Showing 141001 words to 144000 words out of 257873 words

Chapter 48 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

502

bargo sannan ya koma kan kujerar dake gaban gadon ya zauna yana kallona.

Har ya sauka Lagos zuciyarsa babu daɗi gaba ɗaya hankalin sa na ga son sanin dalilin zuwan Halima gida da sassafe haka da kuma yanayin daya ganta a ciki. Yana so ya kira Mama yaji ko ta faɗa mata wani abu amma kuma baya son yaji abinda zai ɗaga masa hankali ya hanshi nutsuwar yin abinda zajeyi Lagos ɗin. Da zai shiga meeting ya saka wayarsa a Flight mood dan haka sai bayan Magriba lokacin sun tashi gaba ɗaya ya shiga hotel room ɗin sa kafin ya buɗe wayar yana so ya kira wani Abokinsa, Network na daidaita kuma saƙon Mama ya faɗo tana gaya masa Halina na Asibiti sun sameta a sume a ɗaki har lokacin kuma dukda bai san ƙarfe nawa ta tura saƙon ba bata farka ba kuma likita yaƙi ce musu komai yace dashi zai yi magana.

Cikin tsananin tashin hankali ya shiga neman layin Maman amma bai samu ba dan haka ya mayar da akalar kiran kan Mu'azzam wanda bugu ɗaya ya ɗauka kuma yanda ya jishi da bayanin da ya masa akan yanayin Haliman ya saka yaji ba zai iya ƙara koda awa ɗaya a Lagos ɗin ba duk kuwa da bai kammala uzurin da yaje yi ba, sai dai yayi rashin sa'ar rasa jirgi, haka ya kwana a zaune tamkar yanda suma a Kano suka kwana cikin tashin hankali da zullumin halin da Halima take ciki da gari ya waye kuwa ko wanka bai tsaya yiba ya hawo jirgi ya taho musamman yanda Mama ta kira tana rusa masa kuka akan yayiwa likita magana ita dai ayi mata bayanin halin da yarta take ciki idan ma mutuwa tayi a gaya mata kawai saboda tunda aka kawota take nan kwance kan gado bata motsa ba gara ta sani in mutuwa tayi ta ɗauki dangana a basu gawarta su wuce gida su mata sutura.

Koda yazo ma babu wani gamsasshen bayani daya samu daga bakin likitan, abinda ya gaya masa kawai zuciyar Haliman ta kumbura kuma jininta yayi hau sosai wanda yayi sanadiyyar samun partial stroke da tayi sannan ta shiga doguwar suma. Shi dai Abba daya gama sauraronsa saida ya kwashi kusan minti goma a zaune kafin ya iya buɗe baki yayi magana tsabar yanda ya shiga shock, suna raye a duniya wace irin damuwa ce haka Halima take da ita da har take barazana ga rayuwarta amma basu sani ba?

Dr ne ya ringa kwantar masa da hankalin ganin yanda jikin sa yayi laƙwas ya kasa cewa komai sai ajiyar numfashi kawai yakeyi. Haka nan ya shanye maganar a cikin sa duk yanda Mama ta ringa nacin ya faɗa mata yanda sukayi da likitan amma yace mata babu komai, ta kaɗa ta raya tayi kukan duk a banza yaƙi faɗa mata domin ya san damuwar da take ciki a yanzu kaɗan ce akan ya sanar mata da ainihin halin da Haliman take ciki.

Buɗe ƙofar da akayi ya sake ya dawo daga dogon tunanin daya tafi, Alh Saleh mijin Anty Labiba ya tsaya daga bakin ƙofar yana cewa
"Dan Allah Alhaji kazo kayi mata magana ko kai zata saurareka" sai ya miƙe yana cewa
"Wacece"
"Labiba mana, gata nan wai gidansu Mijin Halima zata tafi" ya bashi amsa jin haka ya saka Abba ya fita da sauri dan dama tunda ya dawo ya tarar da rigimar Anty Labiba taje har can gidan Bilal bata same shi ba ranar da aka kai Haliman asibiti taji ba'asin me yayi mata shine yanzun ma ta tada bala'i kamar zata hau iskokai Mama da Mama Fauziyya na riƙeta tana fizgewa wai gidansu Bilal zata tafi idan ma bata same shi ba sai ta saka an ɗaure Hajja ai dole ya fito duk ma inda ya shiga ya musu bayanin abinda yayiwa Halima.

