Showing 150001 words to 153000 words out of 257873 words

Chapter 51 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

485

rufa masa asiri kada ta furta wani abu da zai jawo zubewar mutunchin sa a idon yan gidansu musamman Abbanta. Haka ya shirya ya tafi Abuja saboda Jalilah da take ta kiran sa har tana iƙirarin idan bai zo ba ita zata taho. Satinsa biyu acan a tsayin kwanakin da yayi kuma har ita kanta saida ta fahimci baya cikin nutsuwarsa.

Bai tsammaci zai damu da tafiyar Halima haka ba kuma ya kasa kiranta saboda zuciyar sa dake raya masa idan ya kirata zai buɗe ƙofar da zata sake zuwar masa da wani rainin gara ya rabu da ita da kanta idan ta huce yasan zata neme shi su daidaita sai dai kuma wani ɓangaren na zuciyarsa yana raya masa rashin kyautuwar abinda yakeyi ɗin. Ya mata laifi kuma kamata yayi ya rarrasheta ya nuna mata ya karɓi kuskurensa ba wai ya wofantar da ita haka nan ba.

A bakin Hajja yaji ashe ma bata da lafiya har ta kwanta a Asibiti ya kuma ji babu daɗi sosai dan a ranar har sai da ya kira wayarta amma yaji ta a kashe kuma dai ko giyar hauka yasha ba zai fara kiran wani daga cikin Ahalinta da sunan ya tambayi halin da take ciki ba dole ya haƙura ya bar damuwarsa a ransa akan sai ya dawo tukunna yaje ya dubata yanzun yanda zai samu ya shawo kan Hajja data kunno masa wuta akan zancen Jalila har ta samu Kawu Sani ta gaya masa ya sanarwa Yayyensu Bilal da suke Uba ɗaya za'aje nema masa aure tuni har ta fara shelantawa dangi da maƙwafta da suke ta surutun an ce baƙin cikin Bilal ne ya ɗorawa Halima ciwon zuciya ya kuma korata gida can iyayenta suyi jinyarta labari na isketa ta ringa sababi tana tijara wai sun ɓatawa ɗanta suna saboda sun rufa mata basu faɗi abinda tayi har ya koreta gidan ba shine su zata bibiye su da sharri?

Ba tsoron Allah ta ringa shirgawa mutane ƙarya akan wai aure zai ƙara shine ta nemi ta illata shi da nata samu nasara ba shi ne ta ci shinkafar ɓera shine dalilin da ya saka ya mayar da ita gidansu karta mutu a laƙa masa sharri.
Da ya nuna rashin jin daɗin maganar da suka ƙulla haka nan take kuwa ta rufe shi da faɗa tana cewa
"Ka fita daga ido na Bilal in kulle, ko ka shirya ko baka shirya ba ni na shirya aure zaka ƙara dan ma kaji da jinka kuma zanje in samu Sani yau ɗin nan ba sai gobe ba su shirya su tambayo maka auren ayi kowa ya huta. Banda ƙaddara dama ai Halima ba matarka bace iya zaman da akayi ya isa ka aika mata da takardarta kawai in san kun rabu gaba ɗaya mu tattara hankalinmu akan wani abun kuma". Ko kafin ya sake cewa wani abu ta katse wayar ta shiga mitar duk yanda akayi wani baƙin asirin aka yi masa ake so a kautar da hankalinsa toh kuwa muddin tana raye Bilal ya gama zama da Halima domin aurenta bai musu ranar da suka tsammata ba. Nan yayan ƙawayenta da suke auren yaran masu kuɗi tana kallon yanda ake sauke musu kaɓakin arziƙi. Kayan azumi, turamen sallah masu tsada haka da babbar sallah a gwangwaje su da tiƙa tiƙan raguna Hajji da Umarar nan duk an kaisu amma ita komai shiru saboda baƙin hali ita kanta yar tasu ma mugunta suke mata suna jira sai dai miji ya mata toh ina dalili? Gara dai kowa ya kama gabansa can ga irin wacce ta dace dashi ya samo wadda abun hannunta bai rufe mata ido ba kuma ba yar gari ba balle a samu munafukainsu zugeta yanda aka zuge Halima tunda itan ma ai farko ba haka take ba.

