Showing 246001 words to 249000 words out of 257873 words

Chapter 83 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

472

shiga banɗaki dukda dai yaba dafe kansa da yace yana sara masa har sannan. Tarar dashi ido biyu da Abubakar yayi ya saka yace a basu transfer kawai su koma can gaba ɗaya likita kuma bai ɓata lokaci ba ya basu aka ɗauke shi a Ambulance shi dai Bilal kallonsu kawai yakeyi dan tunda ya farka bai yi wata doguwar magana ba har aka kai shi ɗakin da Hajja take a Retainership.

Bayan da Anty Amina taje aka ɗauketa itama daga General Emergency da aka fara kaita aka mayar da ita can tunda suna da file kuma account ɗin su is loaded, ɗaki ɗaya aka kwanar dasu, ganin Hajja da har sannan bata ko motsa ba ya saka ya magantu ya shiga tambayarsu mai ya sameta?

Sai yammacin ranar Hajja ta farka wannan ya saka hankalinsu ya sake kwanciya sai dai bata ko yi awa ɗaya ba jiki ya sake rikicewa kuma aka rasa abinda ya sameta sai daga baya wata nurse ta lura da kumburin da guiwarta tayi baby ɓata lokaci aka wuce da ita X-ray, ashe faɗuwar da tayi ne karayar da tayi a guiwar wancan lokacin ƙashin ya sake gocewa dan dama lallaɓa ƙafar kawai takeyi tun lokacin ba wai ta koma dai-dai bane. Sabon ɗori aka sakeyi mata sannan aka raba musu ɗaki da Bilal saboda yan dubiya da likitan yace surutansu zasu dameta, shi kansa Bilal ɗin sun ƙi su barshi ya samu isasshen hutun da yake da buƙata balle ita da aiki ya dawo sabo.

Sai da suka kwana uku a Asibiti kafin Fadila da Mijinta sukaje. Allah ne kawai ya ɗorata a kansa, duk irin kuka da kururuwar data ringayi bayan Abubakar ya kirata a waya ko kallonta Ahlan ɗin bai yi ba daga ƙarshe data ishe shi ya kamata ya mata shegen duka wanda dama ya riga ya zame mata tamkar abinci, idan bata ci da safe na zata ci da rana ko da dare sai dai idan Allah bai saka tayi kuskuren da yaga ba zai iya ɗauke ido ba.

Tunda yan rakiyarta suka gama ficewa daga gidan ta tashi ta gyara kwalliya tayi amfani da duk wasu abubuwa da aka bata saboda lokacin ta fita falon saman ta zauna tana jiran Ango da sai da dare ya fara nisa kafin ya shigo gidan ya kuma fara da kwance mata jakar tsabar rashin mutunchi da tijarar daya tanadar mata.

Bai ko iya jira gari ya waye ba, a daren tana naɗe kan kujera tana dakon zuwan Habibinta su murji soyayya cikin aminci. Burinta ya cika tayi irin auren da take fata, ta samu matashin mai kuɗi kuma kyakkyawa ga gida na nunawa sa'a da kayan alatu cike duk masu yi mata dariya da cewar alhakin Umar tsohon mijinta ne yake bibiyarta gashi nan tunda suka rabu ta kasa samun miji shi kuwa tuni yayi aure har matarsa tayi haihuwa biyu basu san tanadin da Allah ya mata ba yanzu sai su banbance tsakanin ita da shi waye yafi wani samun cigaba?

Tana tsaka da wannan tunanin ta ji ana kwarara mata kira kamar yaƙi daga ƙasa, da fari bata ɗauka muryarsa bace sai da ya fara hawowa saman sukaci karo a bakin ƙofa zata fito yana shirin shiga ya kuwa kwaso ashar ya watsa mata yana tambayar shi ɗin sa'an uwarta ne da tana ji yana kiranta amma tayi masa banza?

