Showing 126001 words to 129000 words out of 257873 words
Bilal ya tafi? Na kai hannu na share laimar da naji akan fuskata wadda ban tantance hawaye bane ko zufa kafin na shiga tare abin hawa, gidanmu na wuce, ban ko karɓi canji ba bayan na sauka na shige gidan a bakin ƙofa na zauna kamar wata zararriya na fasa kukan da ya saka Mama ta fito daga falo kamar zata hantsila da Sharifa a hannunta ta shiga tambayata mai ya faru?
"Mutuwa Hajjan tayi?" Ta faɗa tana kallona sai na girgiza kai ina turza ƙafa kamar ƙaramar yarinya na sake gyara zama ina cigaba da kukan. Sai ta buga mun tsawa tace
"Bana son iskanci Halima haka nan zakizo ki faɗar mun da gaba na tambaye ki menene kuma kinƙi faɗa to tashi ki fita tun ban rufeki da duka ba". Ganin ta ajiye Sharifa na san zata iya dukan nawa kamar yanda ta faɗa hakan yasa na miƙe na shige falon da sauri ina cigaba da kukan. Bata sake bi ta kaina ba, sai da nayi mai isata kafin na kama hanyar gida ba tareda nayiwa Mama sallama ko na ɗauki su Sharifa ba na tafi.
Ina ƙoƙarin buɗe gida naji muryar Maman Yusuf tana kirana, na waiga ganin ta nufoni yasa na tura ƙofar na shiga itama ta biyo bayana.
"Kin dawo kenan" ta faɗa tana kallona ba tareda mun haɗa ido ba dan bana son ta fara tuhumata mai ya sameni na bata amsa da "eh na dawo".
"Ai har zan shigo ɗazun sai kuma naga kina da baƙi sai kawai na wuce dama can gidan Hajiya Zainab zan ce miki ko zamu leƙa ta gamu da tsautsayi ta karye a hannu" ta sake faɗa, sai nayi jimm dalilin cewar da tayi wai ɗazu taga nayi baƙi, su wa ta gani ko in ce suwaye suka zo gidan tunda no dai nasan kafin na fita babu wanda yazo mun amma saboda bana son dogon surutu sai kawai nace mata
"Allah sarki Allah ya bata lafiya nima surukata ce bata da lafiya tana Aminu Kano a kwance". Jajantawa tayi haɗi da yiwa Hajjan fatan samun sauƙi kafin tace zata yiwa su Amina magana in zasu samu dama ko zuwa gobe su leƙa su dubata. A raina Allah Allah nake ta wuce shiyasa ma na tsaya ban bari mun shiga falo ba, ganin bani da niyyar bata gurin zama ya saka tayi mun sallama akan in zasu samu zuwa dubiyar gobe zata kirani nace mata toh.
Na ringa kallon tarkacen dana tarar cikin falona, daga kan kofunan da aka sha lemo da robobi har zuwa disposable packs wanda ke ɗauke da sauran abinci ga kaza da aka yiwa cin wulaƙanci duk anyi mun kaca kaca da gurin dana gyara tsaf na saka turare kafin na fita daga gidan. Ko ba'a faɗa mun ba nasan Bilal ne, wani abu ya taso daga ƙasan zuciyata ya tokare mun maƙogaro. Kenan nan ya kawo su ya buɗe musu ɗakina suka shiga ba tareda izinina ba? A hankali na ringa takawa saboda yanda nakejin tamkar zan faɗi saboda ƙuncin daya mamayemun zuciya. Ɗaki na wuce na samu gefen gado ma zauna lokaci ɗaya hawaye masu tsananin zafi suka ɓalle mun. Bansan adadin lokacin dana ɗauka zaune ba saida na jiyo ana kiran sallar magriba lokacin kuma naji ana bugun ƙofa kamar za'a ɓalla ta.
Tun daga ƙofar falo na fara jiyo ihun kukan Sharifa, na ƙarasa da sauri na buɗe naci karo da Mu'azzam fuskar nan kamar zeyi aman wuta yana ganin na buɗe ya direta a ƙasa ya juya ba tareda ya ce mun komai ba haka na jasu muka shige cikin gidan Al'amin na gaya mun sun daɗe a tsaye suna ta buga ƙofa ba'a buɗe ba.
