Showing 219001 words to 222000 words out of 257873 words

Chapter 74 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

513

da ake ta sake kiransa da ita. Tana fita kuwa kiran ya sake shigowa, saida ya kashe motar kafin ya ɗaga murya can ƙasa kamar mai bacci yayi sallama.

Muryar Jalilah ta sauka raɗau a kunnensa
"Yau dai Allah yayi na sameka a waya" ta faɗa, ya sake narke murya ya ce
"Nayi kewarki Babe, mai nayi miki? Kin toshe duk wata hanya da zan iya samunki phone call, Whatsapp, IG duk kinyi blocking ɗina what have i done to deserve such punishment Jalilah?"

"Nayi blocking ɗin ka ko kayi blocking ɗina?" Ta bashi amsa da sauri ya ce
"Saɓo kikeyi kema kin san hakan ba zai taɓa zama gaskiya ba ya za'ayi nayi blocking ɗin ki?"

"Ai shikenan dai, kwana biyu? Nayi missing ɗin ka sosai" ta rage murya ta faɗa. Ya gyara zama yana cewa

"I missed you more Lily, yaushe zaki dawo?"

"Ya kamata ace jiya zan dawo sai kuma na wuce gurin Mom bata jin daɗi" ta bashi amsa

"Subhanallah, mai ya sameta? Amma da sauƙi ko?" Ya faɗa a cikin rikicewar ƙarya ta amsa masa
"Da sauƙi, kaya fa har sun kamo hanya kuma ba zasu daɗe ba dan ƙila ma su rigani isowa dan haka ka saka a gyara gurin da kace zamu mayar dashi store kafin na dawo a fara loading kamfani, sai kaga kayayyakin da muka samu abubuwa da yawa ma basu tura mana ba sai da nazo na gansu na so tare muka zo kaima na san da ka sake ganin wasu abubuwan da zamu iya ƙarawa da su".

Window aka buga ya sauke Zulaiha ta ziro kai tana cewa
"Menene pin ɗin?" Ya danne speaker wayar kafin ya gaya mata ta koma Jalilah ta ce
"Baka gida kenan?"

"Aa, eh mai kika ji?" Ya faɗa a duburce. Ta ce
"Naji muryar Mace"

"Halima ce Shawarma zata siya" yayi saurin bata amsa sai ta ce

"Allah sarki ta dawo kenan?"
"Eh ta dawo" ya sake bata amsa. Zancen kaya ta cigaba dayi masa yana sauraronta yana kuma kallon hanya dan kar Zulaiha ta taho bai lura ba kusan minti goma kafin ya cewa Jalilan zai kirata idan sun isa gida ya ajiye wayar ganin Zulaihan tareda wani ya ruƙo mata ledar abinda ta siya. Kallonsu ya ringayi, da farko ɗauka yayi ko yaron shagon ne sai da suka matso yaga Normal kaya ne a jikinsa ba rigar ma'aikata ba kuma magana yakeyi mata dukda fuskarta bata nuna sauraronsa takeyi ba amma yanda suka jero kamar ma jikinsa na gugar nata ya harzuƙa shi bai san sanda ya buɗe motar ya fita ba dai dai lokacin da suka ƙarasa ta nuna Bilal ɗin tana cewa

"Ga Mijina nan tunda na faɗa maka baka yarda ba shi sai yayi maka bayani" ta fizge ledar ta shige mota ta barsu a tsaye. Haƙuri mutumin ya shiga bashi kafin ya juya da sauri ya bar gurin shi kuma ya koma motar cikin fushi ya ce mata

"Akan me kika tsaya kika kula shi?"

"Ni a yaushe na kula shi? Kuma idan da mun fita tare da kai ai babu wanda ya isa yayi mun magana amma kayi zamanka a mota ka turani tsakiyar maza saboda baka kishina" ta ƙarasa idonta na kawo hawaye. Tsaki yayi ya tayar da motar har suka isa gida bai ce mata komai ba.

