Asibitin daya faɗa se naji kamar an mun busharar ciwo lokaci ɗaya wani ciwon baya da mara da bansan yanda zan misaltasu ba suka kawo mun ziyara. Hannu na shiga yarfewa ina cewa
"Bazan iya tashi ba, wayya Allah ina ga ma mutuwa zanyi ni dai". Kiran Mama ya shigayi da ƙarfi se gata, ganin yanda nake dafe ciki ina nanata mutuwa zanyi yasa ta koma da baya se gasu tare da Anty Labiba. Tare suka kamani suka sani a mota. Cikin ikon Allah da zuwan mu asibiti ban fi awa ɗaya ba na haifo ɗan ƙaramin ɗana me tsananin kama da Bilal.
Anty Labiba ce taje ta siyo kayan da aka sakawa yaron da sauran abubuwan da zan buƙata kamar pad da pant, kayan jikina dake dama riga d zani ne muna shiga na yaye zanin dan haka dana gyara jiki na nayi wanka su na mayar duk se nake jin ƙyamar jikina. A hannun Anty Labiba na tarar da yaron bayan na fito daga labor room ɗin, ta mun kallo ɗaya ta watsar dani da alama duk lahaula da salatin data ringayi tana safa da marwa a bakin labor room duk na lokaci ne ba wai ta manta da fushi na dake ranta bane. Mama kanta a fizge ta mun sannu tareda tambayar badai abinda nake ji nace mata eh, Abba ne kaɗai ya ringa jera mun sannu yana mun addu'a kafin ya fita ya bamu guri.
Duk se naji jiki na yayi sanyi, na kwanta akan gado ina satar kallon su biyun Anty Labiba na riƙe da Baby Mama kuma na ƙoƙarin haɗa mun shayi ta gama ta miƙo mun se ta ɗauki Hijabin ta ta saka tana kallon Anty Labiba tace
"Bari naje gida Labiba naga idan Hasana tayi abinda nace mata; kin santa da shirme. Idan suka kawo abincin ita se ta zauna ta kwana dasu ki tafi gida ko?" Bata jira amsar ta ba ta juyo kaina tace
"Se ki kira shi ki gaya masa za'a zo a ɗaukar miki kaya kar kuma yace an shigar masa gida ba izini".
Anty Labiba dai bata ce komai ba se ɗaukar Babyn hoto da take a wayar ta haka Mama ta fita ta barmu kusan minti biyar a raina na tafi tunanin ko sun gayawa Bilal na haihu?
Anya kuwa? In da ya sani nasan baze kasa zuwa ba ko wani nasa, ina so na tambayi Anty Labiba aron wayar ta na kirashin amma babu fuska se kawai na kama kaina na kwanta kawai, shi kansa Babyn ina kwaɗayin na riƙe shi a hannu na na sake tantance kamannin sa dana hanga daga nesa amma nayi ƙarya nace ta bani shi.
Kamar ta shiga zuciyata kuwa se gata ta miƙe ta iso kusa da gadon ta aje mun babyn tare da wayarta kafin tayi ficewarta waje. Nayi murmushi a fili nace
"Antyna ta kaina kenan iyayen daru". Shagala nayi da kallon Babyn da kamar yasan guri na aka kawo shi ya fara motsa baki yana wulla yan ƙafafun sa da hannayen sa. Na ɗauke shi na rungume shi, wani farincikin mara misaltuwa ya tsarga rai da ruhi na. Na tuna sanda nake yiwa Hansa'u tsiyar bata da kunya, a hotunan sunan yarta data haifa wata biyu kenan, ƙiri ƙiri Bilal ya hanani zuwa Abuja sunan bayan har Maman mu se da taje. A kowanne hoto data tura mun tana rungume da yarinyar kamar za'a ƙwace mata ita da nace bata da kunya tace mun bazan gane ba se ranar dana riƙe nawa ɗan zan fahimci ba rashin kunya bane.