Da yammacin ranar ta kama hanyar gidan Kawu Sani ƙanin mahaifinsu Bilal ɗin, matarsa Suwaiba mutuniyar Hajja ce dan tare suke yawon biye biyen Malamansu ko yanzun ita take mata yawace yawacen saboda ciwon da taji a can kuma aka gaya mata ai Jalila ita ce matar arziƙin Bilal ba Halima ba kamar yanda Malamin ya fara faɗa musu a farko ya kuma ce musu ba zai yuwu su zauna tare ba sai dai ya saki Halima in dai yana so taurarinsa su haska dan ita take danne shi.

Sanda taje Malam Sani baya nan amma Suwaiba ta gaya mata ba nisa yayi ba dan haka suka ƙule a ɗaki suka cigaba da tattaunawa, sai bayan Magriba ya dawo, dake Suwaiba ta rigada ta gama karanta masa ƙarya da gaskiya akan abinda ya faru haka ya ringa faɗa har yana cewa sun haɗu da Alhaji Aminu a masallaci ya masa kallon banza shi dama tun farko dan dai sun dage ne amma bai ga abinda suka hanga a tattare da gidan Alhaji Aminun ba. Kan ta tafi ta jaddada masa ya san yanda zai sha kan yayyen Bilal ɗin da suke uba ɗaya su tafi neman auren tare tunda gidan manyan mutane za'a je kuma yan boko ya kamata shima su san ba banza bane yana da tsayayyu.

"In zai yuwu ma ni a ɗauro auren kawai ba sai an tsaya jeka ka dawo ba tunda naga yanzu ai haka akeyi ko?" Ta faɗa tana zura takalmi daga nan sukayi sallama ta wuce tana sake jaddada masa kar a wuce satin nan fa ba tareda an je neman auren ba.

Sati biyu yayi ya dawo da kuɗaɗe masu nauyi wanda Jalila ta bashi akan za'ayi gyaran gidan da zata zauna. Sun gama magana akan nan da wata biyu za'ayi komai da komai na auren su saboda Dadynta baya nan dan haka da zarar ya dawo za'ayi komai na auren su a wuce gurin. Ransa fes da samun kuɗin domin kuwa zasu ishe shi yayi duk hidimar aurensa da Zulaiha dukda ba wani biki za'ayi ba ko da ba haka ya so ba amma a yanda auren ya zo dole ya haƙura da duk wani buri da ya ciwa lokacin auren nasu.

Damuwar sa bata wuce ɗaya zuwa biyu ba, ta farko yanda zai shawo kan Hajja ta amince da al'amarinsa da Zulaiha sai kuma Halima duk da ita ya san ba wata matsala bace sosai amma kuma har ransa yan jin yanda zata karɓi auren da zaiyi itama. Ganin lokaci yana ƙurewa domin bai fi saura kwanaki biyar ya rage cikar kwana arba'in da rasuwar mahaifin su Zulaihan ba kuma kamar yanda Kawun su ya sha alwashi yace ranar zai aurar dasu dan haka ya yanke shawarar zuwa ya samu Baba Sani kawai kuma cikin ikon Allah daya haɗo gabas da yamma ƙarya da gaskiya ya faɗa masa akan shi ba waccen yarinyar ta Abuja yake so ba Hajja ce kawai take so ya aureta saboda yar masu kuɗi ce amma shi wannan ita yake so tun ma kafin Halima Hajja ce taƙi, ya gama kawo masa bayanai wanda Kawun kuma gamsu dasu ya tabbatar masa da ya kwantar da hankalinsa.

