Showing 111001 words to 114000 words out of 257873 words
ƙaruwa, tun magriba na shiga ɗaki na kwanta da sunan kaina yana mun ciwo amma a zahiri maganganun Anty Labiba na shiga ɗaki na ke ta tusawa a ƙwaƙwalwa ta. Ina buɗe ƙofa Mu'azzam na turowa da Al'amin ɗin a hannun sa ya miƙo mun shi yana cewa
"Ungo ɗanki mun gaji" na karɓe shi na koma ciki. Ina tsaka da shayar da shi Mama ta shigo ɗakin da tafasasshen ruwa a bokiti ta ajiye ta sake fita ta dawo da baho. Wanka ta masa da ruwa masu ɗan banzan zafi ya ringa canyara kuka fatar jikin za ta yi jajir har ƙwalla na yi ita kuwa ko a jikin ta, kafin ta gama shirya shi ya yi bacci. Ta kwantar da shi tana cewa
"Yanzu Fauziyya ta kira waya ta ji kukan sa shine Baba Jummai ta ce duk yanda aka yi wanka ne ba'a masa ba ko kuma ruwan babu zafi yanda ya saba ji"
"Amma fa Mama likitoci sun ce a dena saka musu ruwa me zafi sosai wankan yammar ma su suka ce a dena masa ai" na faɗa ba tare da na kalle ta ba. Ta harare ni ta ce
"Da ruwan zafin na kisa da baki girma kin kawo yanzu har kin haife shi ba, ni tun jiyan ma sha'afa na yi kema haka kika ringa mana wannan kukan sai da Goggo Habi ta zo ta fara gasa ki haka sannan muka samu lafiya to irin ƙashin ki ya gado, kuma na ga har yanzu idan kika gaji in ba kinyi wankan da ruwa mai zafi ba bakya iya bacci".
Shiru na yi dan gaskiya ta faɗa, da na taho na ce na yada wanka amma tun jiyan da jikina ya fara gaya mun babu wanda ya tuna mun na saka Zainab ta ɗora mun ruwa a gas ɗin waje na girkin sallah yana tafasa na cewa Mama ruwa ya tafasa ta saka aka tsinko ganye a waje ta mun wankan sannan na ji daidai a jiki na.
Cikin bacci na ji kamar waya ta tana ƙara, ido a rufe na laluba na janyo ta daga ƙasan pillow da nake kai. 'My world' da na gani ya saka na wartsake ba shiri na tashi zaune. Sai da ta katse ya sake kira, wani ɓangare na zuciya ta na hanani da in amsa wayar amma gefen dake cike da bege da kewar sa ta ingizani na danna.
"Fushi dai har yanzu My Halims" ya faɗa cikin wani sauti da ya sakani sakin ajiyar zuciya ba tare da na shirya ba, ban amsa shi ba na yi shiru. Ya yi murmushi mai sauti da na ji har ƙasan zuciya ta kafin ya ce
"Allah ya huci zuciyar Hali dubu fitila mai haska duniyar Bilal".
Da sauri na toshe baki na saboda murmushin da ke shirin kufce mun, kamar ya ji ya ce
"Nasan dariya kike yi, ni dama na sani ba zaki iya dogon fushi da ni ba".
"Oh, haka ma ka ce?" Na faɗa a shagwaɓe, ya ce
"Yes, na shaida kina So na, masoyi kuma baya fushi da abin ƙaunar sa ai".
"Hmmm, da wannan kake fakewa kenan kana mun duk abinda kaga dama tunda ka san ina son ka" na faɗa cikin karyewar sauti, so na ke ya ce mun ba haka ba ne, ya bani amsar da zata shafe maganganun Anty Labiba amma maimakon haka sai ya canza maganar da cewa
"Tun jiya baki kira kin ji ya na sauka ba, ina Al'amin? Ya ji daɗin gadon Mama ya dena kukan banza ko?"
Kasa ce masa komai na yi shima bai damu ba ya sake cewa
"Ɗazu Oga Hafiz ya ke ce mun sun zo tare da Madam sun kawo muku tsarabar Finland, Al'amin ya sha kaya na sa ni" ya faɗi ainihin dalilin kiran wayar, sai na saki murmushin takaici na cije leɓe na na ce
"Ai kuwa dai, sun zo, sun kawo masa kaya ya kuma gode dama abin da ka kira ka tambaya kenan?"
"Kamar ya ya abinda na kira na tambaya kenan haka na ce miki? Ai ke ya kamata ma ki kira ni tun sanda suka zo ɗin ki gaya mun ba wai ki jira sai ni na kira ki ba. Kuma ni ba dalilin da ya saka na kira ki ba kenan saboda ina so naji muryar ki ne tunda kin fara ɗaukar zugar mutane kin canza hali".