Part ɗin sa ya wuce yana fita itama ta sakawa falon muƙulli ta fitar da Shawarmarta da Smoothie ta shiga ci bayan ta kunna kallo, wayarta tayi kara, tayi murmushi ganin mai kiran ta ɗaga. Mutumin da suka haɗu ɗazu ne, ba tayi niyyar kulashi ba dan daya mata magana kai tsaye tace masa ita matar aure ce amma bai yarda ba da zata biya kuɗin siyayyar da tayi ya ce ta barshi taƙi shine ya zuba mata cash ɗin da sai da tazo gida yanzu taga dubu ɗari biyu ce a ledar. Ta san ba zai wuce a gurin Teejay ɗaya daga cikin yaran gurin ya samu number, Ahlan da ta gani a true caller kuma ya saka ta gane shi ne dan sunan da yake kan complement card ɗin daya haɗa mata da shi kenan.

Ba tsoro ko fargabar komai ta shiga yin wayarta kamar yanda ya ce aurenta ba matsalar sa bace in dai ta yarda su ƙulla alaƙa. Har sha biyu da wani abu kafin sukayi sallama ta wuce ta kwanta ba tareda ta bi ta kan Bilal ba wanda yake can shima yana sheƙe ayarsa da Jalilah dan daga waya ta fara hillatarsa da abinda yayi rantsuwar ba zai sake ba ya tuba sai gashi bai san sanda yayi unblocking nata a Whatsapp ba da kansa kuma ya kirata Video call sukayi abinda bayan sun gama kuma yayi bacci dan sai lokacin yaji ya samu nutsuwa. Duk daɗewar da yayi da Zulaiha wuya kawai ya ci amma yanzu a ɗan lokaci ya samu nutsuwar da ya daɗe bai sameta ba.

Tunani ya ringayi ko dai ta Hajjan ya yarda ya auri Jalilah ne? Aurensa da ita riba biyu ne, ga kuɗi ga kuma jin daɗi domin ita ɗin ta san ta kan duniya amma kuma kishi ba zai taɓa bari ya zauna lafiya da ita ba dan zuciyarsa ba zata samu nutsuwa ba zai yi ta zargi da hasashen tana kula wasu a bayan idonsa wannan ya saka ko yaji zuciyarsa na son kwaɗaita masa auren Jalilah da abinda zai samu a silar hakan zai kore tunanin domin dai bariki ta haɗa su a nan kuma zasu rabu.

Washe gari kamar yanda sukayi da Kamalu yaje ya same shi sun tafi gurin Alhaji Balarabe mamallakin plazar da Jalilah ta siyi shagunan. Alhajin ya karɓi takaddun take kuma ya kira Lawyer da wanda aka ci sa'a yana ta gurin dan haka ba'a wani ɗauki lokaci ba ya je ya same su.
"Gaskiya waɗannan takardun ba namu bane" Lawyer ya faɗa bayan daya gama dubasu. Alhaji ya tashi ya ɗakko wata folder ya ringa fitar da original takardu na sauran shagunan da ba'a siyar ba yana miƙewa Bilal da Kamalu suna dubawa, ya kwashe su ya mayar sannan ya ɗakko photocopy ya ware su ya cire masa na ainihin shagonsu ya bashi yana cewa

"Kaga photocopy ɗin original ɗin da muka baka nan" ba wani dogon bincike Bilal da kansa ya gane banbanci ƙarara na takardun hannunsa da photocopy waɗanda akace sune wanda aka bashi. Duk kansa sai ya ƙulle, ya kuma tuna tabbas irin waɗancan aka bashi domin bai manta stamp ɗin su da yake a kai ba wanda sai yanzu ya lura babu shi a na hannun nasa.

Alhaji Balarabe ya ce ya tafi da photocopy ɗin sannan a shirye suke domin su taimaka masa t duk inda zasu iya idan buƙatar hakan ta taso.
"Kayi tunani ko takardun sun shiga hannun wani bayan kai kar ka ce cire kowa walau ya uwa ko Amini muddin sun je hannunsa toh abin zargi ne domin babu yanda za'ayi a tashi rana ɗaya ace takaddu sun canza daga yanda suke zuwa wani abu na daban dole wani ne ya canza su" cewar Lawyer Alhaji Balarabe.