Mamaki ya saka ta cewa
"Lafiyarka kuwa Ahlan? Mai kasha haka?" Take kuwa ya naɗe hannun riga ya gwada mata aikin marasa lafiya na gaske. Ya mata dukan tsiya sannan ya tankaɗa ƙeyarta ciki ya kwanta da ita cikin mafi ƙasƙancin yanayi sai kace wata dabba kafin ya tsallaketa yayi ficewarsa bata sake sanya shi a ido ba sai washe gari da yamma zuwa lokacin tayi kuka har idanuwanta suna neman su daina gani ba kuma ta jira wani ya biya mata karatun ba ta fahimci in da kwaɗaiyi da son zuciyarta data mahaifiyarta ya jefo ta.

Da yammacin ranar kuma ya ƙarasa warware mata komai, kamar yanda ya sanar mata shi tun farko bai yi niyyar aurenta ba, rashin amince masa da batayi a waje bane ya saka ya canza shawara dan tunda yawunsa ya tsinke to fa ba zai haɗiye ba sai ya ɗanɗana shiyasa ya yanke shawarar aurenta da niyyar ya saketa bayan burinsa ya cika amma kuma bayan faruwar komai yaji tayi masa yanda yake so dan haka ya fasa ba zai saketa ba sai dai ta sani babu soyayya a zamansu, zata zauna ne kawai a matsayin abun biyan buƙatarsa domin ita ɗin bata kai ya kirata da matarsa ba.

"Sharaɗin zaman lafiyarki a gidan nan na farko ban yarda wani daga cikin makwaɗaitan danginki ko uwarki suzo gidan nan ba, balle aje kan ƙawaye ko wasu tarkace hakanan kema ba zaki fita ko ina ba" ya faɗa mata. Ya lissafa mata sauran Sharuɗan sa, ta ringa kuka tana roƙonsa daya taimaka mata ya sawwaƙe mata amma yace bai san zance ba ko tana so ko bata so sai fa ta zauna dashi kuma ya ƙwace wayarta. A ɗan lokacin nan taga bala'i ganin idonta, babu rashin ci babu na sha ga muhalli mai kyau Ac har ta isheta kuma bata isa ta kashe ba idan ya so mugunta haka zai ƙure sanyin duka Ac gidan idan kuma yan iskansa suna kusa yace ta cire kayanta tayi ta yawo tsirara yana kallonta bata isa kuma tayi ko jimm kafin ta aikata abinda ya umarceta ba zai rufeta da duka duk ya canza mata kamannin fuska saboda mari da hauri da ƙafa.

Yau ɗin ma tayi mamakin yanda tana zaune kawai ya shiga yace ta shirya suje duba Hajja. A hanya toshe kunnuwanta kawai tayi saboda cin mutunchi da zagin da ya ringa mata da iyayenta kuma bata isa ta yi ko tari ba balle ta mayar da martani.

Kallonta suka ringayi kamar sunga wata baƙuwar halitta, ga dai Lace har Lace a jikinta da mayafi na garari amma sai tayi daban a cikin kayan kai idan ba wanda ya mata mugun sani ba ma ba lallai a kallo ɗaya ka gane Fadilan bace. Hajja dai sai ido, duk inda Fadilan ta motsa sai ta bita da kallo kawai ko sannun da take mata ta kasa amsawa. A ɗar ɗar Fadilan ta ringa gaishe su tana satar kallon Ahlan ɗin daya kame a gefe yana kallonsu a ɗage kamar yaga kashi, sai da ya mula kafin kuma ya musu gaisuwar jam'u kuma ta raini wai
"Sannunku" sai kace ba yayyen matarsa ba harma da iyayenta dan akwai ƙannen Hajja biyu da matan Baba Sani a gurin.

Daƙyar ta iya tambayar Yaya Bilal suka ce mata yana ɗakin dake kallon wannan, ta saci kallon Hajja wadda da alama mamaki ne ya kulle mata baki kafin cikin murya tsantsar ladabi ta ce masa suje can ɗakin su duba Bilal. Rafar yan dubu-dubu guda biyar ya zaro ya ajiye akan drawer dake gefen gadon kafin ya juya cike da taƙama ya fice daga ɗakin duk suka rakashi da ido itama ta bishi simi simi kamar marainiyar kyanwa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un mun shiga uku dama haka mijin Fadilan yake?" Anty Habiba ta faɗa tana tafe hannu, nan ta buɗewa masu jira fili suka fara sakin maganganun da suka cika musu baki, Anty Amina ta miƙe tana cewa

"Amma dai kun san nan ba gurin mayar da zance bane ko? Dan Allah ku fita, dama ai sun ce anyi yawa a ragu haka ko ta samu ta koma bacci ta huta".