"Mami me akayi miki kike kuka ko baki da lafiya?" Ya faɗa yana kallona dan guri na sake nema na zauna ina shayar da Sharifan ina hawaye. Maganar sa ta saka na shiga goge fuskata can ƙasan zuciyata wani ɓangare yana tunasar dani cewa
"Kuka ba zai miki maganin damuwarki ba Halima".
Sai ƙarfe sha ɗaya da mintuna Bilal ya dawo gidan ina zaune a falon da ban ɗaga ko tsinke daga abinda na dawo na tarar ba naji motsin buɗe ƙofa, ban motsa ba saida naji an cire kwaɗon dake jikin get ana ƙoƙarin zugeshi kafin na miƙe a tsorace saboda tun da aka ƙwace Mashin ɗin Bilal ba'a buɗe get ɗin amma dana hangoshi ta window sai hankalina ya kwanta na koma na zauna, gunjin mota da naji ana ƙoƙarin shigowa da ita gidan ya saka na sake miƙewa da sauri na tafi bakin ƙofa. Ina tsaye har ya gama daidaita parking ya fita ya kulle get ua sake komawa cikin motar, motar da suka tafi daga Asibitin a ciki ce ɗazu.
Sai da ya kwashi kusan minti biyar a ciki kafin ya fito waya kare a kunnensa ya wuce part ɗin sa ba tareda ya nuna koda alamar yaga tsayuwata ba dukda nasan cewar ya ganni dan ƙofa a buɗe take. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na koma na zauna ƙwaƙwalwata da zuciyata cunkushe har na rasa wane tunani ya kamata nayi a lokacin, ina nan zaune ya sake fitowa ina jiyo takunsa kan barander nayi saurin kwanciya kan kujera haɗi da lumshe idanuwana tamkar me bacci. Har raina naji tsakin daya ja bayan daya shigo falon ya tsaya a kaina kafin ya shiga jijjiga ƙafata yana kiran sunana.
Na tashi na zauna ina kare idona tamkar daga baccin gaske na farka, da ido ya nuna mun tsakiyar falon kafin ya ce
"Menene haka? Amma dai kin san na tsani kwana da datti a cikin gida ko?"
Na bi gurin da kallo nima kafin cikin zafin ran da ban taɓa sanin ina da shi ba na ce
"Mai ya hana ka faɗawa waɗanda suka ɓata gurin su gyara ko kuwa haka suka zo suka tarar dashi?"
Ga mamakina sai gani nayi ya saki murmushin dake narkar da zuciyata a duk sanda nayi katarin arba dashi kafin ya zaune gefena harda ɗora ƙafafu akan cinyarsa cikin murya mai cike da annashuwa ya ce
"Kuma kin san saida tace in bari ta gyara amma na hana".
Ji nayi tamkar ya daɓa mun wuƙa a ƙahon zuci, na janye ƙafafu na daga jikinsa haɗi da gyara zamana ina kallonsa, sau biyu ina buɗe baki amma sautin muryata yaƙi bani haɗin kai gurin furta kalaman dake kan harshe na sai kawai na fashe da kuka, abinda ya sake karyar mun da zuciya yanda ya miƙe tamkar baiga hawayen da nakeyi ba ya wuce kitchen ya ɗakko tsintsiya da dustbin ya shiga tattare gurin, saida ya share tas ya gyara gurin sannan ya dawo kusa dani ya zauna haɗi da jana jikinsa. Duk yanda na so na ƙwaci kaina yaƙi bani dama.
