Showing 99001 words to 102000 words out of 257873 words

Chapter 34 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

494

ya zo ya na ƙwanƙwasawa wai na fito ga su Hajja sun zo, se da na kwashi kusan minti biyar kafin na fita falon kaina a ƙasa ba tare da na bari mun haɗa ido ba na samu gefe can na zauna na shiga gaishe su. Bata amsa ba ta fara zazzage mun asalin abin da ya kawo ta wato bin ba'asin wulaƙanta yayanta da yan uwanta da aka yi jiya.
"Har su zo miki taro a hana su abinci, ban da tsiya me akai aka yi abinci da har kuke rowar sa? Ko da yake dama shi taka hayen arziƙi in be nuna halin sa ba ta ya za'a gane shi? Duk wata fuffukar da kuke yi kallon ku kawai muke yi wlh har yaushe Aminun ya zama wata tsiya da har kuke ƙafafa, ai wanda bai san asalin ungulu ba ne za'a ce masa daga masar take ya yarda. Ke ba dan mutuwa me tonin asiri ba har Aminu za'a saka shi a jerin masu arziƙi ne balle ya haife ki kamar Bilal ya kalle ki ya aura ai ƙaryar ki" cewar Hajja.

Na rasa dalilin da ya saka a koda yaushe take ƙoƙarin cin mutunchin iyaye na. Idan ma laifi na mata me yasa ba zata zageni ni kaɗai ba dole se ta haɗo da iyaye na da basu mata komai ba ta zage su ta yi musu cin mutunchi? A karo na biyu Bilal na zaune akan idon sa da kunnuwan sa Hajja ta ke aibata ni da iyaye na Lanti da suka zo tare tana taya ta amma be iya ce musu komai ba.

Baba Jummai ta fito daga ɗaki, na tabbata kuma hayaniyar su Hajjan ce ta tashe ta daga bacci tayi mici mici da ido tana kallon ta ta ce
"Amma dai ko wacece ke baki da ɗa'a ba kuma ki da mutunchi. Ki shigo har ɗakin yarinya ki sakata a gaba kina zagin iyayen ta da basu ji ba basu gani ba"

"Ni a uwar Bilal" Hajja ta bata amsa, hakan be saka Baba Jumman ta tausasa lafazi ba sai ma Kara harzuƙa da ta yi ta ce
"Eh lallai ba shakka ashe rashin arziƙin na ku gado ne. Yanzu dai ban da bakya tsoron Allah har ke zaki cewa wani bai gaji arziƙi ba alhalin ga tsiya nan har ta yi kuka a jikin ku tana neman a kawo mata ɗauki. Ai wlh Halimatu ce da kaico domin ba tayi miji ba, banda ƙaddara ina ita ina ita ina haɗa hanya da kwaɗayayyu irin ku? Da zaki ce sun zo suna an hana su abinci gayyar su aka yi ko kuma shi mara zuciyar ɗan na ki ya bada ƙwayar shinkafa ya ce a dafa balle har ki tada jijiyar wuya saboda an hana su abinci? Se ka ce dai ana yunwa zaki taho ƙafa da ƙafa kiyi rashin arziƙi saboda an hana abinci ba'a bayar ba ki ɗauki matakin".

Nemar hawayen da na ke yi na yi na rasa, na zabura na miƙe tsaye tare da ɗora hannu biyu a kai ina juya wuya kamar wacce aka tsare da bindiga tsabar yanda jini na ya daskare na ma kasa furta komai balle na hana Baba Jummai cigaba da wannna ɓarin bakin da take kamar wacce aka kwancewa kai.

Hankali na ya sake dugunzuma jin Hajja ta fashe da kuka ta na kallon Bilal ta ce
"Kana ji Bilal? A gaban ka Halima take zagi na?" Mamaki da tsoro suka dirar mun lokaci ɗaya, wai Halima ta zage ta ni? Yaushe?
Bilal na kalla, fuskar sa ta yi jajir kamar an watsa masa barkono jijiyoyin goshin sa sun fito kamar an zana su, cikin murya kamar wanda aka shaƙewa wuya ya ce
"Jummai dai ta zage ki Hajja ba Halima ba" se ta ƙarawa kukan ta ƙaimi tana cewa
"Wlh Halima ce ta zage ni, kalaman bakin ta ne saboda ba zata iya faɗa ba ne ta karanta mata idan ba haka ba me ya haɗa ni da wannan matar? a ina ta sanni balle ta zage ni haka? Wlh duk Halima ce ta shirya mata tun da dama ai ta san dole zan zo gidan" ta ƙarasa tana sake rushewa da wani irin kuka irin wanda yake nuna zafin dake cikin zuciyar me yin sa.