Haka ya bar gurin cikin damuwa duk kuma yanda zaiyi ya gano abinda ya faru ya kasa, to wa ma zai zarga bayan daga shi sai Jalilah da waɗanda suka siya a hannunsu ne kaɗai suka san da maganar ita kuma a hoto kawai ya tura mata su bata gansu a zahiri ba. Haka yayi ta kame kame daga ƙarshe ya watsar ya kama sabgoginsa tunda lissafin sa na farko ya wargatse ya sake dawo da Jalilar rayuwarsa sai dai ya jira kuma ya sake shiri.

BAYAN WATA BIYU

HALIMA
Na fara Bautar ƙasa na gadan-gadan, wani Private Research Center aka kai ni, mai gurin Abokin Uncle Mudassir ne na sha mamakin lokacin da naje gurin dan ban taɓa sanin wanzuwarsa a Kano ba. Guri ne mai ɗauke da Laboratories babu adadi ga kayayyakin aiki yyanda kasan a irin fina finan Turawan nan na Scientist haka da yawan ma'aikatan gurin duk fararen fata ne kaɗan ne baƙaƙe iri na.

Fara aiki na ya sa na yarda dagaske da aka ce zaman banza ne yake kashe zuciya har mutum yayi ta tunane-tunanen banza da wofi mai abunyi sau tari ya kan manta da duk wata matsala idan ba wacce ta shafi aiki ko sana'arsa ba. Toh nima hakan ce ta kasance dani domin ban rufa sati ba na fara ɗaukar saiti, na tattara duk wata damuwa na watsar na kama aiki na domin gani nayi tamkar ban taɓa zama a aji ba komai sai ya zamar mun baƙo a lab ɗin da aka kaini, da yake kuma har raina a shirye nake da na mayar da hankali na koyi abin sosai sai na ware duk wani test da akayi idan na koma gida zan zauna nayi Reserch a waya har sai na samu cikakkiyar fahimta akan abun, na ƙulla abota da ChatGPT, duk abinda ya shige mun dubu shi zan tambaya ya warware mun musamman da na gano yana jin hausa shikenan na samu abinyi ko Whatsapp sai in wuni na kwana ban leƙa ba ina can ina kwasar romon ilimi har na fara hasaso kaina na koma makaranta nan da wani ɗan lokaci nima na zama babbar Scientist tamkar mamallakin gurinmu dukda a hoto kawai na taɓa ganinsa sai dai ya burgeni, matashi don bai kai shekarun Uncle Mudassir ɗin ba ma idan kuma ba hoton ne ya mayar dashi yaro ba amma har mamakin irin abubuwan da yayi nayi wanda suke rubuce cikin tarihinsa da akayi bango guda a cikin reception ɗin gurin.

A cikin satin daya mutu na kammala iddar Bilal, mun rabu kenan ko in ce na cire duk wani sauran fata da nake dashi akan al'amura zasu iya canzawa ko da ace akwai sauran zama a tsakaninmu toh fa sabon lale ne, sabon nema, sabon ɗaurin aure wanda na tabbatar abu ne mai matuƙar wahala ace waliyyai na su sake karɓar maganar auren Bilal, sai dai ƙaddara mai girma irin wacce ta haɗa mu a baya wadda a yanzu ni da kaina bana fatan ta sake giftawa.

Aurensa ya zame mun darasi a rayuwa, banyi nadamar kasancewa tareda shi ba domin zaɓi na ne ba dole aka mun ba amma kuma na godewa Allah daya farkar dani a dai-dai lokacin da rayuwara take da sauran ma'anar da zan iya canza gobe na.

Tun ranar daya bani takardata ban sake haɗuwa da shi ba ko da a hanya haka bai sake nemana ba in banda text message daya turamun sau biyu akan cewar zai ƙwace yaransa shikenan bai kuma waiwayata ba ya tare da amaryarsa ya manta da ni da yaran da muka haifa tare.