Ban taɓa jin na tsani tarayya da Bilal ba irin na wannan daren, nayi kuka tamkar raina zai fita shi kuwa ko a jikinsa daga ƙarshe da yaga zan ɓata masa lokaci ma ƙarfi ya sakamun yayi yanda yaga dama dani kafin ya tsallake ya barni a nan falon ya koma part ɗinsa. Saida idanuwana suka daina kawo ruwa suka fara mun raɗaɗi tamkar na yi kwalli da yaji kafin na haƙurewa kaina kukan na tashi na gyara jikina. Ranar yanda naga rana haka naga dare, ina zaune inda na idar da sallar asuba ya shigo falon, kan kujera ya zauna yana danna qayar dake hannun sa nayi masa kallo ɗaya na mayar da kaina ƙasa ba tareda nace masa komai kusan minti biyar kafin ya ce
"Ga kaya can a kitchen ki haɗa abin kari na mutum uku ƙarfe takwas zan fita dashi ba sai kinyi wanda za'a kai Asibiti ba" yayi maganar cikin sigar bayar da umarni. Sai na ɗaga kai na kalle shi, so nakeyi nace ba zanyi ba amma kamar wadda aka ɗinkewa baki na kasa furta hakan, kusan minti goma bayan fitarsa ya sake dawowa har lokacin kuma ina zaune a inda ya barni, a gabana ya tsugunna ya kama hannayena yana murzawa cikin salon da yake yaudarar zuciyata da shi yace
"Kada ki fara abinda ba halinki ba Halima, tun jiya na lura shaiɗan yana yawo a cikin kanki idan kika biye masa zai saka ki aikata abinda zakizo kina dana sani daga baya alhalin baki da wata hujja akan hakan".
Ina aiki ina tuna maganganunsa dana kasa basu fassara ɗaya harna kammala na zauna ina bawa Sharifa dankalin dana soya Al'amin kuma yana ci da kansa. Muna zaune ya shigo cikin kwalliyar data saka zuciyata bugawa, zama yayi yace na kawo masa nasa abin karin na tafi na ɗakko na ajiye masa yana ci ina kallon sa rabin hankalinsa duk yana kan wayarsa dake kawo haske lokaci lokaci da tayi hasken kuma zai ɗauka yayi yan danne danne kafin ya ajiye yaci gaba da cin abincin. Da zai fita ya ajiye mun dubu biyar yace na bayar a siyo kaji tunda akwai kayan miya cikin kayan daya shigo dasu da dare nayi abinci na mutum ukun zai turo a ɗauka. Muƙulli ɗakin sa ma nan ya bar mun shi ya fita tareda su Al'amin ya ɗano su a mota kafin ya maido su ya wuce inda ban sani ba.
Ina tsaka da shiryawa bayan nayi wanka kiran Mama ya shigo wayata, bayan mun gaisa ta ce
"Halima mai yake damunki?"
"Babu komai ko wani abun kika gani Mama?" Na bata amsa, daga can ta sauke numfashi tace
"Babu komai kika zo kina rusa kuka jiya sannan har sanda Mu'azzam ya kawo yaran nan yace kukan kike baki daina ba, shin Halima a duniyar nan idan baki faɗa mun damuwarki ba kinada wadda ta fini ne ban sani ba?"
Sai nayi shiru kafin a sanyaye nace
"Wani abu ne amma kawai kici gaba dayi mun addu'a Mama" na faɗa muryata tana karyewa daga can tace
"Kullum cikin yi miki addu'a nake Halima, ban taɓa kai goshina ƙasa na tashi ba tareda na nema miki taimakon ubangiji cikin lamuranki ba amma dukda haka kema sai kin miƙe tsaye kin ringa yiwa kanki addu'a Halima na sanki sarai kina da sakaci gurin addu'a kullum kuma ina tunatar dake rayuwa ba zata taɓa daidaitar maka ba muddin kace zakayita sakaka ba tareda ka saka Allah a gaba da komai naka ba". Nasiha ta shiga yi mun nayi shiru ina sauraronta harta gama mukayi sallama, ina aje wayar kiran Bilal ya shigo na amsa a taƙaice ya ce mun
"Ki bar girkin nan kawai yanzu zasu wuce" yana gama faɗar hakan kuma ya katse wayar. Nayi shiru ina kallon screen ɗin tamkar zan hango waɗanda yake magana akansu ta ciki, la shakka nasan su JALILA ne amma kuma maganganun sa na ɗazu sunyi tasiri a ƙwaƙwalwata da har naji nauyin da ƙirji na yayi mun ya sauka, ko da bai fito ƙarara ya faɗa mun ita ɗin ba yanda nake zato bace a gurinsa amma abunda ya faɗa na karna aikata abinda zanzo ina dana sani daga baya alhalin bani da hujja akai ya warwaremun duk wani ƙulli da nake buƙatar amsa akai. Dukda haka walwalata bata dawo gaba ɗaya ba haka nayi wunin ranar ko da wasa kuma banma kawo da na koma Asibiti gurin Hajja ba abinci ma tunda yace kar nayi na safe da su banyi tunanin da rana nayi ba kuma shima daya dawo da yamma bai yi zancen ko an kai musu abincin ba har ranar litinin tukunna da yamma yace idan akayi sallar magriba mu shirya za muje can gidan ashe ma an sallamota yau da rana.
