Showing 54001 words to 57000 words out of 257873 words

Chapter 19 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

491

da kallon da na kasa mantawa kafin ya ja tsaki kamar ze ture ni ya fice, daga in da nake na jiyo yanda ya buga ƙofar get. A nan gurin na sulale na zura kaina cikin cinyoyi na se dai hawaye ko ɗis be zubo mun ba zuciyata ce kaɗai take suya wani abu me ɗaci da maƙaƙi na yawo cikin maƙoshi na. Nafi minti ashirin a zaune a gurin kamar ma ba a duniyar nake ba, kalaman Bilal na mun amsa kuwwa tamkar a lokacin yake faɗa mun su. Jin ana kiran wayata a karo na uku yasa na yunƙura daƙyar na tashi, Mama ce take kira na, na san har idan na amsa tilas zata fahimci halin da nake ciki hakan yasa na mayar da wayar na ajiye na kwanta akan kujera.

A nan na wuni sur sallah kaɗai ke tayar dani gaba ɗaya ji nayi duniyar tayi mun duhu komai ya haɗe mun na kuma rasa ta ina zan fara gyarota, wa zan kira na faɗa masa matsala ta? Ban san me yasa sam naji na kasa kiran Anty Labiba ba dukda ita ta fara zuwar mun se kuma Hansa'u amma duk su biyu dana tuna basa son Bilal se naji be kamata na kai kuka na kan abin da ya shafe su gurin sa ba daga ƙarshe na yanke shawarar na shanye ɓacin raina ni kaɗai tun da dama cikin nasihohin da aka mun an jaddada mun muhimmancin riƙe sirrin gidan aure na.

Rashin cin abinci da ɓacin ran da nake ciki suka haifar mun da ciwon kai da ciwon ciki me tsanani. Shida saura Bilal ya dawo, sama sama nake jiyo muryar sa da alama waya yakeyi yana ta raha amma dana ɗaga kai bayan daya turo ƙofa ya shigo gani nayi ya haɗe rai tamkar be taɓa dariya a rayuwar sa ba. Tsayuwa yayi a kaina yana kallo na, nayi kamar bacci nakeyi ina jin sa ya saki tsaki kafin ya wuce yana ƙunƙuni se na bishi da kallo hawaye na gangarowa ta gefen ido na, kitchen ya shige, daga can naji ya fara kiran suna na ban amsa ba se gyara kwanciya da nayi na bada baya ina goge hawayen da suka ɓalle mun.

"Wato baki ma ɗora mun abin shan ruwa ba ko? Na lura nema na kike yi da fiti na Halima. Iya asarar da kika mun bata ishe ki ha yanzu kuma hora ni kike so kiyi da yunwa ko? shikenan kiyi yanda kika so" ya faɗa ni dai ban juyo ba ya wuce ɗaki be ɗauki lokaci ba ya fito ya sake shiga kitchen ina jin sa yana haɗa tukwane yana gwarawa ƙarar tana shigar mun har tsakiyar kai. Ina kwance a gurin aka kira sallah na yunƙura na tashi da ƙyar ina dafe da kaina ga ciki na daya fara yamutsawa dalilin ƙamshin suyar ƙwai daya fara tasowa daga kitchen ɗin.

