Showing 174001 words to 177000 words out of 257873 words
tarar da kai kana yi zan kuna watsa shi a duniya kowa ya gani dan ba zai yuwu yar uwata ta cigaba da shaƙar baƙin ciki ita kaɗai ba" abinda Mu'azzam ɗin ya faɗa masa kenan daya fito daga motar bai kuma tsaya ya bashi damar cewa wani abu ba ya juya ya tafi.
Shi yanzu ina zai tsoma rayuwar sa yaji sanyi? Idan ta tabba Mu'azzam ya ɗauke hoton su ai ya gama yawo domin ya san yaron farin sani bashi da mutunchi kuma dama can ba ƙaunar sa yakeyi ba tsaf zai aikata masa abinda ya ambata. Komawa yayi ciki yana jan ƙafa kamar wanda ya sauka daga iskokai, a falon Halima ya zauna kan kujera ya dafe kai da hannu biyu cikin tsananin tashin hankali da rashin sanin madafa.
Duk Jalilah ce ta janyo masa, shiyasa tun jiyan data kira shi kwata kwata bai yi farin ciki ba jikin sa kuma ya ringa bashi kamar akwai wani sharri dake tareda ita ilai kuwa gashi nan ta jefa shi a masifa.
Ya shafe sama da awa biyu a zaune a gurin yana sharce zufa dan tunanin sa ma ya ƙi tsayuwa guri ɗaya balle ya nemi mafita, Jalilah ko tana cikin ɗaki tana bacci abunta tamkar babu abinda ya faru. Ana ƙwala kiran Azahar ya jiyo ana buga get. Zabura yayi ya miƙe, abinda ya fara zuwar masa yan gidansu Halima ne suka zo kwashe kaya shikenan ta faru ta ƙare wai an yi wa mai dami ɗaya sata.
Kasa fita yayi ya buɗe sai da ya ji bugun na ƙaruwa nan kuma ya shiga tunanin idan Jalilah ta farka wani sabon case ɗin ne dan haka ba shiri ya fita. Wayar sa ya ɗauka a bayan pillow daya ɓoyeta kafin ya fita ya tsaya daga baya yana tambayar waye?
Muryar Fadila ya ji ta saka shi sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi hankalin sa ya ɗan kwanta, amma kuma daya tuna lokaci da kuma irin bugun da takeyi ya san ba haka kawai ta kawota ba, to ko yan gidansu ya turawa? Amma kuwa da ya gama dashi. Har wasu maiƙon hawaye yaji a idon sa saboda tunanin da yayi, amma kuma ai cewa yayi idan ya sake takurawa Halima yanzu kuma shi ko bin su bai yi ba ma ai.
Cigaba da buga ƙofar da tayi da ƙarfi ya saka ya zura muƙulli ya buɗe, tare hanya yayi ganin tana ƙoƙarin shiga ya ce
"Ke meye haka? Ina zaki je?"
"Dan Allah ka matsa na shiga ni na gaji ka san uwar ranar dana kwaso kuwa? Sannan minti na nawa a tsaye ina bugu baka buɗe ba" ta bashi amsa tana ƙoƙarin raɓe shi ta shiga amma ya hanata. Babu wasa ya ce
"Ke baki da hankali ko kwai mace a gidan ne da zaki ce zaki shiga ne?"
Tsayawa tayi ta kalle shi daga sama har ƙasa ta ce
"Lallai ma Yaya Bilal sai kace ni ɗin ba muharramarka bace ko kuwa ma yau na fara zuwa gidan Haliman bata nan?"
"To na canza tsari daga yanzu ba zaki sake shiga ba sai matar gidan ta dawo" ya bata amsa yana sake babbake ƙofar. Shiru tayi kamar mai nazarinsa kafin ta ce
"Sai dai idan kuma wani abun kake ɓoyewa a ciki da baka so a gani"
"Ke ni kike gayawa haka dan ubanki sa'anki ne ni?" Ya taso mata. Tayi baya tana magana ƙasa ƙasa ta ce
"Zancen gaskiya dai ai ga alamun rashin gaskiya nan sun bayyana a tareda kai"
"Bar nan kafin na saɓa miki" ya faɗa yana nuna mata hanya, ta harareshi kafin ta ce
"Toh Hajja ce ta aiko ni in kira mata kai kuma tace kazo yanzu yanzu take son ganinka tun safe akw ta neman ka a waya ka kashe har Yaya Hafiz ta kira ya ce baka je Office ba shiyasa ma tace na zo gidan ƙila kana nan".