Su Fadila kuwa ɗakin da Bilal yake suka shiga, ita ta fara shiga ya tsaya yana amsa waya. A nan ta tarar da Abubakar, sai da tayi dagaske gurin danne kukan daya so ƙwace mata dalilin ganin wanda take ganin shi kaɗai zai iya cetota daga bala'in da take ciki amma bata isa ta faɗi wani abu a yanzu da suke tareda Ahlan ɗin ba. Gaban gadon da Bilal ke kwance ta isa tana amsa sannu bayan ta gaida Abubakar daya zuba mata ido cike da mamaki yana kallonta, ta gaisa Zulaiha dake zaune gefensa dai-dai nan Ahlan ɗin ya shigo ɗakin da sallama kamar bashi ba.

Fuska a sake ya miƙawa Abubakar hannu suka gaisa kafin ya matsa gaban gadon yana yiwa Bilal dake kallonsa kamar ya samu Tv sannu.
Gyara tsayuwa yayi kafin ya shammaci Zulaiha da ganinsa ya saka tayi suman zaune ya mintsineta a gefen ciki. Ba ƙaramin ƙoƙari tayi gurin hana kanta yin ihu ba, sai ta mike da sauri ta fice daga ɗakin ya zauna a inda ta tashi yana sake yiwa Bilal sannu ya gyaɗa masa kai alamar amsawa.

"Baya magana ne?" Fadila ta tambayi Abubakar, ya ce mata
"Yana yi amma ba sosai ba"
"Wai mai ya same su Yaya?" Ta sake tambaya idanuwanta suna kawo ruwa, Abubakar ya ce
"Hawan jini ne dai duk su biyun, silar sa kuma bamu sani ba har yanzu tunda itama Hajjan kinga bata magana gara shi yana yi kawai yaƙi faɗar abinda ya same shi ne"

"Toh fa hawan jini duka su biyu toh Allah ya basu lafiya ya mayar musu kaffara kuma" Ahlan ya faɗa yana miƙewa. Ganin ya nufi ƙofa Fadila ta bishi ya dakatar da ita yana cewa
"Waya zanyi ina zuwa" ya fita.

Can nesa ya hango Zulaiha ya nufeta, a firgice ta waiga ta kalleshi ta shiga zare ido tana dubawa ko wani yana kallonsu kafin murya na rawa tace masa
"Yanzu dama ƙanwar Mijina kake aure amma shine...shine" sai ta kasa ƙarasawa saboda tashin hankalin daya mata rubdugu har muryarta ta bayyanar da hakan.

Gira ya ɗage mata yana cewa
"Shine akayi me?"

"Wlh idan ka kashe mun aure Allah ba zai barka ba" ta faɗa hawaye na ɓalle mata. Yayi dariya kafin ya ce

"Sai dai idan ke kika so ki kashewa kanki aure, tun ranar dana fara ganinki na san alaƙarki da wacce nake shirin aure a lokacin. Kin mun, da ace kuma baki da aure na gaya miki da zan aureki, tunda kuma mun samu sararin da zamu mori junanmu menene aibu a ciki? Ni dai maganar nan ba zata taɓa fita daga bakina ba idan har wani ya jita to sai dai daga gurinki. Kuma mijin naki da kike magana akai kina zaton ko kamamu yayi zai ɗauki wani mataki akan hakan ne? Kafin kiyi shi ya fara ko baki da labarin abinda ya rabashi da matarsa ne?

Ni yanzu ki san yanda zaki zille muje mu dawo dan wlh tun waccen ranar kin barni da kewarki ko yi nawa zanyi da ita bana jin na ƙoshi sam bata da juriya kamarki" ya ƙarasa yana ɗage mata gira cike da iskanci.

