Showing 198001 words to 201000 words out of 257873 words

Chapter 67 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

516

ce yanzu ka rasa in d zaka ringa kawo matan banza ne shine zaka fiti kana wani ƙaramin hauka"

"Kai, dan abu ta kazanka ni kake faɗawa haka?" Bilal ya zaburo kamar zai kama shi da kokawa. Alhaji Bashir, mijin Maman Yusuf da mai gidan da yake jikin nasa Alhaji Sharif suka ƙaraso gurin da sauri dukda tun daga nesa duk sun ji abinda Bilal ɗin da kuma masu gadin suke tattaunawa. Su suka shiga tsakani ganin Basiru ya tattare hannun riga yana jira Bilal dake hargagi kamar zai kai masa duka Ilyas yana riƙeshi.

"Haba Alhaji Bashir, wane irin abu ne haka da girmanka zaka tsaya kana irin wannan abun da yara?" Alhaji Sharif da ya shiga tsakani ya faɗa. Bilal yayi tsaki yana kallon masu gadin ya ce
"Sata suka mun a gida na tambayi ba'asi kuma shine zasu mun rashin kunya".

"Me aka satar maka?" Alhaji Bashir ya tambaya kafin Bilal ya bashi amsa Ilyas yayi saurin cewa
"Ranka ya daɗe tabarmar kunya kawai yake naɗewa da hauka, dama kusan wata biyu kenan ai matar gidan bata nan to shine yau suka zo suka kwashe kaya da alama aure ya ƙare shikenan fa zai sauke fushinsa akanmu sai kace mu muka saka ya saketa".

"Yanzu menene amfanin haka saboda Allah? Sanda aka kwashe kayan nan babu kowa ma a layin sai su, ni kaina ba dan yar uwarta data shiga gidana neman abu ba ba zan san meya faru ba amma yanzu ka fito kana hayagaga a layi har masu wucewa ka sanar musu da kun rabu da matarka" Alhaji Bashir ya faɗa kafin ya juya kan masu gadin ya ce su wuce bakin aikinsu kowa ya fashe suka barshi shi kaɗai yana muzurai da zare ido. Sai da ya gaji da tsayuwa kafin ya koma ciki ya tsaya cike da tunanin mai ya kamata ya yi yanzu? Ko bargo baya tunanin akwai da zai shimfiɗa ya kwanta akai kafin wayewar gari, haka ya ɗauki tsintsiya a daren sai da ya share compound ɗin tas ya watsa sharar waje yanayi yana tsinewa yan uwan Halima da suka masa wannan abun.

Ɗakin sa ya shiga ya tsinci kaya kala biyu ya saka a leda dan yana ayyana abinda zaiyiwa Halima akan wannan tozarcin da ta saka aka masa, hatta takardunsa da suke cikin jakunkunanta sai da suka zazzage masa balle kayan sa na cikin akwati tunda dama ai ba shi ya siya mata ba suke nufi. Kulle gidan yayi bayan ya saukw wutar gaba ɗaya dan ba ƙaramin baƙin ciki ke kama zuciyarsa idan yaga kangon da aka bar masa ba.

Hotel ya tafi ya kama ya kwana yana Allah Allah washe gari tayi yaje ya saukewa Halima kwandon rashin mutunchi, banda dai su sun gaji tsiya sai kace wasu kayan Gwal ne aka saka mata da dan an saketa zasuce zasu kwashe kaya ya tabbatar masu arziƙin gaske ba haka sukeyi ba kuma tsabar rashin mutunchi har ajiye ajiyen sa na cikin fridge da freezer suka tattara suka tafi kamar ubansu ya siya masa.