Cikin gidan ya koma bayan yace ta tafi zai zo kafin ya mayar da ƙofar ya rufe Wallet ɗin sa ya ɗauka da key ɗin mota, sai da ya leƙa Jalilah dake bacci kamar a gadon Mamanta kafin ya fita daga gida bai ɗauki motar ba ma gudun kar ƙarar ta ta tashi Jalilar.
A baki titi ya tarar da Fadila tana jiran abin hawa fuskar nan da ta sha mai tayi jajir saboda rana shi sai lokacin ma ya lura, cikin sa'a yana zuwa suka samu Adaidaita. Bayan ya zauna ya kunna wayarsa tamkar Zulaiha na jira kuwa ko gama kamawa batayi ba kiranta ya shigo.
Ya ɗaga, mita ta dasa masa akan katse wayar da sukeyi ɗazu da yayi kuma ya kashe gaba ɗaya daya sake kira bata same shi ba ya bata haƙuri kafin ta faɗa masa ainihin dalilin kiran wai taji shiru cikon kuɗi.
"Ina ganin 2m da yawa sai da muka shiga kasuwa sai kaga yan kayan da muka siyo da ita. Ni wlh da na san haka ne gara ka haɗa mun lefena da kanka na san sai ka fi sakin jiki ka zuba mun kaya masu kyau da tsada" ta faɗa cikin shagwaɓa.
Mamakin maganarta ya kamashi amma dai bai nuna ba ya ce zai aika mata da saƙon kawai saboda Fadila data baza kunnuwa dukda tayi kamar bata sauraronsa amma yasan hankalinta yana kansa. Suna sauka daga Adaidaitan kiran Jalilah ya shigo wayarsa, sai da gaban sa ya faɗi dan bai zaci zata farka da wuri ba.
Waje ya tsaya ya amsa, cike da izza da kuma muryar bacci kamar wata uwarsa ta ce
"Ina ka tafi?"
"Na ɗan fita ne daga nan zan biya na siyo miki lunch" ya bata amsa, shiru tayi kamar na zata sake magana ba kafin ta ce
"Karka zauna, Chinese rice nake so da grilled chicken kuma ka san ta inda nake so"
"Na sani ranki ya daɗe ai dama can zan je" ya faɗa cikin lallashi, tayi gajeran tsaki kafin ta kashe wayar. Ajiyar zuciya ya sauke a ransa yana ayyana kalar rashin mutunchin da zai mata daga sanda ya kammala shirinsa akanta.
Tun da ya ga takalma da yawa a ƙofar ɗakin Hajjan hankalinsa ya sake tashi amma haka ya daure ya shiga da sallama, gaba ɗaya yayan ɗakin su su shidda shi na bakwai suna zaune sai kuma Hajja. Idanuwa suka zuba masa kamar sunga bakuwar halitta hakan ya sake jefa shi cikin tashin hankali amma yayi namijin ƙoƙari gurin ɓoye firgicinsa ya samu guri can nesa ya zauna kai a ƙasa saboda harar da Hajja take aika masa.
Daƙyar ya buɗe baki ya fara gaisar da Hajjan ta dakatar da shi tana cewa
"Ni na isa? Riƙe gaisuwarka yau kwananka nawa rabon da ka tako gidan nan balle ka kira ni a su wa Bilal?"
Ƙasa ya sakeyi da kai bugun da zuciyarsa take yi kuma ya ragu dan ya ɗan samu nutsuwa daga maganar Hajjan ya fahimci wani abun daban ya saka ta kirashi ba wanda yake tunani ba. Anty Amina ce ta ce
"Amma dai koma menene tunda ya gaishe shi da kin amsa Hajja" ai kuwa ta taso mata tana cewa
"Ba zan amsa ba uwata Amina na ce bazan amsa ba idan ya so ki tsine mun in bi duniya saboda ban amsa gaisuwar Bilal ba"
"Allah ya baki haƙuri" Aminar ta faɗa tana gyara zama, Hajja tayi ƙwafa ta ce
"Ba tareda ɓata lokaci ba zan gabatar da abinda ya saka na taraku, ba kuma wani abu bane illah ku zame mana shaida tsakani na da Bilal". Da sauri ya ɗaga kai ya kalleta cikin rashin sanin mai yayi mata da har zata kawo shaidu kuma?
