Showing 207001 words to 210000 words out of 257873 words
musamman da suka koma unguwar da babu wanda ya sansu suka fara sabuwar rayuwa.
Kullum ƙawayenta suna mata mitar basuga amfanin kuɗin da take samu ba domin dai kullum ka ganta tana nan kalar tausayi cikin tsumma ba sutura mai kyau mayukan gyaran fata da turaruka ma saboda ƙorafin mazan da take ta'ammali dasu ya saka ta fara siya saboda ta gyara jikinta duk a salon kada a fahimci halin da take ciki ya saka take takatsantsan da gudun mallakar duk wani abu da zai janyo hankalin mutane kanta, suna dai cin daɗi a cikinsu amma abubuwan more rayuwa dole ta haƙura da su saboda gujewa zargi sai dai tayi ta tara kuɗin idan sunyi yawa ta siyi wani abu kamar zobe ko fili ta ajiye.
A silar Nuratun asirinsu ya tonu har yan uwan mahaifinsu suka san halin da suke ciki dukda suna ji a jita jita wanda kuma da yawa Bilal da kowa ya san yana wahalta musu har gida ya siya musu shi mutane sukewa kallon abokin shashancin nata domin dai a rayuwar da muke ciki yanzu haka kawai wani bare ya ringa maka hidima kwatankwacin wacce yake musu tabbas abar dubawa ce dukda na Allah basa ƙarewa a duniya.
Ciki Nuratun tayi wanda baƙin cikin haka shine silar ajalin mahaifinsu. Ita bata kai wayewa da buɗewar idon Zulaihan ba kusan ma tursasawata sukayi ta shiga rayuwar da ba tata ba, bata ma san da tayi cikin ba har saida ya bayyana kansa fallasa kansa tukunna aka sha gurmi da dangin Babansu duk kuma yanda Umman da Zulaiha suka kaɗa suka raya tace ba zata zubar ba iya zunubin data kwasa harta same shi ya isheta ba zasu ɗora mata wani ba da Allah kuma ya nufa ba mai taka ƙasa bane tayi ɓari dukda da saka hannun su Zulaihan daga nan kuma ta tuba ita kanta Zulaihan daga lokacin ta rage abubuwa da yawa musamman kuma da Bilal ya fara taso da maganar aurensu ta shiga tsoron kar maganar ta koma masa a samu matsala dukda dai na Nuratu ne ya fito fili ita aka san bata ji amma ta san hakan zai iya shafarta shiyasa ta tattara hankalinta guri ɗaya ta saki harkar dama kuma tayi alƙawarin daga sanda aka saka musu rana zata bari to hakance ta kasance ta dena zuwa gurin kowa sai dai yan dabaru na waya data cigaba domin cigaba da samun kuɗin riƙe kai zuwa sanda zatayi auren.
Sai da ta cire Bedsheet ɗin da ɗaure shi a leda domin ba zata iya wankewa ba dama kuma amfaninsa kenan bata shimfiɗa wani ba ta shiga wanka a gurguje sai dai tana saɓa sabulu ta jiyo bugun ƙofa ta kasa kunne taji ko Bilal data leƙa falo ta ganshi a kwance zai tashi ya buɗe amma shiru shine ta zuciya ta fito da kumfa a jikinta zataje ta buɗe musu.
Wankan ta koma bayan sun gama iyashegensu suna tsokanarta wai amarya suka ringa dariyar da su suka san dalilinta sanin yana gidan kuma ya saka suka kama bakunansu dake cike da maganganu da son jin ya aka ƙare, abubuwan da suka kashe kuɗi tayi dan ta lulluɓe rayuwarta ta baya sun ci ko kuwa an samu akasi?
Wanka ta koma ta barsu suna haɗa TV da suka biya suka karɓo mata, Asmy ta ce bata karya ba gashi dan wulaƙanci bata ajiye musu sauran kaza ba kamar yanda ta ce sun cinye dan haka ta duba kitchen babu komai sai kayan shayi da burodi, ganin akwai ƙwai da mai babu albasa dai haka ta fitar da camping gas tsakar gidan suka ɗora ruwan tea bayan ya tafasa aka soua ƙwai dan ma Suby ta taho mata kayan spices garda garlic powder da yayarta ta bata gudummawa shi suka saka a ƙwan da suka fashe kusan rabin creat suka baje a falo suka karya tareda amarya bayan ta yi sallah ta fito.