"Bacci na ke ji zamu yi magana da safe idan Allah ya kaimu" na faɗa saboda wani yanayi da naji yana taso mun na san a kowanne lokaci zan iya fashewa da kuka. Yayi shiru kafin ya ce
"Shikenan, Allah ya tashe mu lafiya" ya katse wayar ba tareda ya tsaya ya tambaye ni me yake damuna ko ya lallashe ni ba. Kife kaina nayi a pillow na fashe da kukan da takamimai ban san dalilin yin sa ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 28*
Washe gari da wuri na fara haɗa kayan mu dan komawa gidan Anty Labiba duk da jirgin dare su Mama zasu bi amma da wuri nake so na tafi can ɗin dan ko rakiya ba zan tsaya yi musu ba. Gaba ɗaya raina babu daɗi na tashi, na ɗauka Bilal zai sake kira na daga baya ko kuma da asuba amma shiru. Ina zuge akwatin kaya na Zainab ta shigo ta ce mun na zo na yi baƙi, na ɗora mayafin doguwar rigar yadin jiki na ina ƙoƙarin kawar da ɓacin ran dake kwance akan fuskata na fita falon.
Turus na yi a bakin ƙofa ganin Fadila da wata mata da na ga suna yanayin kama sai kuma wata tsohuwa da ita ma ban gama tantance fuskarta ba. Sake tattaro fushin dana ɗauke a kan fuskata na yi na maido da shi na ƙarasa da sallama ciki ciki. Da "ina kwana" na gaishe su baki ɗaya matar ta amsa fuskar ta ɗauke da fara'a Fadila kuma ta gaishe ni baki a kumbure kamar an mata dole. Sai bayan na zauna na gane tsohuwar Lanti ce wacce suka je gida na tare da Hajja har suka yi faɗa da Baba Jummai.
Kamar dole Fadilan ta ce
"Dama Anty Sa'adatu ce ta zo shine Hajja ta ce a rakota ta ga Aminu". Na watsa mata wani kallo jin yanda ta ambaci Aminun garangatsau kana ji kasan da rashin mutunchi ta yi abun dama, matar ta harare ta ta ce
"Haka ake kiran sa dama?"
"Sunan sa kenan ai Anty" ta bata amsa tana ƙoƙarin sakko yaron ta daga baya. Girgiza kai kawai na yi a raina ina takaicin sakewa yarinyar tun farko, da nasan haka take bata da mutunchi da wlh bata isa na mata abubuwan da na mata a baya ba. Mayafin da ke jikin ta ma nawa ne daga aro na ma manta da shi sai yanzun tun da mukayi aure hatta da plates da cups sai da na ƙara mata a cikin nawa da muka je gidan ta naga duk tarkace ne natan ba wasu na ƙwarai ba ni a ganina an zama ɗaya ina da su har sun mun yawa na ɗibar mata amma tun daga zuwan da ta mana ta tafi ta ƙulla mun sharri ta fita a kaina ita ma kuma ta dena ɓoye ɓoye ta fito mun a asalin halin ta yanzu.
"Ina maigidan nawa ne ko bacci ya ke yi?" Matar ta katse mun tunani, na ji kamar na ce mata Eh baccin yake kuma ba za'a ɗakko shi ba amma hakan sai ta mun kwarjini dan haka na miƙe na wuce falon Abba bayan na ce mata bari na karɓo shi.
Sai bayan da Mama ta fito kafin Fadila da Lanti suka gabatar mata da matar da suka zo tare a matsayin ƙanwar Hajja ta Jos, dama ni ɗaki kom na cigaba da abinda nake yi. A ɗakin Fadila ta tarar dani, ban ko ɗaga kai na kalle ta daga danna wayar da nake yi ba. Ta gama kalle kallenta kamar tayi ajiyar wani abu kafin ta ceygg
"Hajja ta ce idan mun zo ki nuna mun kayan da Yaya Hafiz ya kawo muku".
Ban ko yi motsin da zai nuna mata alamar na ji me ta faɗa ba, a raina kuwa juya maganar na ringayi. Hajja tace na nuna mata kayan da Hafiz ya kawo, to ya akayi ta sani? Sai dai idan Bilal ne ya gaya mata shine zata turo ta tunda shi bai gani ba su suzo su gani ko?
Wane ɓangare na zuciya ta ya shiga ƙoƙarin kare Bilal ta hanyar gwada mun ba shi ya turo su ba amma kuma tunani mafi rinjaye shi ɗin ne tunda ina da tabbacin Hafiz dai ba zai je ko ya kira su ya faɗa musu ba.
"Zan je na faɗa mata kin ce na ƙarfi ne idan muna da gado a ciki mu taru mu ƙwata" ta sake faɗa kamar wata yarinya ƙarama.