A hankali na kalli Bilal ya fito daga kitchen da plate me ɗauke da ƙwai da cup ɗin shayi. Kan center table ya ajiye su ya wuce cikin ɗaki, ganin ƙwan da ƙamshin daya sake kusanto ni ya hautsina mun zuciya. Da ƙarfin da ban san in da na same shi ba na miƙe muka ci karo a bakin ƙofa yana shirin fitowa ni kuma zan shiga ganin yanda na tafi zan kifa ya ruƙoni kafin na ƙwace aman da nake dannewa ya fi ƙarfi na na shiga kwarara masa a jiki. Irin kallon da yake mun kaɗai naji gara ya rufe ni da masifa ko ya doke ni yafi wannan kallon. A ƙasa na kwanta ina juyi cikin aman saboda wani irin yanayi da nake ji da bazan iya fasaltawa ba. Bansan ko imani ne ya shige shi tausayi na ya kama shi ba ya tsugunna dukda kallon da yake mun wanda daga baya na fahimci na ƙyamar ƙazantar aman da nayi ne be bar fuskar sa ba ya shiga kiran sunana yana tambayata menene. Da hannu na nuna masa kaina da ciki na, tashi yayi ya cire rigar jikin sa ya ajiye a gurin sannan ya ɗauke ni, se da ya ɗauraye mun jiki da ruwan ɗumin da nake jin kamar ruwan dalma yake watsamun take zazzaɓi ya rufe ni.

Yana tsaki kamar ze katse harshen sa ya gyara gurin aman tsaf ya goge ya fesa room freshener sannan ya ɗauraye kayan sa da nawa da suka ɓaci kafin ya gama bacci ya kwashe ni ban zan ya ya ƙare ba se cikin dare na farka yunwa na neman yin ajali na. A kan center table na samu sauran jallop ɗin shinkafa daya ci ya rage na cinye na haɗa da sauran wacce na gani a tukunya sannan na fara gane kaina. Ƙarfe uku da kwata lokacin, a falo nayi sallar magriba da isha'i da banyi ba ina lazumi Bilal ya fito daga ɗaya ɗakin. Kallo ɗaya ya mun ya wuce kitchen, zuciya ta ta shigan bugawa ina jira na ji ya fara masifar abincin da naci amma naji shiru se gashi ya fito da cup da ruwan zafi ya haɗa tea a kan dining ya zauna yasha da ƙaton bread ɗin sa bayan ya gama ya koma ɗaki ya canzo kayan jikin sa ba tare da yayi mun magana ba ya tayar da sallah nan kusa da in da nake.

Ina zaune gurin ya dawo daga sallar asuba, kan kujera ya kwanta ya harɗe hannunsa biyu bayan kansa yana kallon sama, na shafa addu'a na gyara zama ina kallon sa kamar me tsoro na shiga gaishe shi. Nayi mamakin yanda ya amsa ba yabo ba fallasa har ya tambaye ni jiki na na sanar masa babu abunda yake damu na a lokacin.
"Naga dankali da doya da wasu kaya a ɗakin can" ya faɗa bayan daya tashi zaune, kaina na ƙasa na ce
"Eh, Abba ne ya aiko da su shekaran jiya"
"Shine baki faɗa mun ba?" Ya faɗa cikin sautin daya fi na farko taushi. Se na ɗaga kai na kalle shi maganganun daya yaɓa mun jiya suka shiga dawo mun take ido na ya ciko da hawaye na sadda kaina ƙasa ba tare da nace komai ba.

"Zan kwanta, idan ƙarfe bakwai tayi ban farka ba ki tashe ni" ya faɗa yana komawa cikin kujerar ya kwanta. Hakan da yayi ya nuna mun ya huce daga fushin jiyan, amma ni kuma cin mutunchin da ya mun fa? Shikenan a ganin sa komai ya wuce?

"Amma Bilal abinda ka mun jiya kana ganin ka kyauta?" Na faɗa murya ta na karyewa. Se ya tashi zaune yana kallo na yace
"Kin sani bana son dawo da abinda ya wuce karki ɓata mun rai Halima" daga haka ya miƙe ya shige ɗaki ya barni a zaune na rakashi da ido. Duk yanda naso na ƙarfafi kaina na nunawa Bilal jin zafin abin da ya mun na kasa, ganin ya sakko kawai se na lallashi zuciyata nima na haƙura. A haka azumi ya fara ja har an kai na goma. Daƙyar nayi guda huɗu saboda yanda lafiya tayi mun ƙaranci. Ciwon mara da ciwon kai suke damuna ga amai ba dama na shaƙi ƙamshin abinci ko banyi aman ba nayi ta kakari kenan. Munje chemist da Bilal suka rubutamun magungunan malaria harda allura ta kwana uku an mun amma banji sauƙi ba. Ganin lokacin al'ada ta ya wuce yasa na fara zargin ko ciki ne dani.

