Showing 147001 words to 150000 words out of 257873 words

Chapter 50 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

515

yaya zan faɗa musu alaƙar banza na kama Bilal yanayi da wata mace a waje? Da wanne ido zasu cigaba da kallonsa? Ba shi ba ina zaton har yayana sai martabar su ta taɓu idan wannan maganar ta fita shiyasa nayiwa kaina alƙawarin shanye baƙin ciki na ni kaɗai ba zan taɓa faɗawa kowa komai ba tunda dama damuwata tace bai kamata kuma naci gaba da raba baƙin ciki na dasu ba.

"Halima magana nake so muyi" ta faɗa hakan kuma ya saka bugun zuciyata ƙara gudu, na kalleta kafin na sakw sadda kaina ƙasa ina ji tayi murmushi mai sauti kafin ta kamo hannuna cikin nata tace
"Mai ya faru Halima?"

Nayi kamar ban fahimci mai take nufi ba hakan ya saka ta sakw cewa
"Ina nufin mai ya faru tsakaninki da Bilal?"
Jimm nayi amsoshi da yawa suna yawo a raina amma na rasa wacce ta dace da in bata, yanda take kallona kuma nasan koma me zan faɗa da yake akasin gaskiya zata amma kuma dole inyi mata ƙarya domin wannan gaskiyar ba mai faɗuwa bace. Cikin in ina nace

"Babu komai Mama"
"Babu komai kika ce?, babu komai ya kawo ki gida ƙarfe bakwai na safe kuma tunda ya tafi bai sake waiwayarki ba?" Ta faɗa tana tsareni da ido. Na ɗauke kaina gefe nace

"Tafiya zaiyi ai shiyasa ya kawo mu gida". Shiru tayi dan har saida na sace kallonta naga itama ni take kallo da alama ta rasa abun faɗa ne shiyasa tayi shiru tana kallona, can taja numfashi tace
"Ba wasa nakeyi ba Halima ki faɗa mun wace damuwa gareki a aurenki da har take barazana ga rayuwarki?"

Ɓata fuska nayi kamar zan fashe da kuka nace
"Na faɗa miki babu komai Mama idan da akwai ai kin san ba zan ɓoye miki ba zan gaya miki ko?" Shirun ta sakeyi kafin ta miƙe a sanyaye tana cewa
"Shikenan" daga haka ta fice daga ɗakin na bita da kallo jiki a sanyaye ina jin kamar na tashi na bita na faɗa mata amma kuma bazan iya ba. Cusa kaina nayi cikin pillow na fashe da kuka.

Tun daga ranar kuma Mama ta janye mun duk wata hidima da take mun da kanta ta saki sai Zainab ce takeyi ko kuma inyiwa kaina hakan kuma ba ƙaramin ƙara mun damuwa yayi akan wacce nake ciki ba duk gidan sai ya mun ba daɗi, Abba ya koma Lagos, Amirah ta koma makaranta Al'amin dama tun da aka kwantar dani Anty Labiba ta tafi dashi gidanta har ta sakashi makarantar su Inaayah ya fara zuwa Sharifa ma kuma Mama Fauziyya ta ɗauke ta da muka dawo saboda na huta karta ringa damuna da rigima dan haka dagani sai Mama da Zainab sai kuma su Suraj a bakin Gate duk sai gidan ya mun faɗi babu daɗi tarairayar da nake samu an janye mun tallafi kusan magana ma sai ta zama dole sannan take mun.

Ranar dana cika sati ɗaya da dawowa daga Asibiti wanda ya kama sati uku kenan da barowata gidan Bilal ina zaune a falo na zubawa Tv ido, gajiya nayi da zaman ɗaki na fito ina zama kuma Mama ta tashi ta fita can tsakar gida ta fara aikin da bansan na menene ba, ni dai na fahimci kawai zama tareda ni ɗin ne bata so, har nayi kamar na bita sai kuma na fasa na zauna, dama tunda Anty Labiba tazo jiya naga tana wani hararata na san sai ta sake zugata ilai kuwa gashinan.

