Showing 72001 words to 75000 words out of 257873 words
kawai na tashi na bashi guri ba tare da nace komai ba.
Washe gari bayan an sakko daga sallar idi ya kira ni wai na shirya na tafi can gidan nasu muyi aikin nama; se naji maganar ma kamar ta rainin wayau. Shi da yace ya kai can ne saboda ina fama da kaina ba zan iya a gida na ba kuma yanzu in tafi taya su acan. Ce masa nayi kaina na mun ciwo se dai gobe, nayi kwanciya ta haka na wuni ƙamshin suyar hanjin maƙwafta duk ya gama cika mun ciki na ringa ji kamar na yafa mayafi na leƙa ɗaya daga gidajen a bani taɓi. Naci burin suyar naman sallah har spices na karɓo a gida da naje amma ya wani ɗauka ya kai gidan su. Da magriba naji ba zan iya haɗiye kwaɗayi na ba kawai na kira Mama nace ta bayar da hanji a kawo mun na ji daɗin da bata tsaya bin ba'asi ba tace toh ba a ɗauki lokaci ba kuwa Imam ya kawo mun da zafin sa da alama sunyi daren aiki lokacin aka sauke.
A falo na zauna na baɗe hanjin da yajin daddawa ga zoɓo na me sanyi a gefe ina ci farin ciki na ratsa ni. A haka ya shigo ya same ni; ya mun kallo ɗaya ya ɗauke kai. Ban damu ba na shiga yi masa sannu da zuwa ya amsa a ciki ya wuce ɗaki ko me ya tuna kuma se gashi ya fito fuska a sake har ya zauna muka ci kayan cikin tare yana mun mitar na rage cin yaji. A kitchen na tsunto farar leda daya ajiye da wani yan kayan ciki kamar za'a bawa mage tun daga kalar suyar ma ji nayi zuciyata ta fara tashi na mayar in da na ganshi na ajiye masa washe gari kuwa tun sassafe muka fita tare ya kaini can gidan su, yana fita nima na sulale ban ko yiwa Hajjan sallama ba na tafi gidan mu shikenan salsalar laifin nawa. Har aka ci kwana uku da sallah ban ga an aiko da namu rabon naman ba tsautsayi yasa nayi masa zancen shikenan ya balbale ni da masifar da se da naji ina ban kula shi ba.
Wai har shi yake ce mun zalamammiya akan nama, dama tun da aka zo ɗaukan Ragon sun gaya masa maganganun dana faɗa kawai shiru ya mun yanzun ma kuma yana sane ya hana a kawo dan yaga gudun ruwa na amma na kasa haƙuri se da na tambaya ko mai se na nuna zalamata ba zan taɓa haƙuri na jira naga abu ze tarar da ni ko kuwa se in fara maganganu ina kai magana gidan mu. Na ringa juya maganar a raina wai nice zalamammiya. Kuna ya rasa akan me ma ze mun cin mutunchin se akan nama, naman da bayan soyayye da dambu da kilishi har ɗanye aka kawo mun daga gidan mu na saka a freezer amma shine yake faɗin nayi zalama akai.
A duk abinda yake mun babu wanda naji ciwon sa irin wannan duk yanda naso na danne zuciya ta kar na maida masa da martani na ƙasa daga ƙarshe nace masa zalamamme ya san kansa domin tun kafin a kawo lokacin ze ɗauki naman layya ya bani ni na bashi yafi sau ba adadi. Ina wuta kuma ya jefani a ciki? Daga martani yace na masa gori, ya ringa jidali kwana da kwanaki be sauka ba se da yaga na kwanta riris rai a hannun Allah muka je asibiti aka ce jini na ne ya hau kuma shikenan haka suka cinye naman ko tsoka ɗaya ba'a bani ba ƙarshe ma saboda rashin kunya cikin nawa ya ringa ɗiba yana bawa abokanan sa idan sun zo ni dai nawa ido kawai dan lamarin Bilal ya fara shallake mamaki tsoro ya fara bani.
A haka ciki na ya shiga wata na takwas har ya kusa tara amma ko pant be siya ko ya bani na siya ba. Ban damu ba; saboda cikin abinda nake samu na siyi duk wani abu na buƙatar farko irin wanda nake so. Abin da na sakawa raina shine ba zan taɓa tsayawa jiran Bilal a komai ba, idan ya ɗakko ya bani fine idan ma be bani ba zanyi wa kaina na sakawa raina komai lokaci ne akwai ranar da dolen sa ze yin.
