Showing 255001 words to 257873 words out of 257873 words

Chapter 86 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

465

cewa
"Menene laifi a ciki Labiba? Zuri'a fa ta rigada ta shiga tsakani babu yanda za'ayi a raba. Tunda kunce ba zamuje ba ba'a mata kara ba ai sai taje da kanta"

"Tunda wani yace yaja ya damfari mutane ina ruwanmu da zuwar masa jaje? Dama ai ita take da jiɓi dashi idan ma zuwan ne ita ya kama kuma taje" Mama ta goyawa Anty Labiba baya. Zama nayi tunda Mama Fauziyya na nan na san ba zata bari su mun rubdugu ba.

"Ina Dr ko ba tare kuka je ba?" Anty Labiba ta sake soko wata maganar, na ɓata fuska Mama tace
"A haka dai shima kamar Namijin gaske amma ya zauna yarinya ƙarama tana juyashi. Tsabar sakarci wai har zaman kotu ya rakata ashe, dama zan gayawa Mudassir idan ba dagaske yakeyi ba ya kama gabansa in kuma auren zaiyi ya fito ayi a wuce gurin tun bata mayar dashi shashasha irinta ba. Ni na rasa wannan azababbiyar soyayya da kike yiwa Bilal sai kace wacce ya wanke ya bawa ta sha" Mama ta sake faɗa cikin fushi.

Miƙewa nayi na wuce ɗakin Amirah ina jin Mama Fauziyya tana cewa
"Sai a hankali, irin su Halima suna da yawa fa kawai dan ita muka fara gani shiyasa abun ya zo mana a sabo. Idan suka so abu kafin su barshi gaba ɗaya sai sun samu madadinsa. Wuyarta ɗaya ta samu wanda zai ringa mata irin soyayyar da take ƙulafuci a gurinsa shikenan zai zama tarihi kuma idan ba'a yi wasa ba idan ta tsane shi sai a ringa roƙonta data sassauta ƙiyayyar. Kawai dai yanda kika ce idan auren zai yi ya fito ayi a wuce gurin".

Haka sukayi ta juya maganar ni dai na shige ɗaki na kwanta bacci na fara fizgata wayata dana ajiye a saman pillow da nake kwance ta shiga ƙara ba shiri na tashi zaune ina tura baki kamar wani ya ajiye mun. Salman ne, sai da ta kusa katsewa kafin na amsa da sallama ya amsa ya ce

"Abba ya ce in turo ko kina so ko bakya so ya bani ke, zaɓi biyu ki zuba ruwa a ƙasa kisha idan kina farinciki ko ki bari idan aka kaiki ɗakina ki haɗe zuciya amma karki mutu dan nima binki zanyi".

A gurguje
BILAL
Ganin da yayiwa Halima sai ya sake dawo masa da komai saboda, mutumin daya ganta tareda shi kuma ya tabbatar masa da cewar tayi masa nisa. "Dama da irin sa ta dace ba kai ba" zuciyarsa ta ringa ƙara masa zafi. Duk juyin da zaiyi sai ya tunata, idan kuma ya tuna ya da yaransa suka nuna basu sanshi ba sai yaji dagaske dai ya tasarma rasa komai a rayuwarsa. Ya rasa duk abinda ya mallaka, ya rasa Halimarsa sannan yana shirin rasa yaransa amma ba zai bari hakan ta kasance ba.

Haka ya cigaba da jinya tsayin wata guda baya zuwa ko ina hatta masallaci sai da Hajja tayi dagaske kafin ya fara fita tace zamansa a gida ba zai canza komai ba sai dai tunani da damuwa su ƙarasa kassarasu kawai. Ita yanzu kacokam damuwarta tana kan Fadila da kowa yake cewa wai ta haƙura ta ɗauke kai tunda dai Fadilar taji ta gani zata zauna a cikin uƙubar da take ita na menene zata ringa ɗora danuwarta ranta kullum jininta yayi ta hawa sama?

