Showing 231001 words to 234000 words out of 257873 words
yana cewa
"Wane irin rashin hankali ne haka? Ita Hajara wai sai yaushe zata girma ta fara abu irin na mutane masu hankali? Dama mace ta taɓa aurar da kanta ne ko kuwa uwa ce take bayar da auren yarta? Daga ku har uwar taku sai a rasa wayafi wani tunani, kaima nan zancen ya iskeni ance ka saki uwargidanka dama kuma duk ina jin labarin irin ɗiban albarkar da kai da uwarka da yan uwanka kuka ringayi mata, toh hausawa dai suka ce duk wanda bai yi sharar kasuwa ba zaiyi ta masallaci dan haka tun wuri in dai da gyara ina baka shawarar ka dawo da matarka dan ba zaka gane illar da kayiwa kanka ba sai a gaba. Ita kuma Hajara zan kirata" akan haka suka rabu.
Washe gari kuwa ya kira Hajjan yace taje gida ta sameshi yana son magana da ita ba musu kuma ta shirya ta tafi yayi mata tatas sannan yace su dakatar da duk wani shiri da sukeyi Fadila ta gayawa yaron yaje ya gaida iyayenta maza tukunna idan sukayi bincike sukaga bashida wani aibu sannan su bashi lokacin da zai turo ayi magana.
Ta koma gida ta saukewa Bilal tijarar da batayi a gaban Kawu Ɗayyabun ba tunda shi ya kai masa gulmar amma kuma dole tayi abinda yace ta kira Baba Sani yaƙi ɗauka sai a wayar matarsa ta sameshi shima daƙyar ya karɓa sukayi magana tana gaya masa dalilin kiran kuma yace babu shi a cikin wannan magana
"Kin manta kashedin da kika mun akan yayanki Hajara? Ai ko ni na kawo rashin zuciya duniya ba zan sake tsoma baki cikin abinda ya shafeku ba, bani kaɗai bane ɗan uwan ubansu ai muna da yawa ki nemi wani" ya bata amsa daga haka kuma ya katse wayar. Daga ƙarshe dai sai babban yayansu Bilal ɗin Alhaji Salisu ta taka har gida ta samu dan Kawunnansu duk wanda ta kira sai yace yana Aa dan kowa nada labarin ɗibar albarkar da tayiwa Baba Sani da Aminu akan zancen Bilal.
Fadilan ce ta raka shi gurin Yayan nasu akayi sa'a ashe ma sun san juna akwai hulɗa ta cinikayya tsakaninsu, kamar yanda ya cewa Hajja a tsayin lokacin daya san Alhaji Ahlan saurayin Fadilan ya san mutumin kirki ne kuma yayi tambaya akansa an tabbatar masa da mutumin kirki be kuma yana da asali mai kyau dan Babansa nada sarauta acan Zarian ma. Ya taɓa aure sau biyu, ta farkon rasuwa tayi suna da yara biyu Mace da Namiji ta biyun kuma rabuwa sukayi, shikenan aka cigaba da shirin biki, maza sunzo sun sake kawo kuɗin aure da Sadaki bayan wanda ya rigada ya bata.
Bayan ya gama sauke musu kayan miyan a tsaitsaye suka gaisa ya wuce saboda zaije ya ɗakko Jalilah ne a airport.
Motarsa ce taƙi tashi, ganin zata ɓata masa lokaci ya barta ya kira wani abokinsa dake siyar da motoci a Gadon ƙaya yace zaizo ya karɓi mota yanzu, da wannan saurin ya faɗa Adaidaitan daya gani a bakin layin ashe rabon su haɗu da Halima ne.
Harga Allah har ya zauna bai san ita bace a ciki dan hankalinsa na kan wayarsa sai da tayi magana kafin yaji muryarta ya kuma yi mamaki matuƙa amma bai nuna hakan ba har ransa kuma sai yaji rashin daɗi da bai san dalilin sa musamman ganin da yayi mata ta canza tayi wani kyau fatarta har wani ƙyalli takeyi baka buƙatar a faɗa maka ta samu hutu da kwanciyar hankali. Shi da yake nan yana tunanin tana can cikin halin ƙaƙanikayi soyayyarsa ta hanata sakata ko wacce daƙiƙa cikin dakon kiranta yakeyi domin ya tabbatar ba zata taɓa iya rayuwa mai ma'ana ba tareda dashi ba.