Sai lokacin na kalle ta, murmushin takaici ya ƙwace mun na girgiza kai na ce
"Ai ba yau zan fara sanin ke ɗin maƙaryaciya bace kuma masharranciya, kije ki faɗi hakan ni yanzu bani da lokacin ki" na kwanta haɗi da juya mata baya. Ina ji ta ja ƙwafa kafin ta fita ta bugo mun ƙofa, da Zainab ta sake zuwa akan nazo muyi sallama zasu tafi ce mata nayi ta ce ina banɗaki kawai. Sai da na tabbatar sun bar gidan kafin na fito falo Mama ta bani dubu goma da turmin Atamfa Holland sai riguna masu kyau guda uku in ji Hajiya Sa'adatu.
"Ai da kin ɗakko mata ta gani dai tun da har ta tambaya" Mama ta faɗa bayan da na gaya mata yanda muka yi da Fadila, na taɓe baki kawai ba tare da na ce komai ba. Da gaske ban shirya sake ɗaukar kowanne wulaƙanci daga gurin su ba, ko Anty Labiba ba ta ce na tashi na ƙwaci yancina ba nima a karan kaina na ƙosa da abinda Hajja da yayanta suke yi mun, ko zan ɗaga wa wani ƙafa a cikin su yanzu ita Hajjan ce darajar ta haifi Bilal, bayan haka babu wani da zan sake takurawa kaina akan sai ya so ni, miji na ne kaɗai zan tabbatar da soyayyar sa gare ni ko ta halin ya ya.
Sai bayan la'asar na tafi gidan Anty Labiba saboda Abba da na yi ta jira ya dawo muyi sallama. A ɗakin ta ta sauke ni, tun kuma daga zuwa na na san yanzu ne zan yi jegon gaske, gyaran da nake ta zullumin ta ina zan fara da na zauna a can gida na nasan duk zata yi mun.
Har muka kwanta ina jiran tsammanin kiran Bilal ko dan zuwan su Fadila amma na ji shiru, sai da asubar washe gari na ga missed calls ɗin sa kiran kuma gurin ƙarfe biyu da rabi aka yi shi. Ban bi sahu ba na watsar da shi kuma ni da kaina na yi mamakin yanda na iya share shi duk da yanda zuciya ta take azazzalata da kewar sa da kuma son jin muryar sa amma na kanne, ina so na tabbatar da gaske ni kaɗai na ke haukana akan Bilal kamar yanda kowa yake cewa ko kuwa ba haka bane?
Ina cikin karyawa ya sake kira, ji na yi kamar an yi mun yayyafin ruwan sanyi, na saci kallon Anty Labiba dake rirriga Al'amin naga sam hankalin ta baya kaina, dama shayi ya rage ban ƙarasa shanyewa ba dan haka na miƙe da kofin har kuma na shige ɗaki aka yi sa'a bata ce mun komai ba. Ajiye wayar na yi ganin ta katse kafin na kai ga amsawa na cigaba da kurɓar shayin da ya daina mun daɗi a baki, na saki ajiyar zuciya jin wayar ta sake ɗaukar ƙara, duk da haka sai da ma ɗan ja aji kafin na amsa cikin shan ƙamshi.
"Lallai kin ji daɗin gida wato sai yanzu ma kika tashi" ya faɗa bayan da na amsa sallamar da ya farayi, gaishe shi na shiga yi ya amsa kafin ya sake cewa
"Ina fatan dai yanzu zuciyar gimbiya ta yi sanyi?"
"Da na ce maka zuciya ta tayi zafi ne?" Na faɗa sai ya sake kwantar da murya ya ce
"Shekaran jiya, daga kalamanki na san bakya cikin yanayi me daɗi a lokacin shiyasa na barki har tsayin jiya ki huta amma na kasa jurewa cikin dare bacci ya gaza ɗauka ta na kira ki amma baki amsa ba" ya ƙarasa da wani munafukin sauti kamar me shirin fashewa da kuka. Take jiki na ya hau tsuma, So da muradin kasancewa tare da shi irin wanda na ke ciki a koda yaushe suka motsa mun. Nima na narke murya na ce
"Ashe ma ka fahimci bana cikin yanayi mai daɗi amma ka kasa tsayawa ka lallashe ni"
"Ba haka bane" ya faɗa nayi saurin katse shi da cewa
"To yaya ne? Saboda bani da muhimmanci ne ko?" Na ƙarasa ina fashewa da kukan kissa. Tamkar lokacin yammatanci haka ya rikice ya shiga rarrashi na, ni kuma na samu yanda nake so na cigaba da kukan ina faɗar maganganun da na tabbatar zasu ƙara hargitsa masa tunani. Mun fi minti talatin muna waya yana rarrashi na ina ƙara botsarewa har kuma muka gama ban ji ya sako zancen zuwan su Fadila ba dan da farko na zata ko ta kai gulmar ne shi ne ya biyo kadi ashe ba haka ba ne.
