Showing 189001 words to 192000 words out of 257873 words
yanke shawara ba Anty amma In sha Allahu yau zan sanar da ke matsayata". Tayi jimm kamar tana so ta ce wani abu amma kuma ta fasa sai ta ce
"Toh Allah ya sa muji alkhairi" na amsa da "Amin".
"Zaki tanadar masa wani abu ne?" Ta tambayeni, sai da nayi ɗan murmushi kafin na ce
"Sniper kika tanada ko green leaf?"
Ta fashe da dariya ta ce
"Daga abin kirki?"
"Ai ko shi na san sai yayi shakkar cin wani abu a gidan nan yau" na bata amsa ta wuce kitchen tana cewa
"Toh ai shikenan, bari in ɗorawa mijina abinci yana hanya". Tashi nayi na bita na kama mata aikin, hirar duniya muka taɓa tun ina amsawa kaɗan kaɗan har na ware abinda na manta rabon da inyi doguwar magana irin haka harda dariya inaga tun ranar dana dawo daga Camp ɗin NYSC.
BILAL
Tamkar zai fasa kuka ya faɗawa Nasir inda Halima ta ce su haɗu,
"Tare zamuje amma" ya faɗa Nasir ya ce
"Wa? Ni? Idan ka ganni a lahira toh kaini akayi. Ai kayi mai wuyar tunda har ta amince ku haɗu ai akwai haske a lamarin kawai kaci gaba da addu'a shine ya rage yanzu".
Bilal ya goge zufar da ta keto masa dukda sanyin Ac daya cika motar kafin ya ce
"Toh dan Allah zaka rakani gurin Kawun su Zulaiha, ta ce yana son ganina yau saboda ita ma na kashe wayata tun safe idan ba haka ba addabata zatayi da kira".
Dariya Nasir yayi ya ce
"Ita amaryar ce tun yanzu ta fara isarka? Ikon Allah. Haɗe rai Bilal yayi ya zaro wayarsa daga aljihu ya kunnata tun bata gama saituwa ba kuwa sai ga kira ya faɗo ko suna bai fito ba alamar contacts ɗin ma basu gama booting ba amma ya gane number Zulaiha ce. Ya nunawa Nasir yana cewa
"Ka gani ko?" Ai kuwa Nasir ya bushe da dariya ya ce
"Bala'i, sai kace bokanya? Ta hango ka kunna wayar a madubinta. Alamar yayi shiru Bilal ya masa kafin ya amsa wayar, yanda kasan ɗan da ta haifa tanaji ya amsa ta ce
"Wannan wane irin kut****uba ne zaka kashe waya ayi ta kiranka ba'a samu?"
Sai da ya zare wayar daga kunnensa ya duba screen ɗin ga sunanta nan ya fito yanzu DUNIYATA kafin ya sake mayar da ita kunne mamaki na neman kashe shi da jin abinda ta faɗa, ita kuwa ko a jikinta ta balbale shi da masifa akan me y kashe waya gashi nan ya janyo Kawunta ya kira yana ta musu tijara su da Ummansu akan rashin zuwan da bai yi ba.
"Ya ce kazo ka same shi a nan gidan bayan sallar magriba idan kaga dama karka zo na rantse da girman Allah sai ka gane baka da wayo sai na nuna maka kai ƙaramin yen yen ne" ta ƙarƙare maganar kafin ta ja dogon tsaki ta kashe wayar.
Bilal dai kasa cire tasa wayar yayi daga kunne yayi sakato kamar wani wawa tsabar mamaki. Nasir daya gama jin komai, duk yanda ya so ya hana kansa yin dariyar data taso masa dole ya saketa jin tana nema ta shaƙe masa maƙogaro, Bilal ya kalle shi da idon sa da suka kaɗa sukayi jajir sai kawai ya ɓalle murfin motar ya fita waje ya ringa sheƙa dariya kamar wani taɓaɓɓe.
