Showing 78001 words to 81000 words out of 257873 words

Chapter 27 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

508

Tsayuwar da kaga nayi a nan yanzu Yayanta Abdurrashid ya gama mun barka shine na tsaya ina jiran wanda ze zo ya faɗa mun gaskiya ko aka sin zancen kuma se gaka, amma lallai mutanen nan sun raina ni. Ace matar tawa ta fara naƙuda har ta haihu babu wanda ya kira ni ya gaya mun? Kenan da mutuwa tayi se dai kawai ace nazo na ga gawarta ko me?" Ya faɗa cikin ɓacin rai. Nasir ya dafa shi yace

"Kar dai kayi saurin yanke hukunci; nima yanzu Fauziyya ta kira ni take gaya mun taga Zubaida ta saka, ƙila yanzu ta haihu kuma kasan sharrin network ta yuwu ma sun kira ka be shigo ba. Tun da dai ta haihu lafiya ai anyi me wahalar yanzu se ka kirata muji suna wane asibitin ne se muje".

"Zance ma kakeyi wlh, ai har idan an ɗauke ni da muhimmanci tun kafin a fita da ita daga gida ya kamata a kira a nemi izini na kuma a gaya mun. Idan basu same ni a waya ba bani da dangi ne? Taku nawa ne tsakanin mu dasu da ba zasu aiko a gayawa mahaifiya ta ko wani ɗan uwana yaje a tafi dashi asibitin ba?. Ashe dai da ake faɗar irin wulaƙancin da masu kuɗi suke yi su mayar da mazajen yayan su ba komai ba dagaske ne tunda gashi ya biyo ta kaina se dai ni ba shashasha bane da zan ɗauka wlh se na nuna musu nasan mutunchin kaina" ya ƙarasa a fusace yana zaro wayar sa daga aljihunsa.

Lokaci ɗaya karsashin rashin mutunchin daya hau ya sake shi daya shiga jerin missed calls ɗin daya gani akan wayar sa. Kafin kiran Anty Labiba da kusan minti talatin Abban su Halima ya kira shi har sau biyu, alamar saƙon daya gani a saman wayar ya duba Abban ne dai ya aje masa saƙo yana sanar dashi Halima tana cikin halin naƙuda ya rubuta masa sunan Asibitin da suke da har da kwatancen inda ɗakin haihuwar yake. Kamar an watsawa kaza ruwa haka yayi laƙwas, Nasir yace
"Ka gani sun kira ka ko?"
Kamar mara gaskiya ya mayar da wayar aljihunsa yana gyara zaman rigar sa yace

"Oho dai koma menene ba'a mutunta ni an bani ƙima ta ta mijin ta ba tun farko ma ai ni ya kamata ta kira ta gayawa naƙuda ta kamata ba wai yan gidan su ba ai" ya faɗa tamkar bashi da masaniya akan ta fita daga gidan. Nasir dake kallon sa kawai ya girgiza kai yace

"Kaji dashi, yanzu dai idan zamu je asibitin bismillah; idan kuma ba zaka je ɗin ba ni in kama gabana ina da abinda zanyi a chemist".

"Babu in da zanje, idan ina da muhimmanci zasu zo har in da nake su buƙace ni" Bilal ya faɗa yana wani buɗa hannu, hannu biyu Nasir ya ɗaga yana cewa
"Allah ya taimaka ya bada sa'a; idan ta dawo gida se ka sanar dani idan ma kuma can gidan su ta wuce duk dai ka gaya mun, ko da yake karka damu zan ji a inda na samu labarin haihuwar kawai ba se ka kira ni ba" daga haka ya juya yayi tafiyar sa Bilal ɗin na tsayar dashi be kula shi ba ya shige motar sa daya ajiye gefeb masallacin ya tafi.