Ranar da aka kai azumi na goma tun yamma dama yace mun idan an sha ruwa zamu je gidan su mu gaishe su haka yasa dana tashi yin abin shan ruwa nayi da ɗan yawa zan ɗibar wa Hajjansu. A raina na raya se yayi magana dan kullum ne se yayi mitar ina dafa abinci yana yin yawa da zarar yaga kwanuka ze fara buɗe buɗe yana mitar duk cikin mu zamu cinye wannan a hakan ma ba wani abin kirki nakeyi ba saboda bana jin daɗi baya wuce abu biyu me dan sauƙin saraffawa na buɗa baki se kuma abinci da za'a sake ci da kuma lokacin sahur amma haka ze yi ta surutun nayi da yawa kuma a hakan ze cinye tas har ya ringa cewa beyi sahur me kyau ba. Dama ƙiri ƙiri ya hanani yin kunu da ƙosai na sadakar da nayi niyya wai da me zanji?

A kwando na jera kwanukan abincin dana zuba, ina jin kamar zazzaɓi ze rufe ni amma na daure, a sabon mashin ɗin daya buɗe shekaran jiya muka fita. Tun lokacin biki yace mun ya siyar da mashin ɗin sa se yanzu ya sake siyan wani. Muna tafe muna hira gwanin sha'awa har muka isa gidan a raina nayi gulmar yanda bece komai ba daya ga basket ɗin abincin,
kamar Hajiyar su zata goya ni haka ta ringa nan nan da ni. Taji daɗin abincin dana kai mata, ina zaune ta soya mun ƙosai tace tasan da yawan mutane sun fi son ƙosai da an sauke daga mai shiyasa da yace zamu zo ta ajiye ƙullin. Sosai kuwa naci ƙosan da kunun tsakiya a nan take gaya mun ai geron da waken ma daga gidan mu aka kawo musu harda buhun shinkafa dana sugar da pastar mangyaɗa. Se gurin goma saura muka bar gidan, a hanya naga gurin gasa tsire tun daga nesa naji raina ya biya dan haka nace masa dan Allah ya tsaya ya mu siya ba musu kuwa ya tsaya ya siya muka wuce gida.

A haka aka ƙara azumi biyar, tun washe garin da muka je gidan su nake jira naji yace na shirya muje gaida nawa iyayen amma shiru. Har Mama se da ta gaji ta mun magana akan yaushe zamu zo? Na ce mata bani da lafiya ne amma zamu zo, Allah sarki uwa washe garin da mukayi maganar kuwa se ga Imam da Amira da Nabila yar ƙanwar Abbanmu Anty Surayya da tazo hutu gidan Mama tace su zo su dubani. Ran da aka kai azumi na sha biyar ɗin tun asuba na masa zancen se yaushe zamu je gidan mu ne?

"Akwai abin da nake jira ne kin ga ai ba daɗi muje musu hannu haka babu wata tsaraba" amsar daya bani kenan. Se nace masa
"Yanzu ita Hajja ba haka muka je muka gaishe ta ba bamu kai mata komai ba suma gaisuwa ce ai ba wani abu aka ce dole se an kawo ba". Kamar baze yarda ba har na fitar da rai kuma bayan la'asar ina ƙoƙarin ɗora abin shan ruwa yace na shirya kawai ya kaini gidan. Sosai naji daɗi, da muka je be shiga ba ya ce mun se ya dawo ɗauka ta tukunna yanzu sauri yake ana jiran sa a wani guri. Mama na kitchen da Nabila suna aiki ta ringa kallo na da mamaki na rungumeta cikin jin daɗin ganin ta dan rabo na da gidan tun zuwan da nayi akan registration ɗin NYSC. Abba kansa se da ya tsokane ni yace dama gobe suke shirin zuwa ban haƙuri ace azumi har ya raba basu ga ido na ba gara suzo suji wane laifi sukayi haka.