Ina nan zaune a zahiri Tv nake kallo amma a baɗini nayi zurfi cikin tunani. Ni da kaina na san na zama wata iri, nayi rama mara fasali duk da yanda Mama take matsamun kan cin abinci amma tamkar yana bin rariya yana tsiyayewa ne dan babu abinda yake nunawa a jikina azabar tunani da ƙuncin daya cunkushe mun zuciya su suka hana sassan jikina karɓar abincin su sarrafa shi yanda ya kamata.

Daga waje na ringa jiyo kamar muryar Hansa'u suna gaisawa da Mama, ba zan iya tuna rabon da nayi magana da ita ba dan an ɗauki lokaci mai yawan gaske tun kafin na haifi Sharifa wani zuwa da tayi taje gidana ta tarar da abincin da Bilal ya auna mun zan dafa tayi mun magana akan kada na kuskura na fara rayuwar da a gaba zanzo ina kuka da kaina har tayi iƙirarin zata gayawa Mama halin da nake ciki a sannan haka na rufe ido na gaya mata maganganu son raina kuma nace ta fita a duk wata sabgatar gidan aurena ko da take ɗaga kafaɗa tana iyayi ai sai dai idan ba zata faɗi gaskiya ba amma itama tana da nata matsalar ƙila ma halin da take ciki yafi nawa dan haka kowa yaji da kansa idan gulma zata ringa kawota ni na yafe kada ta sake zuwa in da nake.

Haka muka rabu dutse a hannun riga ta kuma ɗaukar mun alƙawarin ba zan sake ganin ƙafarta a gida na ba dama kuma duk cikin ƙawayen mu ita kaɗai ce take har sannan dan su Baby su Zainab mun daɗe da yin uwaka ubanka tun bayan haihuwar Al'amin da suka sameni har gida zasu gaya mun maganar banza akan wai labari ya baza gari komai daga gidanmu aka mun nan ma na musus tatas nace nagodewa Allah inada gatan da za'a mun a gidan namu su dai da suke taƙama da miji randa bai musu ba sai in ga ina zasu kama shikenan mukayi baran baran suka fita harkata.

Idona akan ƙofa harta shigo falon cikin kyakkyawar shigar Abaya data matuƙar karɓar ta. Ko dan na jima ban ganta ba sai naga ta ƙara wani kyau da kwarjini ta sake zama bababar mace kana kallonta ba sai an gaya maka nutsuwa da kwanciyar hankali sun bi jikinta ba. Da sauri ta ƙaraso in da nake tana kallona kafin ta rungume ni lokaci ɗaya ta fashe da kuka wanda tamkar nima ina jira na fashe da kukan da na daɗe ina so nayi amma damuwar Mama ta saka nake haɗiye shi. Rungume da juna muna kukan kamar ƙananan yara muka shiga ɗaki na, kan gado muka zauna muka cigaba da kukan zuwa wani lokaci kafin ta sassauta nata ta fara rarrashi na wanda daƙyar mukayi shiru a ƙarshe.

"Halima mai ya faru? Mai yayi zafi a duniyar nan kika mayar da kanki haka Halima kina kallon mudubi kuwa?" Ta faɗa tana ɗauke sabbin hawayen da suka far zubo mata. Na kwantar da kaina a kafaɗar ta nace
"Hansa'u ƙirji na zafi yake mun zuciyata ina jin tamkar zata fashe"

"Me kika aje a zuciyar? Ki amayar da koma menene Halima zaki samu sauƙi duk wani nauyi da kika ji zai sauka" ta faɗa tana ɗagoni daga jikinta. Nayi shiru ina kallonta, tabbatas ina da buƙatar fitar da abinda yake ci mun zuciya tun bai gama yi mun illar da ba zata gyaru ba, na buɗe baki da niyyar magana sautin muryar Bilal ya shiga yawo a kunnena sanda yake cewa
"Kafin su zageni sai sun fara yi miki dariya sunce Allah ya ƙara Halima duk wanda kika faɗawa aibu na laifinki zai gani ba ni ba" tuna hakan y aka na rufe bakina ba tareda na ce komai ba na zame daga riƙon da ta mun na kwanta ina ajiyar numfashi. A hankali tace

"Bazan miki dole akan ki faɗa mun abinda yake damunki ba amma ki sani barin kashi a ciki baya taɓa maganin yunwa Halima. Meye ribarki ki rayu cikin fushin iyaye Halima? Ace da ki faɗi damuwarki wacce kulawa ce ma har ta saka aka damu da aji domin a nema miki mafita amma ke kin gwammace ki ƙara jefa kanki cikin wani bala'in ta hanyar shiga fushin iyaye?