Gida Bilal ya juya, yana shiga ya tarar da Hajja na saka hijabi; da mamaki ya kalle ta yace
"Unguwa zaki je ne Hajja?"
"Yanzu Fainusa tayo waya tace mana Halima ta haihu shine zamu je mu gano su" ta bashi amsa. Se ya wani ɓata fuska yace
"Yanzu an kira ki ne an gaya miki haihuwar balle ki ɗauki ƙafa ki tafi? Ke da Fainusa waya fi zama a haƙƙu da su kira? To ki koma ɗaki kiyi zamanki ko ni da nake uban ɗan basu kira sun gaya mun ba nima a wai wai naji a gari dan haka babu in da zamu je, idan sunga muna da muhimmanci sun san inda zasu same mu ai zasu zo" ya faɗa yana shigewa ɗakin Hajjan.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 20*

Washe gari har azahar banga Bilal kuma babu wani daga dangin sa se yan uwana da suke ta kaikawo a gurin. A ƙa'ida da safe za'a sallame mu tunda na cike awanni shida na ƙa'ida amma da likita ya shigo duba mu ya ɗauki yaron se yace akwai alamun jundice a tare dashi dan haka ba zasu sallame mu a lokacin ba se mun ƙara 12 hours under observation idan abun is not severe da zamu iya tafiya gida tohm. Nan da nan hankali na ya tashi saboda yanda nake jin labarin jundice ance yana kashe jarirai, shaiɗan da saƙe saƙe tuni har na fara hasaso wai babyn ma mutuwa zeyi. Ina kwance nake wannan tunanin se kawai na tsinci kaina da fashewa da kuka kamar har abun ya faru ne.

Gwaggo, ƙanwar Abbanmu ta taso da sauri ta iskeni tana cewa
"Lafiya Yaya? Ko ciwon ciki ne?" Nan hankalin sauran mutanen ɗakin ya dawo kaina duk suka shiga jera tambayar meya same ni? Ko wani gurin ke yi mun ciwo ni kuwa kamar suna tunzura ni na samu guri na cigaba da Sheƙa kuka ba ji ba gani.
"Ku rabu da ita babu inda yake mata ciwo baze wuce akan wancan mijin nata da be san daraja da ƙimar ta ba take wannan kukan. Ace ka haihu gari ɗaya ba wai daga wata nisan duniya ba miji ya kasa zuwa ya duba halin da kake ciki ko abinda ka haifa ba? Ko da yake ita ta jawa kanta ba wani da dan haka namu ido".

Maganganun ta suka buɗe musu fili kowa ta shiga tofa albarkacin bakinta dukdai be wuce zagin Bilal da Ahalin sa ba.
"Ai wlh ko a wata jaha suke daga dai haihuwar ta tun jira da yamma zuwa yanzu azahar yaci ace ko mutum biyu sun taso sun zo amma ce gari ɗaya ko shi uban cikin be zo ba balle wani nasa yayi kara shima yazo? To Alla ya rufa asiri, duk irin abunda aka ringa hango mata kenan soyayya ta rufe mata ido shima Yaya Aminu ya biyewa Yaya Salamatu, dan kai ka auri mace ka mata halacci se aka ce yarka ma idan tayi irin auren zata dace? Tsabar lalacewa ma fa ase daidai da ginin gidan shi ya bashi maƙudan kuɗaɗe ya ƙarasa duk a shawarar Yaya Salamatu. Wannan yaron yace mun a gurin sa aka siyi ƙofofi da wundunan gidan yace saboda samun guri wanda ma sukayi magana da Yaya Aminun za'a bashi da yaje se cewa yayi basu yake so ba ya nuna wasu daban kuma Yayan yace a bayar. Abun nan ya daɗe yana cimun rai kawai nayi shiru ne dan kar ace a baki na magana ta fito".