Tafiya ta taso wa Bilal zuwa Enugu zasu halarci wani taron bita. Tafiyar kwana huɗu ce, tunanin yanda zanyi na shiga yi dan bazan iya zama ni kaɗai ba. Da farko nayi tunanin ko na tafi gida se kuma na canza shawara kawai tun da Amirah suna hutu se na kira ta ta taya ni zama kawai. Da ze tafi yace mun Abubakar ze zo ya zauna a gidan kafin ya dawo, dake an gyara fallen ɗakin dake tsakar gida nan ya fito masa da katifar ɗakin sa tunda akwai banɗaki ze zauna a gurin.
Dubu goma ya bani yace idan na fita awo washe gari se na biya nayi yan tsince tsince kafin ya dawo muga sauran abinda za'a siya.
Mama na kira na gaya mata Bilal yayi tafiya Amirah tazo ta taya ni zama da yamma kuwa se gata, ni shaf na sha'afa ban gaya masa zan kirawo Amirahn bama se washe gari da muna waya yaji muryar ta yake tambaya ta yaushe tazo na sanar masa tun jiya na kirata.
"Amma da kin gaya mun zata zo ai ba se Abubakar ya zo ba shi" ya faɗa se nace masa
"To yanzu ban da abinka meya haɗa zaman Amirah dana Abubakar? Na ɗauka ya zo ne saboda ko da wani abu na emergency ze tashi akwai namiji a gida ita kuma kasan ai ina buƙatar me kama mun ayyukan cikin gida shara da sauran su tun da kai kake yanzu kuma baka nan koma ba haka ba idan ciwo ya tasar mun cikin dare Abubakar na can waje ta yaya za'ayi yi ya sani?"
"Toh ai da kawai se kiyi tafiyar ki gida idan na dawo se ki dawo amma meye amfanin a cika gida da mutane" ya sake faɗa, se nayi shiru kawai dan nawa kaina alƙawarin dena biye masa amma har raina naji zafin maganar zuwan Amirah yake nufin an cika masa gida da mutane tunda shi ya kawo Abubakar ai. Da yamma muna zaune Abubakar ya shigo bayan mun gaisa yace mun ze wuce gida, ban tambayi ba'asi ba tunda na san dalili mukayi sallama ya tafi. Har ya kwana huɗun sama muke gaisawa in ya kira sau ɗaya shikenan shima ba wata doguwar hira zamuyi ba ze kashe. Haka ya dawo yana ta wani fizge fizge ni kam ko a jiki na dan babu in da Amirah zata je ma se na haihu tunda hutun su da saura sosai.
Kwanan sa biyu da dawowa be dai ce mun komai akan zaman da takeyi ba amma yanayin sa na fahimci ba'a son ransa ba, to mutumin daya kori ƙanwar sa ciki ɗaya ma me ze dame ni dan ya nuna baya maraba da zaman tawa ƙanwar?
Kwana biyun a nan cikin ɗakuna na yake kwana rana ta uku da dawowar sa ya koma can part ɗin sa, dana masa magana se cewa yayi wai babu privacy yana son ya sake babu dama saboda Amirah. Murmushi kawai nayi na rabu dashi, da dare yayi na bishi can ɗakin yace da nayi zamana ai be kamata na barta ita kaɗai ba; se kace wata jinjira; ko a fuska ban nuna masa na fahimci abinda yake nufi ba. Dan ya kori yar uwarsa ni bazan bashi ƙofar da ze hana nawa yan uwan zuwa ba. Haka muka cigaba da zama idan ya shigo ta gaishe shi se dai ya amsa a fizge ya wuce wani lokacin ma baze amsa ba Amirah da saurin fushi tace ta dena gaishe shi tunda ma abun nasa wulaƙanci ne.
Ganin duk hakan be sa nayi fushi nace ta tafi ba har an cinye sati ɗaya se ya canza salo ta hanyar rage cefane. Dama maneji nakeyi; a irin rayuwar dana tashi cikin ta soyayya ce kawai ta rufe mun ido bana ganin gazawar Bilal a riƙon gida.
