Showing 66001 words to 69000 words out of 257873 words

Chapter 23 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

487

hawaye shaaa suka ɓalle mun, "subhanallahi Halima me kuma ya faru?" Ya faɗa yana gangarewa gefen titi. Haɗe kai nayi da guiwa na shiga rera kuka kamar wadda aka daka.

A karon farko tun auren mu naga rikicewar gaske tattare da Bilal akan ɓacin raina. Fita yayi ya zagayo ta in da nake na durƙusa kamar zeyi kukan shima yana roƙon na gaya masa mene ne. Se da nayi me isata kafin nace
"Yanzu saboda baka farin ciki da kyautar da Allah yayi mana shi yasa ko a fuska baka nuna mun ka sani ba, ni kaɗai nake shirme na kai ko a jikin ka" na sake fashewa da kuka. Se ya dafa kai kafin ya miƙe yana murmushi ya koma mazaunin sa.
"Na lura so kike kiyi surprising ɗina shiyasa nake acting along kar na ɓata miki shiri amma da na san ranki ze ɓaci akan haka da tun sanda na gane nayi magana. Kuma Allah ba wani daɗewa akayi ba, ranar da kika ce na siyo miki mangwaro ne shine nayi suspecting kuma dama na lura ba kiyi period da azumi ba. Nasan akwai shirin da kike yi da ya sa baki gaya mun ba kar nayi magana kuma na lalata miki" yayi maganar ta sigar da ko ba gaskiya ya faɗa ba dole na yarda da abin da yace. Har kaza ya siya mun ƙatuwa da yoghurt me sanyi, da muka isa gida kuwa a hannu ya ɗauke ni har da yi mun rawa wai dan na yarda yana murna da ƙaruwar da muka samu.

Baki san yanda nake son yara bane Halims, ko da kika ga ina yi kamar ban damu ba tun da mukayi aure bana so na ringa magana ne hankalin ki ya tashi bayan kuma bamu zamu bawa kanmu haihuwar ba amma ban taɓa zaton zamu tsallake watan farko na auren mu baki ɗauki ciki ba ke baki ga irin ƙoƙarin da nake yi ba?" Ya faɗa yana kashe mun ido. Da hannu biyu na rufe fuskata ina murmushi, daren ya shiga cikin dararen farin ciki na a gidan Bilal, washe gari da yamma muka je asibiti, an sake mun scanning cikin har yayi wata uku yana shirin shiga na huɗu, a hanya bayan mun fito daga asibitin yake cemun
"Naga da file ɗin ki na gida kikayi amfani, kuma na san kai tsaye daga account ɗin Abba ake cire kuɗin magani babu matsala?"

"Ka jika da wata magana kuma wace irin matsala? Duk yan gidan mu kasan asibitin da muke zuwa kenan nasan idan ma na canza wani ƙarshe hakan ne ze zama laifi shiyasa ban ma yi maka maganar kuɗin asibiti ba ko wani abu, da har ma na buɗe file a wannan asibitin na gaban mu dan can na fara zuwa ma kuma da naga dai nan ɗin ya fi sun kuma fi ma'aikata da kayan aiki shiyasa ban koma can ɗin ba" na bashi amsa.

Da dare se ga kiran Mama, tun da na jiyo muryar Anty Labiba a background dama nasan wani abun ta ƙulla ilai kuwa bayan mun gaisa Mama tace
"Ɗazu an turowa da Abban ku bill na kuɗin antinatal shine na kira naji shi uban cikin ne yace ba ze ɗauki nauyin sa ba ko kuwa kalar naki sanin ya kamatan ne yasa zaki ɗorawa Abbanki haƙƙin da ba nasa ba?"

Nayi shiru na kasa ce mata komai, bata damu ba taci gaba da cewa
"To baze biya ba, idan kina so kici gaba da awo a nan ki gayawa mijin ki ya yankar muku kati idan kuma yana da wani gurin da yake ganin yafi masa ki koma can tunda kin san dai tsare tsaren su da cin kuɗi kar ki kuskura ki ɗora masa abin da kika san baze iya ba" bata ma jira na amsa ba ta mun sallama ta kashe wayar ta. Ni dai kacokam na ɗora laifi kan Anty Labiba nasan ita ta zugata dan dai Abba baze ce baze biya mun kuɗin asibiti ba ita ma Maman a ra'ayin kanta ba zata hana ba se dai idan mazuga irin su Anty Labiba da Mu'azzam sun shiga lamarin. Rasa ta in da zan farawa Bilal magana nayi, batun ya biya mun kuɗin awo a wannan asibitin ma be taso ba dan tsakani da Allah a matsayin da yake kai yanzu services ɗin su sun masa tsada dama dai ace bashi da hidimar kowa ne se tawa da abin da zamu haifa balle ma nasan Bilal a yanda baya maraba da duk harkar kashe kuɗi bana zaton ko yana da sararin ma ze biya dan da an fara maganar asibiti dama ze ce shi yafi gane aje Aminu Kano ko Murtala sun fi manayan likitoci da kayan aiki privet ɗin nan duk kame kame ne.