Haka ya kwana saƙe saƙe, washe gari da wuri ya fita gurin kafinta dan ya samo kayan da za'a jerawa Zulaihan. Ya rigada ya karɓi kuɗin sa na kayan daya fara aka farayi tuni ƙarya kawai yayi mata, ya je ya samu ready made kaya kuwa na wata amarya da akayi sai kuma aka fasa auren, dake yana tsaye suka gama magana da kafintan daya karya wa kayan farashi saboda tsabar mugunta tamkar ba'a gurinsa sukayi ba wai ai tunda an rigada an ɗauka kaya sun zama second sai kuma da Bilal ɗin ya nuna yana son su ya nemi raina masa wayo zai siyar masa a sababbi daƙyar dai ciniki ya faɗa ya ɗaukar mata su set ɗin gado da kujera masu kyau harda dining ya ƙara wani set ɗin gadon ɗaya da zai saka a can ɗakinsa, har kujera ya so ya siya sai dai kuma abinda yake account ɗin sa ba zai ishe shi ba dan akawai sauran abubuwan da yake so yayi bayan nan.

A gurin ya bar musu akan gobe Alhamis za'a je a ɗauka dan yana so a ɗan sake fentin gidan yau dukda ba abinda gurin yayi amma dai amarya ce zata shiga ya kamata a gyara mata. Daga nan ya wuce gidan Hajja ya faɗa mata Halima tazo ta kwashe kaya,

"Matsitana banza da wofi, ka rabu da ita taje tayi ta yawo da aurenka a kanta ba kaya ba koma me ta kwashe a banza dan wlh ba zaka saketa ba" Hajjan ta sake jaddada masa. Shi dai bai ce komai ba dukda yayi niyyar ya gaya mata ya saki Haliman amma yanda ta haƙiƙance tana jaddada ba za'a saketa ba shiyasa yayi shiru dan ba laifi yau ɗin ya samu ta sake masa fuska dan a gidan ya tarar da Anty Habiba ya san kuma ba zai wuce zancen tariyar Zulaiha sukeyi ba tunda ya tura mata kuɗin da tace zasuyi yinin biki da shi tun jiya.

"Yanzu ina kuka tsaya da ita waccen shaiɗaniyar kuma?" Hajja ta dakatar dashi ganin yana shirin tashi, bai fahimci wa take nufi ba gane hakan ya saka ta ce

"Jalilah mana, ka san dai kamar da ƙasa aurenka da ita dan bata isa ta iskanta mun kai ta zubar mana da mutunchi sannan kuma ta ce ba zata aureka ba" cewar Hajjan. Abun sai ya ma bashi dariya, sai kace shine macen irin saurayi ya yaudareshi Hajjan take cewa dole sai an aure shi kuma. Anty Habiba ce ta ce

"Yanzu Hajja ba zaki bar maganar nan na har sai ta fita inda ba zamu so ba ko? Abinda ya faru ya faru sai mu lulluɓe magana ta wuce amma so kike sai kin ɗaga ta, tsakani da Allah yanzu ko ce miki yayi zai aureta sai ki yarda? Mai za'ayi da mace irinta? Bayan shi kika san maza nawa take ta'ammali dasu da har zaki ce kina so ki haɗa zuri'a da ita bayan abinda ya faru? Toh Allah ya rufa mana asiri gaskiya ba zaki bankaɗa mana ba kuma babu wannan maganar kai Bilal babu kai babu ita ka kama matanka ka riƙe Allah ya yafe maka abinda ya faru a baya kawai".

Haka ya lallaɓa ya fice, anan unguwar ya samu wanda zasu masa aikin fenti suka tafi tare suka duba ya basu kuɗin da suka buƙata na abinda zasu siya daga nan ya wuce gidan Hafiz wanda ya kira shi akan idan babu damuwa yana so ya ganshi.

Shi kam yanzu idan ba Hafiz ɗin ne ya kirashi ba mantawa ma yakeyi da wnazuwarsa a duniyar nan baki ɗaya. To dama dalilin bibiyar Hafiz ɗin ai saboda abun hannunsa ne da bajintar da yakeyi masa yanzu kuwa da ya fara kama ƙasa shima gani yake Hafiz ɗin ba komai bane dan sai ya ga kamar Jalilah ma tafi Hafiz ɗin kuɗi saboda irin kyautar da takeyi masa a dunƙule tashi ɗaya sai Hafiz ya rabata gida goma ko fiye da haka.

Fuska a sake kamar babu wani abu tsakani Hafiz ɗin ya tarbeshi, Suhaila ce dai ya karanci canjin fuska a gurinta hakan kuma ya saka ya zargi ko dai Halima ce ta kai masa ƙarar sa shine yar taya ɓera ɓuruntu take tayata fushi da shi.