Suna tsaka da jin labarin yanda akayi ya kirata, tayi tsaki bayan ta kashe wayar ta ce
"Banda rashin Imani ya raba dare yana sukuwa akaina yanzu gari ya waye ya ce wai in bashi abin kari maimakon shi ya dafa mun".
Sadiya ta ce
"Maganar gaskiya ba shiya kamata ki haɗawa abinci harda farfesu ma saboda ya mayar da jinin jikinsa dan abinda kika zuƙe ya fi ƙarfin ruwa ma" gaba ɗaya suka sheƙe da dariyar shaƙiyanci suna tafawa. A wani shegen tea flask iya ta da ta zuba masa ruwan zafin data taro a banɗaki ta haɗa da guntun bread ɗin da suka rage da sauran Milo dan sun shanye ledar Peak 500g daya siyo, a hannu ta riƙe kayan Suby na cewa ta ɗora a try mana tayi wucewarta.
BILAL
Kallon sama zuwa ƙasa yayi mata kafin ya tsayar da idonsa kan hannunta yana duban abinda ta ruƙo harta dungurar dasu a gabansa tana cika tana batsewa ko me ta tuna kuma sai ta saki fuska kaɗan ta zauna a gefensa ta shiga gaishe shi tana ƙoƙarin shiga jikinsa cike da kissa. Janyeta yayi ya miƙe zaune daƙyar dan kwanciyar da yayi zazzaɓi ya rufe shi, ya dafw kansa dake bugawa yana kallon kayan dake gabansa kafin ya ce
"Menene wannan?"
"Breakfast mana" ta faɗa tana sake matsawa kusa da shi dan ganinsa da tayi babu riga ya saka ta fara jin muradin kasancewa dashi dan abubuwan data sha jiya basu gama sakinta ba dukda taga alama shi nasa ya sake shi.
"Ni zanci wannan sauran biredin sai kace wani almajiri kuma ina madarar?" Ya faɗa, ta yamutsa fuska ta ce
"Ai dai kana kallo baƙi nayi ka godewa Allah ma daka samu sauran madara kuma sun shanye"ta ƙarasa tana harararsa. Da mamaki ya ce
"Ita madarar suka shanye duka?"
"Dan Allah ji yanda kake magana sai kace wanda suka shanye bugu ɗaya, su huɗu fa, ko ni kaɗai waccen yar madarar da ƙalau nake ai zama ɗaya zan shanyeta".
Kasa ce mata komai yayi ya tsaya kawai yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya kwanta saboda yanda zazzaɓin yake nuƙurƙusar jikinsa ya ce
"Ki soya mun ƙwai toh".
Haka ya ringa tura ƙwan daya ga kamar da gayya aka ƙone shi ga ga uban ƙarni daƙyar ya iya haɗa Milon a kofin robar data haɗo masa da shi. Safiyarsu ta farko da Halima ta shiga dawo masa, dukda yanda ta ke a wani yanayi na shiga sabuwar rayuwa haka ta ringa kai da kawowa bata nutsu ba saida ta cika masa dining da lafiyayyun breakfast bayan dankali da ƙwai nama kansu kusan kala uku ga sauran kazar amarci ga wanda aka taho mata da su daga gida komai cikin kwanuka na alfarma suna ci suna annashuwa amma yau shine aka bawa sauran biredi a gidansa da shayi a flask ɗin roba da kofin roba kuma babu yanda ya iya ya ci.
Baccin wahala ya sake komawa bayan ya sha paracetamol Zulaiha kuwa dama tunda ta dangwarar masa da ƙwan ta koma gurin ƙawayenta suka cigaba da sabgarsu.
