Showing 204001 words to 207000 words out of 257873 words

Chapter 69 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

523

mayar masa da tambaya tana wani tsare shi da ido, a ransa ya shiga karanta a'uziyya yana ayyana mutanen nata ne suka motsa kenan. Ya matsa ya shiga ware ledojin, ta kayan tea sai lemukan da har sun fara hucewa tsiren ma yayi sanyi ya buɗe mata yana cewa

"Bismillah, ba'a samu kaza bane sai wannan".

Sai da tayi dagaske kafin ta danne ashar ɗin data taho bakinta, tsire za'a kawo mata a siyan baki?

Ganin ya nufo bakinta da tsiren ya saka ta haɗiye abubuwan da suke kokawa suna ƙoƙarin fitowa ta ƙarfi ta buɗe baki ya saka mata, ganin ta karɓa ya saka ya tashi ya shiga kitchen dan ya ɗakko kofi amma bai ga irin wanda yake nema ba haka ya ɗakko wani dakw haɗe da jug na roba ya fito yana ƙaramin tsaki. Ya ringa kallonta da mamaki ganin taci rabin tsiren dukda yana sa yawa na dubu goma ne kuma yankan naman nasu nada girma.

Haka dai suka raka ya ɗan ci abinda ta rage saboda yunwar da yaji ta taso masa lokaci ɗaya, dukda haka sai daya ɗebi ruwan zafi a banɗaki dan babu butar tafasa ruwa ya haɗa tea wanda itama ta ce zata sha ya haɗa mata kafin ya tattare kayan ya adana komai a inda ya kamata dan miƙe ƙafa tayi tana shan Ac tana sauke numfashi. Sukayi sallah raka'a biyu da yana ji tana ƙunƙunin wai ita bacci takeji. Ɗaki ta wuce bayan sun idar da sallar, ya leƙa da niyyar ya mata sai da safe saboda bacci yakeji ga kansa da yake masa azabar ciwo amma ƙamshin wani turare da bai san ko na menene bane ya sake buga masa kai, ba zai ce ga sanda ya isa gareta ba daga nan kuma labari ya canza.

Dukda yanda turaren da yawan shakaryda yake masa yawan yanda ya ringa fitar dashi daga hayyacinsa amma hakan bai sa ya kasa tantance akwai matsala a tafiyar da aka fara ba dan haye shi tayi yanda kasan ita ce mijin shine matar musamman da jikinsa ya mutu sai yanda tayi da shi kawai. Bai san me ta shafa masa ba lokaci ɗaya ya ji jikinsa ya kawo ƙarfi har ya juya ta koma ƙasansa babu ɓata lokaci kuma ya nemi hanyar sa da ya ji ta kamar filin kasuwa ƙarfe ukun dare ma'ana babu wani cinkoso ko wani matsatsi ko tangarɗar da zata hanshi wucewa.

Lokaci ɗaya duk wani abu dake yawo akansa ya yaye hatta da mayen dolen da ta sakashi lokaci ɗaya ya wartsake sai dai duk yanda ya so ya saketa saboda yanda takaici da baƙin ciki suka kashe duk wani zumuɗin da yake ciki amma kuma abinda bai san ko menene bane ya riƙe shi kamar mayen ƙarfe haka kuma ba dan daɗi ko yana so ba ya ringa abinda har kuka sai da yayi na baƙin ciki gashi yana so ya daina amma kamar wanda inji yake sarrafawa ya kasa raba jikinsa da nata wanda a nata shirmen ta ɗauka na daɗi ne nan kuwa ta ware baki ta manta da ya kamata ta nuna cewar farin shiga ce ita ta shiga taya shi kukan wanda nata na gaske ne na jin daɗi.

Sai da dan kanta ta gaji lokacin Bilal ya gama shiga uku ya ma dena kukan hawaye ya koma na zuci kafin ya samu kansa dukda bai san ta yaya ta rabashi da abinda ya gagara hana kansa dainawa ba. Ya zube kan gado yana mayar da numfashi kamar wanda yayi gudun famfalaƙi haka itama Zulaihan numfashi take mayarwa murna mara misaltuwa ta cika mata zuciya domin kuwa Bilal ɗin ya mata har ya wuce yanda tayi zato, ta yi mu'amala da mazan da ba zasu irgu ba amma zata cw bata taɓa samun wanda ya mata kamar sa ba ko dan shi ɗin tana son sa ne saɓanin waɗancan da take basu kanta saboda kuɗi kawai?