Motsin ƙofa yasa nayi saurin raba shi da jiki na na zata Anty Labiba ce kafin ta fara mun taratsi ashe nurse ce, ita ta taimakamun tare da koya mun yanda zan shayar dashi. Dake tun kafin na haihu dama ruwan nonon ya fara kawowa dan haka ba ɓata lokaci ya kama kamar dama a yunwace yake. Tana tsaye har ya ƙoshi kafin ta karɓe shi ta sakashi a kafaɗa tana nuna mun yanda zan sakashi yayi gyatsa. Bacci ya koma ta kwantar dashi tace na shanye shayin da aka haɗa mun zata yi mun allura ne. Se lokacin na tuna ban ma kira Bilal ɗin ba, seda ta gama abun da zata mun ta fita kafin na danna lambobin sa a wayar Anty Labiba takaici da dariya suka kamani lokaci ɗaya ganin sunan data masa saving, wai BILAL BATI. Lallai Anty Labiba ta raina mun miji.
Kira uku nayi masa be amsa ba, dake ana shirin shiga sallar magriba ne se na bashi uzurin ƙila ko yana alwala ko ma ya shiga masallaci ne. Hotunan da tayiwa Babyn na shiga dubawa ina murmushi ni kaɗai, shigowar ta tare da su Mama Fauziyya yasa na aje wayar. Har ƙarfe goma wasu daga cikin yan uwan Mama da suka zo harma dangin Abba basu tafi ba. Ashe har tayi sanarwar haihuwar a group ɗinmu na family ta kuma tura hoton Babyn shi kuma Mu'azzam ya ɗauka ya tura ana ɓangaren Abba. Tunda nace mata ban samu Bilal ɗin ba se kawai tayi waya gidan ta aka ɗakko mun dogayen riguna dan kiba kawai ta fini da tsayi kaɗan kowa cewa yake ita na gado a rashin auki to yanzu cikin nan daya hura ni ma mun kusa kai ɗaya. Haka na kwana da zullumin ko Bilal ya san na haihu? Idan yaji ya ya karɓi al'amarin dan nasan abu ne me wahala idan be ji haushi ba ace sedai kawai ya tsinci zancen haihuwa ta a sama bayan yana da haƙƙin daya kamata ace tun muna hanyar asibiti an kirashi an gaya masa. Haka nayi bacci cikin zullumi.
BILAL
Se da ya fita daga gidan kuma ya ringa jin babu daɗi kamar abinda yayi ya zarce misali. Can gefe ya nemi guri ya zauna yana tunanin ya koma ne ya bawa Halima haƙuri ko kuwa? Amma daya tuna Haliman da irin son da take masa se ya samu nutsuwa yasan ba zata ɗauki abun sa zafin da ze iya zame musu matsala ba amma kuma waccen ƙanwar tata mara kunya ita ce zata iya kai zancen gaba har ya zama wani abu daban. Sau biyu yana miƙewa da niyyar komawa gidan idan ma ta kama ya basu haƙuri ne duk su biyun zancen dai ya wuce karya koma kunnen yan gidansu amma shigiyar zuciyar sa me yi masa huɗubar tsiya ta zuge shi akan ze siyawa kansa raini ne kawai ai itama Haliman ba zata fara bari zancen yaje gidan ba.
Da haka ya bawa kansa ƙwarin guiwa, da yayi niyyar zama gurin yayi gadi ko da zata ce zata fita se kuma ya fasa yayi tafiyar sa dan yasan babu in da zata je ita dai Amirah yasan dole zata bar gidan tunda Halima na gudun ɓacin ransa. A masallacin unguwar yayi sallar la'asar yana zaune ya hango gilmawar su, har ya miƙe da niyyar bin su kuma se ya fasa a ransa ya raya mafita ce ta samu. Yanzu duk inda aka je aka dawo ze juya lefin ne ya koma kanta ta fita daga gidan sa ba tare da ya bata izini ba tunda ai ba ita yace ta tafi ba. Komawa yayi ya ɗauki mashin ɗin sa cikin sa'a har ya fito bakin titi se lokacin suka samu abun hawa. Se da ya rakasu har gida yaga sun shiga kafin ya wuce gidan su yana ayyana yanda ze canza maganar idan ma ta tashi ance y zagi uban matar sa dukda yayi amanna Halima ba zata taɓa bari maganar ta fita ba yasan ma baze rasa dalilin da ya saka tabi Amiran ba kenan dan kar taje ta faɗi abin da ba shikenan ba.
Daya isa gidan suna gaisawa da Hajja abinda ta fara tambayar sa shine
"Wai yaushe matar ka zata tafi wanka ne ko kuwa kana nufin a gidan ka zata haihu su tatse maka tattalin arziƙi?"