Bayan dawowar Bilal Fadilan da mijinta sunzo gidan har yayi alƙawarin warwarewa Bilal ɗin sauran bashin da yake tsakaninsa da Jalilah. Haka Hajja ta manta da haushinsa takeji ta ringa masa godiya harda hawaye, Bilal dai ko a fuska bai nuna jin daɗi ba balle ma yayi masa godiya. Bakinsu ɗaya, kuɗin da yake maganar zai bata kuma dama ƙarya ce bai ci ba dan kayan daya ɗiba miliyan bakwai da motsi ya siyar dasu ya san kuma dukda karyar dasu yayi sunyi wutar duniya ace miliyan goma ba talatin ɗin data ƙaƙaba masa ba. Amma ya ya iya? Dama an ce tsuntsun daya ja ruwa ai shi ruwa zai doka.

Shikenan maganar Jalilah ta mutu dan kwana biyu a tsakani ta kirashi da kanta kamar ba zai ɗauka bama amma ya amsa, ta faɗa masa Ahlan ya biya masa sauran kuɗin da take binsa dan haka ya faɗawa lauyansa yaje kotu ya ƙarasa warware abinda yayi saura.

"Dukda mugun halinka Allah ya taimakeka ya haɗaka da mutanen kirki a rayuwarka. Ban zata Hafiz zai sake waiwayarka ba sai gashi ya biya maka tara. Toh ka saurareni da kyau, kada ka ɗauka shikenan iya wannan taskun dana sakaka kaci banza. Daga yau ba lallai ka sake jin ko da labarina ba amma kafin na fita daga rayuwarka ina mai tabbatar maka sai na bar maka tabon da har ka koma ga Allah ba zai taɓa gogewa daga zuciyarka ba Bilal" daga haka ta katse wayar shima yayi tsaki ya danna mata block.

Tunda sun rigada sun warware babu wani abu data isa tayi masa idan ma batayi wasa ba a yanzu zai ita ɗaura ɗamarar yin wasan Kura da ita tunda ba ita kaɗai ta iya haɗa sharri ba ai.

Haka rayuwa ta cigaba da gurgurawa tsakanin Hajja da Zulaiha ana zaman doya da manja, ba Hajja kaɗai ba hatta da shi kansa zama suke kamar wasu roommates na Hostel ya rasa dalili yanzu idan zasu kwana su wuni idan ba shi yayi mata magana ba ba zata ce masa uffan ba ko maganar yayi mata ma sai taga dama zata mayar masa da mai daɗi. Idan zaman gidan ya isheta ta gaji da sababin Hajja tayi wanka ta fice tace ta tafi gida.

Satinsu shida a gidan tace masa tace masa ita ta gaji, ko dai ya sama musu wani gidan su koma bata damu ba ko gidan haya ne mai ɗaki ɗaya yafi mata zaman nan ko kuma ta tafi gidansu, bata ce ya saketa ba amma zata tafi zuwa duk sanda ya samu sarari da zai samar mata inda zata zauna sai ta dawo.

Shi kansa a takuren yake toh amma bashida halin da zaice zai nemi gidan haya a yanzu. Yan kuɗaɗen da sukayi saura da Abubakar ya bashi a ciki yacd yayo musu siyayyar kayan abinci da zasu ɗan ja lokaci sauran kuma ya rike ya juya masa tunda bayan aiki Abubakar ɗin yana taɓa kasuwanci kuma ba laifi abun ya karɓe shi banda sabgar Bilal ɗin daya laƙume masa fin rabin jarinsa dole ya ture maganar aurensa data taso a gefe yanzu yake ƙoƙarin sake farfaɗo da jarin.

Tunani yayi ko ya karɓi wani abu a hannun Abubakar ɗin ya kama gidan sai kuma ya fasa dan har ga Allah ƙoƙari yakeyi ya gyara kura-kurensa na baya. Yanzun ya zama ba sawa babu hanawa, ba ruwansa da kowa daga gida sai masallaci tunda ta tabbata an koreshi daga aiki dama kuma shi ba wata sana'a ya iya ba balle yace zai yi shiyasa ma yace Abubakar ya juya masa kuɗin, idan
sai idan kaɗaici ya dameshi ya tafi Chemist Nasir na nan unguwar idan yana nan kenan dan yanzu kuzan branch huɗu gareshi a unguwanni daban daban, diploma da Bilal yake masa iskanci akanta wai ba abinda zata tsinana masa ya tafi suyi degree gashi da ita ya fara kuma ita ce tushen duk abinda ya samu a yanzu.