"Ni na rasa me yake damun Hajjaju, ita dai kuɗi kawai bata duban mutunchi. Yanzu idan da gidan talakawan da suka san ƙima da mutunchi kayo aure ta ina haka nan yarinya zata kwashe kaya ta tafi gidansu dan za'a mata kishiya kuma dake iyayenta ba dattijai bane a rasa wanda zai biyo sahu yaji dalili aa suna jira mu mu bisu kenan muji me akayi mata da tayi fushi ta tafi ai wlh ka burgeni da ka rabu da ita idan sun gaji da kansu zasu magantu ai tunda dai ba uban da zai so yarsa ta dawo gabansa da sunan zawarci a wannan lokacin da muke ciki, rimi rimi lokacin auren nan kai kace mutanen kirki ne yanda akayi harkar girma da arziƙi ashe abun bai kai zuci ba" cewar Baba Sani. Shi dai Bilal bai sake cewa komai ba dukda he felt guilty yanda ya kawo sukar Halima domin wanke kansa kuma gashi Baba Sanin ya hau yayi daram akai amma ya zaiyi?

Bai bar gidan ba sai da ya aje masa kuɗin aure da sadaki da zasu kai ya kuma yi masa ihisani mai tsoka ya kuwa ringa saka masa albarka yana jaddada masa karya ji komai yaje yayi shirye shiryensa kawai Hajja kuma ya barshi da ita ya san yanda zaiyi mata. Hankalin sa ya kwanta domin ya gama da wannan ɓangaren, nan ya shiga gyaran gidan Jalilah domin dai ba zai haɗa Zulaiha da Halima gida ɗaya ba.
Hankali kwance ya shiga irgen kwanakin da suka rage gefe ɗaya kuma yana shirya yanda zai tunkari Halima itama bayan ya gama da sabgar Zulaiha.

HALIMA

Ina kwance a ɗaki idanuwana rufe ina latsa digital counter dake hannuna laɓɓana suna motsawa a hankali, tunda na zubar da komai na koma ga Allah na durfafi Istigfari, hailala, salatin annabi da wurudin Hasbunallahu wani'imal wakeel na samu sauƙi sosai cikin al'amurana. Nauyin da nakeji a ƙirji na ya ragu haka faɗuwar gaba da cushewar tunani haɗi da ɗimuwar da nake shiga duk sun barni.

Cikin abinda bai kai sati ba nutsuwa ta saukar mun sosai hatta da gangar jikina kuma ta nuna hakan kuma ko jiya da muka koma Asibiti check up a gwajin da aka mun likita yace an samu cigaba sosai sai ɗan abinda baza'a rasa ba kawai yayi saura. Dukda haka can ƙasan raina ina jin Bilal sai dai tasirin addu'ar da nakeyi ya disashe duk wani abu da a baya nakeji a duk sanda na tuna shi, bana jin farin ciki haka bana jin baƙin ciki, gaba ɗaya na zama neutral.

Dana fuskanci yawan shirun da nakeyi yake sakani tunani a dole na fara tilastawa kaina zama cikin mutane dukda na rasa yanda zanyi da Mama akan fushin da ta ɗauka dani har magana nayi mata na roƙi tayi haƙuri idan ma wani abu na mata daya ɓata mata rai take fushi dani amma tace babu komai a hakan nake shisshige mata ina mata magana wani lokacin ta kulani muyi hira wani lokacin sai sai na haƙura na tashi, Abba dai ba ruwansa daɗi sosai yakeji da canzawar da nayi dan haka idan yana gida muna tare dan wani lokacin har sai na gaji ma da hira nace masa zanje na kwanta kafin zai rabu dani na kuma sha jin sa yana yiwa Maman magana akan abinda yaga tana yi mun yanzu amma shima ɗin sai dai tace masa babu komai.

Yau ɗin ma ni kaɗai ce a gidan Mama sun fita tareda Zainab da Sharifa dubo Inaayan Anty Labiba da bata da lafiya. Har na shirya zan bisu kuma kawai na fasa dan na san gidan nata ba zai rasa yan dubiya dan dangin Mijinta nasa raina abun taro ciwon kai wani yayi har idan sun samu labari haka zasu yo ƙungiya suzo a wuni ana cecekuce.