Nayi mamakin ganin motar ranar nan a ƙofar gida sanda muka fito zamu tafi gidan Hajjan a zatona ai ta su Jalilan ce kuma sun tafi da abarsu musamman da ban sake ganinta yazo da ita gidan ba tun waccen ranar. Da kansa ya buɗe mun gidan gaba na shiga na zauna ya zuba su Al'amin a baya, maigidan dake jikin namu ya fito suka gaisa ina jinsa yana yi masa Allah ya sanya alkhairin motar ni dai ban ce masa komai akai ba har saida muka hau titi sosai kafin ya kalle ni ya ce
"Ni ko kina ciki baƙi da kyautar da Allah yayi mun ne?"
Sai na juya na kalle shi cikin rashin fahimta, ya wani taɓe baki ya ce
"Mota na siya har mutanen waje suna mun Allah sanya alkhairi amma ke kinyi tamkar ma baki gani ba ko a jikinki". Dariya ma maganar sa ta bani dan haka nayi murmushin da iyakar sa leɓe kafin na ce
"Ashe kana da kuɗin da zaka iya siyan mota"
"Au da kallon matsiyaci kike mun kenan?" Ya faɗa yana kallona, sai na girgiza kai nace
"Ko kusa, amma a yanda muke da kai banyi zaton kana da halin da zaka iya siyan ko keke ba a yanzu balle aje ga batun mota. Allah ya sanya alkhairi ya tsare ka daga sharrin ƙarfe".
"Hmmm Halima kenan, shi mallakar abun duniya ai zuciya ne ba wai arziƙi ba, kuma su kuɗi ai basa magana. Kin san akwai masu arziƙin da sai na kusa da su ne zai bayar da labarin alkhairin su akwai kuma kuɗin da duniya ta san su amma kuɗin cizo ne gasu da baƙin ciki da hassadar wani ya raɓe su har yaci arziƙin su. Mungode wa Allah daya haɗa mu da masu arziƙin bayarwa" ya sake faɗa, na kalle shi kawai nayi murmushi nace
"Masha Allah, Allah ya ƙaro ire irensu ya kuma ƙara yalwata arziƙi mu kuma Allah ya ƙara mana wadatar zuciya, dama ai hannun da yake bayarwa baya taɓa rasawa" sai ya ce
"Idan ma magana kike faɗa mun dama kika samu ki faɗa son ranki yarinya lokacin ki ne. Kuma ita rayuwa ai kayi fatan Allah ya haɗa ka da mutanen da zakayi benefiting da su ba waɗanda zasu zame maka liability ba. Ni shiyasa kika ga duk wani mutum da zanyi mu'amala dashi sai na duba ta ina zai iya taimako na a rayuwa? Dan ba zan ɓata lokaci da wanda bashi da wani role da zaiyi playing cikin rayuwata ba".
Bamu sake cewa komai ba har muka isa gidan Hajjan can cikin kaina dai ina ta nanata maganar da yace shi duk wanda zai yi mu'amala dashi sai ya tabbatar da akwai rawar da zai taka a rayuwar sa. Maganar Mu'azzam ta zama gaskiya kenan tunda gashi ya nanata hakan da bakinsa shima, kenan shi baya burin ya taimaki wani sai dai shi a koda yaushe a taimake shi kenan.
