Showing 84001 words to 87000 words out of 257873 words
ni gida amma basu saurare ni ba, ƙarshe ma fasa jiran zuwan Mu'azzam ɗin suka yi da zasu tafi Mama Fauziyya ta ce mai aikin ta Baba Jummai zata dawo gobe zuwa jibi idan yaso se tazo ta ringa mana wanka Zainab kuma ta taya ni raino da gyaran gida tun da yanzu Yayar Bilal tana nan base ita ɗin ta rin ga zuwa ta mana kamar yanda ta yi niyya a farko ba.
Bayan sun fito Hajja ta tsayar dasu kamar gaske tana cewa
"Har kun fito kenan?" Mama Fauziyya ce ta amsa mata da
"Eh, mun fito".
"Allah sarki, abu dai duk yazo ba yanda aka tsammace shi ba. Banda ma dai Allah ya taƙaita ƙila da wata maganar ake yi yanzu ba wannan ba, daga zangar fa wai ya fita yabi sahun Halima shiru shiru tun da tace zata je gida da rana har gurin sha ɗaya bata dawo ba shi kuma wayar sa wai ta mutu taƙi ɗaukar caji kwata-kwata. Ni nayi mamaki ace a unguwa kamar wannan me cike da tsaro har a iya buge mutum a masa ƙwace; su kuma wanda suka tsince shi da rashin azanci maimaikon ko a masallaci ne su bayar da sanarwa se kawai suka kai shi asibiti suka yasar wai ashe suma ba yan unguwa bane hanya ce kawai ta biyo da su, mun dai shiga tashin hankali matuƙa amma dai mun godewa Allah tun da ya bayya na babu dai mashin babu waya, kuɗin akawut ɗin sa ma se jiya daya tura Habubakar ya ciro aka ce an kwashe komai; waɗannan azzaluman mutane dai se dai kawai mu bar su da Allah" ta ƙarasa tana share hawaye.
"Toh fa subhanallahi ashe abin da ya faru kenan" Mama Fauziyya ta faɗa cikin jimami, Hajja tace
"Wlh Hajiya. Abun dai ba daɗi, duk hankulan mu sun tashi ace mutum magidanci an neme shi a rasa har kwana biyu abun akwai ruɗani".
"Ikon Allah, amma Bilal ɗin ya ɓata har kwana biyu amma ba'a sanarwa da matar sa ba?" Anty Mimi ta faɗa, se Hajja tace
"To ai mu ma bamu san abin da ya faru ba se jiya da safe. Tun dai da ya baro can gidan waccen ranar bamu sake ji daga gare shi ba na san kuma lafiyar Allah Bilalu baze kwashe kwana biyu bai je mana ba, idan kuma tafiya ce ta kamashi dole ze sanar mun kuma ze kira a waya mu gaisa amma dai bamu ɗauki abun da girma ba tun da ba wani labari muka samu mara daɗi ba.
Abokin ƙanin sa ne fa can ya gano shi a Asibiti, banda shaƙiyancin kuma irin na yan zamani maimakon kai tsaye ya faɗa masa ga Bilal a asibiti kawai se yace masa wai ina yayan su? Ya kamata ya bincika shi yaji ko yana lafiya. To tun da dama muna ta jimamin kwana biyu mun ji shi shiru shine fa yana faɗa mun hankali na ya tashi muka taho nan gidan babu kowa se makwafcin sa yace mana ai yau kwana biyu kenan ba kowa a gidan. A lokacin har Habubakar ɗin yace a kira Halima muji ko tana da masaniyar in da yake ni kuma nasan in har ita wani abu ya same ta ba zamu kasa ji daga gare ku ba dan haka na ce masa aa kar a tayar mata da hankali ga tsohon ciki mu tafi gurin yan sanda kawai a kamo shi abokin nasa daya fara kawo zancen a tuntuɓi Bilal aji ko yana lafiya. Shine fa da aka kamo shi ya ce ya ganshi a Asibitin Murtala se likita ne ya mana bayanin yanda aka kawo shi babu waya kuma baya magana shi yasa suka rasa ta yanda zasu nemi yan uwan sa dama jiyan suke niyyar kai cigiya gidan radio".
"Toh Allah ya rufa asiri ya kiyaye faruwar na gaba bari muje mu har an fara kiran sallah" Anty Labiba data gaji da sauraron ta ta faɗa tana yin gaba se Hajja tayi saurin tare su da cewa
"Nace mai zai hana ku tafi da Halima gida Hajiya? Tun da kunga shi mijin nata ba lafiya ga ɗanyan jiki kada ɗawainiyar tayi mata yawa dan shi ɗin ma can gida na zamu wuce dashi yanzu".