Ganin yanda Hajja da Zulaiha suka zama kamar wasu sa'anni kullum cikin kacenace wanda yake ganin kamar da gayya Zulaihan take yin abinda ta san Hajjan zatayi magana dole ya nemi sharar Nasir akan zancen neman gida ya ce masa hakan babu laifi dama ya sani da wahala zaman ya yuwu baya ga haka akwai takura dan haka ya barta ta tafi gida idan ya so sai ayi ƙoƙarin a nema masa ko ƙarami ne da zasu zauna kafin kuma aga tanadin da Allah yayi a gaba.
Shikenan Zulaiha ta koma gida Hajja ta huta da surutu.

Ranar Juma'a yana kwance a falon Hajja bayan an sakko daga sallar Juma'a, da zazzaɓi ya tashi ranar dan daƙyar ya iya fita masallacin yana dawowa kuma shine ya kwanta. Yana kwancen wayarsa ta shiga ƙara, yayi mamakin ganin mai kiran, Hafiz ne. Ji yayi yana jin kunyar magana dashi dan haka ya kasa ɗagawa har saida ta katse wani kiran ya sake shigowa kafin yayi ta maza ya amsa.

Muryar Hafiz a sake suka gaisa yace masa yana waje. Fita yayi ya tarar dasu su uku suka shiga ciki sai da sukayi jiran Hajja dake sallah a cikin ɗaki ta idar kafin ta lallaɓa ta fito suka gaisa. Damuwar Fadila data saka a ranta ta saka lafiya take mata wasa hawan jininta ya tsananta har ta dawo shan magani kullum.
"Idonka kenan Hafizu" Hajja ta faɗa bayan data zauna ba kunya, yayi murmushi suka gaisheta ta tambayeshi iyali sai lokacin Bilal yaji ashe Suhaila ta sake haihu mace.

"Ɗaurin aure muka zo can ƙasa, shine nace bari na ratso mu gaisa dan na jima ban yuwo ta nan haka ba" Hafiz ɗin ya faɗa. Hajja tace
"Allah sarki ai kuwa ka kyauta. Munji abin arziƙi da akayi ubangiji ya sa a ɗauka a gaba, tun lokacin nake cewa zamuzo har gida muyi godiya toh ka ganmu daga ni har shi ɗin mun zama lafi-lafiya, yau lafiya gobe ciwo"

"Allah ya rufa asiri ya ƙara lafiya" cewar Hafiz kafin ya juya kan Bilal da yayi shiru yana sauraronsu ya ce
"Wani abokinmu ne yayi aure, ba shiri ma fa tambaya aka zo ɗazu da safe kawai iyayen yarinyar suka ce a ɗaura aure. Shine yace dan Allah su bari a sakko Juma'a kafin nan ya sanarwa mutanensa na kusa aka taso mu babu shiri sai da mukaje gaisuwa bayan an ɗauro auren abin mamaki naga ashe Halima ce amaryar".

Yanda Bilal yayi sai ka ɗauka bindiga ko wuƙa aka nuna masa amma ya kasa cewa komai sai idanuwa da yake zarewa, Hajja ce ta tambayi wace Halimar ya bata amsa da

"Halima dai Maman Al'amin tsohuwar matarsa. Wlh nasha mamaki na kuma yi masa musu murna shi da ita dan kowanne ya dace da abokin zama na ƙwarai. Halima mutuniyar kirkice shima kuma Salman babu laifi na san shi junior na ne a secondary school kafin muka zama abokai a Jami'a sama da shekara ashirin da ɗori muna tare har familyn mu an zama kamar yan uwa".

