Showing 9001 words to 12000 words out of 257873 words
bakwai yanzu ta haifi Amina takwarar Mama. Ba ƙaramar kunya naji ba sanda Bilal ya gama zamansa a falon Antyn ya tafi ba tareda ya bada ko sisin kwabo da sunan barka ba. Dama tun kafin suna dana ke masa hirar me ya kamata mu siya na takwarar da akawa Mama ya fara kawo zancen wata yazo ƙarshe har yanzu ba'a fara salary, a zato na ze bada wani abu amma se gashi ya tashi ko asi dukda uban naman suna da abincin da na jibga masa har yan gidansu seda suka ci.
Kwananta goma sha shida da haihuwa na koma gida saboda wata ƙanwar Mijinta bazawara data zo daga zaria, sena fake da zanje na maida kaya na na ɗebo wasu daga nan na fece ba komai ya saka hakan ba kuma illah Munir dake neman takura rayuwata yana kuma haɗa ni faɗa da Bilal. Ranar talata na koma gida Bilal baya gari yaje Jos mijin ƙanwar Hajjan su ne ya rasu babban mutum ne sosai shine duk suka tafi. Ranar alhamis zasu dawo tunda suka tafi kullum mukayi waya kwana uku kacal amma ya ringa mitar yayi missing Kano yayi missing abincin Kano ze kace wanda ya tafi wata ƙasar ta daban. Ran da ze dawo tun safe na tashi da shirin yi masa girki, na yi da ɗan yawa tunda duka tare da Hajja da yayyensa mata biyu da ƙaninsa ɗaya suka tafi se matar wansa nasna kuma duka a gidan Hajjan zasu sauka kan kowa ta tafi gidansu. Ina aikin Mama namun tsiyar da sakani tayi se nayi ƙorafin abincin yayi yawa amma dake na Bilal ne na zage inayi sedai kawai nayi murmushi har na gama na shirya komai nayi wanka a Adaidaita na ɗauki Amirah muka tafi gidan bayan munyi waya ya gaya mun sun dawo.
Ba wannan ne zuwa na na farko gidansu Bilal ba, badan ma Mama ta kafta mun warning ba da haka nan ko faɗa mukayi na kirashi a waya be amsa ba zan zari jiki in tafi, tun Hansa'u na rakani har ta dena yanzun ko nasan ko giyar wake nasha bazan cw tazo muje ba shiyasa ma naja Amirah ko Maman ce mata nayi Aliyu me Adaidaita zan bawa ya kai musu ni kuma zan wuce gidan kitso badan ba nasan ba zata bari in kai abincin da kaina ba. A kuyance muka gaisa da yan gidan nasu suna ta nan nan dani kamar su goyani ban wani jima ba nayi musu sallama muka fita se da muka fito waje kafin naga Bilal dan sanda muka je ance yana ɗakinsa yana wanka. Se naga kamar ya rame a kwana ukun da ban ganshi ba, ya jingina jikin bango yana kashe ni da kallon so yace
"Ashe dagaske kike zaki zo"
"Oh da ka ɗauka da wasa nakeyi? Ai na gaya maka zanzo nawa Hajja gaisuwa dama" na bashi amsa seta miƙe tsaye sosai yana cewa
"Kin kyauta, kuma naji daɗi sosai". Ya shafa cikinsa yace
"Kin san ruwan tea kaɗai nasha muka kamo hanya, ina kwanukan kuma na ganki ke kaɗai?"
"Suna cikin gida na bashi amsa" se ya wani kalleni yace
"Cikin gida kuma? Abincin nawa kika kai mun cikin gida Halims? Maimakon ki buga mun ƙofa ki ajiye a nan kafin ki shiga?"