Daɗewar da akayi yanzun ma bata waiwayeshi ba ya sani cikin biyu, ko dai an ƙwace wayarta ne tunda kowa nata ba son su tare yakeyi ba ya san zasu iya ƙwacewa dan kar ta kirashi kuma a hanata fita idan kuma ba haka ba toh bata da lafiya, yana kuma lissafe da kwanaki jira yakeyi sai ya rage saura kwanaki ta fara period ɗin ta na ƙarshe sannan zaije ya mayar da ita sai dai su mutu da baƙin ciki a lissafi kuma yau saura kwana goma sha biyu ya aiwatar da shirinsa tunda saura kwana sha biyar a calendar ta da take cikin wayarsa sai kuma kwatsam gata a yanayin da bai tsammaci ganinta ba ita ashe tuni tayi move on har ta buɗe sabon babi a rayuwarta.
Ya daki stirring a fili ya ce
"Ba zai yuwu ba, ba zan taɓa barinki ba Halima. Kece silar lalacewar komai dan haka duk yanda rayuwa ta juya tare zamu fuskanceta".
Daga Airport ɗin kai tsaye store suka wuce, a hanya Jalilah take ce masa
"Amma ban taɓa zaton Sudais zai iya cin amanata ba"
"Ai kallonki kawai nakeyi, ban fahimci ko rashin yarda bane ko menene ya saka ni baki bani keys ɗin gurin ba kika bawa wani, gashi yanzu abinda ya faru" ya faɗa ba tareda ya kalleta ba. Jalilah dake danna waya ta ɗaga kai ta kalleshi haɗi da yin ƙaramin murmushi amma bata ce komai ba. Da suka isa shi ya riƙe mata jakarta, ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sanda ya zura mata keys ɗin daya zare ranar da zata koma Abuja yabi bayanta kamar yana wani murmushi irin na samun nasara.
Bai zaci komai zai zo masa da sauƙi ba, ana gobe zata tafi wancan zuwan da tayi suka zo ta nuna masa store ɗin da kuma kayan da aka sauke ta kuma nuna masa Sudais da tace ɗan ƙawar Momynta ne store ɗin na Babansa ne ya basu aro. Ko a fuska bai nuna mata jin haushi ba sanda ta maidawa da Sudais ɗin muƙulli da zasu tafi a hanya tana ta yabon yaron da irin amanarsa ransa ya ƙara ɓaci ya ringa ji kamar jurwaye take masa mai kamar wanka wato shine mara amana kenan?
A mota ya tsinci muƙullin bayan ya dawo daga kaita Airport, har yayi niyyar kiranta kuma ya fasa da daddare kuwa sai gashi ta kirashi akan yaje ɗakin data zauna ya duba mata ta manta spare keys na store da Sudais ya bata, har yayi niyyar ya ce mata suna gurinsa kuma kawai ya fasa yace mata toh kawai, da safe kuwa bai ko je Hotel ɗin ba ya kirata yace yaje an duba basu ga komai ba daga nan kuma zuciyarsa ta fara raya masa akan ya ɗibi wasu daga cikin kayan ya siyar tunda yana tsaka da buƙatar kuɗi kuma babu yanda za'ayi asirinsa ya tonu tunda dai ba'a sakashi a cikin sabgar ba.
Sai da ya saita hanya ta yanda ba wata ƙura da zata iya biyo baya kafin ya fitar da kayan ya karɓi kuɗaɗen sa yake ta kashe gararin gabansa dasu, ko da yake a yanzu yanda yake ji baya tsoron Jalilan ta sani dan a shirye yake domin daga yanda Alhaji Lawan yake threatening nasa ya san dole allura zata tono garma duk kuma abinda zai faru ba dai za'a kashe shi ba kuma ba zai kullu ba dan shari'a yanzu kuɗi ce kuma ya shirya shiyasa ko da ya tura masa da message jiya akan kowanne lokaci za'a iya kawo masa sammaci mayar masa amsa yayi da cewa
"Do your worst" yayi blocking layin.
Bayan sun gama da can suka kama hanya yana murmushin da shi kaɗai ya san ma'anar sa ya tambayeta ina zai kaita yanzu?