Tsawa Abba ya daka mata ganin yanda ake riƙeta tana fizgewa duk ta tara mutane sun tsaya suna kallonsu, ta fashe da kuka tace
"Na rantse da girman Allah bai isa ya kasheta yaci banza ba har in wani abu ya samu Halima wlh sai na ɗaukar mata fansa akansa". Cikin faɗa Abba yace

"Bana son shashanci Labiba da girman ki zaki ringa abu kamar wata ƙaramar yarinya shikenan Allah ba zai jarabci bawa da lalura ba sai wani ya zama sila? Kada na sake ji, ku tashi ma ku wuce gida kawai tunda hayaniya zaki tayarwa da mutane". Haka ya tattarasu duka da sauran yan dubiyar da suka zo dukda babu wanda ake bari yana ganinta bayan su amma dangi kamar masu jira ana cewa bata da lafiya suke ta tururuwar zuwa dubiya, gashi dai babu wanda ya san takamaiman abinda yake damunta haka nan duk wanda yazo ya tafi zai haɗa nasa kalar labarin da ciwon da zai ɗora mata, amma dai maganar data fi ƙarfi ta kuma fi shahara a gari ita ce Guba ta ci saboda Bilal zai ƙara aure kamar yanda wacce ta fara kai labari Galadanci can gidan kakannita tace daga majiya mai ƙarfi ta samo bayanin gurin ɗaya daga cikin ƙannen Bilal.

BILAL

Bayan daya sauke su kai tsaye gidan Hajja ya nufa, tuƙi kawai yake amma bashi da nutsuwa a tattare dashi. Tsakanin sa Allah tun waccen ranar da Halima ta bankaɗo sirrinsa yake jinsa tamkar tsirara yake yawo, kamar kowa ma yasan abinda yake aikatawa a ɓoye. Koda da yake nuna tamkar komai ba komai bane kawai yana yi ne saboda ya ceci kansa amma shi kaɗai yasan kalar kunya da nadamar da yake ciki a yanzu. Tsautsayi da ƙaddara ya saka koda ya lura ya bar wayarsa a gida bai koma ya ɗakko ba saboda yasan Halima bata da ɗabi'ar bibiyar masa waya ko lokacin da baya saka password babu ruwanta da wayar sa balle yanzu daya kulleta ya kuma san babu ta yanda za'ayi ta iya buɗewa koda ace ma tayi niyyar hakan.

A tsakar gida ya tarar dasu Fadila tsaye da akwatinta tana ganin sa tace
"Yawwa gashi nan ma yazo ai" Hajja tace
"Kai kuwa ina ka jefa wayarka tun asuba nake kira baka amsa ba ko ka manta sammako zatayi? Shiyasa fa tuntuni nace ka bata kuɗin motar ta a hannu saboda irin haka yanzu da ƙyar idan zata samu motar farko sai tayi jira wata ta cika".

Cikin falo ya shige ba tareda ya amsa ta ba ya zauna kan kujera haɗi da dafe kansa da hannu biyu, Hajja ta shiga tana cewa
"Au ina magana shine zaka shige ɗaki ko ka amsa ni?"

"Ai tafiyar tata ba zata yuwu ba ma Hajja" ya faɗa yana gyara zama, sai ta zauna itama tana cewa
"Saboda me?"
"Mun ɗan samu matsala ne da Halima ta tafi gida, kinga kuma idan ta tafi ai ba zai yuwu ki zauna ke kaɗai ba tunda har yanzu jikin ki da saura" ya bata amsa. Sai kuwa ta zabura tace

"Kaji yar abu ta kazan uba au saboda zanzo gidan shine tayi yaji?"