Ni dai ban sanki a haka ba ban kuma san mai ya canza ki ba shiyasa ko da nayi fushi dake nace zan fita a sabgarki bana iyawa saboda nasan ke ɗin a yanzu ba Halimar dana sani a baya bace kuma kina da buƙatar mu domin idonki ya buɗe ki gane gaskiya a yanda take ki fita daga iziyar zaton da kike ciki amma kuma duk yanda muka so da mutaimakeki har idan baki so ba babu hali tunda ba zamu miki dole ba, amma ina so ki sani rai ɗaya ne kuma a duniyar nan babu wani namiji daya cancanci sadaukarwar rayuwa domin a yau kika mutu a gobe zai samu madadinki na sani kuma ko a yanzu kinga izina da ranki baki mutu ba to kiyi hasashen makomar yayanki a bayan ba ranki sai ki yiwa kanki Hisabi kan abinda ya kamata kiyi" ta ƙarasa tana miƙewa haɗi da ɗaukar jakarta.

Da sauri na ruƙota ina juya kai lokaci ɗaya hawaye ya ɓalle mun nace
"Bazan iya gayawa Mama ba Hansa'u"
"Anty Labiba fa?" Ta faɗa sai nayi saurin girgiza kai nace
"Gara kowa akanta". Murmushi tayi ta koma ta zauna ta dafa kafaɗata tace

"Ban sani ba ko har yanzu kina ɗaukata a irin matsayin da kike dashi a gurina". Nayi shiru ina kokawa da muryar Bilal dake nanata mun kaina zan tozarta idan na tona asirinsa. Da hannu biyu na toshe kunne na kafin na fizgo maganar da ƙarfi nace
"Matan banza yake bi Hansa'u" wannan maganar kuma tasa naji tamkar na buɗe wata ƙofa cikin zuciyata dan haka tiryan tiryan na shiga koro mata bayani tun daga aurena da Bilal duk wani abu da na haɗiye saida ya samu hanya ya fito da kansa na furtawa Hansa'u shi harda furucin da yayi akan Mama ban rage ba saida na amayar mata. Haka muka rungume juna ni kuka ita kuka babu mai rarrashin wani, mun daɗe a cikin yanayin kafin ta miƙe tana cewa

"Zanje na dawo Halima idan na zauna yanzu ina kallonki bazan samu ƙarfin guiwar ce miki komai ba zanje gida amma komai dare zan dawo". Ban ɗago na kalleta ba na ɗaga mata kai alamar "Toh".

Bayan tafiyar ta ji na ringayi kamar an kwashe mun wani ɓangare na jikina, tsabar yanda nauyin da ƙirji na yake mun ya ragu ina tsaka da kukan bacci ya kwashe ni dana farka kuma sai na ringa ji kamar bani ba, babu wannan abun da nake ji yana mun yawo tsakanin ƙirji da maƙogaro, haka na ƙarasa yinin ranar, har na fitar da rai da dawowar Hansa'u sai gata lokacin ƙarfe tara harta gota. Fuskarta duk ta tashi da alama bayan tafiyarta kuka ta cigaba dayi, a ɗaki muka sake ƙulewa, ta faɗa mun maganganu da sukayi tasiri sosai cikin ƙwaƙwalwata. Abu uku da na fi riƙewa cikin maganganunta tunatarwar da tayi mun akan addu'a.