"Muje can gida na huta tukunna idan yamma tayi sai ka kaini gidan Hajja na gaisheta kwanaki da yawa ko a waya idan na kira bana samunta" ta faɗa tana lafewa a cikin kujera. Gabansa ya faɗi, wai mai take nufi da mayar da gidansa gurin saukarta yanzu? Amma dai bai ce mata komai ba ya kama hanya abinda ya sa bai damu sosai ba ya san zuwa yanzu Zulaiha ta tafi gidan Hajja tunda sunyi magana tun sanda zai fito ta faɗa masa zataje.
Clashing sukayi da wata mota suna shiga layin ita kuma tana fita sai da suka wuce ƙwaƙwalwarsa ta tariyo kamar fuskar Zulaiha ya gani a gaban motar, ita kanta motar sai yaga kamar ya santa a wani guri amma ya manta a ina ne. Saida yayi parking Jalilah ta fita ta wuce part ɗin sa kafin ya kira Zulaiha.
"Kina ina?" Ya tambayeta bayan data amsa daga can tace masa
"Ina gidan Umma mai ya faru?"
"Gidan Umma kuma? Baki tafi gidan bikin ba kenan?" Ya sake tambayarta bayan daya sauke ajiyar zuciya ta samun nutsuwa. Sanar masa tayi wai Umman ce bata jin daɗi tana shiri zata fita Nuratu ta kirata shine ta fara zuwa can gidan kuma ta kira wayarsa ta gaya masa amma bata sameshi daga nan sukayi sallama bayan yace ta zauna a gidan Umman kawai ta kula da ita zaije ya ɗakko ta bayan isha'i.
Ganin Jalilah ta fito ya saka yayi saurin kashe wayar yana kallonta, ta yamutsa fuska ta ce
"Na fasa ka kaini Hotel kawai". Bai damu ba suka sake fita, yana tareda ita har gurin goma kafin ya mata sallama ya biya gidansu Zulaiha ya ɗauketa suka wuce gida.
Washe gari bayan an sakko daga sallar Juma'a aka ɗaura auren Fadila da angonta Alhaji Ahlan. Kusan suman zaune Bilal yayi lokacin da sukayi arba da angon Fadilan, mutumin daya siyi gidan Jalilah, wanda ya biyo Zulaiha ranar da sukaje siyan shawarama kenan gidan ne za'a saka Fadila a ciki. Ji yayi kansa ya na nema ya kama ciwo ya sulale ya fita daga masallacin yana shiga mota wayarsa ta fara ƙara ganin Zulaiha ce ya ɗauka a taƙaice ta sanar masa wai yayi baƙi, ya tambayeta su waye tace wai bata sansu ba Mace da Namiji ne.
"Toh ke mai kika zauna yi dama baki taho gidan bikin ba?" Ya tambayeta, daga can tace
"Ina shirin fitowa suka zo ai ko sai in kulle in hana su shiga?"
Tsaki yayi ya kashe wayar kafin ya kunna motar yana tafe yana tunani wane mace da Namiji ne zasuje gurinsa? Hafiz ya kawo da matarsa dan shi kaɗai ne dai yake tunani dukda baya zaton ganin Hafiz a gidansa saboda tun ranar daya sanar masa daya saki Halima ɗan shirin da suka dawo yi ya sake ja baya balle matarsa daya fahimci ta ma fishi ɗaukar ɗumi akan lamarin.
Bai gane motar daya gani a ajiye ba dan haka shima yayi parking a waje ya kuma tsaya yaƙi shiga gidan wani abu mai kama da tsoro ko fargaba ya ɗarsu a ransa, to wai wane baƙo ne haka da shi ba zai kirashi a waya ba sai dai Zulaiha? Kuma da yace ta basu waya yaji su waye suka ƙi karɓa wai surprise zasu yi masa. Ƙarfin hali yayi ya buɗe gidan ya shiga yana ayyana koma dai menene ya san ba abin cutarwa bane tunda bai ji wata fargaba ko tsoro tattare da Zulaihan ba.