"Babu damuwa ai Hajiya ku tafi da shi ɗin Allah ya bashi lafiya ita ɗin se tayi zaman ta za'a kawo mata waɗan da zasu taya ta zama" Mama Fauziyya ta faɗa. Se Hajja tayi shiru kafin kuma ta tace
"Amma dai haihuwar fari a al'ada ai gida ake tafiya ayi wanka balle ita wannan da ga halin da ake ciki"
"Wace al'ada mu ai tuni muka yada zancen zuwa wanka gida, gara dai yarinya ta zauna a ɗakin ta. Dama saka ruwa ne wahalar jegon ai kuma za'a kawo wacce zata ringa yi mata ina ganin ai babu wata damuwa" Mama Fauziyyar ta sake bata amsa dan tuni Anty Labiba ta fice Anty Mimi kuma ta zama hoto kallon Hajjan kawai takeyi.
"Ai shikenan tun da haka kuka zaɓa se ta zauna, amma kowa na ɗauke ɗan sa ya kula dashi ki zaku bar taku bakwa ko tsoron ya lallaɓa da ɗanyan jego ya haike mata duk matsalar data sameta ai ku ne da kuka na wani ba" Hajja ta faɗa cikin fushi fushi.
"Ba abinda ze same ta se alkhairi Hajiya idan ma kuma ya haike mata ai ba haramun bane matar sa ce, Halima dai ba in da zata je a gidan ta zata yi jego" Mama Fauziyyar ta bata amsa itama cikin fushi daga nan suka yi tafiyar su.
Komawa nayi na zauna kan gado na tallafe fuskata naci gaba da share hawaye ina jiyo Hajja na masifa da faɗar maganganu bayan data tabbatar sun fice daga gidan. Ban san ya akayi ba kuma da Hajja ta tashi tafiya basu tafi da Bilal ɗin ba kamar yanda tace. Na zata ita ma Anty Aminar ta tafi se bayan tafiyar su Hajjan kuma naga ta dawo tace mun gida taje ta dawo, har da cefanen kayan miya tayo da nama da kaji guda biyu a daren ta dafa mun ɗaya tace na zauna na ci, se da na ƙoshi kafin ta sakawa Bilal sauran yaci.
Da Bilal ya shiga ɗaki ze kwanta ta ce na tashi na je ko akwai abin da ze buƙata na taimaka masa tunda har sannan jikin sa be gama yin karfi ba. Yana zaune akan carpet ya ɗora kansa jikin gado na shiga, cikin sanyin da muryar sa tayi ya miƙa mun hannu yana cewa
"Zo Halima". Na isa kusa dashi na zauna ya kwantar da kaina a kafaɗar sa yana cewa
"Ki yafe mun Halima" ban san yafiyar me yake nema ba amma kawai naji hawaye sun ɓalle mun. Ya rungumeni yana cewa
"Nasan haƙƙin ku ne ya kama ni amma na godewa Allah da ban mutu ba tareda na nemi yafiyar ku ba, je ki karɓo mun ɗana na ganshi" ya faɗa yana saki na. Se da na share hawayen kafin na fita na karɓo shi, ya haɗa ya rungume mu ni da yaron yana cewa
"Kiyi haƙuri da abin da nayi miki ke da Amirah waccen ranar wlh sharrin shaiɗan ne ban ma san meya hau kaina har na aikata abin da nayi ba".
"Amma Bilal na haihu ka kasa zuwa, Abba na ya kira ka nima na kira ka kuma na san ko ba'a faɗa maka ba ba zaka kasa jin labari a unguwa ba" na faɗa cikin shassheƙa. Ya sake rungume ni yace
"Na ga kiran Abba Halima; nayi zaton ƙarata kika kai akan abin da na yi wa Amirah shi ya sa na kasa ɗagawa. San da naga saƙon sa na kin haihu a lokacin dare yayi sosai, na so na bari se da safe na zo amma na kasa jurewa. Tunanin halin da kike ciki da kuma taraddadin kin haihu ko akasin haka yasa na kasa jurewa. Ban san me ya faru ba, nayan na fito daga gida wasu suka tare ni daga nan ban sake gane kai na ba kawai na tashi na ganni a asibiti kuma duk ƙoƙarin da na yi akan nayi magana na kasa. Se daga baya na samu labarin wasu ne suka tsince ni suka kaini asibitin" yayi maganar ba tare da ya bari mun haɗa ido ba.
Wani irin tausayin sa ne ya lulluɓe ni, ni dama na san Bilal baze wofantar dani haka kawai ba, ashe abin da ya same shi kenan. Kuka sosai na fashe dashi da wani tunani ya ɗarsu a raina. Yanzu da ace kuma Bilal ya rasa ransa ne fa ina zan sa kaina a duniyar nan naji sanyi?
Rungume ni yayi ina jin ɗumin hawayen sa a dokin wuya na ya ce
"Ki yafe mun Halima, ba da gayya bane".