Murmushi kawai Anty Labiba ta ringa yi tana gyaɗa kai irin abun ya mata daɗi, Anty Rakiya wadda yayan maza suke da su Abba tace
"Kuma shine saboda su ɗin ba gadon arziƙi bane yayi mata lefe a leda; wato bata kai ko a cikin kuɗin da uban nata ya bashi ya ragi wani abun ya siya mata akwati ba"
"Ke kuwa idan suka zubo a akwati ai abun tsiyar ƙara yawa zeyi, yo ina abun zubawa a akwatin ma banda abinki Rakiya? An dai cuci yarinya kawai an kaita an baro" Gwaggo Hajiyayye ta faɗa. Se Anty Labiba tayi caraf tace
"Ta dai cuci kanta waya mata dole a auren sa?"

Dana gaji da sauraron cin mutunchin da suke mun se kawai na tashi daga kan gadon na shige banɗaki. Tunani nake dagaske Abba ne ya bawa Bilal kuɗin daya ƙarasa ginin sa ko dai surutun su ne kawai?

Da ace Anty Labiba ce ta faɗa zan iya cewa duk cikin son ta cusa mun tsanar Bilal ne amma kuma banga hujjar da ze saka Anty Rakiya tayi ƙarya cikin wannan maganar ba, a karon farko naji haushin Bilal har zuciyata. Idan har ta tabbata dagaske Abba ne ya bashi kuɗin nan amma har ya iya buɗe baki ya kira ni da yar matsiyata ba sau ɗaya ba sau biyu ba lallai Bilal ban ma san a wane aji ya kamata na ajiye shi ba. Kuka na se ya canza salo, dama ɗazu na jin daɗi ne yanzu ko dana samu dalili me ƙarfi se na shiga kukan tausayin kaina. Bubbuga ƙofar banɗakin da akayi yasa na wanke fuskata na fito.

Abba, Baba Salahu se abokin Abba Baba Lawan ne suka zo, ban yarda mun haɗa ido ba na gaishe su Baba Salahu ya shiga tambayar meya same ni ido na ya kumbura ba kunya Anty Labiba tace wai kumburin haihuwa ne.
"Shine haka har ido kamar wadda tasha kuka?" Baba Lawan ya tambaya. Ni dai shiru nayi bance komai ba, basu jima ba suka tafi. Haka yinin ranar ya doshi ƙarewa har la'asar banga Bilal ba ban kuma ga wani daga ɓangaren sa yazo ba.

Zuwa lokacin har na rasa wane tunani zanyi akan ma'anar abinda Bilal ɗin yayi mun. Da kunne na naji Abba yana faɗar ya kirashi be amasa ba kuma ya tura masa da saƙo tun sanda aka kawo ni asibiti; sannan ni ma da kai na na kira shi da wayar Anty Labiba be amsa ba. Nama rasa wane tunani zanyi, shin yana sane yaƙi amsa wayoyin kuma yaƙi zuwa ko kuwa akwai wani al'amari daban da bamu sani ba?

Haka muka sake kwana; ƙarfe goma na safiyar washe gari aka sallame mu. Gidan mu aka wuce dani, a ɗakin Mama na kwanta dan na shiga tsohon ɗaki na in da yake na Amirah a yanzu ganin kayan ta a barbaje yasa na fahimci ba a nan zamu zauna ba ƙila ko ɗakin baƙi za'a gyara mun.

Mama Fauziyya ce tayi mun wanka, nasha kuka amma kuma naji daɗin jiki na duk gajiyar dake tare dani ta warware. Se da naci abinci kafin na kwanta, bacci nake so nayi se dai tunanin daya cunkushe mun zuciya ya hanani.
Gaba ɗaya zuciyata babu daɗi, kwanaki biyu daya kamata su zama mafiya farin cikin a rayuwata sun juye zuwa na akasin haka. Ace na haihu har kwana biyu uban ɗan yana raye amma be iya zuwa in da muke ba, idan wani ne ya gaya mun haka zata iya kasancewa tabbas bazan yarda ba se gashi ni da kaina na shaida hakan. Amma dana tafi lissafin baya tun daga goyon cikin da yanda sam ban shida irin ɗoki da farin cikin da ƙawaye na suke bani labarin mazajen su na yi ba a lokacin da suka samu ƙaruwa se banyi mamaki da abinda ya aikata mana a yanzun ba.