Se naji abun wani iri amma na kanne nace
"To banda abinka dama abincin ai ba kai kaɗai nayiwa ba kuma yana da yawa zasu ɗiba nasu su rage maka"
"Ragowar wasu zanci kenan?" Ya faɗa kamar a fusace, se kuma yayi shiru na tsaida idona akansa ina karantar yanayin fuskarsa, se kuma yayi murmushi yace
"To an gode My Halims Allah ya bada lada. Bari na shiga ciki muyi sallama da Yaya Zubaida nasan yanzu zata wuce se nazo na raka ku". Gefe muka tsaya kusan minti biyar ya fito kamar ransa a ɓace, Adaidaita ya tare mana muka shiga ganin ya tsaya be shiga ba yasa na kalle shi nace
"Ka fasa raka mu ne kuma?"
"Zanzo kawai anjima, yanzu zanje gidan gidan Muslim ne naga ko zan samu abinda zanci dan yunwa nake ji sosai wlh". Da mamaki nace
"Wannan abincin kuma fa?" Ya ɗauke kai gefe yace
"Sun cinye, kin san duk bamu wani tsaya munci abinci ba muka taho shiyasa dama da a gurina kika ajiye na ɗiba nawa se na kai musu sauran".
Harga Allah seda naji wata kunta ta kamani amma kuma yunwar da yace yanaji ita ce a gabana yanzu dan haka nace
"Amma basu kyauta ba, to ko muje gida se na dafa maka ko indomie ce. Matar Muslim dake fama da kanta babu lallai ai tayi girki ma". Seda yayi jimm kafin yace
"Amma ba zaki wahala ba? Kin gama wannan girkin ki sake yin wani?"
"Dafa maka abinda zaka ci kake kira da wahala?" Na faɗa ina langwaɓar da kaina ina kallonsa. Me Adaidaitan ya kalla kafin yace
"Shikenan nan, kuje bari na canza kaya se na taho" ya ciro ɗari biyar daga aljihunsa ya bawa me Adaidaitan, seda ya karɓi canji kafin ya koma cikin gidan mu kuma muka wuce. Kallona kawai Mama tayi sanda nake gaya mata zan sake dafawa Bilal abinci wancan da aka kai musu ya ƙare,
"Wato gidansu kika je? Ke wace irin yarinya ce mara jin magana anya Halima kina son ki siyawa kanki ƙima da mutunchi a idon dangin Bilal kuwa? Banda ke sakarya ce a ina kika taɓa ganin mace na zirgilli irin haka akan namiji?" Mama ta faɗa cikin ɓacin rai, nayi ƙasa da kaina kawai na kasa ce mata komai ta cigaba da bambamin faɗa kafin ta wuce ɗaki, seda ta kullo ƙofa sannan na wuce kitchen jiki na rawa na ɗora masa Indomin. Kaji biyu na saka a abincin da na musu ɗazu, dubu biyar Abba ya bani yace nayi cefane harda lemo katan ɗaya da ruwa shima katan na siya musu. Seda na duba freezer babu sauran nam se kifi, Bilal baya son kifi dan haka kawai na daga masa ita da karas da kabeji na soya masa ƙwai guda huɗu. A falon Abba na shirya komai, seda na fita tsakar gida zan wanke kayan da nayi amfani dasu dan famfon cikin kitchen ɗin ya lalace se na gashi tsugunne gaban Abba suna magana.
Ban sam me suka tattauna ba na koma ciki bayan ya shigo seda ya cinye indomin tas yasha lemo kafin ya kalleni yana murmushi yace
"Se yanzu na fara gane kaina"
"Dole ai, ka sha tafiya ga yunwa kuma ai kayi ƙoƙari ma" na faɗa ina murmushi se yace
"Yanzu Abba yake mun magana. Ai ma zata ma kin gaya masa abinda na sanar dake se yace mun wai kin ce masa ƙarshen wata za'a zo gashi watan ya mutu wani ya kama shima harya ƙare shiru me yasa zaki masa ƙarya?"