Bilal ya sauke ajiyar zuciya bayan daya ajiye wayar maganganun Zulaihan na masa amsa kuwwa a kunne, a fili ya ce
"Ba ita bace, aljanunta ne suka motsa"
"Aljanu ko?" Nasir daya buɗe kofar motar ya faɗa yana sake sheƙewa da dariyar data fi ta farko. Sai da yayi da gaske kafin ya iya riƙe kansa ganin Bilal ɗin ya cika yayi fam kamar zai fashe. Suna tafi Nasir na cewa
"Amarya, Amarya bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida" shi dai Bilal tafi ka mutu bai ce masa ba har ya sauke shi a ƙofar gidansa.
"Dan Allah ka shirya da wuri" Bilal ya faɗa bayan Nasir ɗin ya sauka, Nasir ya danne dariyarsa kafin ya ce
"Baka da matsala mutumina sai ka zo" ya wuce ciki yana sake tuntsurewa da dariya.
"Daɗi na da gobe saurin zuwa" ya faɗa a fili yana shiga gida.
Bilal kuwa gida ya wuce, sai da ya shiga gidan ya tuna ashe ko breakfast bai yi ba yau ɗin. Sai lokacin ya haɗa tea ya sha da ya ringa jin sa kamar maɗaci, yanzu Allah kaɗai ya san mutum nawa suka san halin da yake ciki. Ƙila har yan unguwar ma sun sani yanzu da ya shigo sai ya ga kamar masu gadin layin daya wuce sunyi gulmar sa gaba ɗaya ya tsargu ji yake kamar duk in da ya wuce kawai kallonsa akeyi amma labari ya gama baza ko ina ga halin sa.
Zuciyarsa ta raya masa komai zai wuce da zarar Halima ta dawo kuma Zulaiha ta tare, musamman tunda dama maganar daga ɓangaren Haliman ta fita idan aka ga ta dawo gidansa hakan zai aka kokonto a zukatan mutane domin da wahala ace bayan wannan abun ya faru kuma ta sake komawa gidansa amma idan akayi haka kuma gashi yayi aure za'a iya cewa ma saboda ƙarin auren ya saka tayi masa yarfe yanda mata suka saba yiwa mazajensu idan zasuyi aure.
Wannan tunanin da yayi ya sanyaya masa zuciya har ya ɗan samu nutsuwa ya shiga kiran Agent ɗin daya bawa tallar shagunan Jalilah. Duk ma abinda zai faru a ƙalla ya tsira da abinda zai riƙe kansa surutun mutane mai wucewa ne da sunyi sun gaji zasuyi shiru. Agent ɗin ya sanar masa an samu mai siyan gurin kuma da daraja sosai dan haka gobe yaje a ƙarƙare magana dan dagaske suke kuma da kuɗin su a hannu.
Wannan labarin ya sake faranta masa rai, yana kashe wayar ya kira Engineer dake aikin gyaran sabon gidan da ya siya wanda Zulaiha zata zauna a ciki. Sabon gini ne bene na zamani wanda har plaster anyi matsuwa ta saka mai shi siyarwa kuma ya same shi kwasha kwasha, ɗan gyara kaɗan akayi na abinda baiyi masa ba, jiya da ya je an gama komai ƙwayayen wuya ake ƙarasa sakawa dan har yaran da zasu share gidan su wanke ya tarar an samo yana kiran Engineer kuwa ya gaya masa ai an gama komai yanzu ya bar gidan muƙullin yana hannun maigadin gidan da yake jikin nasan dama shi ake barwa ya ma tura masa video ta WhatsApp tun ɗazu.
Godiya ya masa, a ransa ya ayyana da gidan zaiyi bikon Halima. In dai ta yarda kawai ita ta koma can idan ya so a canzawa Zulaihan penti ta shiga nan ita tunda babu abinda gidan yayi a matsayinta kuma ko wanda bai kaishi ta samu ba ai sai dai ta godewa Allah ita kuwa Halima dama gidan bene shi ya dace da ita tunda daga cikinsa ta fito.
Ƙarfe shida ya fesa wanka ya tafi gidan Nasir daga can zasu wuce gidansu Zulaiha dukda idan ya tuna abinda ta faɗa masa ɗazun sai ya ji kamar kar ya je sai kuma zuciyarsa ta tuna masa ba laifinta bane iskokin da Ummansu ta faɗa ne suke taɓa ta sa wannan ya taushi zuciyarsa ya isa gidan Nasir ɗin.