Wunin ranar da sauran ranakun da suka biyo bayan ta cikin farin ciki na yi su saboda yanda Bilal ya rikice akan boren da na tayar masa, bini bini zai kira ni ya cigaba da bani haƙuri da maganganu masu daɗi haɗi da tsayawa a zuciya.
Kwanan mu uku a gidan Anty Labiba wanda ya kama kwanan Bilal biyar a Abuja ya gaya mun zai dawo jibi, kwanaki bakwai kenan kamar yanda dama ya sanar mun zai yi.
"Me zan samu idan na dawo My Halims? Kin san nayi kewar ki da yawa har ban san iyaka ba" ya faɗa cikin marairaicewa, maganar da yayi ta sa na ji ina ma ina can gida na zai dawo dan gaskiya nima nayi kewar sa da gaske musamman yanzu da nake ganin komai ya dai daitu idan ya dawo zamu cigaba da gudanar da rayuwa ne irin yanda na ke mafarkin kasancewa da shi.
Na sake nitsewa cikin gadon da nake kwance kafin na ce
"Nima na yi kewar ka sosai, zan girka maka duka favourites, har da alawar madara da Iloka zan yi maka" na ƙarasa cikin dariyar tsokana"
"Amma kin san ba abinda nake nufi kenan ba ko? Wane kalar abinci ne bana ci kin san a in da na sauka kuwa a Abuja kin san kalar daɗin abincin su?" Cewar Bilal. A shagwaɓe na ce
"Kana nufin abincin su ya fiye maka nawa daɗi kuma baka kewar girki na kenan?"
"Ba haka nake nufin ba ai kin sani a guri na komai na ki daban ne kawai dai ina gaya miki akwai abin da zan iya samu a ko ina akwai kuma wanda a gurin kaɗai zan samu na ci na ƙoshi kuma ya gamsar da ni".
Da maganar, da yanda ya yi maganar sai da na rufe ido saboda nauyi da kunyar da suka saukar mun, ina jin sa yana cewa
"Kawai ki san yanda zakiyi da ni shiyasa ma na gaya miki tun yau idan ba dan haka ba sai dai kawai na ce miki gani na dawo"
"Amma dai kasan jego nakeyi" na faɗa jin yana so ya mayar da maganar da gaske, ya ce
"And so? Ai kin fara sallah. Ni fa ba wani abu da zaki kawo mun uzuri da shi na karɓa, kawai ki shirya tarbata Hajiya".
Haka na shiga zullumin yanda zata kaya tsakanina da Bilal domin dai ko karen hauka ya cijeni ba zan biye masa muyi wani abu a cikin gidan Anty Labiba ba. Na ce kuma zan bishi na sani shine abu na ƙarshe da zanyi tunanin aikatawa, tsine mun zatayi kawai na bi duniya. Na dai yi ƙarfin halin sanar mata da zancen dawowar sa.
"Allah ya dawo da shi lafiya" ta faɗa na amsa da "Amin" daga nan muka yi shiru. Akwai shaƙuwa da sakewa tsakanina da ita da zan iya tattauna maganar da mukayi da Bilal amma yanda abubuwa suke tafiya yanzu a tsakanin mu nasan wani ruwan zan ɓallo duk da dai na lura dagaske kamar yanda ta faɗa babu ruwanta da sabgata da Bilal ta zame hannun ta a ciki ba wasa take yi ba.
Ranar da zai dawo ɗin da kanta tace na duba kitchen naga idan akwai abin da zan buƙata da babu a siyo, jirgin sha biyu ya ce zai biyo dan haka da wuri na fara girkin mai aikin ta ta taya ni kafin sha biyun mun gama komai. Bilal na sauka ya kira ni ya gaya mun,
"Na biyo mu tafi ko zaki zo daga baya?" Ya faɗa. Na rasa me zance masa sai kawai na ɓige da cewar bana jin sa na kashe wayar. Babu daɗewa ya sake kira na akan gashi a waje, da na gaya mata ta ce ya shigo mana ko kuma gidan baƙon sa ne.
Nayi zaton yanda yake nanata yayi kewata idan muka haɗu zai yi kamar ya cinyeni amma sai naga akasin haka, rungumar da ya mun ma ni ban wani ji ta ba, a gidan ya ci abinci yana ta mun hirar aikin da suka je. Anty Labiba suka fita harda Al'amin ta ce zasu je karɓo ɗinki ba jimawa zasuyi ba na yi zaton zaiyi amfani da wannan lokaci ya rage zafi kamar yanda yake ta kwakwazo a waya amma bai nuna alamar