HALIMA
Dole ta saka nake ƙarfafa jikina domin na yiwa kaina alƙawarin ƙaryata Bilal da yake cewa dole ya san zan neme shi. Ina son sa ba zan ƙaryata hakan ba amma kuma ni da kaina dana nutsu na fahimci cewar rabuwata da shi shine alkhairi a tare da ni.
Daga kalaman daya kalli idona ya faɗa mun na tabbatar dagaske yakeyi baya so na, albarkacin soyayyar da nakeyi masa ta saka ya aureni idan ma kuma yana so na ɗin tunda ya fahimci so na ya fi nasa yawa ya sakawa ransa zan zauna dashi komai wahala zan jure shine dalilin daya saka ya ringa azabtar dani a fili da baɗini har kuma da yake gargadar rasani bai yi nadamar hakan ba sai ma ƙara tabbatar mun da yakeyi ya sani ba zan iya rayuwa da waninsa ba.
Tsayin wata biyu da nayi tun barowata daga gidansa bai biyo ni ba ko a waya bai kirani ba sai yanzu haka wani nasa bai zo ba duk sai bayan da iyayena suka ɗauki matakin da suke ganin shi zai kawo mun maslaha a rayuwata.
Abu uku ne dama fargabata idan na rabu da shi, Soyayyata, makomar yarana sai kuma yanda mutane zasu karɓe ni.
Soyayyar da nake masa batayi mun rana ba, bata amfana mun komai a zamantakewata da shi ba face wahala, baƙin ciki, ƙasƙanci da zubewar mutunchi. Na bashi zuciyata, rayuwata da komai nawa. Na zaɓi kasancewawa dashi sama da farin cikin dangina amma abin da ya mayar min da shi? Cin amana, ƙarya da yaudara.
A yanzu na fahimci wata soyayyar ba rahama ba ce kamar dai soyayyata da Bilal azaba ce.
Da ace Bilal ya mutuntani ko da baya so na ya kare martabata ya kuma riƙeni amana ƙila ba zan taɓa fahimtar komai ba Soyayyata zata cigaba da riƙe aurenmu har zuwa lokacin da ubangiji ya ɗiba mana amma sai ya kasance mai butulci, a sanda ya gama cin moriyar ganga kamar yanda Anty Labiba da Hansa'u sukayi nasarar haska mun gaskiyar abinda na rintse ido a baya naƙi yarda dashi. Ya mayar da ni daddawar ɓurma, ya ɗana tarko dani. Ta yuwu ya samu iya abinda yake farauta shiyasa amfanina ya ƙare a gurinsa ko kuma na gaza samar masa da abinda yake muradi shiyasa ya watsar dani.
Bana son tuna ƙazantar da kunnuwana suka jiye mun da wanda idanuwana suka gane mun yana aikatawa shi da Jalilah, a yanzu dana tabbatar da ba ita ya aura ba, buri na na ƙarshe shine sanin da me wacce ya aura ɗin ta fini? Ta ina na gaza? Me take da shi wanda ya ɗauki hankalinsa da ni bai samu a tattare da ni ba? Ta yaya tayi nasarar cafkar soyayyarsa? Domin na tabbatar tunda ba Jalilah bace toh wannan da yayiwa lakaɓi da DUNIYARSA ya aura ita ce kuma ya kaini gidansu a unguwarsu Anty Labiba.
Da hannu biyu na share hawayen da tunanin da na tafi mai zurfi yayi mun sanadin zubarsu, zan daina kuka na sani amma ba yanzu ba domin ciwon da yake danƙare a zuciyata bai ko kama hanyar warkewa ba balle na dena kukan zugi da raɗaɗin da yake mun.
Wayata dake aje saman kaina ta shiga ƙara, agogo na fara dubawa karfe tara da rabi lokacin, duk da naga mai kiran Maman Yusuf ce maƙwafciyata amma sai na mayar da wayar na ajiye dan bani da sukunin da zan iya amsata a lokacin na san kuma ba zai wuce zancen kwashe kaya zatayi mun ba tunda Anty Labiba ta ce ta shiga gidan neman guduma dukda bata tarar da ita ba sai yara amma na san sun bata labari.