"Bafa dalilin zuwanki bane" yayi saurin katseta, Fadila tayi tsugul tace
"Wlh saboda haka ne dama ai na gaya miki wlh da wahala ta yarda ki zauna a gidan nan dan ji take kamar na ubanta bata so kowa ya shiga sai ita da danginta".

"Ke, waya sako bakinki ko sa'anninki ne suke magana?" Ya faɗa yana ballawa Fadilan harara, Hajja ta taso masa itama tana cewa
"Ko ba'a sako da ita ba ai gaskiya ta faɗa, to kuwa bata isa ta hanani zuwa gidan ka ba billahilazi tunda haka ta zaɓa to kuwa ta tafi kenan sai ka tafa mata resit ka bita dashi kaga sai tayi zama mai lasisi kai kuma ka samu sarari ka auro mutuniyar kirki da suka gaji arziƙi ka saka ina dama duk ita ta kanainaye komai da anyi magana kace Halima to yanzu ta tafi Kuma in dai da yarda ne kar ta sake dawowa cikin gidanka ya isa kuma haka a canza sheƙa".

Shiru yayi kansa a ƙasa, ya za'ayi Hajja tace ya saki Halima? Sannan kuma tayaya zai gaya mata shi fa ko aure zaiyi ba Jalila zai aura ba ko dan bata san ainihin alaƙar dake tsakaninsa a Jalila bane?

Miƙewa yayi a a sanyaye yana cewa
"Idan ta huce dai na san zata dawo"
"Ta dawo ina? Ai wlh kaji ma na rantse ta tafi kenan. Ba dai dama ni na dage sai ka aureta ba na ɗauka dangin arziƙi ne ashe duk shigo shigo ba zurfi suka mana, tunda kuwa yanzu ta saka ƙafarta ta tafi to kuwa ba zata dawo ba kama cireta maza daga ranka ka tattara hankalinka kan wannan yarinya Jalila ayi maza ayi komai ita kuma can su ƙarata Allah sauki tsiya lafiya".

Da wata sabuwar damuwar ya fito daga gidan Hajja, can gefen hanya ya gangare ya kashe mota ya kife kansa jikin sitiyari ya tafi tunanin haɗuwar sa da Jalila.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 36*

Ƙaddara da kwaɗayi haɗi da son zuciya irin nasa ya janyo masa faɗawa tarkon nadama. Dukda dai tsohon halin sa ne, a baya lokacin samartaka ya kan kwatanta domin rage zafi kamar yanda hakan yake ɗabi'ar dayawan Samari a wannan zamanin. Sun ɗauki hakan a matsayin wayo ko dabara a ganin su ai basu aikata Zina a zahiri ba sai dai suna mantawa da hanin ubangiji da yace kada a kusanci Zina ba wai kada a aikatata ba Aa kwata kwata kada a kusanci duk wani abu da yake da jiɓi da ita. Da yawan su sun ɗauki hakan a matsayin ƙaramin zunubi domin wasu basu ma yarda cewa dasu da wanda ya keta haddin macen da ba halalinsa basu da banbancin zunubi. Su kan manta ita kanta Zina ta kasu kashi da yawa, a ciki akwai Zinar idanu da kuma ta baki da kunnuwa wadda suke aikatawa domin kuwa suna kallon haram, su saurari haram su kuma furta haram da bakunan su wanda illolin hakan dai dai suke da wanda yayi fasiƙanci da mace a zahiri.

Ko farkon haɗuwar sa da Halima ya so ya gabatar mata da irin wannan soyayyar sai dai bata bashi fuskar hakan ba shima kuma bai takura mata ba daga baya ma kuma ya tuba ya bari har zuwa lokacin da sukayi aure kafin lokaci ɗaya Jalila ta faɗo rayuwarsa ta wargaza komai ta sake jansa ruwa har ta kaishi da aikata abubawan da suka zarce waɗanda yake aikatawa a baya.