"Ashe bayan tsiya har da sharri kuka iya" Baba Jummai ta sake faɗa se kawai na fashe da kukan da ya fi na Hajjan tashin hankali, murya ta bata ko fita na ce
"Dan girman Allah kiyi shiru, ki tafi babu ruwanki wa ma ya kira wo ki haka kawai yanzu kin ga abinda kika jawo mun"

"Haka kika kawo Amirah gidan nan ta zage ni yanzu kuma kin sake kawo wata ta zagi mahaifiya ta. Ni Bilal ban yi lalacewar da zan ɗauki haka ba Halima, idan ni kin zage ni na shanye baki isa ki zagi mahaifiya ta ba ko ki wulaƙanta dangi na na ɗaga miki ƙafa. Ki tafi gidan ku Halima ki tafi gidan ku.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 25*

Ina zaune a falon har Baba Jummai ta gama haɗa kayan ta tana kukan da nake ji kamar na tashi na shaƙe mata wuya idan ya so ta yi mai dalili. Ni da ta ke neman ta kashewa aure ai ni ce da kuka ba ita ba, akan na ce ta tafi tun da ita ta janyo ni ma aka ce na tafin shi ne ta fasa kuka wai na mata rashin kunya tana ƙoƙarin kare mun mutunchi na watsa mata ƙasa a ido. Ta shi na yi na goya Al'amin bayan da ta fito da jakar ta daga ɗaki ina kallon ta na ce

"Kuma wlh karki gayawa kowa abin da ya faru, kawai ki ce musu kin gaji da zama a nan ne kika koma gidan Mama".

"Allah ya shirya ki Halimatu Allah ya buɗe miki idanuwan ki tun kina da sauran lokaci kafin ki ƙarasa makancewa, kuma baki isa ki saka na yi ƙarya ba, tun da baki da zuciya har namiji ya ce ki bar masa gida ki share guri ki zaune zan je na faɗawa Hajiya Amina duk irin cin mutunchi da tijarar da ya ke miki ki ke zaune da shi, kuma zaki san idan zamana yana da amfani ko ba shi da shi, zaki gane baki da wayo yarinya ga ki ga Mijin nan ga kuma ɗanyan jego" Baba Jumman ta faɗa tana goge fuska.

Na zumɓuri baki ba tare da na sake ce mata komai na ta fice daga falon. Bin bayan ta na yi, se da ta fita ta bugu kofar get ɗin da ƙarfi kafin na taɓe baki na koma cikin falon a fili ina cewa

"Haka kawai mata babu dangin iya babu na Baba zaki zo ki kashe mun aure, ko meye haɗin ta da Abban da zata fi ni ɗaukar zafi saboda an zage shi? Ai dai ba Bilal ne ya zage shi ba. Hajja ce, faɗan iyaye ne za ta wani tsoma baki ta janyowa mutum masifa" na yi tsaki na kwance Al'amin ma kwantar da shi na fita falon. Sauran naman da su Hajja suka bari na ɗauke na kai kitchen, kashi uku Baba Jummai ta yi dama, nawa, na dangi na da kuma na Bilal da nasa dangin bayan Hajja ta gama fisajin rashin mutunchi da kanta ta shiga kitchen ta haɗe kashi biyu ta tafi da shi a roba ko murfi bata tsaya an bata ba.

Sai da na gama gyaran kitchen zuwa cikin falon kafin na koma ɗaki na kwanta kaina yana sara mun saboda kukan da na yi. Motsin taɓa ƙofa da na ji ya sa na miƙe zaune da sauri ina raba ido ƙirji na na bugawa kamar zuciya ta zata faso ta fito, ban san ya Bilal ze tarbi zaman da na yi ban tafi gidan mu kamar yanda ya ambata ba.

A yanda ya fusata ɗazun ta yuwu zama na ya sake fusata shi. Ta shi na yi da sauri na buɗe wardrobe ɗita na fara ciro kaya ina ajiyewa akan gado, ina jin an taɓa ƙofar ɗakina na saki kayan hannu na na haye kan gado da sauri na matsa can ƙarshe gado haɗi da cusa kai na tsakanin cinyoyi na da sauri dai dai sanda ya shigo ɗakin, saurare kawai nake ya rufe ni da duka ko makamancin haka musamman da na ji takun sa yana kusanto in da na ke, tsoro na ya nunku har jiki na ya ɗauki rawa. Ga mamaki na se ji na yi ya kira sunana kamar a rikice ya ce
"Kaya kike haɗawa Halims da gaske kenan zaki iya tafiya ki barni?"