Ta zaro takarda da biro daga saƙon kujerar da take zaune ta jefa masa tana cewa
"Gashi nan ka rubuta komai da zan faɗa maka". Gabansa ne ya yanke ya faɗi, tsakanin Halima da Zulaiha gaskiya babu wacce zai iya saki a yanzu idan ma abinda Hajjan take buƙata kenan sai dai tayi haƙuri.
"Na ɗauki cikinka tsayin wata goma dan sai da ka haura wata tara a ciki na ka samu guri ka bararraje. Duk yayan dana haifa babu wanda na sha wahalar laulayi da naƙudar haihuwarsa kamar kai. Faɗar hidimar da nayi ta sunanka kuwa ɓata lokaci ne saboda akanka na fara haifar ɗa namiji. Tun da ka fara taka ƙafarka ban huta saboda jaye jayen jidali, ka shiga ɗakin Saude kayi mata ɓarna haka zata yi ta surfa bala'i tana mun gori banida kayan jere irin nata shiyasa nake turaka san ka lalata mata.
Sai da na daina gaisawa da kowa a unguwar nan saboda kai dan baka da aiki sai neman tsokanar yara a unguwa ko a makaranta kai ko kallon banza yaro ya maka ka faɗa mun har gaban uwarsa nake takawa naje na rama maka balle kuma mutum ya taɓa ka" ta fyace majina tana cewa
"Ai na san Amina da Ladi ba ku manta ba har a cell ɗin yan sanda sai da na taɓa kwana saboda Bilal, kaje ka daki wani yaro ashe Babansa ɗansanda ne suka zo zasu tafi da kai na hana ƙarshe ni suka tafi dani. Ban huta da jidalinka ba saida ka tafi Jami'a. Duk wani tanadi na da abinda nake dashi sai da ya ƙare akanka bayan rasuwar mahaifinku saboda yanda ka ɗauki rayuwar jin daɗi da ƙyale ƙyale, daga sanda ka gama makaranta ka samu aikinyi a maimakon ni da na sha wahalar ka ace ni zan mori samunka sai labari ya sha banban" ta ƙarasa tana fashewa da kuka kamar wacce aka daka.
Kallonta ya ringayi cikin rashin fahimta kafin ya juya yana kallon sauran yan uwansa kowanne da kalar yanayin da fuskarsa take ciki. A kan Hajja ya tsaida idonsa ganin yanda take kuka hankalinsa ya sake tashi, shi sam bai fahimci in da waɗannan maganganun suka dosa ba kuma ta yaya ma Hajja zata ce wai bata morar samun sa tsakani da Allah?
"Dan Allah Hajja kiyi haƙuri kiyi mun magana da yaren da fahimta duk mai ya kawo waɗannan maganganun har kina kuka haka?" Ya faɗa yana matsawa gabanta. Ta fyace hanci da gefen ɗankwalinta kafin ta ce
"Tun ina yar shekara goma sha huɗu aka saka mun lalle da ubanku kuma wannan ɗakin cikinsa aka kawo ni yau shekarata arba'in da biyar kenan a cikin har ubanku ya mutu aka raba gado a nan ɗin dai nake zaune kuma ginin shine tun na usuli babu abinda aka canza sai yan toshe toshe da manne manne da akayi,
Ina zaune anan ɗin nan ace ɗan da na haifa na sha wahalar sa ya tafi can duniya ya samu wata uwar da yan uwan daban yana bauta musu har ka siya musu gida kuma kai kake riƙe da su kan jiki kan ƙarfi, nan da Fadila da Abubakar suka gama sakandire zasu tafi Jami'a cewa kayi sai sai ɗaya daga cikinsu ya haƙura dan ba zaka iya ɗaukar nauyin su duka biyun ba amma can ba dangin iya ba na Baba a duniya ka ɗauki nauyinsu har gaban abinda ya fi Jami'a ma to wlh cikin biyu dole ayi ɗaya, ko dai ka saketa ko kuma daga yau ka nemi wata wacce zaka ringa kira da uwarka amma ba ni ba" ta sake rushewa da kuka.