Haka Hafiz ya tafi ya bar Bilal cikin yanayin da bai taɓa zaton zai shiga akan Halima ba. Ƙasa ya zame y zauna ya saki hawayen da suka cika masa ido, Hajja kanta ɗaki ta koma duk jikinta yayi sanyi. Zuwan da Halima tayi yanda taga ta zama wata babbar mace ko makaho ya shafata ya san tana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali saɓanin Bilal da tunda ya rabu da ita iftila suke dirar masa daga wannan sai wannan.

Tun ranar take lissafa ta inda Bilal ɗin zai fara gyaro ɓarnar daya tafka. Dukda Abubakar yace mata wanda suka zo tare wai Mijin da zata aura ne amma bata sare ba. Iya zuwan da tayi ya isa shaidar har yanzun akwai ɓurɓushin soyayyarsa a zuciyarta ba kuma za'a sha wahalar dawo da komai ba. Tana ganin idan har Allah ya yarda Haliman ta dawo Bilal ɗin zai samu madafa domin dai Mahaifin Halimar baze barshi haka ba sai kuma ga wannan magana wai ta ɗaura aure.

Bilal kuwa ɗaki ya koma ya kwanta yana jinyar jiki da zuciya. Bayan sallar isha'i yana zaune in da yayi sallah ya jiyo Hajja na ƙwala masa kira, yanda take kiran kamar ba lafiya ba ya fita da sauri a tsakar gidan ya tarar da ita da rarrafe ta fito daga ɗakin tana haki tace yayi maza ya nemo mata Adaidaita sahu da zai kaita gidan Fadila.

Taƙi ta masa bayanin komai dole ya fita ya taro mashin ɗin kafin yazo ya kamata suka kama hanya ko gidan bai rufe ba saboda yanda duk ta firgita shi. A hanya take ce masa "Kirana tayi tana kuka azo a taimaka mata zai kasheta saboda ya kawo karuwa gidan tace yaji tsoron Allah shine ya hau dukanta ya turota ta faɗo daga bene har yana cewa ni uwarta nice mazinaciya ba, tana can cikin jiini kuma wai ciki ne da ita" Hajjan ta faɗa tana rushewa da kuka.

Ranar da Halima ta buɗe wayarsa ya tuna har ya mareta ya kuma danganta mahaifiyarta da zina ce ta dawo masa, ya runtse ido ba tareda ya ce komai ba. Da suka isa suna tura ƙofar gidan ta buɗe suka shiga yana riƙe da Hajja dan bata ko taho da sandunanta ba saboda kiɗima. A falon ƙasa ta zauna suka ringa kiran sunan Fadila shiru tace ya hau sama ya dubo mata yarta. Haka nan ya ringa jin gabansa yana faɗuwa duk taku ɗaya da yayi akan benen, ƙofar falon saman ma a buɗe take an turo bata ƙarasa rufewa ba dan haka yana hango mutum biyu Mace da Namiji dake zaune Namijin yayi matashi da cinyar Macen.

Tura ƙofar yayi, dai-dai da gama buɗewa gaba ɗaya kuma idanuwansa sukayi kyakkyawan gani, irin ganin da Halima tayi masa a cikin gidanta shi yayiwa matarsa Zulaiha da Mijin ƙanwarsa.

Kwanansa uku a Asibiti kafin aka sallameshi tunda ya yanke jiki ya faɗi bayan kyakkyawan ganin da yayi. Zulaihan ce tayi jinyar sa dan bayan da aka kaishi Asibiti ita Hajja tace a kira tunda ta gudu yanzu da wahala tazo sai ta dawo tayi jinyar Mijinta. Da ace Hajja ta ganta a gidan Fadilan iya kumburin da idanuwanta sukayi ya isa ya sa ta fahimci mai ya faru dan Ahlan da Fadilan ce mata sukayi yana shiga falon ya yanke jiki ya faɗi tunda kuma ta san dama bashi da lafiya suka tafi bata musa ba.

Daga Asibiti bayan an sallame su ya cewa Zulaiha ta wuce gida, shi da ita ne a ɗakin ta fashe da kuka haɗi da durƙushewa a gurin tana cewa
"Wlh tilastani yayi. Cewa yayi idan ban amince ba zasu mayar da kai gidan yari dan girman Allah kayi haƙuri karka sakeni ina sonka kum wlh iya abinda ka gani ne kawai babu abunda ya shiga tsakaninmu banda wasannin daka gani".