Duk da Mahaifina ba wai shahararren mai kuɗi bane irin yanda mutane suke ɗaukar sa; shi ɗin mutum ne da idan ya samu naira ɗari ze kashewa iyalansa hamsin ya rabawa al'umar annabi hamsin. Baya tara kuɗi; kuma a koda yaushe yana gaya mana jin daɗin da yake gwada mana a yanzu shi kaɗai ne abinda ze bar mana koda bayan ransa mu ringa tunowa muna amsa addu'a. Musamman Mu'azzam da yake biyewa abokai suna hura masa kai ɗan Alhaji yaƙi mayar da kai ga karatu Abban yana yawan tunasar dashi akan ya tashi ya nemi na kansa. Ya kance
"Sanda mahaifina ya rasu gidan gadon mu kaɗai ya bar mana kuma munfi mu talatin akai wanda ko cewa akayi a ɗaga shi a siyar a lokacin da wuya mu tsira da naira goma goma. Ban dan daɗin kuɗi ko kadarar gado ba balle nayi kwaɗayin tara muku, abun da na fi yarda dashi ka gina yayanka ta yanda zasu rayu su riƙe kansu ba tare da tunanin dogaro da wani ba shine babban gadon da zaka bar musu dan haka ku tashi ku nemi na kanku jin daɗin rayuwa kam babu wanda ba zan baku ba har idan ina da hali amma karku taɓa sawa a ranku zan tara muku dukiya".
Duk wata cima ta jin daɗi muna cin ta a gidan mu shi kansa Bilal ɗin shaida ne, abinci se dai sha'awa tasa mu yishi babu nama ko kifi ba dan babu ba amma wai nice a gidan Bilal se in jera wata nama be shiga cikin tukunya ta ba balle aje ga tsire ko balangu idan ba muna tsananin yar daɗi bane ze siyo kuma ya cinye rabi in kwaɗayi ya dame ni se dai na bayar da kuɗi na ya siyo kuma ya fini ci. Dankali da doya kam banda albakacin na azumi dana samu na manta rabon dana sarrafa su a cikin gidan tun da kuma suka ƙare aka koma gidan jiya tun ma ina kwaɗayin har na haƙura. A ma ce su nama ba abu bane na kullum hatta da kayan miya da kamar gaske ze siyo da ɗan yawa a ajiye daga baya yace wai ɓarnar su nakeyi saboda na gansu a banza se dai kullum ya siyo ko ya isa ko karya isa oho wani sa'in se na gwammace nayi mai da yaji dan kayan miyan ba zasu wadace ni yanda nake so ba musamman idan miya zanyi nan kuma se ya fara bala'i yace ina kira masa tsiya a gida nayi mai da yaji. Abu dai iri iri ni kaɗai nasan me nake shanyewa, ina buƙatar wanda zan tattauna dashi ya bani shawara kuma duk wanda nayi tunani se naga dariya zasu mun su ce dama sun faɗa naƙi ji se kawai na bar damuwata a raina kullum addu'a ta da fatana Allah ya canza mun shi kyawawan halayen sa su rinjayi na banzar dan dai yanzu sun yi kankan kan.
Tun daren jiya nake ji na ba yanda na saba ba; yau ɗin mun tashi da walwala a gidan dan a ɗakin Bilal na kwana kusan kwana goma kenan tun bayan dawowar sa ya ƙaurace mun duk saboda Amirah. Se da ya fita aiki sannan koma na kwanta ina jin ciwon marar dake tsikarata idan ya tsinka sakan biyu uku kuma se ya sake ni shikenan se wani lokaci. Tunani nayi ko didimar da muka sha ce ta janyo dan daman nasan dole zanji jiki saboda yanda dani dashi ɗin duk muka manta da cikin gashi yanzu ni nake ji a jiki na.
Sanin se yamma ze dawo da Amirah ta tambaye ni me nake so naci nace ta mana taliya da manja; yar murji ce da jiya ta taho mana da ita daga gida. Ina bacci naji kamar ana shafa fuskata, hankali na buɗe ido naci karo da Bilal dake durƙushe kaina yana mun murmushi. Hanci na yaja yana cewa
"Sleepy head; tunda na tafi kike bacci har ƙarfe uku".
Yunƙurawa nayi na tashi ya taimaka mun nace
"Yau ka dawo da wuri" yana cire maɓallin rigar sa yace
"Gudowa nayi, duk kin tara mun gajiya so kawai nake na kwanta na huta" ya faɗa yana kashe mun ido ɗaya. Kasa nayi da kaina ina murmushi kafin na sauke ƙafafu na ƙasa ina cije leɓe saboda wani sharp ciwo daya ziyarce ni lokaci ɗaya kuma ya baje.