Ƙasa ya sauke kai, shi kam yau tazo masa ba'a yadda ya tsammata ba wane irin bala'i ne haka wani na bin wani?
Yana ji Anty Habiba tayi caraf ta ce
"Ai wlh tallahi Hajja ba dan Bilal yana kama da mu ba ni zan ce canza miki shi akayi a Asibiti ba ɗanki bane. Ai ko ɗan ruƙo ba zai yi abinda Bilal yayi ba caɓ" ta kyaɓe baki tana rufe baki Anty Ladi da Hadiza ma suka ɗauka. Fadila ce ta ce
"Taɓ, to ai baki ji komai ba ma Hajja yanzu haka in kinji miliyoyin kuɗin ya basu wai kuɗin lefe sai kun riƙe baki a haka ma kiransa take wai na zai isa ba ya ƙara musu" su ukun suka haɗa baki suna cewa
"Kinji ko, ai wlh ba haka suka barshi ba. Ba'a fita daga masifar Halima ba shine zai sake jajubo mana wata"
"Ku dai ba zaku taɓa iya zama ku tashi ba tareda kun sako Halima a ciki ba? Yanzu kuma menene nata a maganar da kukeyi?" Anty Amina da bata tsoma musu baki ba sai yanzun ta faɗa. Hajja ta ce
"Ai duk ita ce silar komai, tunda ya auri yarinyar nan kamar wanda aka sakawa hannu shikenan al'amuransa suka taɓarɓare ni dai aurenta babu abinda ya tsinana mun idan ba ɓacin rai da baƙin ciki ba, wannan auren da yayi ai da saninta amma da yake muguwa ce mai baƙar zuciya taja bakinta tayi gum idan da ta faɗa mun tun farko ta ina zan bari haka ta faru?"
"Yanzun ma ai bata ɓaci ba Hajja yanda kikace dole ya saketa in dai yana so yaga haske a rayuwarsa. Matar da tun babu aure yake musu wannan uwar hidimar idan ta tare kuma ai wlh janye shi zatayi ba zaki sake ganinsa ba.
Ta bakin naki mugunta ta saka Halima yin shiru bata faɗa ba tunda ai ba zata ce bata san duk tsayin lokacin nan mijinta na tareda wata ba shine saboda tsabar munafunci ta bar gidan ai in sha Allahu itama ta tafi kenan itama wannan kuma ka sallameta ga mace har mace irin arziƙi na binka soko ka tsaya kana bin wanda ba zasu tsinana maka komai ba" cewar Anty Habiba.
Sai lokacin Abubakar da yayi kamar baya gurin ya ce
"Wlh tallahi ku kuka da kanku sanda haƙƙin Anty Halima zai tambayeku amma duk ba laifin kowa bane laifinki ne Hajja saboda a gidan nan yanda kika dama haka ake sha.
Duk cikinmu babu mai iya miki musu, Allah ya hore miki yayanki mutum nawa ne suke addu'a da fatan Allah ya ɗora su akan yayansu ta yanda zasu ringa jin maganarsu amma ke Allah ya miki wannan arziƙin a maimakon kiyi amfani da hakan ki tarbiyyantar damu ta yanda ko bayan ranki za'ayi alfahari da abinda kika haifa amma kin bari son zuciya da shaiɗan sunyi tasiri a zuciyarki suna kuma jagorantar al'amuranki".
Tsit sukayi kamar ruwa ya cinye su suna sauraronsa, ya miƙe tsaye yana cigaba da cewa
"Wlh idan har baku canza wannan hanyar da kuke tafiya akai ba nan ba da daɗewa ba zaku fara dana sani mara amfani, abinda Yaya Bilal yayi idan da da niyya mai kyau yayi shi ai ba aibu bane har a gurin Allah kuma zai samu lada, amma yanzu kuwa aikin banza kayi domin ka tsallake farilla ka bar dolenka a gida matar aurenka ka barta ɗauke da nauyin kanta dana yayanka ka tafi kana bautawa wasu. Kuma nan ba da daɗewa ba zaka gane kallon kitse ka daɗe kana yiwa rogo" ya ƙarasa yana wata yar dariya mai cike da ma'anoni daga nan ya fice daga falon.