Hannu ta kai da niyyar shafa ƙirjinsa ya doke hannun nata da ƙarfi kafin ya tashi daƙyar yana tafiya a duƙe ya fice daga ɗakin, ta bishi da kallo sai kuma ta saki murmushi mai kama da dariya tana godewa Suby da taimakon da tayi mata. Ta tashi tana jin jikinta ko ina yana amsawa ta kunna filila, kamar mahaukaciya ta sheƙe da dariya tana kallon bedsheet ɗin da tana sane ta canza asalin wanda aka shimfiɗa daya kasance mai duhu ta saka fari gashi kuwa yayi kaca kaca da fake hymen (jinin budurcin ƙarya) da Subyn ta siyo mata.

Banɗaki ta shiga ta ɗan ɗauraye jikinta a maimakon tayi wanka gaba ɗaya ta dawo ta kwanta akan gadon a yanda yake a ranta tana raya ai ba jinin gaske bane bata ko ƙara minti biyar ba kuma bacci mai nauyi ya kasheta.

Bilal kuwa ɗaya ɗakin ya shiga yana tafiya a sunkuye dan ji yake kamar wanda akawa operation, marar sa ta ƙulle, duk wannan bala'in daya gamu dashi kusan awa biyu yana abu ɗaya amma bai fitarta komai ba, ga gajiya, da baƙin cikin abinda ya tarar ga kuma wani kata'in ya sako shi a gaba.

Haka yayi wanka ya ringa zarya tsakanin falo da ɗakin kamar mai naƙuda kafin ya samu komai ya lafa masa ya nemi kan kujera ya kwanta yana mayar da numfashi haɗi da tunanin abinda ya faru. Duk abinda zai haɗa dan kareta hakan ya gaza karɓuwa a zuciyarsa. Ko dai mahaukaci ne shi kuma ko bai taɓa aure ba ya san ba haka mace budurwa take ba kai ko wacce ba budurwar ba matarsa mai haihuwa biyu ma bata ko kai rabin buɗewar haka ba.

Bai san ya akayi ba kuka ya ƙwace masa, Zulaiha ta cuce shi kuma ta ha'ince shi. Yarinyar da yakeyiwa kallon salaha bata san komai ba bagidajiya ita ce ta juye ta zame masa wani abu na daban da bai ma san me ya kamata ya kirata da shi ba. Maganganun Kawun su ya faɗo masa sanda yake cewa sun san komai dai ko? Ya tuna Faruk ya ce ya sani, kenan ya san su ɗin ba yayan arziƙi bane amma a hakan yaji ya gani ya auri Nuratun ko dai shima irin sa ne an ninke shi a baibai sai yau zai gane ainihin abinda Kawun yake magana a kai.

Zuciyarsa ce ta tambaye shi,
"Yanzun kai da ka sani ɗin mai zakayi akai?" Sai kuma ya gagara bawa kansa amsa kawai ya sake fashewa da kuka dan shi kaɗai ne hanyar da zai rage raɗaɗi da nauyin da zuciyarsa take masa a yanzu.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 52*

Kwana yayi yana tunanin yanda akayi Zulaiha ta yaudareshi, tsayin shekarun da suke tare ace bai taɓa tunani ko hasashen tana da wani hali na daban bayan wanda ya santa da shi ba. Yaran da talauci da matsin rayuwar da suka tashi a ciki ya saka basuda kataɓus ko a cikin unguwa ɗaiɗaikun mutane ne suke mu'amala da su balle makaranta.