Kallonsa nayi jin abinda ya faɗa wai nayiwa Abba ƙarya, bance masa komai ba na maida kaina ƙasa ina jan zaren mayafin jikina ina jinsa yana cewa
"Kin kasa fahimtar abinda nake gaya miki Halima. Bawai bana son azo maganar saka ranar nan bane aa ina duba abubuwan da suke gabana daya kamata na kammala kafin ace an fara maganar aure. Yanzu idan akayi sa rana kowa ze tada hankalinsa ne da son jin yaushe za'ayi biki, da zarar an ɗan samu akasi an ɗaga daga sanda aka faɗa se kiji maganganu su kansu iyaye zakiga sun ɗauka kamar mutum ya shigo da shiririta cikin abun. Ni yanzu babban abinda yafi tsayamun shine na kammala gini na kin san kuma dai gini abu ne me buƙatar tana di da lokaci dan ko da kuɗin a zube kin san aikin gaggawa baya ƙarko"
"Haka ne" na faɗa ina kallonsa ƙwaƙwalwata na son bawa maganganun sa ajin daya dace dasu. Yaci gaba da cewa
"Kin san ina da taste, akwai plan ɗin dana tsarowa gini na da idan yanzu nace na katse ko na canza da wani abu daban baze bada yanda ake so ba. Kinga ginin nan shi kaɗai ne nake so ace na kammala duk wata sauran hidima za'ayi abinda ya samu ne na sani lefe ma zaki iya yafe mun ko My Halims tunda dama ke ai kullum cikin sababbin sutura kike ko waɗannan na jikinki ma ai ban taɓa ganinki dasu ba" ya ƙarasa yana wata dariyar data ƙular dani, kafin nace wani abu ya tareni yana cewa
"Wannan bayanin nake so kiyiwa Abba nasan zw fahimce ni tunda ina da hujja me ƙarfi ko shi Baba Salahun idan aka fahimtar dashi ze gane".
"To amma Bilal me ze hana ka kama haya mana ko da na shekara ɗaya ne pending ka ƙarasa ginin naka? Na faɗa bayan dana gama jin nasa uzurin, seya wani kalleni kamar wadda na faɗa masa mugun abu yace
"Haya? In kama haya fa kike cewa Halims? Yanzu ke ba zakiji kunya ace gidan haya aka kaiki ba?"
"Wace irin kunya kuma Bilal mutane nawa suke rayuwa a gidan haya? Ita kanta hayar ai se wanda ya isa ne ma yake da hali ze kama naga wasu sedai su nemi a basu aro" na bashi amsa ina ɓata fuska seya girgiza kai yace
"No Halims wace irin haya ana zaune ƙalau se kace matsiyaci. Mu gama zagin abokananmu saboda rashin zuciya sun kasa mallakar gidan kansu se kuma kawai nima na ƙare a haya bayan Allah ya rufa mun asiri ina da yanda zanyi"
"Oh ashe ma kana da yanda zakayin niyya ce kawai bakayi ba ko kuma nace auren nawa baka shiryawa ba. Da kuma zaka ce tsiya ce take sakawa ayi haya har kana zaginsu wasu da hakan shi muhalli tamkar rabon haihuwa da silar mutuwa Allah ke saukar dasu don yanda kaso da faruwar su ko kauce musu baka da wayo baka da dabara akai kuma idan Allah yaso ya nuna maka iyakarka seya jarabce ka kaima duk arziƙin ka ya hanaka mallakar gidan kan naka. Mutane nawa keda rufin asiri amma har suka mutu suka ƙare rayuwar su a gidan haya? Ka fito fili kawai ka faɗa mun abinda yake ranka game dani domin na fara gajiya da uzurin ka da basa ƙarewa kullum da wanda zaka zo dashi to kawai ka faɗa mun matsayar maganar mun, idan yi yi idan bari bari kawai nagaji da sa banga ƙaho ba Bilal" na faɗa ina miƙewa tsaye.