Ganin tana ta kira ya saka na ɗaga ba'a son raina ba, murya can ƙasa na mata sallama ta amsa cikin yanayin dayayi kama da wacce take cikin damuwa tace
"Yanzu Maman Al'amin ashe dagaske kike ba zaki dawo ba?"
Nayi murmushi na ce
"Gashi kuwa kin gani har an kwashe kaya"
"Wlh ko da aka ce mun an kwashe kaya ban kawo dagaske ba zaki dawo ba tunda nawa akayi irin hakan kuma aka koma? Ga Amina (Ƙishiyarta da aka saka) itama cikin satin nan zata dawo kuma har kayan ta kwashe. Sai da naji hayaniyar mata da guɗa kafin da Ummi ta dawo take ce mun wai amarya aka kawo gidanki, wlh na ɗauka ko haya ya bayar sai da Abbansu ya ce wai ai dama yayi aure tuntuni tariyarce sai yanzu. Kiyi haƙuri amma Baban Al'amin ɗan abu ta kazan uba ne" ta kora masa ashar.
Murmushin na sakeyi kamar tana gabana ban kuma iya sake ce mata komai ba har ta gaji da surutu ta mun sallama akan zata samu lokaci tazo dukda tayi nauyi abinda ya saka ban ganta ba kenan ma tuntuni amma sun so suzo biko. Bayan da mukayi sallama kamar in kashe wayar sai kuma na fasa na kunna Data na shiga Whatsapp.
Cewar da tayi an saka amarya a gidan sai ya nemi ya hargitsa mun lissafi. Wato dama jira yakeyi a kwashe kaya kenan ya saka amaryarsa? Lallai ta tabbata bana gaban Bilal yaudarar kaina kawai nakeyi amma ya daɗe da kulle shafina.
Kenan da ya ce ba zai sakeni bama so yayi ya cigaba da azabtar dani ta hanyar barina da igiyoyin aurensa ba wai saboda yana buƙatar mu sasanta bane. Status ɗin Fadila na lalubo dan idan har dagaske amaryar Bilal ta tare na san ko kowa bai saka abinda ya shafi bikin ba ita zata saka ilai kuwa ina kunnowa naha write up
'Allah ya sanya alkhairi bro' ga kuma sauran status nan da suka biyo baya hannu na rawa na shiga buɗe su ina fatan in ga fuskar amarya cikin sa'a hoto na biyu kuwa na ci karo da ita, a falon Hajja aka ɗauketa tana durƙushe tsakiyar waɗanda suka kawota amma fuskarta ta fito tar da yake da Iphone aka ɗauki hoton.
Hutun wucin gadi na tafi ina kallon amaryar Bilal. Baƙa ce kuma mummuna domin ko da nima ba farar bace amma akanta balarabiya ce ni ba kuma sai an gaya mun ba na san ta girmeni kuma tana da jiki dukda dai da gani ƙibar tata ta sama da ƙasa ce ba duka jiki ba.
Ji nayi wani kaso na abinda nakeji ya yaye, ko da aka ce yabon kai jahilci amma dole in yabi kaina wlh na mata zarra a ajiyeni a ajiyeta sai na fita yin kasuwa.
"A hakan kuma ta ƙwace miki miji" zuciya ta raya mun nayi fatali da tunanin a fili na ce
"Ba ƙwace ta mun ba, ya raina ni'imar da Allah yayi masa shiyasa aka haɗa shi da daidai halinsa yanzu".
Cigaba da kallon hotunan nayi sauran a can gidan a ɗakunana a da amma akayi su, sai na ringa jin kamar ma na san fuskarta a wani guri, a hoto na ƙarshe naga Suwaiba, cousin sister Hansa'u ce ina ganinta kuma na tabbatar da tabbas na san fuskar amaryar Bilal ɗin tareda Suwaibar na taɓa ganinsu kenan amma me cece alaƙarsu? Itama yar uwarsu ce ko kuwa ƙawar Suwaibar ce kenan?