Waya ta dake gefe ta ɗauki ƙara, sunan Suhaila da na gani yana yawo ya saka na janyota na amsa da ƙaramar sallama. Daga can ɓangaren tace
"Ashe bacci kukeyi tun ɗazu ina ta buga ƙofa na ɗauka ma ko bakya nan". Na ɗan yi shiru kafin na fahimci abinda take nufi can gidana taje dan haka nace mata

"Ai kuwa dai bana nan wlh"
"Subhanallahi, dama Honey ya mun baki yace na kiraki kar nazo bakya nan gashi kuwa, idan ba nisa kikayi ba sai in jira ki dan wuni nazo miki yau" ta sake faɗa a ƙoƙarin ta ƙyaleni ta tafi sai na ce

"Ai kuwa nayi nisa ina can gidanmu wlh" na ajiye wayar bayan da tace mun "toh shikenan".
Tunani na tafi bayan na ajiye wayar shin Mijinta bai faɗa mata bana gidan bane ko kuwa shima bai sani ba? Amma dai da wahala yanda suke da Bilal ace bai sani ba dukda dai Aisha Matar Nasir ma ba'a fi kwana uku ba ta kirani tana tambayar ina gida ne zata zo nace mata Aa, ƙila bai faɗawa abokanan sa ba ko kuma ya faɗa musu matayen nasu ne basu faɗawa ba oho musu dai.

Jin an fara shirin shiga sallah da yake juma'a ce ya saka na miƙe na ɗauro alwala domin dai yanzu Alhamdulillah na hau saiti ina matuƙar ƙoƙari gurin dai daita ibadah ta da kuma yinta akan kari, ina raka'ar ƙarshe na jiyo sallamar Suraj daga falo, sai da na sallame kafin na fito har sannan kuma yana tsaye ya ce mun wai nayi baƙuwa tana waje amma basu buɗe mata get ba dan basu santa ba gashi kuma ni kaɗai ce a gidan sun ce ta kira ni a waya tana ta kira ban ɗaga ba. Wayar na ɗauko naga Suhaila ce ta kira har sau huɗu nace ya buɗe mata ta shigo dukda nayi mamaki ban zaci zata ce zata biyo ni nan ba.

Sai da na kawo mata ruwa na koma na zubo mana abinci kafin na zauna muka sake gaisawa tana kallo na tace
"Amma kinyi rashin lafiya Maman Dady?"
Nayi ɗan murmushi kawai ba tareda nace komai ba ita ɗin ma sakin maganar tayi ta kamo wata, bata bar gidan ba sai bayan la'asar har sannan kuma su Mama basu tafi ba sai na ringajin kamar kar ta tafi dan sosai kuma naji daɗin zuwanta dan Suhaila akwai hira, muna tsaye jikin motarta bayan dana rakata waje ta kalleni tace

"Kinga zan manta Honey yace idan mun haɗu da Bilal in ce yana gaishe shi kuma Allah ya bashi haƙuri idan laifi yayi masa haka da ya share shiz toh na bar miki sallahu tunda bamu haɗu ba" daga haka taja motarta ina tsaye harta fice daga gidan kafin na koma ciki raina cike da tunanin sallahun data bar mun. Yanda Bilal ya ɗaukaka Hafiz mai zai saka ace har yana cigiyarsa a gurina? Naga kusan kullum suna tare idan ba a office ba Bilal ɗin ze je can gidansa ko gurin siyar da motocinsa, na taɓe baki a fili na ce
"Sun fi kusa" daga haka na shiga tattare gurin da muka zauna bayan na gama na shiga kitchen na fara ƙoƙarin ɗora abincin dare ganin yamma tayi har sannan kuma basu dawo ba.