"Baka kyauta ba, ko me Halima tayi maka bai kamata ace zaka turata gida saboda ka samu wata ba" Hafiz ɗin ya faɗa masa dalilin kiran, ya wani yi kinini da fuska ya ce

"Gaskiya ni ban fiya son ana tsoma mun baki cikin sabgar gida na da iyalina ba shiyasa ko iyayena bana kaiwa ƙara balle wasu mutane can bare".

Hafiz dai jijjiga kai yake yana kallon sa yan kuma sauraron abinda yake cewa, wato shine baren? Ko da yake tuni lamarin Bilal ɗin ai ya gama bashi mamaki ko mai zaiyi yanzu sai dai ya kalle shi da ido kawai.

Bilal ya cigaba da cewa
"Ni bani da lokacin da wani zai ajiyeni yanzu ya ringa gaya mun abinda ya kamata nayi da wanda ba zanyi ba, ita bata san dama haƙuri kawai nake ina zama da ita ba dan da ita namiji banbancinsu kaɗan ne a guri na. Saboda kuna na ce zan auro wacce nake so shine zata tada fitina, tace na saketa tun ba'aje ko ina ba shine zata fara bibiyar neman sulhu? Toh wlh ko zan mayar da ita sai ta ji a jikinta ta yanda ko wani ya sakw zugata ta mun abinda tayi a baya ba zata kuskura ta ji ba".

Mamakin jin wai ya saketa ya hana Hafiz sake ce masa komai sai kallonsa kawai da ya ringayi, daƙyar ya ce
"Ai bata gaya mun ba, toh Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi a tsakaninku amma gaskiya kamar kayi ganganci"

"Ba wani ganganci ni nake zaune da ita ni na san halinta ku kawai daga nesa kuke mata kallon ta ƙwarai amma yarinyar nan bata da mutunchi, kawai dan ni ba mai tona sirrikan mutane bane amma dai shikenan" ya sake faɗa kafin yaja farantin kayan ciye ciyen da sai da Hafiz yayi magana kafin Suhaila ta saka mai aiki ta kai masa.

Shi dai Hafiz kallon sa kawai yakeyi bakin sa na so ya furzar da maganganun da suka cika shi taf amma ya danne domin komai yana da lokaci. A hankali ya ce masa

"To ita wacce ka aura ɗin yanzu ka san halinta ne?"
"Yarinyar da na shafe sama da shekara goma da ita kake tambaya na san halinta? Kamar yanda na san kaina kuwa" ya bashi amsa, Hafiz ya sakeyin shiru sannan ya ce

"Allah ya sanya alkhairi toh, ni na ɗauka ma yar gida za'ayi da uwarɗakin naka dukda kana ɓoye mun, ashe kai da Target ɗin ka a gefe".

Dukda Hafiz bai ambaci sunanta ba amma ya gane wa yake nufi cewar da yayi kuma wai dukda suna ɓoye masa ta saka lokaci ɗaya tashin hankali ya rufto masa har sai da ya ƙware da lemon da yake sha ya shiga tuttula tari shi dai Hafiz sannu yake masa a ransa yana dariyar wautar Bilal ɗin. Shi fa duk a zatonsa ya fi kowa wayo ne ko me yake nufi oho?

Sai da tarin ya lafa masa kafin ya ce
"Wacece uwar ɗaki na?" Yana kallon Hafiz ɗin ƙasa ƙasa shi kuma ya gyara zama ya ce
"Jalilah mana. Ai ta gaya mun soyayya kukeyi a yanda ta ce nan da yan satittika ma za'a fara maganar aurenku, amma na san bata da labarin auren da kayi ko? Dan na santa da baƙin kishi gaskiya da taji da yanzu ta tayar da hankalinta musamman da na fahimci tayi nisa a soyayyarka kuma da gaske take. Amma wai yaushe duk hakan ta faru bani da labari?"

Bilal dai yanda kasan wanda za'a rataye haka ya tsure, fuskarsa kaɗai zaka kalla ka hangi tsantsar tashin hankalin da kalaman Hafiz suka jefa shi a ciki.