Shigar sa cikin rayuwarsu ne ya kawo musu ɗauki har suka samu yanci dukda hakan kuma suna gabatar da rayuwarsu ne cikin takatsantsan dan ya sha tambayarta mai yasa bai taɓa ganinta da wata da sunan ƙawarta ba sai ta ce Ummansu ta hana wai bata so suyi ƙawaye kada zuciyarsu ta ringa ƙawata musu abubuwan da basu da halin mallaka dan haka bata da wata ƙawa daga unguwa har makaranta kuwa sai dai yayan yan uwa da ya kan gansu jefi jefi.

A saninsa kuma babu in da suke zuwa daga makarantar boko sai Islamiyya kuma suk inda zasu je ɗin cikin shigar Hijabi harda safa da Niƙab babu wata suffa ta a tattare dasu da zata taɓa bayar da hanyar da za'a zargesu da wani abu mara kyau. Ashe dai su ɗin Abin tsoro ne wai KURA A RUMBU.

Kalaman Kawun su zuwan da yayi suka ringa masa yawo a kai kamar tilawa ya ringa haɗasu da labarukan da take bashi akan sharrin da Kawun nasu yake musu dalilin karatun jami'ar da shi ya ɗauki nauyinta amma Kawun sai ya ce yawon lalatarta kawai takeyi ba wani karatu ba da yanda ta ce mutanen unguwa suna surutu akan alaƙarsu ana cewa iskanci sukeyi shiyasa yake wahalta mata ashe duk raina masa wayau kawai ta ringayi tsayin lokaci Allah kaɗai ya san irin rayuwar da take yi a bayan idonsa.

Haka ya raba dare har asuba yana tunani, sai da aka kira sallah kafin ya tashi daƙyar saboda ciwon kai ga cikinsa daya ɗaure kamar an saka masa dutse. Haka ya lallaɓa yayi alwala, dukda haushinta da yake ji haka nan zuciyarsa ta tilasta masa zuwa tashinta. Munsharinta yayi masa maraba, sabon baƙin ciki ya turnuƙeshi. Fitilun ɗakin ya kunna gaba ɗaya haske ya gauraye ko ina a zatonsa irin Halima ce da duk baccin da takeyi aka kunna fitila sai ta farka amma ina Zulaihan kamar matacciya munshari kawai take ja.

Ya matsa yana ƙarewa gadon da ya ɓaci da jini sai kace wanda aka yanka kaza a kai, mamaki ya kamshi, daga ina aka samu jinin b dai daga jikinta ba? Domin shi dai ya san free get ya wuce sai dai idan kuma shine ya zubar da jinin ba zaiyi mamaki ba. Sai lokacin ya tuna da zaiyi wanka ma yaga jinin a jikinsa amma da yake lokacin ba'a nutse yake ba bai mayar da hankali ba. A saitin kanta ya tsaya yana matse fuska, ji yake kamar ya sharara mata mari a baƙar fuskarta da yaga tayi masa muni irin wanda bai taɓa ganinta da shi ba.

Ya ringa kokawa da zuciyarsa dake ingizashi akan wai ya sharara mata mari ta tashi tayi masa bayanin abinda yake ci masa zuciya amma ya kasa ƙarshe ya shiga kiran sunanta ya ringa maimaitawa amma ko gezau baiga alamar zata amsa ba sai ya shiga dukan katakon gadon nan ma ya fi minti biyar kafin tayi juyi cikin muryar bacci take cewa
"wai meye haka dan Allah ka rabu da ni bacci nakeji"

"Ki tashi, kalli fa cikin ƙazantar da kike kwance" ya bata amsa yana sake kallon gadon, tayi tsaki kawai tana sake gyara kwanciya, ya kai mata duka mai zafi ta zabura ta miƙe zaune kamar zata mayar da martanin dukan amma ta tsaya tana hararasa da manyan idanuwanta da yaji shakkar kallonsu ta kamashi. Ganin ta tashi zaune ya saka ya juya yana ce mata
"Ki tashi kiyi sallah" ya fice daga ɗakin haushin kansa yana kama shi.

Tsaki tayi ta koma baccinta ba tareda tayi abinda ya ce ɗin ba. Bilal kuwa a kan dardumar daya yi sallah bacci ya kwashe shi dama ga gajiya bai farka ba sai ƙarfe tara da mintuna sakamakon bugun ƙofar da ya ringa jiyowa kamar za'a karyata.