Ko kusa ban taɓa kawo cewar ko da cewar baya sona na kuma yarda da hakan babu haufi amma kuma na ɗauka albarkacin zaman da mukayi na shekaru zan samu gurbin da zai ringa tunawa da ni a zuciyarsa har ya tuntuɓe ni, kai ko bai nemeni ba ya kamata ace ya nemi yaransa, ko da yake tun kafin ya sakeni ma zaman da mukayi bai taɓa waiwayarsu ba har gara ni a sanda ya so ya yaudareni ya sake mayar da rayuwata cikin uƙuba ya bibiyeni amma bai taɓa tambayar yaransa ba, bai san cin su ba, bai san shan su balle suturar su ba shi ba hatta da yan uwansa babu wanda har kawo yau yayi tunani ko karar dai dai da rana ɗaya yazo ya gansu ko ya kira yaji lafiyarsu sai Abubakar.

Shi kaɗai yake tuntuɓata duk kuma sanda ya zo Weekend sai yazo ya gansu ba kuma zai zo hannu haka ba idan ma bai kawo komai ba zai basu kuɗi ya ce a siya musu bayan shi hatta Anty Amina da nake zaton tana so na tun ranar da suka zo biko suka tafi ban sake jin ɗuriyarta ba balle kuma uwar gayyar Hajja a taƙaice dai sun barmun yaran kawai na kuma yi murna da hakan a kullum kuma ina addu'ar Allah ya raya min su suyi tsahon rai su kai lokacin moro naga yan uwan Bilal ɗin zasu zama ire iren marasa kunyar mutanen da nake samun labari da sai a lokacin da yara suka zama abin moro ne sannan zasu gwada iko akansu matsayin dangin mahaifinsu ko kuwa sun barsu har abada?

*KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 55*

Tarin missed calls ɗin da ya gani daga Alhaji Lawan mutumin daya siya gidan Jalilah a hannunsa ya tabbatar masa da ba lafiya ba, a maimakon ya kira Alhaji Lawan ɗin kai tsaye sai ya fara kiran Nasir domin shi yayi hanyar cinikin.

"Yanzu nake shirin kiranka dama; kana ina?" Nasir ya faɗa bayan daya amsa wayar Bilal ya ce

"Mai ya faru naga mutumin nan daya siya gida a hannuna yana ta kirana a waya ban lura ba sai yanzu?"

"Shiyasa na ce kana ina? Akwai matsala gaskiya" Nasir ya bashi amsa. Bilal ya girgiza kai kamar yana gaban Nasir ɗin kafin ya ce

"Ina Abuja, ka faɗa mun abinda ya faru dalilin daya saka na fara kiranka kenan kafin na bi bayan nasa kiran"

"Wasu mutane ne suka je gidan, a faɗar su sun siyi gidan ne dan har takardu suka nuna masa kuma daya ɗakko musu nasa aka haɗa sai ya gane na gurin sa fake ne su suke da original ɗin" Nasir ya faɗa.

Wata hajijiya da bugawar ƙirji suka ziyarci Bilal lokaci ɗaya, a hankali ya sulale ya zauna akan gado zufa ta shiga keto masa kamar wanda yayi gudu. Yana jiyo Nasir ta cikin wayar yana cewa

"Idan kuskure ne tun wuri ka nemo hanyar da zaka gyara dan wlh Alhaji Lawan bashida daɗi musamman akan maganar kuɗi; yanda ya kirani kuma yanzu na san a shirye yake da yin koma menene dan haka asirinka a rufe ko dai ka mayar masa da kuɗinsa ko kuma su waɗanda ka siyarwa yanzun su haƙura ka basu kuɗinsu tun kafin magana tayi nisa".

Kusan minti biyar yana zaune ya rasa tunanin da zai kama, Su waye suka siyi gidan? Kuma wanene ma ya siyar musu? Yanzu da Nasir yake cewa ya mayarwa da Alhaji Lawan kuɗinsa ina ya gansu? shi da dubu ɗari ma yanzu sai dai a ɗaure shi dan bashida ita. Watansa biyu rabon daya samu albashi, da yaje yayi ƙorafi sai lokacin ma ya san wai ashe an sake bashi query toh bai ma sani ba balle yaje yayi depending kansa daga amsar da account ɗin kuma ya bashi wai yaje yayi ta addu'a ya san abu ne mai wahala idan bai rasa aikinsa ba.