Tunani yakeyi, me da me Hafiz ɗin ya sani? Iya kacin zancen soyayyar su? Ko kuwa harda ɓoyayyiyar alaƙar da take tsakaninsu? Kai ko ma dai Halima ta faɗa masa komai kawai wasa yake masa da hankali ne?"

Ya akayi ne duk ka wani firgice daga zancen Jalilah kar dai kaima tsoronta kakeyi?" Hafi ya faɗa cikin wasa kafin ya cigaba da cewa

"Allah ne ya kamata dan na tabbatar yaudararka kawai takeyi amma Jalilah ta fi ƙarfin matasa irinmu yanzu ai ta yuwu sai dai kawai kaji tayi aure dan akwai ƙishin ƙishin ɗin da naji kan wani Senator da yake sonta kamar har an kai gaisuwa ma"

Sai ya ji kamar an tsundumashi a ruwan ƙanƙara har ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke Hafiz kuwa canza akalar hirar tasu yayi zuwa zancen office wanda shi ya bar gurin yanzu ya koma jagorancin ɗaya daga kamfanonin mahaifinsa dama shi ya nace akan aikin gomnati amma Babansa baya so yanzu kuma da kansa ya saki, farin ciki ya mamaye Bilal, bai wani damu da ce masa da yayi gaskiya idan bai yi wasa ba za'a iya sallamarsa daga aiki saboda sunce sun gaji da abinda yakeyi gashi dama anyi sabon DG a ministry akwai shirye shiryen kora da ɗibar sababbin ma'aikata kuma yanda Ogansu na nan yake ƙorafi akansa yana tsoron kada abun ya rutsa da shi.

Ko a jikinsa domin ko an koreshi ya san zai samu in da zai lafe a kamfanin Hafiz ɗin. A gidan ya kusan wuni suka sha hirar yaushe gamo har ya tallatawa Hafiz shagunan gurin Jalilah wanda ya ce na wani yayan abokinsa ne saboda waɗancan mutanen da aka ce suna so yaga alamar wasa a lamarin su yana kwatantawa Hafiz ɗin in da suke kuwa ya nuna sha'awa har ya ce bari rana tayi sanyi sai suje su duba dan dama yana neman shaguna zai siya.

HALIMA

Sosai naji daɗin sallar da nayi, har gabannin asuba kafin bacci ya fara fizgata amma na daure sai da nayi sallahr asuba sannan na kwanta. Gurin ƙarfe takwas Anty Labiba ta tashe ni, na kalleta ganinta cikin shiri da key ɗin mota a hannu.
"Zan fita, ga abin kari nan a dining, ki tashi da wuri dan Allah kiyi lunch kin san za'a kaiwa yara makaranta idan akwai abinda kike buƙata a taho miki dashi daga gidan Mama kuma ki kirani anjima dan kar in manta" ta faɗa tana kallona. Na yamutsa fuska, abinda ya faru jiya ya shiga dawo mun sai nayi narai da ido na ce

"Nima ai gidan zan tafi"
"Yana falon sa kije ki gaya masa" ta bani amsa tana nufar ƙofa, sai na miƙe ina cewa

"Ni dai wlh gidanmu zan tafi in dai na son a takurawa rayuwar mutun ba ta yaya za'a ce ya zauna a nan gidan?"

Bata ko kalleni ba tayi ficewarta dan haka na haɗiye kukan da na so in fasa mata na koma na kwanta tunda ta ce Uncle Saleh yana nan amma da zarar ya fita zan kama gabana dan ba zan zauna a gidansu ba wlh.

Bacci na so ta koma amma na gagara yi sai kawai na tashi nayi wanka na shirya kafin na fita na karya. Bayan na gama na ɗauki wayarta a shiga latsawa dan babu wani aiki da zan mata a gidan sun gama komai, fitowar Uncle Saleh ta saka na shiga taitayina na sauka ƙasa na shiga gaishe shi sai ya dakata ya samu guri ya zauna, nasiha ya shiga mun amma da yake muryar tasa kullum a kaurare take fuska kuma babu fara'a sai na ringa jin maganganun nasa kamar faɗa. Ya gama ya fita kaina na ƙasa sai da na ji ya rufe ƙofa kafin na kona kan kujera na zauna ina sauke numfashi.