Ya tashi zaune daƙyar yana dafe kansa da a maimakon baccin da yayi ya saka ciwon ya ragu ƙaruwa ma yayi, dai dai lokacin Zulaiha kuma ta fito daga ɗakin ɗaure da towel wanda da kaɗan ya wuce mazaunanta jikinta da kumfa alamar wanka takeyi bugun ya fito da ita, suna haɗa ido ta watsa masa wani shegen kallo kamar wacce taga kashi tayi ƙofa tana sakin ƙaramin tsaki. Ya kira sunanta da dasasshiyar murya ta tsaya ba tareda ta waiga ta kalle shi ba, a hankali ya miƙe yana dafa kansa sai da ya isa kusa da ita kafin ya ce

"A haka zaki fita saboda bakida hankali?"
"Aa daga turu aka kwantoni ƙarewar hauka, da kana ji ashe tsabar wulaƙanci baka tashi ka buɗe musu ba". Tsayawa yayi yana kallonta da mamaki ita kuwa ko a jikinta ta juya ɗaki tana kaɗa masa mazaune. Ya haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙogaro kafin ya fita jin masu bugun basu da niyyar dainawa.

Ƙawayenta na jiya ne su huɗu Suby kaɗai ya gane a cikinsu, ya matsa suka shigo fuska a haɗe babu ko wacce ta gaida shi suka wuce ciki da kayan da suka taho dasu kwalin Tv sai ƙananan kwalaye da bai san menene a ciki ba haka ya rakasu da ido har suka shige falon yana jiyo yanda suka fasa ihu da alama su da Zulaihan ne abin mamaki sai kawai ya mayar da ƙofar ya rufe ya wuce ɗakinsa yana sauke ajiyar zuciya kamar wani maraya.

Kwanciya yayi ya sake faɗawa tunani, babban abinda yake damunsa, har ransa haushin Zulaiha yakeji kamar ya kamata ua rufeta da duka har sai yaji yanda akayi tayi masa wannan cin amanar amma kuma a hakan bai ji ko ɗigo ɗaya na daga son da yake mata ya ragu a zuciyarsa ba. Tun daren jiya yake ayyana gari na wayewa zai ce ta tattara ta wuce gidansu ba zai iya zama da ita ba amma kuma zuciyarsa ta kasa bashi haɗin kai akan hakan.

Ya ɗauki wayarsa daya bari a ɗakin tun daren jiyan ya kunna amma kuma ya rasa wa zai kira ya raba baƙin ciki da shi ko zai samu sauƙin abinda yakeji a ransa. Dariya za'a masa ma, ba yan uwa ba ba abokai ba ya tabbatar muddin wani ya san halin da ya tsinci kansa sai ya shiga uku a gari.

Haka ya ringa juyi yana jiyo ihu da hargowar Zulaiha da ƙawayenta suna da sabgogi kamar ma tsakar gidan suka fito, ƙamshin ƙwai daya ringa jiyowa ya tayar masa da yunwar daya kwana da ita. Tun yana jira yaga ta kawo masa ko tazo ta kirashi ya karya har agogo ya buga sha ɗaya ba Zulaiha babu breakfast. A waya ya kirata murya kamar wacce akawa dole ta amsa da
"Menene?" Cikin tasa muryar da yunwa da fara ɗaukewa ya ce
"Ina breakfast ɗina?" Tayi shiru kafin kuma ta kashe wayar ya tashi daƙyar ya shiga banɗaki yayi brush ya fito yana jiranta.

Zulaiha kuwa da Asuba bayan daya tasheta baccinta ta koma bata kuma farka ba sai ƙarfe tara shima saboda kiranta da Suby tayi ta sanar mata gasu nan a hanya sai lokacin ta tashi tana jinta sakayau saboda kwanciya da tayi akan katifa mai kyau ba irin siɗaɗɗiyar tasu ta gida ba. Rai fes take jinta burinta ya cika ta mallaki sahibul karɓinta Bilal ita da shi kuma mutu ka raba.