Abun mamaki kuma, a cikin shirinsa harda barin aikin da zarar abubuwan da yake shiryawa sun tabbata amma kuma sai yaji hankalinsa ya tashi sosai yanzun ko da yake dole, duk abubuwan da yake lissafawar sun ruguje, da kuɗin shagunan Jalilah ya so yayi jari zai fara harkar Import and Export ya gama saita komai amma kuɗi sun ƙi samuwa kamar asiri an rasa mai siyan shagunan duk wanda aka samu sai an fara magana kamar gaske sai wasa ya shigo ciki gashi duk kuɗaɗen da suke account ɗin sa ya kashe su akan auren Zulaiha ɗan canjin daya rage masa ya san ko cikakken cefanen wata ɗaya ba zai musu ba ga wata ya taho gangara itama Hajja zai yi mata nata cefanen ya kuma bata kuɗin da yake bata duk wata.

Wayar daya kashe bayan sun gama magana da Nasir ɗin ya ɗauka da niyyar kunnawa ya kira Jalilah domin dai daga shi sai ita ne a cikin maganar gidan dukda bashida tabbacin samunta a wayar; yau kusan sati biyu kenan rabon da suyi magana tunda ta kirashi ranar tace masa kayan da ta turo sun sauka suna Lagos zata tura masa number wanda zai kira sannan zata tura masa kuɗin da za'ayi clearance shikenan yaji shiru, ya gama shirya da zarar ta tura kuɗin ya dafe su zai sake danna mata block suyi rabuwar ƙarshe sai gashi kwana da kwanaki shiru kuma idan ya kira wayarta a kashe haka ko a Whatsapp baya ganinta.

Ya ɗan shiga damuwa da tunanin ko wani abu ne ya sameta dan har Hafiz ya tambaya ya ce masa tana lafiya sunyi magana, hakan ya bashi mamaki har yayi niyyar ya tambayeshi yaushe sai kuma ya fasa gudun kada Hafiz ɗin y zargi wani abu.

Kunna wayar yayi zuciyarsa ta raya masa daya kira layinta na Nigeria cikin sa'a kuwa yana kira ta shiga murna kamar ya taka rawa sai dai har wayar ta ƙaraci ringing ta katse ba'a amsa ba. Sake kira yayi nan ma shiru bata ɗauka ba, sai kawai ya miƙe ya shiga saka kaya dan dama daga wanka ya fito, a ƙalla tunda ya samu wayar a kunne ai magana ta ƙare komai zai zo da sauƙi.

Yana taje sumar kansa Zulaiha ta shigo ɗakin cikin kwalliyar da idan zata fita kaɗai yake ganinta da ita.

Daga bakin ƙofar ta tsaya tana jifansa da kallon daya fi kama dana raini ta ce
"Zan fita"
"Bada yawuna ba" ya bata amsa yana zura wayarsa a aljihu, tamkar ɗan data haifa haka ta taso masa tana cewa

"Ai kuwa wlh baka isa ba fita kamar naje na dawo, haka kawai; sai kace wata dabba zaka turkeni a gida ba kulawa ba walwala ka kuma hana ƙawaye na zuwa balle na gansu naji daɗi sannan kace ba zan fita waje in shaƙata ba ai wlh kasan ƙarya kakeyi kuwa".

Kallonta ya ringayi dukda tuntuni ya dena mamakinta ya kuma fahimci dagaske wannan itace asalin Zulaiha; Ƙazamar mace, mara kunya kuma mara tarbiyya. Sanin da yayi mata a kamila, nutsattsiya kuma mai kunya duk yaudara ce kamar yanda ta yi nasarar lulluɓe halayyar tata da sunan Aljanu wanda duk sai a hankali da zama ya fara nisawa ya fahimci haka take babu wasu Aljanu ko wata iska

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login