Ganin a sati huɗun da aka ɗibar mun na komawa awo saura kwana biyar yasa nayi ƙundumbalar tarar sa safiyar wata asabar na faɗa masa Abba yace ya kamata mu buɗe file namu na kanmu ba naci gaba da amfani da na gidan mu ba. Bece komai ba amma fuskar sa kaɗai na kalla na gane sam hakan be masa ba, ranar litinin kuwa be fita aiki ba yace ma shirya muje asibiti a buɗe file ɗin, na ɗauka ma zamuje na nan unguwar dana fara zuwa tun farko ina kuma shakkar na masa maganar dan tun ranar asabar ɗin ya shiga ɗaure fuska be dai tafi hutun kulani daya saba idan munyi faɗa ba amma dai magana ma se wadda ta zama dole ce zeyi mun ba sakin fuska ba walwalar da muka saba.

Asibitin Murtala muka je, dama tun da naga mun ɗauki hanya jiki na ya bani amma ban ce komai ba, dake akwai wata cousin sister su dake aiki a gurin se gashi nan da nan an mun komai har an bani ranar zuwa awo muka juya gida. Gidan su ya sauke ni yace se da yamma zezo mu tafi, tun sunan Fadila zuwana biyu suma a tsaitsaye tare muke zuwa mu tafi tare se yau ne ze ajiye ni ya tafi tun kuma daga yanda Hajja ta amsa mun gaisuwa nasha jinin jiki na shi yasa yana tafiya na shige ɗakin da Fadila da har sannan bata koma gidan ta ba take na zauna a can. Na fito alwalar sallar azahar na tarar da Hajjan da Mama Usaina ƙanwar ta suna zaune a falo suna hira, ban san asalin zancen da sukeyi ba amma yanda suka canza magana da gani na se naji kakaryda gayya sukayi dan naji.

"Allah na tuba a zamanin nan lafiyar ɗan ka ma ace se kayiwa kanka mugunta, yan da haihuwar nan ta zama se addu'a kana ji kana gani a son kuɗi se ka kai ɗan ka in da za'a halaka shi kwanan sa be ƙare ba" Mama Usaina ta faɗa. Hajja ta karkace tace
"Kema dai kya faɗa, shi yasa kika ga nayi tsaye kan wannan yarinyar nace ta taho gida in da mun biye ta tasu suman da ɗan nan yayi aka fasa kukan mutuwa da can a gurin su take ai da tuni an binne shi wlh. Yana nan kullum yana zarya ta koma nace aa se tayi arba'in biyu tukun ta murmure ba zata koma da ɗanyan yanka a cuce ni ba. Su dai wanda suka sallamawa duniya nasu yayan ai shikenan se yanda suka gani".

Ina alwalar ina jiyo zantukan nasu se suka ma bani dariya, da zamu tafi Fadila take ce mun se sunzo, na ɗauka yawon arba'in take nufi kwana biyu da yin haka ina kwance da hantsi aka buga gida in buɗe se ganin ta nayi saɓe da babyn ta ga Abubakar da ƙatuwar akwatin kayan su. Da mamaki na basu hanya suka shiga, se da na basu ruwa da lemo muka gaisa kafin take ce mun
"Kin ganmu se yau ko?, se ɗazu su Hajjan suka tafi jiya ruwa ya hana tafiyar se yau ina ga ma yanzu sun sauka ai" Abubakar ya duba agogon hannun sa yace
"Ah ya kamata sun isa yanzu ina Kano ina Jos musamman kuma motar gida ai har hutawa ma sun yi yanzu kam, bari naje Anty se Anjima" yayi mana sallama ya fita.

Ni dai ban fahimci kan zancen nasu ba, bana girki da rana tun da Bilal na gurin aiki amma zuwan Fadila dole na tashi na ɗora mana. Da wuri Bilal ya dawo ranar, Fadila tayi ɗai ɗai a falo yanda kasan sun shekara da zuwa duk inda ka duba kayan ɗan ta gashi da kuka masha Allah tun da suka zo kunne na be huta ba tun ina mata kawaici ƙarshe na koma ɗaki nayi kwanciya ta ina jiran Yayan ta ya dawo naji ba'asin zuwan su. Yana shigowa kuwa ya fara hargagi, nayi saurin shafa addu'a dan na idar da la'asar kenan na fito na tarar dashi yana mata faɗa kamar ze mare ta, ashe kashi yaron yayi akan kujera ta kwantar dashi babu ko zani balle aje batun diaper ko napkin ina doso falon ƙarnin da ban san ko na menene ba ya fara hargitsamun zuciya.