"Halima tun ba yau ba na sani kina da sakaci gurin addu'a. Ki sani Allah yana fushi da bawan da baya roƙonsa. Ko da ace ubangiji ya hore maka komai a rayuwa ka kasance mai godiya a gareshi kuma ka cigaba da yi masa naci da roƙon ya taya ka tattala abinda ya baka ba kuma shikenan idan buƙatarka ta biya sai kuma sanda ka sake faɗawa cikin wata damuwar ne sannan zaka tuna da Allah ka sake roƙon sa ba shiyasa sai ya barmu da iyawarmu muga idan zamu iya yiwa kanmu.

Abu na farko da zaki fara shine ki gyara tsakaninki da mahaliccinki, kinga addu'a Halima tasirinta yawa ne dashi. Addu'a ta kan canza ƙaddara daga mummuna zuwa kyakkyawa, hatta da Bilal addu'a zata iya canza miki shu. Ubangiji yana son bawa mai naci da ƙasƙantar da kai akan buƙatar sa. Wani kuka ko ajiye abu a rai ba zai ƙareki da komai ba abinda yafi miki shine ki dage kiyita roƙon Allah karki gaji lokaci ya wuce da zamu kwanta muyita bacci da cewar ai komai daga Allah ne haka ne amma kuma ba zaka taɓa haɗa nasarar rayuwarka data wanda ya hana idonsa bacci ya roƙi ubangiji ba tamkar ka kwanta a ɗaki ne kana tsammanin ayi ruwan sama abinci ya faɗo ka ɗauka kaci ba tareda ka fita kayi aikin da zai samar maka da kuɗin da zaka siyi abincin ba.

Kada kuma ki ɗauka a sanda kika so a lokacin addu'ar ki zata karɓu ko kuma idan baki samu biyan buƙatar ki ba a lokacin kice kin dena Aa, shi Allah ba haka yake ba. Ubangiji yafi mu sanin kawunanmu yafi mu sanin abinda yafi zama alkhairi a rayuwarmu.

Wani lokacin mu kan nacewa abinda ba alkhairi bane a tattare damu shi kuma Allah sai ya barmu dashi domin hakan ya zame mana izina idan kuma muka laƙanci kuskurenmu muka koma masa sai kiga ya canza mana da abinda tun farko yake shine alkhairinmu amma muka guje masa.

Kina son Bilal kuma ni ba zance ki rabu dashi ba dukda ba zan miki ƙarya ba har raina zanyi fatan hakan amma kuma bamu ke da rayuwarmu ba ba kuma mu isa mu kaucewa ƙaddara ba dan haka addu'ar dai ita zakiyi ki kuma yi ƙoƙarin gyara tsakaninki da mahaifanki domin fushinsu ba ƙaramin masifa bane a tattare dake shi kaɗai ya isa ya hana addu'ar ki yin tasiri ki nemi yardarsu sai kiga komai yazo miki cikin sauƙi.

Abu ma ƙarshe da zan gaya miki shine koda Allah ya ƙaddara cigaban zaman ki da Bilal, dukda dai kin rigada kin yi gini da tubalin toka amma lokaci bai ƙure ba da zaki iya rush ginin nan ki faro shi da sabon foundation. Idan kin fahimci abinda bake nufi duk abinda zakiyi kiyi shi bisa gaskiya, aure ibadah ne ba wai soyayya ba Halima sannan a cikin biyayyar auren kanta zaki iya kai kanki wuta a maimakon Aljanna dan haka dole ku saka Allah ku kuma ɗora aurenku bisa doron shari'a domin samun dacewa".