Tsam na yi a gurin ba tare da na ɗago ba har sai da ya sake maimaita kiran suna na kafin na ɗago kai na rabi ina jam ɗankwali na rufe rabin fuska ta, so na ke yi na tabbatar da gaske ne maganar da yake yi ba wai yaudara ta ya ke so yayi na ɗago ya rufe ni da duka ba. Shammata ta ya yi ya rungume ni, lokaci ɗaya kuma ya fashe da kukan da sai da zuciya ta ta tsallake bugu. Sake tsananta rungumar da ya yi mun ya yi cikin kukan da ya ke yi ya ce

"Yanzu ashe zaki iya bari na Halima?"
"Kai fa ka ce na tafi, kai ka ce na bar maka gidan ka fa" na faɗa ina fashewa da kuka ni ma, sai ya ƙara ƙarfin rungumar da ya yi mun yana cewa
"Kiyi haƙuri ki ya fe mun Halima babu yanda zan yi ne amma har zuciya ta ba abinda nake nufi ba kenan kuma na ji daɗi da baki tafi ba ki ka jira har na dawo da ace ban tarar da ke a gidan nan ba da ban san ya zan yi ba" ya ƙarasa cikin kuka me tafe da shassheƙa.

Wani irin daɗi na ji ya mamaye ni, da na biyewa Baba Jummai shikenan da tuni ta saka ni a uku ni dama na san da wasa Bilal ya ke yi se dai ya faɗi haka dan ya farantawa Hajja ba wai har ransa ba.
Kukan shagwaɓa haɗi da kissa na koma yi ina ture shi daga jiki na na ce
"Amma ai da ta ke zagin iyaye na baka ce komai ba"

"Mahaifiya ta ce fa Halima ya kike so na yi? Kin dai san halin Hajja idan ranta ya ɓaci bata tauna magana tsaf za ta iya yi mun baki idan na saka mata baki a cikin maganar ta shi ya da na yi shiru amma ni ma ban ji daɗin abin da ta yi ba kwata kwata" ya faɗa yana sake riƙe ni a jikin sa, se na kwantar da kaina a ƙirjin sa na ci gaba da kuka ba tare da na sake cewa komai ba shi kuma yana ta aikin rarrashi na da faɗa mun kalamai masu daɗi irin waɗan da na ke da burin saurare daga bakin sa a koda yaushe.

Ɓoye fuska ta nayi a jikin sa ina ci gaba da gunjin kuka amma a zahiri zuciya ta fal farin ciki ji na ke yi kamar na tashi na taka rawa. Mun fi minti talatin yana rarrashi na kafin na bar kukan da na ke. Kiran sallar la'asar ya saka ya fita ya bar ni bayan da ya kwashe kayan da ma fito da su duka ya mayar, na ringa tsalle ina juyi a ɗakin bayan ya fita. Ba saban ba. Wai yau ni Halima Bilal ya ke yiwa kuka ya na bani haƙuri kamar a film ɗin India.

Ringing ɗin waya ta ne ya mayar da ni cikin hankali na, sai lokacin tunanin me Baba Jummai zata faɗa idan ta je gida ya zo kaina, ƙila ma har ta je ta kitsa ƙaryar ta, Allah kaɗai ya san me da me ta faɗa kuma. Ba Mama ke kira ba kamar yanda na yi tunani number ce babu suna dan haka na mayar na ajiye ba tare da na amsa ba. Al'amin da ya farka na ɗauka na shiga shayar da shi bayan ya ƙoshi ganin baccin bai ishe shi ba na goya shi na shiga kitchen dan na ga abinda zan sama mana mu ci da dare cikin raina kuma ina ta zullumin yanda har sannan shiru babu wanda ya kira ni daga gida. To ko gidan Mama Fauziyya Baba Jumman ta wuce kai tsaye? Amma kuma ko can ɗin ta je duk da Maman ba kamar Anty Labiba sarkin masifa ba ce na san zata iya kira ta ji ta baki na akan abinda Baba Jumman zata faɗa mata, sai dai idan kuma ba ta ce musu komai ba wanda na ke fatan hakan.

A can gida kuwa da kuka wurjanjan Baba Jummai t shiga bayan mai adaidaita sahu ya sauke ta. Amirah na alwala a bakin famfo tayi maza maza ta ƙarasa kafin ta nufi Baba Jumman tana tambayar ta me ya faru?
"Kada ki ga irin tijara da wulaƙancin da yar uwar ki ta mun saboda na tsaya mata a gaban sirikar ta da ta tasa ta gaba ta na zagin iyayen ku shi ne ta kore ni wai zan kashe mata aure" Baba Jumman ta faɗa tana sake rushewa da kuka. Bakin Amirah har kunne ta karɓi jakar Baba Jumman ta na cewa
"Mu je, kin kuwa ci sa'a Abba ya na nan" ta wuce falon Abba Baba Jummai ta bi ta. Tiryan tiryan tun daga zuwan ta gidan da abubuwan da ta gani da wanda ta ji har zuwa yau ɗin da rashin kunyar da Haliman ta yi mata duk babu wanda ta manta bata zayyanawa Abba da Mama da ke sauraron ta ba.