Ni kaina ba kamar yanda na kwanta jiya ba yau ɗin da na tashi na jini sakayau kamar an sauke mun wani nauyi a jikina, tabbatas sallolin da nayi sun taimaka mun matuƙa gurin samun nutsuwa amma dukda haka isanyna tuna wai Bilal ya sakeni sai hawaye sun tarar mun a ido ban dai basu damar zubowa bane na daure.

Kan wayata na koma na lalubo number Hansa'u dan ina tura mata text dan ta nan kaɗai nake samunta yanzu shima sai taga sama ne take maido mun da amsa, ido na ya sauka kan sabon saƙo daga Bilal wanda naga time tun biyar bata gama cika ba aka turo, maganganu dai marasa kan gado ya aika mun yana sake jaddada mun sai nayi nadamar rabuwa da shi. Sai naji abun ya bani dariya ma, a fili na ce

"Allah ba dan halina ba ka yaye mun jarabtar son bawan Allah ka bani ikon nuna masa ni ba banza bace yanda yake kallona". Hawaye suka shiga silmiyo mun, Bilal kallon ballagaza yake mun akansa dukda ba laifinsa bane ni na nuna masa hakan nake a soyayyarsa amma yanzu idan Allah ya yarda zanwa kaina faɗa, ko da ace akwai rabon sauran zama a tsakanin mu zai nemawa kaina mutunchi.

"Ashe baki haƙura ba kenan?" Zuciyata ta tuhumeni ban bata amsa ba na kawar da zancen ta hanyar rubutawa Hansa'u saƙo "Bilal ya sake ni, dan Allah idan kina gari ki zo idan ma bakya nan muyi waya dan ina tsaka mai wuya ina buƙata shawara" abinda na aika mata kenan ko minti biyu cikakku kuwa ba'ayi ba sai ga shi ta kira, sai da ta gama ihun murna da hamdala kamar kafin muka shiga magana ta nutsuwa kuma ta fahimta. Yinin ranar sur maganganunta na ringa tisawa wanda zallar gaskiya ce a cikinsu na kuma samu ƙwarin guiwa domin yana daga dalilin da ya saka nake son Hansa'u, za muyi faɗa ta zageni amma kuma ba ta gajiyawa zata faɗa mun gaskiya ta sigar data san zan fahimta saɓanin Anty Labiba da take ganin faɗa da masifarta ne zasu saka na gane abinda take haska mun.

Sai dare Anty Labiban ta dawo da akwatunan kayana harda uniform ɗin NYSC na nan take labarta mun sunje sun kwashe kaya.
Har shara da mopping mukayi, duk albarka da arziƙin da kika je da shi gidan mun kwashe abin mu. Ni wlh badan Yaya Fauziyya ta hana ba so nayi a nemo yan gwangwan muyi musi gwanjon ƙofofi da windunan gidan tunda da kuɗin Abba aka siya amma tace wai ba haka ba. Haka kitchen cabinets ɗin nan nayi takaici Allah bana jin ma zan haƙura sai na koma an ɓalle su"
ta faɗa sai ta bani dariya ma.

A hankali na fara sakawa kaina dangana na shiga Iddah, dama kuma washe garin da akayi sakin da yamma sai ga period wanda na tabbatar damuwa ce ta matso mun da shi domin akwai sauran lokacin zuwansa. Anty Labiba ta ringa cewa
"Ai gara kiyi ki gama tun kafin ɗan akuyar ya ce zai waiwayoki dukda ko da uwarsa yake tafe bai isa ya ce zai maidake kafin ki gama iddah ba wlh Mu'azzam zan saka ya sake tare shi a hanya ya masa dukan tashi kasha gishiri ya ƙarasa miki ɗayan kawai a huta" ni dai jin ta kawai nake ina murmushi, wani nishaɗi naga tanayi, ba ita ba, har Mama da mukayi waya jin muryarta nayi a washe ba kamar lokutan baya ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login