"Ni dai kayi haƙuri ka rabu dani babu wata sauran alaƙa tsakanina da kai" ta faɗa kafin ta raɓe shi ta bar gurin. Murmushi mai kama da dariya yayi yana binta da wani kallo ya ce
"Baki isa ba yarinya, Ahlan bai taɓa neman wani abu ya rasa ba tunda kuma aka fara sai an cigaba har sai idan ni na daina yayinki tukunna".
Mota ya hau ya bar Asibitin ba tareda Fadila ba.

*KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*KURA A RUMBU ya kammala, a biya naira 1k domin karanta shi complete*
*A tuntuɓe ni kai tsaye akan 07061838488*

*GODIYA TA MUSAMMAN*
*Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (SWT) daya hore mun lafiya da tsayin kwana har na kammala rubuta wannan littafi. Salati da aminci su tabbatar ga fiyayyen halitta, katimul anbiya'i, Nabiyyina Muhammad (SAW). Ya Ubangiji ka sake cika zukatanmu da imani tareda soyayyar mafi soyuwar halittarka Annabi Muhammad (SAW).*
*Ina roƙo Ubangiji ya haɗa mu a ladan abinda na rubuta na alkhairi ina kuma roƙonsa da ya shafe zunubin kura-kuren da na aikata a cikin rubutuna. Allah Alhamdulillah nagode da ni'imar da kayi mun*

*Godiya musamman gareku makaranta da kuka bada lokacinku cikin wannan doguwar tafiya ta littfain KURA A RUMBU. Idan nace zan lissafo sunaye toh tabbas littafi mai shafi dubu yayi mun kaɗan. Littafin nan bai zama cikakke ba sai da gudunmawar ku, da kalmomin ƙarfafawa, shawara da goyon bayan da kuka bayar, Nagode ƙwarai da karamci haɗi da soyayya ina fatan ubangiji ya fini yabawa. Ina roƙon Allah Ya saka da alheri ga kowane ɗaya daga cikin ku. Allah Ya sanya wannan rubutu ya kasance hanyar tunani, gyara, da faɗakarwa ga duk wanda ya karanta shi.*

*Idan littafin KURA A RUMBU ya taɓa zuciyarku ko ya ƙara muku hangen nesa game da rayuwa da soyayya, to lallai burina ya cika, ina fatan zakuyi amfani da saƙon da yake ciki ku watsar da duk wani abu daya ci karo da tunani ko rayuwa ta zahiri*
*Allah Ya sa mu dace a dukkan al'amuranmu. Amin.*

*LUBNA SUFYAN yau Allah ya nufa kwana uku ta cika 🤣🤣🤣🤣 na gode ƙwarai da karamchi da ƙarfafa guiwa. Allah ya raya miki Yusra*

*MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*LAST PAGE*

Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita.

Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya dole ya baka tausayi gashi tambayar duniya yaƙi faɗawa kowa abinda yake damunsa sai dai ya samu guri ya zauna shiru wani wani lokacin har idanuwansa su tara ƙwalla da gani akwai wani abu da yake cin ransa amma ya kasa furtawa.

Ranar wata talata daya kama kwana huɗu da sallamo shi daga Asibiti, suna zaune tareda Abubakar da Nasir sai Alhaji Sani Abokinsa da kuma Anty Amina suna jajanta batun motarsa da zuwa lokacin ta tabbata sacewa akayi. Ya ce musu a waje ya barta waccen ranar kuma da muƙullin a jiki sanda ya koma gidan. Kwana biyu kenan daya fara buɗe baki yana magana sosai har yayi hira da masu zuwa dubashi.

Ranar da aka sallamo shi Abubakar yake tambayarsa batun motar tunda Zulaiha tace sanda ta fito itama bataga mota a gurin ba kawai ya saddaƙar itama Azal ta faɗa mata an sace.

Abubakar ɗin ne yaje har gurin masu gadin layin ya tambayesu tunda ba yanda za'ayi ace an sace mota suna gurin suce basu lura ba suka ce masa tabbas suna zaune aka fita da motar amma basu lura bashi bane a ciki tunda sunga shigarsa kuma dama ko horn bayi musu yakeyi ba yanzu balle sallama shiyasa suma da ya taho kawai zasu buɗe masa get ya wuce ne ba ruwansu dashi.