Mun shafe kusan minti goma muna koke koken har se da yaron ya gaji da matsar da aka masa ya fara kuka kafin ya sake ni na karɓe shi daga hannun sa na shiga jijjiga shi yaƙi shiru dole se da na shiga shayar dashi kafin yayi shirun alamar har da yunwa ta dame shi. Se bayan da ya ƙoshi ya sake karɓar sa yana kallo na yace
"Da ni yake kama, hancin sa ne kawai irin na ki".
Shafa hanci na nayi ina murmushi na ce
"Irin na ka dai, ai ban kai ka hanci ba"
"Amma na so ace dake yayi kama se ya fi kyau" ya faɗa yana kwantar da yaron a jikin sa. Na buɗe ido ina dariya na ce "Haba dai, ka fito fili kawai kace da baze ganu ba"
"Allah da gaske na keyi ke kyakkyawa ce Halima. Kina da kyau me sanyi irin wanda a duk kallo yake ƙara ƙawata idanuwan me kallon ki; babbar ni'imar da ubangiji ya yi miki ita ce kyakkyawar zuciya, kin ga ko kwatantan kyawun ki da nawa ma ai ɓata baki ne kawai. Ina addu'ar yanda yaron nan yayi kama ta zahiri da ni, ya yi kama dake ta baɗini" Bilal ya faɗa yana kafe ni da ido. Murmushi na ringa yi kamar wawuya. Ina kallon sa ya ɗago yaron bayan ya tashi zaune sosai ya shiga yi masa kiran sallah a kunnen sa. Se da ya kammala kafin ya kalle ni ya ce
"Wane suna kike so a saka masa?"
Nayi ƙasa da kaina ina murmushi, idan son rai na ne bani da zaɓin daya wuce sunan Abba na, amma na san ƙila a ransa ze zo ya mayar da sunan mahaifin sa ne tun da ya rasu. Hakan ya sa na ce masa
"Duk sunan da yayi maka shi ne zaɓi na". Murmushi me kyau yayi mun kafin ya kammala masa huɗubar kafin ya miƙo mun shi yana cewa
"Allah ya raya Muhammad Al'amin"
"Abba na?" Na faɗa cikin tsananin murna. Ya ɗaga mun kai ya ce
"Na daɗe da sanin burin ki na sakawa yaron ki na fari sunan Abba, ko kin manta kin sha faɗa mun kafin mu yi aure?"
Rungume shi na yi ina cewa
"Na gode Bilal, na gode ƙwarai da wannan karar da kayi mun"
"Ni ne da godiya Halima kin yi mun abubuwa da dama a rayuwa da bazan iya biyan ki ba. Naji daɗi da kika yi farin ciki, Allah ya raya mana shi ya sa ya gaji takwaran sa"
Da "Amin" na amsa ina sake rungume Abba na a jiki na. Badan dare yayi ba da yanzu zan kira Abba na gaya masa ya samu takwara amma Allah ya kaimu safiya.
A ɗakin muka kwana rungume da juna cikin farin cikin da muka kwana biyu bamu samu kamar sa ba. Hatta Abba na be yi koke koken da yake mana kwanaki ukun zuwan sa duniya ba da safe har Anty Amina se da ta ringa masa tsiya wai ya ji ɗumin Dady yayi lif kamar babu jinjiri a gidan.
*******
A hanyar komawa gida Mama Fauziyya ta kalli Anty Labiba ta ce
"Allah sarki Bilal, ashe abin da ya same shi kenan duk mun ɗauki alhakin sa mun zata wulaƙanta yarinyar nan kawai ya so yi". Anty Mimi ta ce
"Wlh fa Anty, ni ma duk se jiki na yayi sanyi tun da muka shiga, ana kallon sa zaka gane yaji jiki wlh. Kamar fa harda ɗinki na gani a gefen kan sa, gaskiya ya daku sosai da alama".
"Amma dai kun bani mamaki wlh, ku yanzu har kun kama ƙaryar waɗancan mutanen kenan?" Anty Labiba ta faɗa se Mama Fauziyya ta ce
"Aa Labiba, wannan fa ba zancen ƙarya bane. Idan sun yi ƙarya akan ainihin abin da ya same shi wannan daban amma a zahiri dai duk wanda ya kalle shi yasan wani abu na rashin daɗi ya faru dashi, gaskiyar me ya faru kuma wannan se Allah. Kuma dama karki kuskura ki ce zaki sake zuga Yaya akan maganar Halima, dan Allah ki bari yarinyar nan ta dawo gida dan ganin idon ki dai gashi abinci ma babu a gidan yini guda jegon kwana uku amma ace sun kasa samar mata abin da zata ci da jikin ta yake buƙata ina ga an sake kwana biyu? Gara ta taho tayi arba'in se ta koma".