Anty Ladi ce ta ce
"Ashe ba iya Bilal ne ɗan abu ta kazan uban ba, koda yake dama shiru shiru mutum ai kaji tsoron sa idan suka tashi sai sunfi uban kowa iya iskanci toh wlh Hajja dole ma ki tashi a tsaye kina dai jin sa tun bai yi aurenba ya iya tsayawa gabanki yana faɗa miki magana wannan ai kuma bamu san kalar matar da zai kwaso ba ƙila haɗuwa zasu ringayi shi da ita suna zaginki"
"Allah ya kiyashe shi da zagin mahaifiyar sa balle har ya auro wacce zasu zageta tare" Anty Amina ta faɗa sannan ta juya kan Hajja ta ce
"Kiyi haƙuri Hajja amma gaskiya Abubakar ya faɗa miki, idan muka gyaru kece haka idan muka lalace duka ke za'a zaga. Yanzu wane kallo kike so duniya tayi miki ba'a gama da Halima ba yanzu ki ce sai ya saki matar da ko tarewa ba tayi a ɗakinsa ba akan me?
Babu wanda ya ce abinda yayi yayi daidai ko ya kyauta amma kuma ya rigada ya faru tunda har ba wani aibu bane a ciki ai babu hujjar kuma ace za'a raba aure ko makamancin haka.
Yanda kika ce kin haƙura kin karɓi ƙaddara kiyi haƙuri ki kuma bishi da addu'a shikenan amma ace da kanki kike nema ki buɗe masa hanyar auri saki wace riba zaki ci akan hakan?
Ni wlh na ɗauka kiran da kika mana maganar Halima zakiyi, yanzu tsakani da Allah ace yarinyar nan kusan watanta biyu a gida amma babu wanda ya bi sahu ko yaje bada haƙuri ai ko shirun da iyayenta sukayi kaɗai ya isa ya saka ku sha jinin jikinku ayi abinda ya kamata domin dai sai dai mutum yaƙi Allah kawai ya zagi Halima baya ga haka duk mun san irin haƙurin zaman da takeyi dashi a yanzu ko a gaba wlh ba zai taɓa samun macen da zai taka kamarta su kwashe lafiya ba kuma har idan yayi kasadar rabuwa da ita ban masa baki ba amma wlh ba zai maida kamarta ba ke kanki na zaki maida suruka kamar Halima ba".
"Ni idan kina magana wlh mamaki kike bani Amina har yaushe kika sauka daga tafiyar da yanzu kike kira ta rashin dai dai da har zaki ringa yiwa mutane wa'azi?" Habiba ta faɗa, Amina ta kalle ta tace
"Kema kika ce na sauka daga turbar ɓata na bi ta gaskiya toh Alhamdulillah tunda na gane kuma kuma fatan da nake muku kenan ku gane kafin lokaci ya ƙure muku"
"Wato mu da Hajjan ne akan turbar ɓata?" Anty Ladi ta faɗa ba tareda shakka ba kuma tace
"Ƙwarai kuwa, kun ɗora ranku akan son zuciya da kwaɗayi ga gaskiya ƙiri ƙiri a gabanku ku rintse iso ku ƙi kallonta. A shekarun Hajja yanzu dama akwai abubuwan da sai an fara mata uzuri, mu ya kamata idan ta kuskure mu nusar da ita ba kuma mu cigaba da biye mata akan abinda mun tabbatar ba gaskiya bane duniyar nan fa ba matabbata bace duk yanda ka so da sonta kuma akwai ranar da zaka barta dan haka gara mu yiwa kanmu faɗa mu kuma yiwa goben mu ta ainihi tanadi. Ni dai idan har ba maganar yanda za'ayi uwargidan sa ta dawo za'a yi ba kiyi haƙuri Hajja kada a sake kirana dan ba zan zo ba" daga haka ta