Ranar Juma'a ta kama sadakar Arba'in ɗin Mahaifinsu Zulaiha a ranar kuma kamar yanda kawunsu yayi alƙawari bayan an sakko daga masallaci ɗaiɗaikun mutane suka shaid ɗaurin auren Bilal da Zulaiha sai kuma Nuratu da Zahraddini angonga. A zauren gidansu aka ɗaura auren cikin mutanen da suka halarta kuma mutum biyu ne daga ɓangaren Bilal, Kawu Sani sai Baba Mudan shima kawunsu ne abokanan wasa suke da Kawu Sanin da kuna mahaifinsu Bilal. Shi kaɗai Kawu Sanin ya kira ya shaida masa komai suka tafi tare, basu baro gidansu Zulaihan ba sai ƙarfe biyar da wani abu saboda Kawunta daya tsayar dasu da waliyyan ɗaya angon ya nemi tayar musu da sabuwar rigima akan shi fa sai dai azo a ɗauke amare a yau ɗin domin bai ga dalilin da zai saka a ɗaura aure kuma a bar yara su cigaba da zama a gida ba. Daga Kawu Sanin har waɗancan waliyyan angon su kuma suka ce basu san zance ba domin aure yace azo a ɗaura kuma sunzo yara kuma basu gama gyara in da zasu ajiye mata ba idan da yasan haka ne sai ya bari ayi komai a nutse ba yanzu ya sake cewa zaiyi musu titsiye tofa sai a warware auren can ya aura musu duk wanda yaga dama tunda abun nasa kuma ya zama da ɗiban albarka.

Kamar hatsaniya zata kaure har saida matan cikin gida dangin Mamansu da da wata yayar Babansu suka fito ita ta tsawatarwa ƙanin nata ta basu haƙuri kafin suka watse kowa ya fito a fusace. Kawu Sani ya kalli Baba Mudan ya ce
"Anya Mudansiru mutanen nan na kirki ne kuwa? kaga fa yanda mutumin nan yake zare mana ido kamar wasu yayansa yana faɗa mana maganganu, ni wlh shaf na sha'afa na tambayi yaron nan ya ma yi bincike da kyau akan asalin yarinyar ko kuwa dan ni kwatancen da ya mun sai da muka zo naga ashe ba Sulaimanun da nake zato bane Babannasu". Baba Mudan yaja numfashi ya ce

"Gaskiya dai wannan ƙanin uban nasu ba za'a kwashe da daɗi dashi ba mutum ba lafazi ba magana mai daɗi wai mu muka sani idan ma sama zamu kai su shi dai a kwashe masa yara daga gida ya dena ganinsu ni wlh sai naga ma kamar ba cikakkun hausawa ba ƙirar jikinsu tafi kama data gwarawa". Haka suka cigaba da tattaunawa har suka ɓullo layin su Anty Labiba, a ƙofar gidan suka ci karo da Mama suna shirin shiga mota Anty Labiba na jikin get ta rako su. Maman ta gane shi tsaf saboda shi ya ringa zarya lokacin auren Halima da Bilal, suna haɗa ido kamar mara gaskiya yayi saurin ɗauke kai gefe kamar bai ganeta ba harda ƙara sauri suka wuce.

Anty Labiba da taga ta bisu da kallo ta tambayeta ko ta sanshi ne ta ce
"Surukin Halima ne ƙanin Babansu Bilal shi yayi masa walicci ma", Anty Labiba ta saki wani murmushi haɗi da girgiza kai tace
"Allah sarki, ƙila bai ganeki bane" Maman ta bata amsa da cewa
"Da alama" sannan ta buɗe mota ta shiga, Anty Labiba ta zura kai ta window tace mata

"Wai ya kuwa zo Bilal ɗin ko har yanzu?"
"Ina fa yazo Labiba?" Mama ta bata amsa sai ta taɓe baki tace
"Toh Allah ya rufa asiri bari na koma kar su ce na barsu su kaɗai" daga haka ta koma cikin gida Mu'azzam ya tayar da mota suka wuce.

Sanda suka dawo har na sauke jollop ɗin shinkafar da nayiz naji daɗi sosai yanda Mama ta nuna jin daɗin girkin da nayi, a daren har hira mukayi na gaya mata zuwan Suhaila, ina so in mata zancen Hafiz da yake cigiyar Bilal kuma naji tsoro kar na ɓata ɗan shirin da muka fara sai kawai nayi shiru.

A ɓangaren Bilal kuwa wunin Juma'ar cur kashe wayarsa yayi yana kuma gida sallar Juma'a kawai ya fita ana idarwa kuma ya dawo ya sake kulle ƙofa, sanda Suhaila taje ma yana ji har ta gama bugu ta haƙura ta tafi ya ɗauka matan unguwar ne masu zuwa gulma da sunan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login