Haka ta tafi ta barni cikin tunani, Tabbas na yarda da sakaci na gurin addu'a, ina ƙoƙarin kiyaye sallolina na farilla idan na idar kuma zanyi yan gajerun addu'oina shikenan bana ɗorawa da nafila. Tun ina gida Mama tayi iya ƙoƙarin ta gurin ɗora mu a hanya a duk sanda zata tashi cikin dare zata zo ta tashe ni wani lokacin nayi sallar ido cike da bacci wani lokacin data fita zan maida kai na kwanta, haka azumin litinin da Alhamis haka nan tun ina kirawa kaina ulcer ƙarya dan kar inyi har ta gaske ta kamani, a hakan ina lallaɓawa da kuma na koma hannun Bilal sai komai ya sake taɓarɓarewa domin dai shima baya ga sallah biyar ta farilla ban ce yana wata nafila ba haka azumi nasha in ce masa mu tashi da azumi ranar Alhamis ko Juma'a yaƙi wani lokacin ma ni zan ɗauka ƙarshe sai ya saka na karya shi. Kai ko sallah nayi na zauna ina doguwar addu'a muddin yana kusa sai ya san yanda ya tayar dani har cewa yakeyi wai idan mace tana doguwar addu'a da wuya ba ƙarar mijinta take kaiwa gurin Allah ba, da sakaci irin nawa da rashin ƙarfafawa dana samu daga gareshi duk ya sake taɓarɓara komai nawa ya zama sai a hankali.

Lissafina, rayuwata gaba ɗaya Bilal nez ko addu'ar zanyi shine, bani da wani buri a koda yaushe sai yanda zanyi na burge Bilal na samu soyayyar ta yanda bani da wata addu'a sai tasa ban kuma taɓa banbacewa ba domin zuciyata ta rigada ta amince shi ɗin shine alkhairi gashi kuma ubangiji ya mallaka mun shi sai dai kuma mallakar tasa bata zamemin komai ba face fitina domin duk wani abu mata kyau da zai sameni yana da nasaba da Bilal, a tarayyata dashi baki ɗaya zan iya cewa Al'amin da Sharifa su kaɗai ne abun ƙwarai da zan ɗaga nace na samu a silar Bilal bayaga haka sai tarin nadama da dana sani.

Kwana nayi ina saƙa da warwarar mataki na gaba, barin Bilal ko kuwa cigaba da zama dashi? Kamar yanda tace zaɓi na ne duk kuma abinda na ɗauka babu mai ce mun saboda me domin ni nasan daɗi na kuma san wahalar dake tattare da zama dashi amma kuma dole na tsaya nayi tunani mai kyau ko saboda goben yayana.

BILAL
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 38*

Madallah da mutane masu karamci. Nagode ƙwarai dagaske, ina lafiya wani aiki ne ya ɗauke ni tsayin kwanaki amma Alhamdulillah mun kammala na kuma gode ƙwarai da haƙurinku ina fatan har mu kammala babu wani uzuri da zai sake gifta mana 🙏🏽🙏🏽🙏🏽

*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne 800, yake mai jira nayi posting ki fitar kiji tsoron Allah dakw da wacce take jira ki turo ta karanta a bati ku guji haƙƙin komai ƙanƙantarsa. Duk wacce ta shirya sauke nauyi ta tura mun kuɗi na a asususun 7061838488 Opay Maryam Farouk. Nagode*

BIlal

Tun barin sa gidansu Zulaiha komai ya sake jagule masa, tunanin sa ya tsaya kwata kwata ya kasa tantance mai ya kamata yayi. Batun ace ya haƙura da Zulaiha ma bai taso ba domin kuwa hakan ba mai yuwuwa bane ba amma bai taɓa zaton za'a masa titsiyen aurenta irin haka ba musamman a wannan lokacin da yake cikin tsaka mai wuya tsakanin sa da Halima. Tabbas yana son Halima tana kuma da matsayi na daban a zuciyarsa domin yasan halacci ya san kuma a zamanin yanzu samun mace da zata so shi tsakani da Allah irinta ta kuma kyautata masa da jikinta da aljihunta abu ne mai matuƙar wahala.

Kawai shima bai san dalilin da ya saka ya kasa kwatanta mata kyautatawar da take masa ba, yanzun kuma wannan abun daya gifta duk ya sake lalata komai tunda har kuma ta iya tafiya gida da kanta ya san tabbas ta kai ƙarshe ne dan haka zai bata lokaci domin ya san fushin ta ba zai ɗore ba ƙila ko bai bi ta bama idan ta sakko da kanta ita zata nemeshi kamar yanda suka saba fatansa kawai shine ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login