Amirah ta ce
"Alhamdulillah, sanda na faɗa ta ce ƙarya na ke yi yanzu ai ba ta gurin balle ta dake ƙarya ta wa. Ai wlh dama ni na san tun da aka yi na farko ya ga an masa shiru..."

"Baki da hankali ko Amirah? Wa ya kira ki gurin nan ma da farko balle har ki buɗe baki waaa kina magana se kace kin ga sa'an ki a nan? Wu ce kafin na kwaɗa miki mari a gurin" Mama ta katse ta cikin tsawa, baki ta tura ta tashi tana waigen su. Ita da ta so ta sake ƙarawa abun gishiri ta yanda Abba ze fusata kawai ya kashe wannan ƙaddararren auren na Halima kowa ma ya huta amma Mama ta kora ta waje.

Bayan fitar Amirah Abba ya dubi Baba Jummai da ke aikin goge hawaye ya ce
"Kiyi haƙuri Hajiya Halima ba ta kyauta ba kuma se na saɓa mata akan hakan ki je cikin gida nagode". Kallon Mama ta yi Maman ta gyaɗa mata kai alamar ta yi abin da Abban ya ce dan haka ta miƙe ta fita. Ta ɗauka a yanda ta zayyana musu abin da yake faruwa da Haliman za su birkice ne take su kira waya su ce ta taho ko kuma ma takanas a tashi wani ya je ya taho da ita amma saɓanin haka sai ta ga kowannen su kamar ma basu kama abubuwan da ta faɗa ba ko dai ma sun ɗauka ƙarya kawai ta shirga musu ne shi yasa Abban ya ce ta tafi cikin gida.

Haushin kan ta ne ya kamata, ita da ta san da Haliman da iyayenna ta duk jirgi ɗaya ya kwaso su ba wani damuwa suka yi dan an ci zarafin su ba ina zata haƙiƙan ce ta tare musu faɗa? Bata shiga cikin gidan ba kamar yanda ya ce mata ta ɗauki Jakarta da Amirah ta aje mata a tsakar gida ta yi tafiyar ta, gara ta je ta faɗawa uwar ɗakin ta ta yuwu ita ta fisu kan gado ta kuma fi su hangen matsalar da Haliman ta ke ciki tunda taga su abun be wani shalle su ba.

Bayan fitar Baba Jumman Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Gaskiya na gaji da lamarin auren nan na Halima, zan ɗauki komai amma ban da wulaƙanci da kuma tozartawa. Idan wancan karon Amirah ce ta faɗa ta ƙaryata ta yanzu ai Baba Jummai ba zata mata ƙarya ba to gaskiya ba za'a yi na uku da ni ba babu dole a ciki, su da suke da abun zagi ba'a zage su ba banga dalilin da mu zasu ringa zagin mu ba" ta ƙarasa tana huci. Murmushi Abba da ke kallon ta ya yi ya ce

"Yanzu me kike so a yi Amina?"
"Gida zata taho tun da ba daina son ta muka yi ba da zamu bar musu ita suna gallaza mata, shi ya mata yan uwan sa su mata uwar sa ta yi abun ya yi yawa ai ba zan ɗauka ba" ta bashi amsa a fusa ce tana laluben lambar Halima a wayar ta. Gyara zama Abban ya yi ya ce

"Amma yanzu da kunnen ki kika ji ta ce shi Bilal ɗin ya ce ta taho gida, kin ha ta taho ɗin? Hakan ya nuna miki tana son zama da Mijin ta a kowanne yana yi. Ni ba goyon bayan Halima nake yi ba ban kuma ƙarya ta abin da Amirah ko Jummai suka faɗa ba amma ki sani ba zan taɓa yankewa Halima hukunci akan abin da ya shafi rayuwar ta da shaidar wasu ba. Ita take zaman aure, da daɗi babu ta zaɓi haka ba kuma ta taɓa zuwa ta ce ya mata wani abu ba dan haka na sakawa raina tana zaune lafiya da Mijin ta.
Son da take masa ya saka na amince na aura masa ita kuma duk ranar da ta nuna bata da ra'ayin ci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login