Showing 39001 words to 42000 words out of 257873 words
ciki a son kar ayi miki dariya ba. Idan kika ji ba zaki iya ba ki tafi tun lokaci be ƙure miki ba" daga haka ya fice ya barni tsaye a gurin ina kuka mara sauti. Se da gabana ya faɗi da naga kiran Mama bayan tafiyar Mu'azzam babu jimawa. Tunanin ko ya faɗa mata wani abu na shiga yi, to amma me ze ce mata?
Se da ta mun kira biyu kafin na amsa a sanyaye muka gaisa ta tambaye ni jiki na ce da sauƙi.
"Karki kuskura ki tasa kayan zaƙi kice zaki ringa sha, Mu'azzam ya gaya mun kin ce ya siyo miki lemo to ki tattara su ki aje in ba haka ba wuya zaki kirawa kanki tun yanzu" ta faɗa. Se naji dariya ta kamani, wato in da lissafin ta ya tafi kenan ciki ne dani amma dan a rabu lafiya se kawai na bita da toh. Bamu jima ba mukayi sallama tana sake jaddadamun na kiyayi kayan zaƙi ni dai da toh kawai na ringa bin ta. Maganar da mukayi da Mama tasa na danu sauƙi cikin zuciyata se kawai nayi shafa'i da wutri nayi kwanciya ta.
Ban sanda Bilal ya dawo gidan ba na dai farka cikin dare na ganshi a baya na. Da safe tamkar bamu samu saɓani jiya ba lafiya lau ya tashi yana jana kamar yanda muka saba ni ce ma nake ɗararewa. Ban yi gigin taɓa masa dankali ba na ɗumama sauran abincin da be ci ba jiya muka karya dashi, da ze fita yace mun na shirya idan ya dawo zamu fita wannan tasa na ware nima. Gidajen yayyen sa mata muka zagaya waɗan da suke ciki ɗaya da wanda suka haɗa uba. Har unguwar su Anty Labiba muka je amma ƙememe yaƙi yarda mu shiga wai takanas zamu shiryo muje ba ratse ba. Dake dai mun shirya ya sakko daga fushin ban matsala ba kar ya sake birkice mun tun da dai yayi alƙawarin zamu je da weekend na wuni shikenan.
Haka rayuwa taci gaba da miƙawa a lissafi aure na da Bilal yana cikin wata na biyar kenan a kuma cikin wannan lokacin nayi karatu game da zamantakewa ta dashi ta rannoni biyu. A bangare ɗaya na tabbatar da cewa Bilal yana so na domin irin kulawa da tattalin da yake bani na san cewa ba duka haka maza suke ba. Yana da sauƙin kai sosai a halayya sannan ya ɗauke ni matsayin ƙawa be hakan ne yake ƙarawa zamanmu armashi.
Idan har yana gida tare muke duka ayyukan gida. Kasancewar sa me tsafta sam baya shiri da ƙazanta be kuma so jikin sa ba, da sassafe kafin ya fita aiki ze share mun tsakar gida ya wanke haka da falo na nasa ze share yayi mopping ni kuma naji da gyaran ɗaku na da girki idan ya wuni a gida kuwa hatta sharar ɗakunan shi zeyi ya gyara ko ina tsaf ya kunna turare dan idan yayi gyaran nafi ganin gurin yayi yanda nake so saboda babu algus, kullum ze yi shara tofa se ya ɗaga kujeru ya share ƙasan su haka duk wani abu dake ajiye se ya ɗaga ya goge har mamaki nake yi yanda sam abin be dame shi ba kamar ma hakan na samar masa da jin daɗi dan cike da walwala yake ayyukansa wankin toilet dama ko na wanke na ɗakin sa cewa ya keyi be fita ba ze zauna ya sake wankewa tas yanda yake so haka wankin kaya har undies yake wanke mun wani lokacin muyi tare ina masa ɗauraya wani lokacin yace ban iya ba na barshi se dai na zauna daga gefe ina masa hira waɗannan halayyar tasa take sake ƙara mun son sa da ƙaunar sa a zuciya nake kuma ganin ɗaya ɓangaren na halayensa da bana jin daɗin su a matsayin ajizanci irin na ɗan adam domin kuwa babu wani mutum da yake cikakke dole ka kasance da halayen abin so da kuma wanda ba kowa yake so ba.
Daga cikin abin da ke yawan janyo saɓani tsakani na Bilal shine ƙorafi. Ko dan yana yawan zama a kusa da ni ne tun da idan ya fita aiki ya dawo idan ba sallah ba ba in da yake zuwa in kuma ranakun hutu ne yana gida, ba ƙaramin abu bane yake fitar dashi ko ya fita ma baya jimawa ze dawo dan haka ko yaushe muna tare dan haka duk abinda zanyi akan idon sa ne kuskure kaɗan kuma zan yi yayi ta mita yana ƙorafi kenan. Abin da be kai ya kawo ba se ya zama na magana a gurin sa.