Ina rufe fuska nace
"Ai kullum ina kiran ku a waya Abba"
"Haka ne, amma muga juna ɗin ma ai da daɗi ko Halimatu? Ko da yake ke fa tunda kika samu Bilal shikenan kika manta da kowa" Abban ya sake tsokanota se kawai na tashi na koma ɗaki dan duk se naji ban kyauta ba na kuma ƙudire a raina zan gyara hakan ba zata sake faruwa ba. Cikin farin ciki nasha ruwa da yan uwana, can ƙasan raina ina tunanin ko Bilal ya ci abinci? Ko dame ya karya azumin sa oho? Ana idar da sallar asham Mu'azzam yace mun
"Ga matsolon mijinki can a waje". Na galla masa harara kawai ba tare da nace komai ba. Tare suka shigo da Abba, a can falon ya zauna bayan sun gaisa da Mama na shiga kitchen na haɗa masa abinci na bawa Amirah ta kai masa, se da ya gama kafin mukayi sallama muka tafi kunya duk ta dabaibayeni jin Mama ta fahimci ina da ciki har tana tambayata wata nawa ne nace mata ban sani ba tun da bamu je asibiti ba pt test kawai nayi naga positive dan ko Bilal ma ban gayawa ba.

"Ya dai kamata kije gidan Labiba tunda kalar naki hankalin be nuna miki ba har yanzu" Mama ta faɗa sanda ta rako ni bakin ƙofa. Tunda nayi aure ko sau ɗaya banje gidan Anty Labiba ba ita ma kuma tun washe garin da aka kaini bata sake komawa ba wata tara kenan muna waya muna chat. Har ga Allah kawai ina jin kunyar abin da na mata akan zancen aure na da Bilal ne, duk da ko a fuska bata nuna mun komai ba amma nasan Anty Labibar da na sani babu yanda za'a yi nayi aure ta ɗauki wata tara bata tako gida na ba har idan ba da wani abu data riƙe a ranta ba ni kuma bana son naje ta tayar da maganar shiyasa kawai nake gudun zuwa gidan nata. Kuma muna haɗuwa a gida yaranta ma kusan duk sanda su Amira zasuje mun tare su ke zuwa dasu.

Amsawa Mama nayi da zanje in sha Allah na wuce tana sake jaddada mun na tabbata naje asibiti bata son sakarci. Washe gari nayiwa Bilal zancen zanje gidan Anty Labiba, be musa yanda ya saba ba yace duk sanda na shirya na je, take na kirata wayarta a kashe ina hawa whatsapp na ganta online dan haka na ce mata gobe zanzo in Allah ya kaimu. Amsar data bani
"Bana nan" na ringa juya maganar, bata ma tambayi ƙarfe nawa zanzo ba ko wani abu kawai tace bata nan. Da take cewa in har na auri Bilal zata yanke zumunta dani ashe dagaske take kenan? Take shaiɗan ya shiga mun famfo, na watsa hannye a fili nace
"Kin huta ai. Bilal dai da bakya ƙaunar gani na dashi shi ɗin Allah ya zaɓa mun muyi rayuwa tare se haƙuri". Shikenan naci gaba da sabgogina. Ganin har an kai azumi na ashirin da uku Bilal be bani ko ƙyalle da sunan na siyi kayan sallah ba na cire rai da zeyi mun ban kuma tambaye shi ba saboda hidimar daya zo masa katsahan ƙanwar sa da akayi bikin mu tare ta haihu haihuwar kuma tazo mata da matsala ƙarshe se CS aka mata mijin dake bashi da mutunchi tunda ta kwana ta wuni tana labor washe garin ya tattaro ta ya kawo ta gida su suka yi duk wata ɗawainiyar asibiti har aka ciro mata babyn kwana uku kenan ko zuwa ganin su beyi ba. Bilal ne ya biya kuɗin aikin yayyen sa mata kuma suka haɗa mata kayan barka da sauran abubuwan buƙata da suka tashi suka yiwa yaron huɗu ba da sunan Babban Yayansu da suke uba ɗaya shine ya bada ragon da aka yanka masa.