"Kaga na Halima angon Zulaiha ga kuma Jalilah a gefe" Nasir ya tsokane shi bayan ya fito, ya haɗe rai tam ya ce
"Bana so"
Nasir ya ɗaga hannu biyu sama ya ce
"Na bari Allah ya baka haƙuri". Suna tafe suna yar hira har suka isa unguwar, sai da suka tsaya sukayi sallar magriba a masallacin layin su Anty Jalilah kafin suka fara wucewa gidansu Zulaiha dan yana sallah ta turo masa text wai ga Kawun fa ya iso.
A tsakar gida suka zaune, Zulaihan da Ummansu sai Nuratu sun sha hijabai kamar masu takaba kowacce ta raɓe a gefe tana zare ido sai Kawun nasu dake zaune kan farar kujerar roba yana girgiza ƙafa. Tare suka isa da Mijin Nuratu wanda shima suka zo tareda wani abokinsa, suka gaisa gaba ɗaya kafin akayi musu iso suka zauna kan tabarmar da aka tanadar musu.
Cewa Kawun yayi Nasir da abokin Faruk Mijin Nuratu su ɗan basu guri.
"Ai komai yana son sirri, dukda ku aminanku ne amma ai akwai abinda ba zaku so suji akan matanku ba ko?" Kawun ya faɗa, Ummansu Zulaiha tayi saurin cewa
"Ai babu wani abu ma"
"Ni dai ban sako bakinki ba idan kuma ba zaki iya yin shiru ba kema ki tashi ki bamu guri" Kawun ya taso mata. Hannunta Zulaiha ta kama cikin alamar tayi shiru, Kawun ya ja tsaki ya ce
"Na san dai dukkaninku ba yara bane tunda kuma kuka yarda har kuka ɗaura aure da yaran nan toh kunji kun gani kuna son su a yanda suke ne musamman kai" ya nuna Bilal. Kallonsa Bilal ɗin yayi yana jira yaji ƙarin bayani Kawu ya cigaba da cewa
"Tone tone dai babu kyau tunda abinda ya faru ya rigada ya wuce amma dukda haka dole in ja musu kunne shiyasa na taraku gaba ɗaya, babu kawo ƙara dan iya shari'ar da nayi a baya masa Allah ya bani lada na gaji. Duk wacce ta muku ba dai dai ba kuci ubanta dai dai gwargwado amma banda dawowa gida iya gatan da zaku musu kenan dan wlh duk wacce ta kuskura aurenta ya mutu ta sani ba sake auruwa zatayi ba dan suma ɗin ba ƙaramin jahadi sukayi ba da suka.... "
"Haba Shafi'u wannan wane irin abu ne?" Ummansu ta sake katse shi. Zulaiha ta ruƙo ta ganin tana shirin miƙewa Nuratu dai na gefe kanta a ƙasa Kawun ya ce
"Mariya, ko dai rufa rufa kuka yiwa yaran nan shiyasa kike ta katseni kar in faɗi gaskiya?"
"Rufa rufar me? Ai duk cikinsu babu wanda bai san tsanar da ka mana ba da irin sharrin da kake bibiyarmu da shi kullum. Kai nake so na rufawa asiri karka zubar da mutunchin ka a gabansu amma ka saki baki bayan duk wanda yake sauraronka yasan tsantsar hassada da baƙin cikin Allah yayiwa yara gata ya basu mazaje irin wanda yayanka basu samu ba shiyasa kake so ka ɓata su toh ta Allah ba taka ba" Umman ta faɗa cikin masifa.
Kawun ma baiyi shiru ba ya ce
"Sai dai ki naɗe tabarmar haukarki da kunya amma ni ɗan gaskiya da gaskiya ne kin sani kuma dole in tabbatar ba'ayi kitso da kwarkwata ba".
Bilal dai kallonsu kawai yake, shi dai Umman da ya sani sama da shekara goma idan aka saka mata hannu ba zata ciza ba amma yau ita ce take tada jijiyar wuya haka tana masifa ana riƙeta kamar zata daki Kawun?