Na tuna sanda Hansa'u ta haihu, yar da a haifa ita ce ta goma sha biyu a jerin yayan mijinta amma hakanan ya baro abin da yake yi a Dubai in da yake kasuwancin sa ya taho a ranar ya duba su sannan ya juya ya tafi. Irin soyayyar da nayi tunanin a gurin yaro matashi sabon jini kaɗai ake samun ta se gashi rayuwar Hansa'u da Mijin ta ta ƙaryata tunani na.

Sau tari har bana son buɗe status ɗin ta saboda abubuwan da nake cin karo dasu da suke sosa mun zuciya har nake jin kamar da gayya ma take ɗorawa saboda na gani. Duk da shekarun mijinta baya kunyar su fita tare su je guraren Shaƙatawa a ciki da wajen ƙasar nan suyi hotunan da kana kallo baka buƙatar a faɗa maka su ɗin masoya ne dake cike da farin ciki. Tun da na auri Bilal sau ɗaya zan ce mun taɓa zuwa wani guri shima ba wai haka nan ba dalili ne ya kaimu birthday budurwar wani abokin aikin sa Patrick da akayi a wani garden. Duk sanda na roƙe shi da mu fita wani guri ko da gidan zoo ne mu sha iska se yace ba yanzu ba.

"Yanzu ke ba zaki ji wani iri ba na ɗauke ki a mashin kawai muje kowa suna zuwa a manyan motoci masu aji?" Abin da yake faɗa mun kenan duk sanda na masa maganar. Na kan yawan tunasar dashi akan
"Shi farin ciki babu ruwan sa da wadata. Shi yasa ma nake ce maka muje irin guraren da nasan munfi da yawan waɗan da zamu tarar wadata ƙila mu zama abin kallo ma a gurin su da bayar da sha'awa. Sannan duk ma inda muka ga damar zuwa ina ruwan mu da masu zuwa a motoci? Se ta yuwu muje mu kashe dubu ɗaya wanda yazo a ƙatuwar motar se dai kawai yayi zagaye ya tafi ba tare da ya kashe ko sisi ba ni ban san me yasa kake yawan damuwa da maganaganun mutane ba ko kallon da mutane zasu maka. A baya da kake ɗauka ta a mashin ɗin muke zuwa me yasa baka taɓa tuna za'a raina ka ba se yanzu?"

Duk sanda mukayi haka daga ƙarshe abin rigima maganar take komawa yace na raina ƙoƙarin sa ina hangen rayuwar da wasu sukeyi; idan nayi haƙuri nima wata rana zamu taka matsayin fa nake hange hangen shi kenan se ya ɗauki fushi idan ba'a yi sa'a ba se anyi kwana biyu ina bin sa da rarrashi da ban baki kafin ya sakko muci gaba da walwala a gidan.

Ƙarfe biyar bayan nayi wankan yamma babyn ma anyi masa ina zaune ina cin gasassun yan shilan da Anty Labiba ta ajiye mun Mama ta shigo ɗakin.
"Kiyi sauri ki ƙarasa kada magriba tayi ku samu ku tafi" ta faɗa daga tsayen da take.

Kallon ta nayi da rashin fahimtar abinda maganar ta take nufi. Kamar ta fahimce ni fuska babu walwala tace
"Abban ku yace ki koma can gidan ki". Se na ture kwanon gabana na fuskance ta da kyau nace

"Me yasa Mama?"
"Saboda haka yaga dama". Ta bani amsa, take hawaye ya ɓalle mun dan dama ba nisa sukayi ba, na karanci akwai tausayi na akan fusakar ta amma ta dake tace
"Tun farko abinda na gudar miki kenan Halima amma kika kasa ganewa. Se kije kiyi ta haƙuri, ita dama rayuwa haka take kowa da kalar nasa ƙalubalen" daga haka ta fita ta barni na haɗa kai da guiwa na shiga kuka kamar wadda aka doka. Tuntuni dama dashi da iyayen sa kullum cikin yi mun shaguɓen na tafi gida na haihu sukeyi yanzu kuma se ace na koma bayan ko da na haihun ma basu zo ba alamar basu damu da ƙaruwar da muka samu ba kenan.