Takalmin mace da namiji, bai gane na namijin ba amma na macen tsinin takalman kawai ya gani ya fahimci na wanene, gabansa ya yanke ya faɗi lokaci ɗaya kuma kansa ya sara, cikin takatsantsan kamar wani ɓarawo ya juya da niyyar komawa muryar Zulaiha da yaji a bayansa ta saka yaci burki ya shiga mayar da numfashi kamar wanda yayi gudu.
"Allah ya so ka da kunyi saɓani" ta faɗa, sai da yayi matuƙar ƙoƙarin gurin saita yanayinsa kafin ya juya ya kalleta yana ɗan murmushi ya ce
"Ina baƙin?"
"Suna ciki shirin tafiya ma sukeyi, gaka nan gaka nan tun ɗazu sai kace wanda ya taho daga Kaduna ai da sun tafi ka huta kuma ga wani saƙon can an kawo maka sammaci daga kotu" ta sake faɗa hankali kwance ta wuce shi ta shige ɗakin Solar. Nepa aka ɗauke shine ta fito zata canza ta ganshi dan basu ji motsin buɗe get ɗin ba ma.
Dafe kansa daya sake sarawa yayi yana nanata sammaci a zuciyarsa, Sai da ya ga zata fito kafin ya lallaɓa ya nufi falon yana ƙaƙalo murmushi a ransa yana haɗa kalaman da zaiyi amfani dasu gurin yi musu magana, Hafiz da Jalilah suka ɗaga kai a tare suka kalle shi haɗi da amsa masa sallama. Ya saki murmushin yaƙe ya nufi Hafiz ya bashi hannu suka gaisa yana cewa
"Lallai kuwa an bani babban surprise, kuma da na san kaine da zance mata karta buɗe maka ƙofa"
Fuska ba yabo ba fallasa Hafiz ya ce
"Idan ni ba'a barni na shigo ba ai ba za'a hana uwarɗakinka shigowa ba ko ba haka ba Hajjaju?" Yayi maganar yana kallon inda Jalilah ke zaune ta harɗe ƙafafu tana latsa waya sai ka rantse bata san da wanzuwarsu a gurin ba.
Murmushin daya saka zuciyar Bilal fara gudun wuce ƙa'ida tayi kafin ta ce
"Ni da aka ɓoyewa amaryar ai ni naci albarkacinka". Ya haɗiye miyau kafin ya samu guri ya zauna yana kallonta ya ce
"Ranki ya daɗe yaushe a gari?"
"Zuwana kenan" ta bashi amsa tana gyara zama idonta akansa. Gyara zama yayi yana murmushin da gara kawai a bashi fili ya fashe da kuka, magan yake so yayi amma wai duk tarin kalaman kare kai daya ke da haddarsu a ka duk wacce ya kamo sai ta zille ya rasa kalaman da zai haɗa yayi magana sai kawai yayi shiru ya sadda kai ƙasa kamar wanda Alƙali ya tsura. Can ya miƙe ganin ba'a ajiye musu ko ledar pure water ba ya shiga kiran Zulaiha, tana ƙofar ɗakin Solar tana replying message ɗin da Ahlan ya turo mata.
Sunyi akan zasu haɗu yau tunda zataje gidan Hajja tana tsaka da shiri baƙin Bilal ɗin sukazo haushin rusa mata plan ya sa ko ruwa bata basu ba suna zaune sama da awa guda kenan suna jiransa. A bakin ƙofa suka haɗu zata shiga shi kuma zai fito yayi ƙasa da murya yana ce mata
"Babu wani abun taɓawa ne a gidan da ba ki basu ba naga ko ruwa ma baki ajiye musu ba?"
"Babu, ruwa kuma pure water muke dashi kuma naga su ɗin ba kalarsa bane shiyasa ban basu ba" ta bashi amsa, ya maka mata harara ya ce
"Ina dambun naman dana gani jiya? Kuma yau kwana nawa dana siyo ruwa katan biyu? Nufinki kin shanye ko me? Kuma ai akwai lemo a fridge kawai kice so kike ki wulaƙanta ni shiyasa kika wulaƙanta baƙi na" yayi tsaki ya koma ciki tabi bayansa. Kitchen suka shiga ya ɗauki try ya kwashi ruwan da tace babu dukda babu sanyi ya ɗora akai, da mamaki ya kalleta bayan daya buɗe fridge ɗin; lemuka kala kala a ciki harda Champagne. Gefe ta ɗauke kai, yayi ƙwafa ya kwashi lemukan ya haɗa da cake ɗin daya gani ya fita ya ajiye musu.