Shiru Anty Labiba tayi bata ce komai ba, ita ta san halin Bilal ko da yanayin sa ya nuna da gaske bashi da lafiya amma a yanda ta sanshi ba wani abun mamaki bane ace shirya wa yayi. Duk se da ta sauke su a gida tunda a motar ta suka fita kafin ta wuce nata gidan, a hanya ta kira Mama taji ko Zainab ɗin ta tafi Maman tace mata aa, Haliman tace mata Yayar Bilal da mahaifiyar sa suna gidan shi yasa ta dakata da tura Zainab ɗin kar kuma suyi yawa. Idan sun tafi se taje in ma kuma su zasu zauna mata shikenan daga nan sukayi sallama akan se washe gari zata je gidan su ƙarasa magana akan yanda za'ayi da kayan barka.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 22*
"Dagaske ne Anty, masu ƙwacen mashin ne suka bige shi; waɗan da suka kai shi asibitin ma na san ɗaya daga cikin su tare muka fara Maitama Sule" Mu'azzam ya faɗa jin Anty Labiba ta dage akan ƙarya kawai Bilal ya shirga ba wani abu daya same shi. Zuwan ta kenan ta tarar suna jimamin abun, Na kira Abba na gaya masa an masa takwara sannan na ƙara da faɗa masa dalilin da ya saka Bilal be duba mu ba har na bawa Bilal ɗin waya suka gaisa da Abban ya sake bashi haƙuri. Bayan mun gama wayar ne ya fito yake gaya wa Mama yan da mu ka yi se ga Anty Labiban.
"Ƙarya ya ke yi, saboda maganar ma bata kama kunne na ba shi yasa tun jiyan ban faɗa miki ba, na ɗauka ma su Yaya Fauziyya zasu gaya miki tun da naga se jiman ta abun suke yi. Haɗin baki ne kawai shi da yan uwan sa saboda su goge laifin wofantar da Halima da suka yi" ta faɗa sanda Mama ta maimaita mata abin da Abban ya gaya mata.
"Yanzu kai ka san haka ta faru da shi amma shi ne ka yi shiru baka faɗawa kowa ba?" Abba ya faɗa yana kallon sa, se ya yi ƙasa da kai ya ce
"Ni ma ai se daga baya na sani Abba. Lokacin da muka mayar da ita gida bayan na dawo aboki na Najib ya kira ni yake gaya mun masu ƙwacen mashin sun bige mai gidan da yaga mota ta a gurin kuma su suka kai shi asibiti ma".
"Ikon Allah, toh Allah ya rufa asiri. Amma wasu irin mutane ne su da irin haka zata faru ba zasu sanar mana ba tun da ai yanzu mun zama abu guda?" Abban ya sake faɗa. Anty Labiba da ta zabga wa Mu'azzam harara ta ce
"In ma da gaske ne ba komai ya ja masa ba illah haƙƙin iyalin sa da baya saukewa kaga an wasu can a banza sun ƙwata ta ƙarfi ai, Allah ya ƙara"
"Haba Labiba ya kuma da irin wannan maganar? Idan da abun ya zo da tsautsayi fa suka hallaka shi ko suka masa wata illar da za'a gwammaci ma mutuwa ya yi fa? Wannan al'amari na masu ƙwacen waya da mashin dai ya fara yawa se dai fatan Allah ya shirye su kawai" Mama ta faɗa cikin jimami.
"Bari na gani idan na fita se mu biya mu duba shi" Abba ya faɗa yana miƙewa, kafin ya zaro kuɗi a aljihun sa ya miƙawa Anty Labiba yana cewa
"Gashi se ku ƙara kayan, kin san yanzu lissafi ya canza aboki ne kuma takwara. Ke ma ya kama ta ki ware akwatin ki daban; idan kuma kin barwa su Fauziyya auren shikenan" ya ƙarasa cikin sigar raha. Ta karɓi kuɗin ta na ɗan murmushi Mama kuma ta taka masa zuwa gurin mota.
"Dama ai son zuciya da kwaɗayin abin da Abban ze masa ne ya saka ya yi masa takwarar ba wai saboda cancanta ya yi ba. Bilal kuma, ai se dai ya cuci wanda be san shi ba wlh amma ni nan kar na ke kallon su" Cewar Anty Labiba bayan Mama ta dawo falon. Mu'azzam yayi dariya ya ce
"Wlh kin gano shi Anty. Tsabar son zuciya ne kawai. Ban da haka ina nasa uban ya mutu? Ba se ya yi masa takwarar ba ko mun ce masa muna so ne?"
"Ai dai zan ga abin da Bilal ze yi ya muku gwanin ta kai da Labiba, ka tashi kaje gidan Hajiya Larai ka amso mun saƙon da ka ce se yau zaka je, ke kuma muje ciki ki duba kayan se muga abin da ya kamata a ƙara. Yau na cewa yan gidan