Faruk ne ya ce
"Dan Allah kuyi haƙuri, ni dai a ɓangarena babu wata matsala dan babu abinda Nuratu ta ɓoye mun kuma iyayena basu nema mun aurenta ba sai da sukayi bincike kuma da yardarsu da komai na aureta dan haka ni dai a gurina babu wata matsala In sha Allahu".
Bilal ya kalle shi, kansa ya fara kullewa. Wai toh meye ake cewa an sani da shi bai sani ba?
Zungurinsa Faruk ɗin yayi yayi diriri kafin ya ce
"Nima haka".
"Toh madallah Allah ya taya ku ruƙo sai aje ayita haƙuri. Ranar Asabar in Allah ya kaimu aka ce tariya ko? Dama babu wani taro da za'ayi, mutum biyu sun isa daga kowanne ɓangare suzo su ɗauki amaren" Kawun ya sake faɗa.
Umma ta zauna tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudun tsira, daga nan Kawu ya miƙe ya musu sallama Faruk ma ya fita bayan ya ce Nuratu ta biyo shi aka bar Bilal da Umma sai Zulaiha data sunkuyar da kai kamar wacce take gaban Alƙali. Yafi minti goma ya gagara ce musu komai suma haka sai da Nasir ya kira shi a waya kafin ya miƙe yana musu sallama ko motsi Zulaihan batayi ba Umman ma kamar a tsorace ta masa Allah ya tsare ya fita, a soro ya tarar da su Nuratu tana rungume jikin Faruk tana kuka ya giftasu yaa jin sa yana cewa
"Ki dena kuka, kowa da kalar ƙaddararsa a rayuwa kuma na gaya miki ko me kika aikata a baya ina sonki a haka tunda dai kin tuba kin dena kuma har kika iya faɗa mun na tabbatar dagaske ne kin bari karki ji komai In sha Allahu daga ni har dangina ba zaki samu matsala da kowa ba".
Ya ringa juya maganar a ransa, to ko dai abun iya ita Nuratun ya shafa shiyasa Zulaiha bata gaya masa ba? To menene ma? Ya ringa tambayar kansa a garin tunani har ya wuce gidan Anty Jalilan ma sai da Nasir ya ankarar dashi.
A falon baƙi suka zauna, ya ringa kallon Al'amin da yayi kamar bai sanshi ba dan da suka shiga yana kallon su ya juya ya wuce sai da Nasir ya kira shi ne ya tsaya amma yaƙi zuwa gurin Bilal ɗin Nasir ɗin ma daya riƙe masa hannu bai sake da shi ba Alhaji Sale na shigowa kuma ya fizge ya tafi gurin sa.
Faran faran suka gaisa da Alhaji Salen da bai daɗe da shiga gidan ba daga tafiya, masallaci zai fita sallar isha'i dan haka suka tafi gaba ɗaya. Can falon ya ce a kai musu abinci bayan sun dawo suka ci tare Nasir dai ya ware ya kashi abincin sa Bilal kuwa dukda yana jin yunwa kaɗan ya ci dan haka kawai yake ji kamar wata manaƙisar aka shirya masa idan ba haka ba shida yake da laifi a gurinsu shine harda bashi abinci?
Sai da aka kwashe kwanukan kafin Alhaji Salen ya wuce ciki ya turo musu Halima. Ta shiga da ƙaramar sallama kai a ƙasa kamar farin shigar maita haka Bilal ya zuba mata ido yana kallonta, rabon da ya sakata a ido tun ranar daya kaita gida. Ramar da tayi ta taɓa shi dan sukda hijab ne har ƙasa a jikinta ramarta ta fito ƙarara.
A hankali ta ringa tafiya harta isa kujerar da tafi kusa da ƙofa ta zauna, murya ba amo ta gaida Nasir da tausayinta ya rufe shi lokaci ɗaya. Halima mace yar gayu amma kalli yanda ta lalace lokaci ɗaya ta zama kalar tausayi. Miƙewa yayi ya fita dan ya basu guri, yana rufo ƙofa Bilal ya tashi da sauri ya nufeta, da sauri itama ta miƙe tayi baya ganin rungumarta yake shirinyi.
Ta galla masa hararar da ta saka gabansa faɗuwa domin ko a mafarki bai taɓa ganin ta da irin kallon nan ba.