Hafiz da Jalilah suka bishi da kallo, dariya ce ta kama Hafiz ya danneta amma dukda haka saida wata ta fito sai ya fake da tari Bilal ya shiga yi masa sannu kafin ya koma ya kofuna ya ajiye musu ya bi Zulaiha data shige ɗaki da harara duk akan idon Hafiz, sai ya girgiza kai kawai ya ɗauki kofi ya tsiyaya lemo ya miƙawa Jalilah bata karɓa ba ta masa alamar aa da hannu tana cigaba da danna waya, ya karɓi kaɗan kafin ya kalli Bilal ya ce
"Su Al'amin fa?"
"Suna can gurin Mamansu" ya bashi amsa yana satar kallon Jalilah. Hafiz ya sake cewa
"Allah sarki, kwanaki na ganta kuwa a Alpen ina ta ɗaga mata hannu amma bata lura da ni ba, ta canza sosai ta ƙara kyau da farko ma nayi tantamar ita ɗin ce kuwa sai da naga ƙaninta sannan na yarda ita ɗin ce dagaske, gaskiya zawarci ya karɓeta idan ba'a faɗa bama zaka ɗauka budurwa ce wlh".
"Hmmm" kawai Bilal ya iya faɗa take kuma haushin Hafiz ɗin ya kamashi amma dai bai nuna ba yaci gaba da satar kallon Jalilah dake ta danna waya alamar wani abun take rubutawa. Kiran sallar la'asar da aka farayi yasa ta miƙe kamar wacce aka tsikara tana kallon Hafiz tace
"Muje ko?"
"Wai mai ya faru ne gaba ɗaya kin canza ba kamar yanda muka fito ba?" Hafiz ya tambayeta. Ta kalli Bilal kafin ta mayar da kallonta kan Hafiz tayi murmushi tace
"Na gaya maka maganar kayan da aka satar mana a store shine duk ya canza mun mood" ta faɗa tana langwaɓar da gefe kai. Mota ya rakasu basu ja sallamar da nisa ba suka wuce shi kuma ya jingina da ƙofa yana mayar da numfashi. Ta faru ta ƙare anyi wa mai dami ɗaya sata, shi dama ya daɗe yana hasashen shigo shigo ba zurfi kawai Hafiz yake yi masa da yakeyi kamar bashida masaniyar komai akan alaƙarsu, idan ma kuna dagaske ne bai sani ba toh yau kam ya san Jalilah ta gama farke masa laya shiyasa suka haɗo kai suka zo su ƙureshi amma ba zaiyi saurin kaiwa ƙasa ba dole ya nemi mafita domin shirun da Jalilah tayi ya sani tabbas ba alkhairi bane.
Ciki ya koma yana zura kai sukayi karo da Zulaiha dake shirin fitowa, tayi baya ta dafe kai kafin tayi tsaki ta raɓeshi har tana tureshi ta fice ya bi bayanta da kallo. Ɗakinsa ya shiga ya ringa safa da marwa tunani kamar kansa zaiyi bindiga ya tarwatse, yanzu ina zai kama? Jalilah tasan yayi aure da alama kuma tana da masaniya akan shi ya ɗauki kayan idan ma kuma bata sani ba toh tabbatas tana dabda sani bai kuma san irin matakin da zata ɗauka akan hakan ba, ga Alhaji Lawan ya makashi a kotu shi yanzu ina zai tsoma ransa yaji daɗi a faɗin ƙasar nan?
Tsabar ruɗin da yake ciki bai tuna baiyi sallar la'asar ba sai da yaji ana kiran sallar magriba tukunna yayi alwala ya haɗa su yayi. Yana nan zaune gida shi kaɗai har ƙarfe goma Hajja harta gaji da kiransa tun magriba wai suzo suyiwa Fadila faɗa kafin a tafi rakata ko faɗan mai zaiyi mata oho?
Ganin har ƙarfe goman Zulaiha bata dawo ba ya sa ya kirata tace masa suna gidan Amarya ba'a tafi kaita da wuri bane amma yanzu zasu taho. Haka