Kukan dana ringayi be hana Mama Fauziyya da Anty Labiba mayar dani gidan Bilal ba. A hanya suna ta hira abun su ni ko na haɗa kai da window ina share hawaye. Gaskiya ba'a kyauta mun ba, an ma nuna neman kai kawai akeyi dani shi yasa za'a tattarani kwana biyu da haihuwa ace za'a mayar dani gidan miji. Da muƙulli na sukayi amfani suka buɗe gidan. Compound ɗin kamar ya shekara babu mutum a ciki ƙura da ganyayyekin bishiya kasancewar sanyi ya fara kankama. Yanayin dana ga gidan yasa na fara shakkar anya kuwa Bilal na gari? Domin Bilal ɗin dana sani in dai ba sharafa yakeyi ba babu yanda za'a yi ya bar muhallin da yake zaune ciki a haka.

Yanayin falon ya tabbatar mun da zargina na Bilal baya nan, hatta da fasassun tangaran da taliyar daya zubar tun shekaran jiyan suna nan ba'a kwashe ba. Ɗaki Mu'azzam ya shigar mana da kayayyakin baby wanda duk a gidan mu aka siya tunda ko abun susar kunne banje dashi ba. Anty Labiba da Mama Fauziyya suka gyara gidan tas, kafin a kira Magriba har tsakar gidan an nemo almajirai sun share sun wanke. Har bayan sallar isha'i kafin sukayi mun sallama zasu tafi, na fashe da kuka ina cewa

"Yanzu tafiya zakuyi ku barni ni kaɗai?"
"To zama kike so muyi Halima? Da can dawa kike zaune ba ke da mijinki bane?" Mama Fauziyya ta faɗa. Na girgiza kai ina cigaba da kukan nace
"To ai yanzu baya nan Mama, kuma ko yana nan da da yanzu ai ba ɗaya ba ni ban ma san yanda zan kula da yaron nan ba kuka yakeyi cikin dare Anty Labiba ce take goya shi kuma idan safiya tayi ya zan masa wanka nima ya zanyi?" Na ƙarasa cikin kuka me tafe da shassheƙa. Shiru suka yi da alamu kukan nawa ya taɓa su. Mama Fauziyya ta zauna kusa dani ta jani jikin ta cikin rarrashi tace

"Mijinki bashi da kirki Halima. Ta yaya za'ayi ace ki haihu har kwana biyu amma be zo ba wani nasa be zo ba a gari ɗaya ba wai can nisan duniya ba? Kin fi kowa sanin sauƙin kai irin na mahaifin ki amma tunda har yayi fushin da yace ki dawo gidan ki tabbatas abun ya ɓata masa rai. Da kansa ya kira Bilal ba wai wani ya saka ya kira shi ba amma be amsa wayar sa ba har yanzun nan kuma be biyo sahun kiran ba, dama ai ga akan yanda kuka rabu har kika tafi gida ko? Kiyi haƙuri ki jira shi ya dawo duk yanda kuka yi ki kira waya domin mahaifin ki yace ba zaki koma ki zauna masa a gida ba har se da dalili, wato idan sakin ki yayi".

Da sauri na kalle ta jin abunda ta faɗa daga ƙarshe, wai Bilal ya sake ni. Baki na har rawa yakeyi nace
"Mama y sake ni kuma?"
"Yanzu bayan wannan kora da halin daya miki har kina tunanin cigaba da zama dashi ne Halima?" Mama Fauziyya ta faɗa kusan da mamaki, se na shiga girgiza mata kai nace
"Bafa faɗa mukayi ba Mama, kuma ni jiki na ma yana bani ba lafiya Bilal yake ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login