Be amsa sannu da zuwan da na masa ba ya shige ɗaki se na bi bayan sa ina shiga kuwa ya rufe ni da faɗa kamar ni na kwantar da yaron.
"Toh ni yanzu menene nawa a ciki? Ka gaya mun zata zo ne balle na san tanadin da zanyi musu?" Na faɗa ina haɗe fuska, tsaki yayi, se a lokacin yake ce mun wai Hajja ce ta tafi Jos gidan ƙanwar ta zata yi sati biyu shine tace Fadilan ta taho nan gidan.

"Se da nace mata kar ta zo ta nemi gurin da zata zauna ko ta koma gidan ta amma taƙi ji to wlh ba zata zauna mun da wannan muguwar ƙazantar tata ba, ni mejego ko wadda ta zamar mun dole ma se naga kamun ludayin ta kafin nasan zaman da zanyi da ita balle Fadila da duk wanda ya zauna tare da ita se ya gane ƙazama ce ta bugawa a jarida. Ji yanda ta mayar da falon nan se kace na mahaukata toh wlh in kina son ganin farin ciki na tun kafin na fito daga wanka ki sallame ta ta kama gaban ta" ya faɗa yana wani kaɗa yatsa kafin ya shige banɗaki.

"Lallai ma" na faɗa a fili ina bin ƙofar daya bugo da kallo, wato in kore ta, ni ze shafawa kashin kaji kenan? banda ma ya raina mun wayo me yasa shi da aka gayawa zata zo be ce aa ba se yanzu ni in koreta in yaso a sakani a bakin duniya ace na kore ta daga gidan ɗan uwanta to wlh ba zanyi ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*Page 17*
Be ko saurari tayin abincin da na masa ba ya fice daga gidan bayan yayi wanka yana sake jaddada mun Fadila ta bar gidan kafin ya dawo, bayan fitar sa na shiga gyara falon da tayi mun kaca kaca da shi dan tun shigowar Bilal ɗin ta koma ɗaki na in da na sauketa. Na tabbatar taji banbamin da yakeyi tun da ba a hankali yayi maganar da ze fita ba, na ɗauka daya fitan zata tuntuɓe ni da zancen amma shiru se ma dawowa falo da tayi zata sake tarwatsa gurin na dakatar da ita ta hanyar ce mata ba nisa yayi ba yanzu ze dawo. Ina kallon ta ta harare ni harda murguɗa baki ta koma ɗaki.

Ranar raba dare mukayi muna tashin hankali da Bilal tunda ya dawo gurin goma ya tarar Fadila bata tafi ba ya tasa mun masifa tun ina bashi haƙuri da nuna masa rashin dacewar abinda yake son nayi har na kai bango nace ba zan kore ta ba ai ƙanwar sa ce kuma gidan sa ne idan da gaske baya buƙatar zamanta ya kore ta da kansa mana shikenan fa ina wuta ya sakani a ciki ya ringa zazzaga da tijara se naga ashe abinda ya mun akan kifi ma somin taɓi ne. Dana gaji na kwanta na juya masa baya se dai na kasa bacci ga ɗan Fadila da kamar ma sa gayya yake ta canyara uban kuka duk suka haɗu suka cazamun ƙwaƙwalwa.

Daƙyar na iya farkawa nayi sallah bayan dana samu bacci ya ɗauke ni, sosai kaina yake mun ciwo ga zuciya ta da babu daɗi. Ina idar da sallah na sake komawa na kwanta ban farka ba se ƙarfe tara harda wani abu. Se da nayi wanka sannan na fita daga ɗaki, Fadila na harɗe akan kujera da remote tana canza tasha, yanda ta kalle ni se ka ɗauka kishiyar ta ce ta fito ta wani basar ta maida kai abinda takeyi nima kallo ɗayan na mata na maida hankali na kan falon dake nan kamar yayi sati bega gyara ba ga kwanukan abincin a ajiye har sun bushe alamar ba amfanin safiyar nan bane harda cup dana hango sauran shayi a ciki.