Zancen kenan kullum yaje kamar karatu tun cikin Halima be wuce wata shida ba take surutun se ta tafi goyon ciki ai haka akeyi a al'ada, se kace ita nata yayan da cikin wata shidan suke tahowa kuma ma banda Amina Babbar Yayar su shi be sake ganin wata tazo wani wankan gida ba se Fadila itama kuma yasan dan Mijin yaƙi daɗin azanci ne dama neman tahowa gidan takeyi shi yasa suka fake da haihuwa badan haka ba da Hajjan ce zata je ta zauna mata kamar yanda ta saba yiwa sauran shine zata takura se Halima ta tafi tun da wurwuri.
Dukda dai shima yana da ra'ayin ta tafi wankan gida saboda ko babu komai za'a rage masa hidimomi da yawa na yan barka har zuwa suna da abubuwan da zasu biyo baya; duk baya jin yan uwan Halima dan tun auren su ze iya irga mutum nawa suka zo gidan kuma ko ta haihu ba zasuyi irin zuwan nan na takura ba nasa dangin yake ji dan yana ganin yanda sukeyi a sauran gidajen yan uwansa idan anyi haihuwa wata tun farar safiya zata taho se taci abincin dare sannan ta tafi gaskiya baze ɗauki wannan zaryar ba shiyasa gara ta tafi can gidan su idan tayi arba'in suka gama yawon zaga dangi se ta dawo dukda ma ya gama gane take taken Haliman bata so ta tafi gidan amma hakan ya zame mata dole tunda yana ra'ayi.
Yana ɗakin Hajja suna hira kiran Anty Labiba ya shiga wayar sa, abinda ya fara zuwar masa shine Amirah taje ta ce ya zagi Abban su shine Anty Labiba ta biyo ba'asi hakan yasa ya maida wayar sa aljihu bayan ya sakata a silent a ransa yana raya harka ta lalace musamman tunda wannan matar ta shigo ciki ko abun beyi zafi ba se ta ƙara rura wuta. Se da aka kira sallah ya fita, bayan an idar Abdurrashid ya tsayar dashi ɗaya daga cikin Yayan Baba Salahu ne kuma abokin Bilal ɗin dan suna buga ƙwallo tare. Da fara'a ya tare shi bayan sunyi musabaha yace
"Angon ƙarni ashe an samu ƙaruwa?"
Tunanin da Bilal ya tafi yana magana ne akan Halima nada ciki, se ya gimtse fuska kishi ya motsa wato kalle masa mata ma yake yi yana sa mata ido tsabar kuma bashi da ta ido har ya iya tarar sa ya masa barka wai matar sa nada ciki. Shi ko Abdurrashid bema gane sauyin fuskar Bilal ɗin ba yace
"Allah ya raya ya ɗayyaba, se munzo barka" daga haka ya saki hannun Bilal ɗin ya wuce abun sa. Sakato Bilal yayi a tsaye yana ƙoƙarin haɗa maganganun Abdurrashid ɗin na ƙarshe, idan ya fahimta barkar haihuwa ya masa ba ta samun ciki ba kenan kuma hakan yana nufin Halima ta haihu ne ko me?
Ƙarasa fita yayi daga harabar masallacin kafin ya sake samun guri ya tsaya ya riƙe ƙugu yana ƙoƙarin haɗa lissafin, Nasir ne ya iske shi fuska a washe ya shiga zolayar sa da "Angon ƙarni".
"Ta tabbata kenan" ya raya a ransa, Nasir ɗin yace
"Be kamata ma na kulaka ka ba, ace se dai muji haihuwa a gari ba zaka iya kirana ka gaya mun ba ko da yake yanzu kayi sababbin abokai yan GRA naga ai baka yayin irin mu yan ghetto".
"Ka aje maganar wasa Nasir dagaske ne wai Halima ta haihu?" Ya tambaye shi. Se Nasir ya kalle shi yace
"Bana son rainin wayau; matar ka ta haihu ka ringa tambaya ta wasa ne ko gaske? Mutuwa kayi ka dawo da zaka ce baka san meya faru a duniyar ba ko wani salon wulaƙancin ne haka?"
"Dagaske nakeyi Nasir ban san Halima ta haihu ba.