Sannan na lura Bilal yana da son ya zama duk wani abu da zanyi ya zama da sanin sa. Sannan mutum ne me tattali da son abin sa. Har idan ina so na ga fushin sa to fa na taɓa abun sa ba tare da izinin sa ba tun da kuma na fahimci hakan nake kiyayewa shikenan nayi maganin fitinarsa. A watanni biyar ɗin nan bani da wata matsala idan aka cire rashin fita da Bilal baya bari na a sanda naso se kuma rashin walwala ta kuɗi a hannu na. Ina samun kuɗi dan kusan duk sanda zanje gida Abba se ya bani ko ya tura mun a account a cewar sa kar na ringa damun miji na da bani bani, Saboda gudun fitinar Bilal ko ƙorafi akan kayan sa bana saurar komai daga gare shi duk abin da nake so cikin kuɗi na nakeyi har shima nayi masa na kuma yiwa yan uwansa.
Abin sa na sake lura dashi yana jin daɗin shi na hidimta masa amma baya so nayi wa wani dan har idan wani ya zo mana nayi masa kyauta a gabansa ko beyi magana ba a fuskar sa ina karantar rashin jin daɗi abun na damuna da na gaji nayi masa magana akan hakan se yace wai abin da nakeyi ze janyo masa raini a gurin masu zuwa gidan mu shi megida ya kamata ace idan ma kyautar ce yayi ba wai ni ba, saboda a zauna lafiya se ya zama idan yana nan mukayi baƙi idan kuɗi ne zan bashi nace ya basu idan kuma wani abun amfani ne zance gashi in ji shi shikenan na samu lafiya da wannan ma.
Tuni result ɗin mu ya fito har wasu daga cikin mu sunyi nisa a service, labarin da naji akan an yi ƙarin kuɗin da ake biyan yan bautar ƙasa ya sa na himmatu nima. Hansa'u na tambaya kuɗin da ake kashewa na clearance kafin a karɓi result dan tuni ta karɓi nata harta fara service a Abuja in da tayi aure, gaba ɗaya kuɗin ya kama dubu goma sha biyu da ɗari biyar. Se da na lissafa abin da nake dashi kwata kwata dubu biyar da dari bakwai yayi mun saura cikin dubu goman da Abba ya bani shekaran jiya da mukaje. A ciki na bawa Bilal yayo mana refilling gas ina tsaka da girki jiya ya ƙare, nasan ba'ayi albashi ba da daddare kuma naji kwaɗayin tsire nan ma na bashi ya siyo mana na dubu ɗaya na dafa mana indomie muka ci.
Mayar da kuɗin nayi ina jiran ya dawo naji yanda zamuyi tun da yɗauka wa gobe nasan zasu iya samun albashi. Se da muka ci abinci kafin na sako masa zancen an yi ƙarin allawee.
"Na zata ma na gaya miki, se naji ina ma yanzu ne zanyi service nima" ya faɗa se na yi dariya nace
"Haba kun riga kun ci rabon ku yanzu mune zamu shana. Ina ganin ranar monday se na shiga makaranta Hansa'u tace zan iya yin komai a rana ɗaya kuma nan da wani satin za'a buɗe registration na Batch B kaga dai dai kenan".
Na ɗauka maganar da nayi masa zata sa ya fahimci abin da nake nufi duk da be tambaye ni nawa ne abin da za'a buƙata ba se na barshi akan se ranar tayi tukunna. Cikin daren salaryn sa ya shigo lokacin wayar tana kusa da ni shi kuma ya shiga kitchen ɗauko abu daya fito kuma ya ɗauki wayar be ce mun komai ba nima ban damu ba. Monday ta kama hutun ranar ma'aikata dan haka babu aiki se washe gari talata a daren na sake tuna masa da washe gari fa zan je makaranta yace Allah ya nuna mana. Washe garin da wuri na shirya, baze fita ba kamar yanda yace suna wani field work ne se ƙarfe sha biyu ze fita zuwa in da yake yin research. Se da nayi masa girkin rana saboda daga makaranta gida nake so na wuce kafin na ƙarasa shiryawa. Ina saka Hijabi na ya shigo ɗakin, ya kalle ni ba yabo ba fallasa nima ina kallon sa nace
"Na gama" yau ce rana ta farko da zan fara fita ni kaɗai a tsayin auren mu. Duk in da zanje tare muke fita ko muje tare ko kuma mu rabu a hanya amma ban taɓa kulle gida na fita ni kaɗai ba.