Yanda take magana ya tuna masa da kansa sai dai a maimakon nadamar daya gani tattare da ita shi a lokacin cikin izza da nuna isa yake nasa bayanin. Dama tun ranar daya fahimci shine wanda ya gani tareda Jalilah jikinsa ya bashi hatta da auren Fadila shirinta ne, ashe ba Fadila kaɗai ba harda matarsa cikin tarkon nata wannan ne abinda take zata masa da har ya mutu ba zai taɓa mantawa ba kenan gashi kuwa tayi nasara domin har ta mutu ba zai taɓa goge wannan mugun ganin daga idanuwansa ba kamar yanda ya barwa Halima tunani mafi muni irin wannan akansa. Wai ta yaya ma har Halima ta iya sake kallonsa da idanun rahma? Lallai ta cika jaruma. Haƙƙin ta ne, yaga sakayya tun a duniya yana fatan kuma ya zama iyaka hukuncinsa ba zai tafi lahira da haƙƙin Halima ba.

"Ki faɗa mun gaskiya kada ki ɓoye mun komai hakan ne zai saka na yarda dake ko akasin haka, bayan shi sai kuma wa kike kulawa" ya faɗa da ƙyar dan wani abu yaji ya tsaya masa a wuya shi bai fita ba kuma bai koma ciki ba.

"Wlh tun bayan da mukayi aure babu abinda ya haɗani da wani Namiji shi kaɗai ne kawai kum dole ya mun" ta faɗa cikin tsananin kuka, ya girgiza kai ya ce
"Halinki ne ba dole yayi miki ba Zulaiha. Na daɗe ina zargin haka amma a koda yaushe zuciyata tana cikin yi miki uzuri kwatankwacin uzurin da Halima ta ringa yi mun akan laifukana. Ki tafi gida ba zan sakeki ba domin idan na rabu dake akan laifin da nima na aikata bansan wace kalar jarabar ubangiji zai ƙara ɗora mun ba. Ki tafi kawai har zuwa lokacin da zan nemeki amma ina so wannan maganar ta zama sirri a tsakaninmu bana fatan wani ya jita.

MURFI
A ba zata saƙon ɗaurin aurena da Salman ya iskeni domin ko da ya samar mun a safiyar Juma'ar iyayensa zasu zo tambayar masa aurena kamar yanda Abba ya buƙata a wasa na ɗauki al'amarin, a lokacin da Mu'azzam ya shigo yayi kirana kawai na amsawa Baba Salahu cewa na amince a ɗaura mun aurene badan na yarda da gaske hakan ce zata faru ba sai dai amincewar da nayi ta zamo hukuncin da bana nadamar yinsa, kuma idan ana sake aure sau dubu toh tabbatas Salman zan zaɓa.

Ya zame mun Mijin, Aboki, Yayan da duk wani matsayi da wani ɗan adam yake iya takawa a rayuwa. Rayuwar auren dana ringa mafarki wacce ta zamemun Fantasy a gidan Bilal comes to reality bayan dana auri Salman. Ya gatatani, ya riritani, yan uwansa sun ƙaunace ni tamkar jininsu, har bayan shekaru goma da aurenmu daya ƙaro mun abokiyar zama domin ni ba kishiya aka yi mun ba na cigaba da kasancewa lamba ɗaya a duniyar Salman.

Na gasgata zancen Mama Fauziyya da tace akwai sanda za'a wayi gari na manta da Bilal tabbas hakan ta kasance domin sai da takai a wasu lokutan na kan manta da cewar ba Salman ne uban yarana biyu na farko ba saboda kyakkyawar alaƙar daya gina tsakaninsu bai taɓa banbantasu da yaya ukun dana haifa masa bayan su ba. Na godewa Allah na kuma godewa dalilin da yayi silar barina rayuwar da bani da gurbi a cikinta.

ALHAMDULILLAH

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login