Ji nayi zuciyata ta sake harzuƙa, ni ya kamata nayi jidali an kawo mun baƙuwa ba tare da an sanar da ni ba kuma tazo tana nema ta mayar mun da gida wani dandalin yan datti ga wani sabon raini da ban santa da shi ba tana nema ta fara gwada mun. Kitchen na wuce ba tare da na ce mata kanzil ba, ko me tayi tunani kuma se ji nayi tace
"Ina kwana Anty, se yanzu kika tashi kenan?"
Da lafiya na amsa mata na shige kitchen, nan ɗin ma kaca kaca komai yana zaune da ƙafarsa. Se da na gyara gurin tas kafin na buɗe fridge in fito da abincin da Bilal yaƙi ci se in ɗumama mu haɗa da baƙin shayi tunda banga alamar ya siyo abin karyawa ba, banga abincin ba se lokacin nayi realizing ai nama wanke kwanon cikin kayan dattin dana tarar a kitchen ɗin. Tunanin wanda yaci na tafiyi, nasan ba Bilal bane zuciyata ta raya mun Fadila ce.

Ina tsaka da jimamin irin wannan abu ta shigo kitchen ɗin tana haɗa fuska kamar zatayi kuka tace
"Kun san da masu jego a gidan saboda Allah se ku kwanta kuyi ta bacci? Ni wlh yunwa nakeji har jiri nake gani asan yanda za'ayi dani".

Ba yabo ba fallasa nace mata
"Wace abinci kuma kike nema bayan wanda kika ci?" Yanda tayi da ido kamae irin na mata ƙage se kuma ta watsa ido tace
"Wai abincin cikin fridge? Yunwa ce ta hanani bacci tun dare naci wannan na duba ma naga ko da dankali ko doya in soya mana naga babu se wani sauran bread na samu akan dining na haɗa shayi nasha amma ji nakeyi ma kamar ƙara mun yunwar akayi". Tunda ta fara magana nake kallon ta har ta kai aya, mamakin ƙarfin halinta nayi. Ɗan bread ɗin da take cewa fa kaɗan ne babu a guda in da dani da Bilal muka ci har saura se yayi mana shine take cewa wai beje mata ko ina ba.

Rufe fridge ɗin nayi ba tare da nave mata komai ba na wuce store, banda shinkafa da ƙwarorin taliya da macaroni babu abin da yayi saura a ciki, taliyar na ɗauka na haɗa da papper mix guda ɗaya daya mun saura na dafa mana mukaci ina jinta a wasance tana cewa wai na bata abinci babu kifi babu nama nayi kamar ban ji ba dan raina a ɓace yake bana so kuma na furta wani abu da daga baya ze zama abin magana tunda naga su basa raina abin laifi. Bata tayani da ko cangwal ba na aikin gida se hayaniyarta data ɗan ta data cika mun kunne. Ina gamawa na koma ɗaki na kulle ƙofa ta na bari akan tunda akwai sauran taliyar taci da rana.

Tunda na kwanta bacci ya kwashe ni ban tashi farkawa ba se ƙarfe uku harda mintoci na rana. Sallah na farayi kafin na leƙa naga halin da Fadila suke ciki, falon babu kowa se pillows dake hargitse kamar anyi wasan dambe. Ɗaki na leƙa nan ma bata nan babyn ta ma baya nan balle nayi zaton ko banɗaki ta shiga. Tunani na shigayi ina ta tafi? In da akwatin ta ke ajiye na duba nan ma babu hakan ya tabbatar mun da fitar taje ta dawo tayi ba ƙila gida ta koma amma me yasa zata tafi bata gaya mun ba?

Ji nayi hankali na ya tashi, kar dai Bilal ya dawo ya kore ta, amma kuma da ya dawo gidan dole ze tayar dani ko da yake tunda ba abin ƙwarai zeyi ba be zama lallai ya tashe ni ɗin ba tunda yasan zan hana.
Duk se naji babu daɗi, layin ta na shiga kira wayar tayi ta ringing ba'a amsa ba dana sake kira kuma se na jita a kashe. Har na mayar da akalar kiran kaj Bilal se kuma na katse na bari idan ya dawo zanji dalilin da yasa be haƙura ba ya koreta. Haka na ƙarasa wunin rai babu daɗi, biyar da rabi ya dawo sallama ma ciki yayi be amsa sannu da zuwan da nake masa ba ya wuce ɗaki abin sa se na tashi na bishi. Ganin ya shiga wanka se na koma na haɗa masa abinci, shinkafa da wake da mai da yaji dan bani da ko ƙwayar attaruhu balle nayi miya ko jallof nasan kuma yanda yake fushin nan ba siyowa zeyi ba. Har ya zauna na manta ban aje masa ruwa ba na koma na ɗakko da sauran zoɓo roba ɗaya daya rage Fadila bata shanye ba.

Yana ci ina satar kallon sa yanda kasan me cin guba, na tabba harda yunwa tasa shi ci ba tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login