"Amma fa kar kiyi dare, ina tunanin Hafiz abokin aiki na zasu zo da matar sa yau ki dawo da wuri saboda ki tanadi abin da zaki tarbe su dashi" ya faɗa. Na ɗaura niƙab a fuskata ina cewa
"In sha Allah bazan daɗe ba". Gefen gado ya zauna ni kuma na gyara tsayuwa jikin chest of drawers ina jiran ya sallemi ni ganin yana ƙoƙarin kwanciya yasa na ce masa
"Na gama fa"
"Na miki a dawo lafiya ai, ko na zo na rakaki titi ne ba sabanba zaki fita ke kaɗai yau?" Ya faɗa yana murmushi. Se na ɗage niƙab ɗin ina kallon sa nace
"Eh da ka rakani ɗin ma zanji daɗi amma bana so na wahalar da kai ga rana ta fara tsayawa sallame ni kawai na tafi".
Aljihun rigar sa ya shiga lalubawa ya zaro kuɗaɗe da nake zaton zasu iya kaiwa 20k ko su fi a ciki ya zari 1k ya miƙa mun yana cewa
"Zata ishe ki ai"
"Nagode" na faɗa ina karɓa. Jimm nayi a tsaye ganin ya gyara kwanciya har da jan bargo zuwa cikin sa yasa na ɗauki jakata kawai na fita. Na fi minti goma zaune a falo ina tunanin in da zan lalubo kuɗin na rasa. Ina jin kunyar na tambayi Abba duk da shi yace duk abin da nake so in gaya masa amma kuma ai nima ina da hankali na san dai dai da aka sin haka. Ganin ina ɓata lokaci yasa kawai na tafi. Gidan mu na fara zuwa, ganin motar Anty Labiba a waje yasa naji kamar na juya amma na daure na shiga.
Su uku na tarar, Mama, Anty Labiba se Anty Fauziyyah.
"Ta Bilal ki ce shigar ninja kuma kika koma" Anty Labiba ta faɗa, nayi murmushi kawai na samu guri na zauna na shiga gaishe su. Anty Fauziyyah tace
"Tun da aka kaiki bamu dawo ba kema baki leƙo mu ba. Muna ta saka rana zuwan be yuwu ba kar ayi mana kiran dole ko bamu shirya ba".
Ni dai kaina yana ƙasa se Anty Labiba ce tace
"Ai bake kaɗai ba jiya Mami ma take ce mun yaushe zamu je nace idan ta shirya tayi tafiyarta kawai to se ku haɗa hanya". Jin zata fara abin da tafi iyawa yasa na tashi na shige ɗakin Mama. Ganin wayarta na kusa da ita yasa na tura mata text, har na ƙosa da jira sannan ta shigo ɗakin tana cewa
"Wane salon iskanci ne kuma haka? Su Labiban ne suka zama baƙin ki yau da zaki wani mun text kina son magana dani?"
"Kin san halin ta Mama yanzu se ta taso da wata maganar ta daban ni kuma sauri nake yi" na faɗa ina marairaicewa. Faɗa mata abinda ya kawo ni nayi, ta riƙe haɓa tana kallona kafin ta juya ta fita ba tare da tace mun komai ba ina kiranta amma bata tsaya. Yanda Anty Labiba ta ƙwala mun kira yasa na gane handsfree Mama ta mun, kamar zan fasa kuka na fita. Allah ya cece ni kafin ta fara mun tijara Anty Fauziyyah ta dakatar da ita ta buɗe jakarta ta ciro rafar yan ɗari biyu sababbi ta miƙa mun tana cewa
"Yi tafiyar ki kin ji".
Ban san ya suka ƙare ba ni dai tun da buƙata ta biya nayi tafiya ta. Ƙarfe uku na gama abin da ya kaini, a hanyar komawa gida na siyi doya dan ina marmarinta tun kusan wata biyu Kenan kuma be siyo ba dana masa magana yace wai taja baya tsada take yi ni kuma yanzu ban ma ga tsadar tata ba. Almajirin Maman Yusuf na bawa ya siyo mun hanta da albasa, se da nayi sallar magriba kafin na ɗora doyar dana rigada na fere ta tafasa na soya da ƙwai a gefe kuma nayi sauce ɗin hanta taji albasa sosai da kayan ƙamshi. Ina jere abincin Bilal ya shigo, sauri sauri ya wuce wanka yace mun sun yi waya da Abokin nasa har sun taho ma suna hanya. Sabon transfer ne aka maido shi Kano daga Enugu, naga jinin su ya haɗu da Bilal sosai dan rana ku ɗai ɗai ne baze yi zancen Hafiz ba.