[5/18, 13:07] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 5*
A motar Nasir na ganshi, ya kame a ciki yanda kasan tasa. A raina nace kuɗi dai ze yi wa Bilal kyau dan kalarsu aka masa. Yanayin surarsa da irin kayan da yake sakawa ba zaka kalli gidansu kace daga nan ya fito ba. Yana son gayu, sau tari na kan raya a raina nan yake kashe kuɗin sa gurin siyan sutura da takalma haɗi da agogo masu tsada duk abin da samari sa'anninsa suke yayi zaka ganshi dashi hakan kuma yana burge ni duk da ba wadata ce dashi ba amma ba yanda za'a yi ka ganshi ka raina shi.
A gaban motar nima na kame Inayah ta shiga baya muka tafi muna hirar mu gwanin sha'awa, ban tambaye shi in da zamu je ba shima be gaya mun ba har muka isa Goron dutse cikin GRA dake bayan matatar ruwa (WRECA). Na ringa kallon unguwar, a iya sani na banda kowa a gurin shima kuma bamu taɓa hirar wani nasu a nan ɗin ba, cikin wani da ke jere da gidaje hagu da dama muka shiga, gidaje uku ne ba kammalallu ba a ciki ɗaya ma kamar da mutane a ciki benen sama ne ba'a ƙarasa ba se fili da aka zagaye da alama ba'a fara gina shi ba. A ƙofar kangon dake ƙarshe layin ya tsaye dake layin baya ɓullewa, ya kashe motar muka fita na cigaba da kallon gurin ganin ya nufi kofar shiga gidan ya buɗe da muƙulli yasa muka bi bayansa se dai ban shiga ba na tsaya a waje ina kallon cikin gidan.
"Ya kuka tsaya a waje? Ku shigo mana" ya fada bayan daya juya ya ganmu a tsaye. Se da na ɗan yi jumm ina kallon cikin gidan kafin nayi bismillah na shiga. Tsakar gidan bashi da girma sosai amma ze iya cin mota ɗaya ko ma biyu. Duk da ginin ba'a kammala shi ba amma yana yin tsarin yayi kyau. Akwai babbar ƙofa dake tsakiya tana kallon get, se kuma daga gefe can akwai wata ƙofar ƙarama. Ya buɗe babbar kofar ya shiga muka bishi, a cikin falon da ba'a yiwa fulasta ba ya tsaya yana kallona yace
"Barka da zuwa gidan Bilal". Se na saki murmushi, wato nan ne gidan da yake gina mana. Ya nuna bangon hagu in da ƙofa take yace
"Bedrooms ne guda biyu kowanne da toilet, suna da girma nasan zasu ci kowanne irin saitin gado". Seya matsa ya buɗe kofar dake bangon gabas yana cewa
"Nan kuma kitchen ne da store", waccen ƙofar ta waje kuma ɗaki ne da falo a ciki Master room kenan ina tunanin ko a faso da ƙofa ta nan" ya nuna mun ɗan corridor dake gefe yace
"Saboda sauƙaƙa miki zirga zirga tsakanin nan da can ko dan yanayi na ruwa da sanyi". Ni dai murmushi kawai nake kamar wata sokuwa. Ya buɗe ɗakunan muka leƙa har cikin toilets ɗin kamar yan da ya faɗa suna da girma sosai kam zasu ɗauki kaya har a samu gurin shimfiɗa carpet me ɗan girma. Har can part ɗin da yace nasa se da muka shiga, a nan naga ya aje buhunhunan sumunti da sauran kwanon da akayi rufi dukda saman gota ce se kayan toilet da sink na kitchen.Tsakar gida muka koma ya nuna mun ɗan filin dake kusa da part ɗin yace
"Da nan gurin Hajja tace se ayi ɗaki tun da ga banɗaki a tsakar gida dama ko da zamuyi baƙi maza masu kwana"
"Uhm" kawai na ce a raina ina lissafa ɗan abinda nake ganin ya rage a aikin ginin. Fulastar ciki ce dan an yi ta waje da ɗakuna guda biyu nawa, falo ne da kitchen suka rage se can ɓangaren sa.