"Ai kaga illar rashin zaman lafiya da mutane, banda sakarci ta yaya za'ayi ka ringa faɗa da masu gadi? Yanzu da lafiya lau kuke zaune ai ko banza ka taho ka saba musu magana idan suka ji shiru zasu iya zargin wani abu ƙila da haka bata faru ba. Yanzu ai sai a kai report police station idan da rabo ƙila a dace a gano wanda ya ɗauka" Alhaji Sani ya faɗa.
Nasir ya buɗe baki zaiyi magana kenan Zulaiha ta shiga falon da sallama.

A bakin ƙofar ta tsaya tana kallon Abubakar tace
"Wasu mutane ne a waje suke sallama dashi".
"Su waye, ko baki sansu ba?"

"Jami'an tsaro ne" ta bashi amsa dai-dai lokacin da baƙin su biyar suka yiwa kansu iso zuwa falon.
Ciki suka shiga, wanda yake Shugabansu ya zaro ID card daga aljihun rigarsa fuska babu wasa ya ce
"Sunana ASP Ɗanjuma Hassan, wanene Bilal Saleh a cikinku?"

Gaba ɗaya suka kalli Bilal ɗin daya sunkuyar da kai ƙasa cikin yanayin na tashin hankali dan lokaci ɗaya zufa ta fara keto masa tamkar wanda ya zauna akan kunama. Abubakar ne yayi ƙarfin halin cewa

"Lafiya dai ranka ya daɗe? Wani abun ne ya faru?"

Ba tareda ya bawa Abubakar ɗin amsa ba idonsa na kan Bilal yace

"Mun zo ne mu tafi da kai bisa zargin fasa shago tare da satar kayan ciki. Haka kuma, ana tuhumarka da zamba cikin aminci, da kuma damfara ta hanyar sayar da gida da takardun bogi, ga kuma laifin raina kotu ta hanyar ƙin amsa gayyatarta.
Kana da ‘yancin yin shiru, domin duk abin da ka faɗa yanzu zamu iya amfani da shi a matsayin hujja a gaban kotu.
Kana da ‘yancin ɗaukar lauya domin kare kanka, dan haka yanzu zamu tafi da kai office domin ci gaba da bincike. Officer, saka masa ankwa" ya ƙarasa maganar yana kallon Ɗansandan dake riƙe da ankwa yana jiran umarni. Gurin Bilal ɗin da yayi mutuwar zaune ya ƙarasa ya kamoshi babu ɓata lokaci ya buga masa Ankwa.

Salati Anty Amina da Zulaiha suka shiga yi kafin suka fashe da kuka a tare, Nasir da Alhaji Sani suka miƙe tsaye kowanne cikin tashin hankali. Cike da damuwa Abubakar ya ce
"Amma ranka ya daɗe baya cikin yanayin d zai iya fuskantar shari'a a yanzu bashida lafiya bai daɗe da fitowa daga Asibiti ba".

"Zaka koya mana aiki ne Malam? Ko a gadon Asibiti yake dole doka zatayi aiki akansa batun rashin lafiya ko wani abu kuma wannan bincike ne zai tabbatar duk kuma abinda ya kamata za'ayi."

"Ranka ya daɗe amma da anyi haƙuri ba sai an saka masa Ankwar ba sai a tafi a haka" Alhaji Sani ya faɗa ba tareda ASP ya kalleshi ba yayiwa yaransa alama da su wuce haka suka tasa Bilal da ko uffan bai iya cewa ba kuma bai kalli kowa ba suka fice daga gidan Alhaji Sani da Nasir suka bisu.i
"Kubar kukan haka Anty, bari mu bisu dan Allah ki kira Yaya Alhaji ko Yaya Aminu sai su samemu a station babu abinda zai faru insha Allah amma dan Allah kada ki bari Hajja taji maganar nan" Abubakar ya faɗa.

Cikin kuka tace
"Kaima ka san su Yaya ba zasu yarda su shiga maganar nan ba tuntuni irin wannan ranar nake guje masa amma yaƙi ji itama Hajja ta ringa goya masa baya yanzu wa gari ya waya?"

"Yanzu ba lokacin mayar da magana bane Anty bari naje" ya bata amsa yana ficewa da sauri jin tashin jiniya alamar sun wuce ko ya akayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login