Cikin kuɗin da Abba ya tura mun tun washe garin da naje gida na siyi lace guda biyu na haɗa da atamfofi biyu cikin na lefe da ban taɓa komai a ciki ba na bada ɗinki. Na san Mama bata san ya bani kuɗin ba dan haka ni ma ban mata zancen ba, da sauran kuɗin nayi sauran buƙatun da nake dasu ciki harda zuwa asibiti na buɗe file na anti natal dan da na yiwa Bilal magana ina so naje asibiti cewa yayi me zanje yi bayan ga magunguna nan an bani kuma na samu sauƙi tun da a zahiri babu abinda yake damu na banda amai se zazzaɓin dare gari na waye wa kuma zan shiga sabgogi na idan naji garau nayi azumi idan naji bazan iya ba na sauke. Saboda ina so nayi masa ba zata akan cikin se kawai nace masa ulcer se ta tasar mun ya siyo mun Omeprazole da gestid a chemist yace na ringa sha.

Cikin ikon Allah azumi ya ƙare anyi sanarwar ganin watan sallah ya tsaya, kasancewar sallah ta ta farko a gidan aure yasa naji ina sha'awar nayi abincin sallah nima yanda naga anayi. Dake tunda Fadila ta haihu Bilal suke ta zirga zirga tsakanin gida da asibiti wata ran se tara yake dawowa yau ɗin ma yana gida aka kira shi jikin yaron ya rikice dake da jundice aka haife shi shine ya fita suka mayar dashi asibiti. Har mamaki nakeyi yanda ya damu sosai da lafiyar ƙanwar tasa ba kuma ya ƙyashin kashe kuɗi, da na tambaye shi ina mijin ta da suke ta ɗawainiya da ita haka ma cewa yayi shi ba ta mijinta su keyi yanzu ba dan idan ta mutu su suke da asara ba mijin ba jira sukeyi ma a ƙare azumi suyi ƙarar sa ya saketa ba zata koma ba. Ban tsawwala da jin dalili ba nace Allah ya rufa asiri kawai muka bar zancen.

Dake muna da kaji da jan nama ba'a fi kwana uku daya siyo su ba kajin guda huɗu ne manya manya se naman shima da ɗan auki se na ɗibi kaji uku na samu yaro ya yiwo mun cefanen miyar taushe na jiƙa farar shinkafa akan zanyi waina da sinasir. Tun daren na haɗa miyar ya rage ganye kawai zan zuba na saka ta a freezer na kwaɓa meat pie shima na haɗa na deɓi kaɗan na soyawa Bilal na saka sauran a fridge. Ina da samosa da spring rolls dama nace se na haɗa da safen na soya su tare. Na gaji lilis se goma saura na gama gyaran gida da wanke wanken abubuwan dana ɓata dan har zoɓo na haɗa, ina wanka Bilal ya dawo daga ganin fuskar sa na san babu lafiya nan yake sanar mun ɗan Fadila ne ya rasu. Na taya su jimami har nace zan kira ta lokacin yace na bari se da safe, haka nan muka kwana yanda Bilal ya damu kamar ɗan cikin sa ya rasa. Na ringa ayyana yanda zeyi farin ciki idan ya san ya kusa samun nasa ɗan shima.

Washe garin da wuri ya shirya dan zasuyi jana'izar yaron kafin lokacin sallar idi. Nima kafin ƙarfe tara na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login