"Yau kin ga gidanki" ya faɗa bayan da muka zauna a mota. Nayi murmushi nace "guri yayi kyau sosai Allah ya sa rai aka yi wa"
"Amin My Halims ai se ma an gama aiki an gwagwaje gurin da kaya yan kamfani kyansa ze sake fitowa" ya bani amsa na amsa masa da
"Haka ne, to Allah ya nuna mana lokaci". Shirun minti biyar ya gifta tsakaninmu ya ci gaba da tuƙi ni kuma na tsunduma tunanin abinda ya rage a aikin gidan yanzu wanda a gani na saura ne kawai tun da an yi me wuyar kammala ginin da rufi. Ni duk da yake ta zancen gini na zata irin ko linta be kai ba ashe ma ƙarashe ne kawai.
"Yanzu kin ga abin da nake gaya miki na akwai sauran shiri a gaba na ko?" Ya katse mun shirun, se na kalle shi. Ya ci gaba da cewa
"Ban siyi ko kwali ɗaya na Tiles ba. Ga gilasan winduna kin ga boggler kawai aka saka. Ban da ƙarashen fulasta sannan azo uwa uba wiring ɗin wuta da ruwa ga fenti dasu pop aikin fa ba ƙarami bane Halima".
Nayi kasaƙe ina sauraronsa, se da ya kai aya kafin nace
"Allahn daya hore akayi wannan ze rufa asiri in sha Allah"
"Haka ne" ya bani amsa daga nan be sake cewa komai ba har muka je unguwar mu. A hanya muka sauka ya wuce ina ɗaga masa hannu, se da na sake komawa gidansu Hansa'u cikin sa'a na tarar ta dawo nan muka zauna na shiga labarta mata yanda gida na yake.
"Lallai Halima ba kunya kika bishi ganin gida ko?" Ta faɗa se na harare ta nace
"Ji banza wai kunya. Kawai naje naga gidan ne wani abu da zan ji kunya lallai ma". Seda Mama ta kira ni kafin muka fito ta rakani rabin hanya. Sau biyu cikin zirgilli na ina kusan gaya wa Mama zancen munje ganin gidan se Allah ya cece ni na canza maganar da wata. Abin na mintsili na, nayi kamar na gayawa Anty Labiba se dai nasan yanda take a cike dani tsaf zata haɗa ni da Mama se kawai na kama kaina na bar murna ta a ciki na. Bilal dai da ake ganin be kai ba gashi nan cikin hukuncin ubangiji ze yi abinda kowa se yayi mamaki ga dai gida nan na nunawa sa'a da nasan iya kar masu ƙaryar kuɗin dai suyi kamar shi ko wanda be kai shi ba kuma a unguwar yan gayu da na tabbatar ƙasa tana tsada a gurin.
Shi ma a yanda yace filin na gadon sa ne ya adana gashi kuwa ya masa rana babu yanda masu gidajen kusa dashi da ma na nesa basuyi akan ya bar musu ba har musanyan ginannen gida aka bashi da cikon kuɗi duk yaƙi a cewar sa baze maida kamar sa ba kuma unguwar ta masa da irin tsarin rayuwar da yake so ya gudanar da iyalansa.
Watanni uku suka shuɗe cikin wata shida na ranar auren mu data rage har sannan kuma daga ɓangare biyu nawa dana Bilal ba zan ce ga wani shiri da aka fara na biki ba. A gidanmu dai nasan Abba ya yiwa Mama magana akan abin da ya kamata ayi tace masa suna kan lissafi ne idan ta gama haɗa komai zata sanar masa ban sake jin sun tada maganar ba. Ina da abubuwan da nake so a mun daga kan zaɓin kayan ɗaki zuwa sauran kayan amfani se dai ban ga fuskar da zan sakowa Mama maganar ba. Anty Labiba ko yanzu ban ma isa na doshe ta da wannan zancen ba tun da