Se da na buɗe fridge zan fitar da lemo da ruwan da zan basu naga ashe ruwan gora ya ƙare dama carton biyu ne na siyo dan tun da na garata ya ƙare daga lemon har ruwan se dai idan naje gida na ɗauko ko na siya da kuɗi na pure water ya dawo siya lemo dai ze siyo pieces biyu uku idan yayi marmari in na masa maganar a siyo koda zakuyi baƙin kunya se ganin sa nayi da kwalin Tiara da poster clark, se kawai na saka aka kawo mun zoɓo baki na alaikum nake yi da yawa ina ajiyewa shima shi yake shanye wa.Jug na ɗauraye na zuba pure water kawai.
Daga Hafiz ɗin har matar sa kana ganin su kasan yan gayu ne da suka jiƙu da kuɗi. Matar me suna Suhaila zata girme mun sosai daƙyar idan bata haura shekara talatin ba se dai dake irin jiki na ne da ita ga kuma gayu in ka kalle ta se ka ɗauka bata fi sa'a ta ba. Tana da fara'a sosai da ganin ta zata yi son mutane haka shima mijin. Tare muka zauna gaba ɗaya a dining muka ci abinci, ina ta satar kallonta ina sabon course ɗin kukayda miji. Yanda kasan ƙaramin yaro haka take kula da duk laumar mijin nata har zuwa ya tauna abincin ya haɗiye, se da yayi rabin nasa sannan ta mayar da hankali ta fara cin nata abincin a raina ina tunanin ni gwana ce a tattalin miji ashe babu in da na kai gwanaye na gaba na dole masa naga shima yana nan nan da ita kamar ya goya ta dan da suka shigo jakarta ma a hannun sa take motsi kaɗan kuma za'a ce mata "are you ok?"
A falo muka bar mazan na jata ɗaki na, yanda muka ringa hira se ka zata mun shekara da sanin juna tana ta bani labarin Enugu, ita da Mijin nata duk yan Kaduna ne watan su uku kenan da aure yanzu. Har gurin goma suna gidan. Muka yo exchanging number ina ta jin daɗi dan in ka cire matar Nasir da dama tun kafin aure na da Bilal mun san juna ita ce matar abokin sa da zamu fara zumunchi yanzu. Da zasu tafi na rasa me zan bata, ina da ingantattun kayan gyara da Anty Labiba take aiko mun da su duk da bata son Bilal amma bata wasa da gyara masa ni, nayi tunanin ko na ɗibar wa Suhaila se kuma na fasa dan ban san ko tana amfani dasu ba tun da ina yawan jin yan gayu na condemning magungunan mata duk da dai nawa guarantee ne da aka sararrafa da ilimi se kawai na ɗibar mata turarukan wutar da take ta yabon ƙamshin su. Sababbi ne na siye su gurin wata ƙawar Maman Salin maƙwafciya ta. Turarukan badai ƙamshi da kama guri ba, na ɗakin da take ta zuzutun ƙamshin sa ya mata daɗi bama kunnawa nayi ba a jiye kawai suke amma idan ka shiga se ka zata a lokacin ake ƙonawa. (08033950747 in dai turaren wuta kike nema me daɗin ƙamshi da kama waje karki wuce BISHAQLINKS).
Dubu ashirin na yan ɗari biyar sababbi Hafiz ɗin ya ajiye mun, nayi nayi ya ɗauke kuɗin sa har matar sa na bawa amma tace aa kyauta ya mun tukuicin girki idan ban karɓa ai ba zasu ji daɗi ba se dai idan rainawa nayi hakan ya sa nayi masa godiya ina ganin Bilal nata kallo na na aje kuɗin kan center table muka raka su muna dawowa ya kwashe su yana cewa
"Tun da bakya so ni bari na ɗauka".
"Kai kuma baka san fulako ba so kake kawai an bani kuɗi nayi zuruf na amshe ai se ka mun faɗa ma" na faɗa ina dariya. Na ɗauka wasa yake da ya ɗauki kuɗin ze ajiye mun daga baya shiyasa ban damu ba. Sati biyu da suka biyo baya aka fara registration na NYSC.
Se da naje Cafe suka ce mun se na kawo certificate of marriage da appointment letter ko ID card na miji na da kuma shaidar canjin suna in dai ina so a bar ni a garin da nake kuma kar nayi zaman camp. Tilas na haƙura da yi a ranar na koma gida, Bilal baya nan sun tafi Katsina gaisuwa acan zasu kwana dan haka na kira shi na gaya masa yace na bari idan ya dawo se muyi magana. Washe gari suka dawo, be tada zancen ba se ni ce na masa magana ya ce mun ze tambayi in da akeyin certificate of marriage ɗin da change of name. Tun ina sauraron naji ya ce an yi ko ga yanda ake ciki har aka kwana uku shiru be ce mun komai ba, da na sake masa magana ma da ɓacin rai yace mun ai yana sane shima jira yake yi wanda ya bawa yayi ya ce masa an gama tun da dai ba da kansa ze yi mun ba ai dole na jira. Ganin