Silar Hafiz ya haɗu da Jalila, ita ɗin tsohuwar budurwar Hafiz ce tare sukayi karatu a London dan har an saka musu ranar aure ya rage saura watanni aka fasa sakamakon ganinta da mahaifinsa yayi tareda wani abokinsa a France sunje wani taron kasuwanci ita kuma tayiwa Abokin nasa rakiya wanda ya kasance Sugar Dadynta.

Hafiz bai taɓa sanin baɗinin Jalila ba, dukda ya san macece me rawar kai dan shi yake tsawatar mata abubuwa da yawa saboda son da take masa kuma take ragewa kuma da yake shi ɗin bai zo mata da fuskar da zasuyi irin rayuwar da takeyi a bayan idonsa ba sai ta ɓoye masa zahirinta, ko da wasa bai taɓa sanin irin rashin jin da takeyi ba sai bayan da mahaifin ya kirashi ya gaya masa babu maganar aure a tsakaninsa da ita ya nemo wata matar yar gidan mutunchi tunda wuri. Koda Dady ya sanar masa sa abinda idon sa ya gani ma da farko har ransa bai yarda ba dukda ya san babu wani dalili da zai saka Dady ya masa ƙarya ko ya hanshi aurenta. Sai sa ya ringa bibiyar takunta a hankali komai ya fito ya gane zahirin wacece ita ya mata kaca kaca suka raba hanya a lokacin har kusan rataye kanta tayi saboda yanda take masifar Son sa, tayi rantsuwa da yi masa alƙawarin zata daina duk wani abu da takeyi in har zai aureta amma yace la la, in taga dama ta tuba saboda Allah amma ba dan shi ba domin ba zai taɓa aurenta ba bayan yasan wacece ita.

Haka nan tayi naci, Tun tana bibiyarsa harta haƙura ta ƙyale shi tana ji tana gani ya fara soyayya da Yasmin har suka yi aure daga ƙarshe ma ya bar Abuja ya dawo aiki a Kano. A hankali bayan wani lokaci da naci da bin binin da take masa ya fara sauraronta suna gaisawa a matsayin abokai kamar yanda suka faro tun asali kafin soyayya ta shiga tsakanin su, har ranta tana fatan a hankali ta shawo ya amince ko a ta biyun ne ya aure ta bata damu ba dan tana tsananin son Hafiz sai dai shi clearly ya gaya mata kada ta yaudari kanta domin ba zai taɓa aurenta ba. Ko da ya ke sauraronta a yanzu ma saboda yaga alamun ta kintsune saboda ya rage mata raɗaɗin takunkumin da iyayenta suka saka mata tun bayanfallasar asirinta da fasa aurensu yake yake sauraronta yana Kuma ƙara yi mata nasiha da nusar da ita gaskiya.

Jalila bata rasa komai ba domin mahaifinta hamshaƙin mai kuɗi ne haka mahaifiyar ta data kasance Balarabiya itama mai kuɗin kanta ce. Babu abinda suka rageta dashi a rayuwa kusan ma gatan da ya mata yawa yana da nasaba da silar lalacewarta. Tun tana secondary school take riƙe manyan kuɗaɗen da suka shallake shekarunta tafiyarta Turai karatu kuma ya sake bata yanci a nan ta haɗu da ƙawayen da suka buɗe mata ido da maza, da kuɗin ta take amfani ta mallaki duk saurayin da yayi mata idan ta gama yayinsa ta sallame shi ta ɗakko wani kusan Abokin Dadyn Hafiz shi kaɗai ne saurayin da ta taɓa yi babba kuma mai kuɗin kansa wanda shima wayewar sa da yanda ya iya soyayya irin wacce take so ta jata harta biye masa suke fita ƙasashe tare har hakan ya zamo silar tonuwar asirinta.