Ko da mukaje babu ma wanda yabi ta kaina suna ta zancen mota kuma a hirar tasu na tsinci kamar dai Hafiz ne ya bashi idan ma ba kyauta ba toh rabin kyauta ya masa dan da alama ba wasu kuɗi ya bayar masu yawa ba aka bashi motar wadda in har siyanta zaiyi Bilal ɗin da na sani bai isa riƙe irinta ba. Bamu jima sosai ba muka tafi abun Allah sai gashi har Rufaida ya kaimu kuma muka shiga tare yace na ɗauki abinda muke so muka zauna a gurin muka yi ciye ciyen mu muka yi hotuna kafin muka wuce gida. Kafin mu isa duk wani sauran ƙunci dake cikin zuciyata yabi sanyin yoghurt da ice cream ya zirare na ware na koma asalin Halimata muna ta raha har muka isa gidan. Daren saɓanin dararen da suka gabaceshi munyi shi cikin walwala da farinciki. A nan ɗakinsa na part ɗina muka kwanta bayan da muka gama shan soyayyar mu bansan ƙarfe nawa ya bar ɗakin ba dan ni dai na farka ƙarfe huɗu da mintoci na tarar baya nan da fari na ɗauka ma ko yana banɗaki na zauna ina jira ya fito na shiga jin shiru yayi yawa yasa na tashi na ƙwanƙwasa kafinna buɗe naga babu kowa.
Saida nayi uzurina na fito kafinna fita falo na tarar dashi kwance kan kujera yana bacci waya kare a kunnensa, mamaki ya kamani, wace waya ce haka cikin dare har kuma yayi bacci a haka? Matsawa nayi kansa na kai hannu zan zare wayar na duba yayi firgigit ya farka haɗi da fizge wayar, nayi baya saboda yanda ya taso kamar zai makeni ya shiga matse ido kafin yayi ƙaramin tsaki ya kalleni ya ce
"Na gaya miki ki dena mun irin haka kar wata rana na kai miki dukan da zan ji miki ciwo". Na tura baki, yana yawan gaya mun baya son yanda nake masa idan yana bacci nace zan gyara masa pillow ko na karɓi wani abu a hannun sa ina razana shi. Tashi yayi ya wuce ɗaki na bi bayan sa ina cewa
"Toh dawa kake waya a daren nan har bacci ya ɗauke ka baka sani ba?"
"Ni nace miki waya nakeyi ko kinji da kunnenki ina magana da wani?" Ya faɗa bayan daya kwanta akan gado. Nayi tsaye ina kallon sa yayi ƙaramin tsaki bayan daya tura wayar ƙasan pillow daya kwanta akai kafin ya rufe ido alamar bacci zai koma.
"Amma dai ka san babu kyau aje waya a ƙasan pillow ko" na faɗa yayi saurin katse ni da cewa
"Dan Allah Halims ki barni bacci nake ji". Fita nayi naje na duba Al'amin da Sharifa ina shiga tana farkawa dan dama dai dai lokacin farkawata kenan na haɗa mata shayi na bata dan na dena bata Nono da dare saboda ina so na yayeta kafin a fara Azumi, sai da ta koma bacci kafin na sake musu addu'a, jin an fara kiraye kirayen sallah sai kawai na ɗauro alwala dan bacci ya bar idona. Ina tura ƙofar ɗakin Bilal dan dama ban rufeta da kyau ba sanda na fita da sauri ya kife wayar sa, dukda na rigada na ganshi amma bance komai ba na wuce na ɗauki Hijabi na na fita na ja masa ƙofar.
Sallah nayi raka'a biyu kafin na ɗauki alƙur'ani da tsakani da Allah na kwana biyu banyi karatu da shi ba. Badan bana karatun alƙur'ani ba aa, na kan yi tilawar surorin dana haddace ko nayi amfani da wayata musamman idan zan tisawa Al'amin karatu. Ni da kaina naji nutsuwa sosai a ruhi da gangar jikina zullumin daya cika mun zuciya akan me Bilal yake a waya da