HALIMA
Ganinsa nayi tamkar baƙin kumurci lokacin daya nufoni, hoton fuskarsa akan cinyar Jalilah ya gifta mun da sauri na miƙe na ja baya ganin yana rungumata.
"Meye haka Halims? Kin san adadin kewarki da nayi kuwa? Dan Allah ki tsaya inji ɗumin ki ko zan samu nutsuwar zuciya nayi kewarki har bansan adadi ba wlh" ya faɗa yana sake nufo ni.
Tsawa na buga masa da dukkan ƙarfin daya rage mun, ya tsaya can a inda yake cikin mamakina, ban damu ba na nuna shi ina cewa
"Ka koma in da ka taso idan ba haka ba zan tafi ba kuma zaka sake samun damar magana dani ba har abadah"
"Haba my Halims sai kace wacce zata mutu?" Ya faɗa yana ja baya bai dai koma kan kujerar daya tashi ba, nayi tsaki na ce
"Ba wasa nakeyi ba, minti goma kake dashi idan kuma ya cika baka nutsu munyi maganar data kawoka ba kada ka tsammaci zaka sake samun irin wannan damar a gaba". Ganin da gaske nake ya saka ya koma kan kujerar ya zauna yana kallo na, nima zama nayi kaina a ƙasa dan ba ƙaramin ƙarfin hali nake ba ji nake kamar an jona mun mayen ƙarfe yana jana in je gare shi amma na dake.
"Wlh Halima duk abinda ya faru ba laifi na bane sharrin shaiɗan ne" ya faɗa yana zamowa daga kujerar kamar zai durƙusa a ƙasa. Ban kalle shi ba ya cigaba da cewa
"Kuma wlh duk abinda kike zato ba haka bane tsakanina da Jalilah. Kawai ƙananan romance ne irin abubuwan da na so mu ringayi lokacin da nake neman aurenki kika ƙi amma wlh ban taɓa kusantarta ba kuma idan baki yarda ba zan kira miki ita ta faɗa miki da bakinta".
Kallonsa nayi ina murmushin da ya fi kuka ciwo na ce
"Amma mai ka ce mun tun a sanda kake neman auren nawa akan hakan? Wane alƙawari ka ɗaukar mun?"
Shiru yayi dan shi bai tuna abinda take magana akai ba, ya san dai ƙi tayi, duk yanda ya kaɗata ya raya ko hannunta ya kama bisa kuskure a lokacin ne kaɗai yake ganin ɓacin ranta har ta iya rufe ido ta masa rashin mutunchi daga baya ya rabu da ita tunda bata so kuma yana samu a wasu gurin a bati ma wasu so suke ya taɓa su.
"Kiyi haƙuri" ya faɗa. Na ɗaga kai na sama saboda hawayen da yake shirin zubo mun sai da suka ɗan tsahirta kafin na kalle shi na ce
"Yanzu ni duk ba wannan maganar nake so muyi ba... "
"Kin haƙura ko my Halims? Ni dama na san soyayyar da kike mun ba zata bari ki yarda a rabamu ba"
"Sonka, soyayyarka kullum maganarka kenan, duk idan zakayi magana sai kace son da nake maka ya saka ko soyayyar da nake maka ba zata bari nayi kaza ba Bilal mai ka ɗauke ni?" Na faɗa ina cije leɓe na. Ya ɗan yi shiru kafin ya ce
"Masoyiyata mana Halims"
"Bilal ka taɓa so na?" Na jefa masa tambayar da take cin raina, ya zaburo zai matso in da nake na ɗaga masa hannu sai ya koma baya yace
"Ina sonki mana Halims ai kema kin sani"
"Mai ya sa duk sanda ka tashi magana baka taɓa cewa nayi abu saboda son da kake yi mun ba sai dai kace saboda son da nake maka" na sake jefa masa wata tambayar.
Kamar an doki bakinsa maganar ta fito
"Saboda son ki ya fi nawa yawa".
Da hannu biyu ya dafe baki bayan daya fuskanci abinda ya faɗa. Na saki murmushin daya taho tareda hawayen da nake ta riƙewa na sake ɗaga masa hannu ganin ya sakw nufoni yana cewa
"Wlh ba abinda zan faɗa ba kenan, cewa zanyi