Tana son Bilal kusan akansa ta fara sanin menene so dukda kafin shi tayi soyayyar ƙuruciya da wani yaro Nura a tsohuwar unguwar su. Yaron babansa nada kuɗi da wannan kuma ya ringa hillatarta da yake ita ɗin Allah yayita da ƙwadayi da son cin daɗi sai dai kuma sun tashi a gidan da ci uku ma wahala yake musu a lokuta da yawa. Da wannan yaron mai suna Nura yayi amfani ya ringa siya mata kayan ƙwalama da sunan yana sonta, lokacin data shiga JS1 ya ce zata ringa zuwa gidansu ta haɗu da ƙannensa a ringa yi musu extra lesson tunda ya fahimci tana da ƙoƙari da kuma son karatu.

Ummansu wacce ita ce sila ko ace musabbabin lalacewarta ta goyawa abun baya dukda mahaifinsu ya nuna ƙin amincewa amma tayi masa tatas kamar yanda ta saba duk sanda magana ta tashi akan yaran sai ta ce yanda ya barta dasu baya tsinana musu komai karya kuskura yace zai ringa tsoma musu baki a sabgoginsu. Shikenan ta fara zuwa extra lesson wanda ba karatun sukeyi ba ɗakinsa yake kaita tun bata son abinda yakeyi mata har ta saba ya zama ko bai kirata ba ko ba ranar lesson ɗin ba zatayi ƙaryar zuwa wani guri ta tafi gurin Nura, tun a lokacin kuma mutane da yawa sun sha kaiwa Ummansu maganar saboda ba a iya gidansu ba har shagunan abokansa suke zuwa amma duk wanda ya faɗa mata zagi da cin mutunchi ne zai raba su tace an yiwa yarta ƙazafi.

A haka suka kwashe kusan shekaru biyu da Nura kafin ya tafi ƙasar waje karatu tun daga nan kuma har kawo yau bata sake ko jin labarinsa ba dan dama ba yan Kano bane daga baya suka bar can unguwar tun ma kafin su Zulaihan su bari. Rabuwarsu da Nura ta saka ta rasa abubuwa da yawa waɗanda yakeyi mata, babu tsoron Allah Ummansu ta ce ai ba zasu zauna haka ba, tunda dai ko da batada fuskar da zata burge maza dukda ƙananan shekarunta da yake tana da garin jiki ai ba zata gagara nemo musu abinda zasu ringa kaiwa bakin salati ba.

Daga nan ta fara zuwa gurin masu shaguna, wasu su biye mata su bata kuɗi ko abin amfani masu tsoron Allah su kai ƙara gurin mahaifinsu wanda yake tamkar hoto dan ko ya faɗa ba ji zatayi ba tunda uwarta ta tsaya mata. A haka Bilal ya shiga rayuwarsu zuwansa kuma ya kawo sauƙi cikin al'amuran domin kan jiki kan karɓi yake tallafa musu kuma shi yayi fafutuka ya samawa Babansu motar haya da yake direba ne yake hawa abinda yake samowa da wanda Bilal ɗin yake basu ya taimaka ƙwarai har Zulaihan ta hau saiti ta mayar da hankali kan karatu.

Sai dai kuma daga sanda ta shiga shekarun budurci na sosai a lokacin mahaifin su ya samu hatsari ya gamu da jinyar da bai warke ba har ya koma ga mahaliccinsa sai ya zamana Bilal ne kaɗai madogararsu dan haka ta sake komawa ruwa har tayi nasarar jan ƙanwarta Nuratu da huɗubar Ummansu wacce kullum take mata tilawar ba zai yuwu ta zauna yar uwarta ta nemo a ci da ita ba tunda itama tana da abin bayarwa idan ta zauna duk idan aurenta ya tashi kada tayi kuka da kowa ta kuka da kanta.

Tafiyar kuma ta canza salo sanda ta shiga Jami'a ta haɗu da gogaggun da suka fita ido a harkar, haka ta ringa zuba sharafinta cikin takatsantsan kuma Allah ya ara mata lokaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login