Yanda suka haɗu da Bilal kuwa lokuta da dama musamman idan zata tafi Umarah yawanci ta Kano take tashi dan haka a duk sanda ta shigo Kanon Hafiz take nema idan tana buƙatar wani abu, a irin haka wani lokaci ta dawo daga Saudiyya lokacin Matar Hafiz ɗin ta haihu suna tare da Bilal ta kirashi akan yazo Airport zai karɓi saƙo wa Baby a lokacin har yace ba zaije ba sai dai kuma ya canza shawara da yayi tunani ko babu komai bai kamata ya wulaƙanta ta ba tunda ya san bashi ya ɗora mata sonsa ba daga Allah ne duk kuma irin cin kashi da tijarar daya mata a baya bata saka ta fita a sabgarsa ba shiya kawai yake jurewa yana biye mata lokutan.

Tare sukaje da Bilal ɗin suka amso saƙon wannan kuma shine haɗuwar su ta farko dukda gaisawa kawai sukayi sama sama suka wuce. Ba'a fi wata ɗaya ba bayan nan ta sake zuwa Kano bikin wata ƙawar ta nan ma ta kira Hafiz akan yayi mata booking hotel bayan ta sauka kuma ta sake kiransa akan ta fasa can gidan bikin zata sauka dan Allah ya zo ya kaita yace ba zaije ba, data ringa masa magiya kawai yace mata toh ya kashe wayar. Bilal da duk yaji yanda sukayi ya shiga bashi baki akan bai kamata ya ringa wulaƙanta ta haka ba duk wanda ya ga yanda take kallonsa yasan tana son sa dan haka ko baya jinta a ransa ya ringa nuna kulawa tunda dai abu ne na lokaci ba wai kullum ne take zuwa inda yake ba, daga ƙarshe da Hafiz ɗin yace shi fa ba zaije ba shine yace shi ya bashi mota yaje ya kaita toh, haka kuwa akayi ya bashi mota da number yaje ya ɗauke ta. Kwana ukun da tayi a Kanon shi ya ringa jigila da ita yawon biki har suka gama ta tafi har sannan kuma babu wata shaƙuwa a tsakanin su kwatsam bayan nan suka sake haɗuwa a Abuja lokacin da yaje wani workshop.

A reception ɗin hotel ɗin da aka sauke su ya ganta, sai da yayi mata dogon bayani ma kafin ta gane shi sai kuma suka shiga hira har tayi masa godiyar hidimar da yayi da ita a Kano da zata wuce ta karɓi number sa shikenan da dare kawai ta kirashi tace ko zasu fita yaga gari kar yayi ta zama a hotel tunda yace mata bai san ko ina ba sai gidan su Hafiz da gidan Babban Yayansu shi kuma a lokacin ma suna Kano sunje hutu. Ranar ta fita dashi suka sha yawo tayo masa shopping kayan sakawa har da waya Iphone dan lokacin keypad ce a hannunsa bayan an ƙwace masa waya da babur. Sai da ta jera kwana uku tana fita dashi kullum kuma haka zata yo masa siyayya kamar bata san ciwon kuɗi ba a kwana na ukun kuma ya gama abinda ya kaishi amma tace masa ya zauna ya sake hutawa mana tunda dai ba wani abu zaiyi idan ya dawo Kanon ba kuma yace matarsa ma tana gida taje wanka.

A lokacin ta fito fili ta faɗa masa ita fa tunda bata samu Hafiz ba zatayi madadi dashi domin duk abinda take so a gurin Hafiz yana dashi har ma yafi Hafiz iya kalaman soyayya, da aure tazo masa dan da ace ya amince tun a lokacin da ƙila kafin Halima ta dawo daga wanka zai auri Jalila amma sai yaƙi ya kawo mata uzurin bai jima dayin aure ba yasan ba lallai mahaifiyar sa ta yarda ba da sauran uzuri dai amma ta bashi wata shida zuwa shekara ɗaya zuwa lokacin ya sun shekara uku da aure ya san babu wanda zaiyi wani surutu dan yace zai ƙara wata matar. Ta yarda da hakan, musamman da itama ya yarda da nata Sharaɗin na yi mata duk abinda take so duk ya ce ba zai taɓa kusantarta ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login