Ba yar uwarsu bace gaskiya domin da ƙila Hansa'u zata san ita ce ya aura ta yuwu dai ƙawarta ce. Haka kawai na shiga zullumin son sanin alaƙar Suwaiba da Amaryar Bilal, har na kashe wayarna sake kunnawa nayi screenshot ɗin hoton da Suwaibar ta fito na turawa Hansa'u.
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 53*
"Lallai su Bilal anyi Amarya, toh Allah ya zaunar lafiya" amsar da Hansa'u ta bani kenan duk kuma yanda na so da naji ƙarin bayani bata sake cewa komai ba, Da na isheta da tambaya ma balbaleni tayi da faɗa tana cewa
"Wai menene haɗin ki da matarsa ne Halima? Mutum ya rabu dake tuni ma shi ya manta ya taɓa rayuwa da wata Halima har yana shirin fara rayuwa da wata amma ke ashe kina nan kina dakon wahala sai anyi magana ki fara rantsuwar kin cireshi a ranki gashi kina bibiyarsa".
Tilas na bar maganar amma kuma na gaza hana zuciyata tunani da hasashen Bilal da amaryarsa a wannan dare. Zuciyata ta ringa zafi, ina kwance lamo akan gado har sha biyu bacci ya gagara ɗaukata, daren mu na farko na ringa tunawa, a hankali na saki kukan da nake ta ƙoƙarin dannewa na cusa kaina a cikin pillow na shiga yin sa a hankali. Na daɗe ina kukan sai da naji sauƙin abinda ya tsaya mun a rai kafin na tashi na ɗauro alwala na shiga yin Nafila har sai da bacci ya fara fizgata kafin na kwanta.
Washe gari da safe ina haɗawa su Amir abincin da zasu tafi Tahfiz da shi Anty Labiba ta shigo kitchen ɗin, ganin tana kallona da wani murmushi na sha jinin jikina ilai kuwa sai ji nayi ta ce
"Ke ashe amaryar Bilal ta tare jiya". Nayi kamar ban jita ba, bata damu ba ta cigaba da cewa
"Sadiyar Shehu ce ta koma tana bawa su Nasiba labari wai sai suka ga gidan kamar kango ba kamar sanda aka kai ki ba, a hakan ma wai an ce shi ya mata kayan ɗaki".
Ni dai ta tafasa sauke ban ce mata ba na cigaba da abinda nakeyi amma cewar da tayi wai Bilal ne yayiwa Amaryarsa kayan ɗaki ya tsaya mun a rai. Bilal da yayi mun lefe a leda kuma a tsayin zamana dashi cokali bai taɓa siyowa ko ya ɗauki kuɗi ya bani na siya ba shine yanzu yayiwa mace kayan ɗaki ɗungurungum? Ko da yake ba abin mamaki bane tunda an ce shi ya siya musu gidan da suke zaune ma. Tambayar kaina na shiga yi wane irin So yake yiwa yarinyar haka?
"Irin soyayyar da kike masa" na bawa kaina amsa. A fili can ƙasa na ce
"Ya Allah na roƙeka, yanda ka jarabceni akan mutumin nan shima ka ɗanɗana masa kwatankwacin wahalar da na ci akan soyayyar sa"
"Iska na wahalar da mai kayan kara" Anty Labiba ta faɗa tana ficewa daga kitchen ɗin na rakata da harara dan haushinta ne ya kamani. Ko menene manufarta na gaya mun ma oho? Haka nayi yinin ranar sukuku gaba ɗaya tunani na yana can yanda take kasancewa da Bilal da sabuwar amaryarsa. Dagaske fa ya gama da babina tunda gashi har ya samu madadina, ko da yake dama ko a sanda nake tareda shi ina gurin ne kawai amma ni da babu duk ɗaya. Da naga ina nema na sake mayar da kaina ruwa bayan duk alƙawarin dana ɗaukar wa kaina dole na yaƙi tunanin na kwaso Khaki na na shiga wankewa bayan ya bushe na hau guga sannan na fitar da duk abinda zan buƙata dan washe gari litinan zan je nayi reporting a PPA na.
BILAL
Sai bayan Azahar ya farka dalilin surutai da ya ringa