"Yunwa nake ji Halims me kuka dafa?" Ya faɗa yana shafa cikin sa. Na kalle shi, kamar in ce masa ai yasan cefanen mu ya ƙare be siyo ba kuma be bada kuɗin siyowa ba amma bana so nayi ruining ɗan farincikin da muka samu jiya zuwa yau se kawai nace
"Taliyar Hausa ce; bari nayi sallah lokaci na tafiya se na zuba maka" na ƙarasa ina nufar banɗaki. Yamutsa fuska yayi kafin yace
"Bazan iya jira ba gaskiya yunwa nake ji sosai"
"To bari nayi fitsari" na sake faɗa ina shigewa ciki. Daƙyar na miƙe bayan nayi fitsarin saboda yanda naji ɗan ciki na ya takure mun a mara kamar yana danno ni. Alwala nayi na fito ina dafa bango, ganin baya falo yasa na ƙwalawa Amirah kira ta fito daga ɗaya ɗakin da alama bacci ma takeyi se nace mata ta haɗawa Bilal abinci zanyi sallah na koma ciki.
A zaune na tada sallar dan bazan iya tsayuwa ba, ina raka'a ta uku na jiyo hargagin Bilal; bana jin me yake cewa se tashin muryar sa kawai kafin na jiyo ƙarar buga ƙofa bam. Ban ko tsaya addu'a ba ina sallamewa na miƙe daƙyar ina dafe baya na da ya ɗauki ciwo na fita falon; da fasasshen tangaran na fara cin karo se taliya da manja sunyi kaca kaca akan milk ɗin center carpet ɗina. Na buɗe baki zan kira Amirah se gata ta fito daga ɗaki tana jan akwatin ta fuska shaɓe shaɓe da hawaye kafin nace wani abu ta riga ni da cewa
"Wallahi tallahi darajarki kawai yaci, badai ya zagi ubana a cikin gidan sa yana ganin yaci banza ba? Allah yasa yayi gigin zuwa gidanmu wallahi se na nuna masa nima na iya rashin kunya" ta faɗa cikin kuka.
"Ke Amirah baki da hankali har tinƙaho ma kike da kin iya rashin kunya kamar wata me faɗar abin arziƙi wai ma tukunna dawa kike?" Na dakatar da ita. Ba tare da shakkar komai ba tace
"Dawannan butulun mijin naki da be dan halacci ba mana. Wai saboda na kawo masa taliya shine ya jefe ni da farantin ba dan Allah ya saka na goce ba ƙila da yanzu shirin jana'izata ake ya yanka mun wuya har yana zagin Abban mu yana ce masa matsiyaci mun zo zamu shafa masa tsiya a gida bayan shine babban matsiya ci..." Kafin ta dire na kwashe ta da marin da se bayan na aikata kuma nadamar yin sa ta kamani; dakewa nayi na shiga yi mata faɗa ina cewa
"Tarbiyyar da kika koyo a boarding ɗin kenan ta raina mutane saboda baki da mutunchi a gabana kike cewa miji na matsiyaci?"
"Ubana fa ya zaga; kenan kin bi bayan mijin ki ko?" Ta faɗa tsabar yanda take jan kuka da magana a haɗe kamar numfashin ta ze ɗauke.
"Zo ki fita daga gidan nan kafin na karya ki dan abu ta kazan ubanki" Bilal daya shigo yana naɗe belt a hannun sa ya faɗa; Amirah ta zabura cike da rashin kunya tace
"Badai ubana ba wlh" se yayiwo kanta na shiga tsakiyar su ina cewa
"Meye haka Bilal da Amirah zakayi faɗa saboda zubar da girma wannan wane irin abu ne?"
"Matsa mun Halima ko in haɗa dake da ita na koya muku tarbiyyar da ba'a muku a gida ba, ni wannan tatsitaiyar yarinyar zata cewa matsiyaci kina tsaye kina kallon ta har kizo mun da wata maganar banza? Da Allah malama matsa tun baki ja nayi abin da za'a ɗaure ni ba" ya faɗa yana ture ni gefe; dake ban zata ba se na tafi luu Allah ya taimake ni na dafe kujera Amirah ma ta riƙe ni. Belt ɗin ya ɗaga da niyyar dukan ta duk da azabar da nake ji saboda faɗuwar bazatan dana kusan yi ta tsinkar mun da zuciya haka na riƙe belt ɗin ina kuka nace
"Wlh se dai ka dake ni; har idan ka dakar mun ƙanwa se kayi nadamar hakan Bilal ina mai tabbatar maka da haka"
"Ni kike cewa zaki zaka nayi nadama Halima saboda zan hukunta mara tarbiyyar ƙanwar ki?" Ya faɗa yana nuna kansa idanun sa suna sake rikiɗewa da ɓacin rai. A ƙasa ya jefar da belt ɗin ya nufi ƙofa yana cewa
"Wallahi tallahi har idan na dawo na same ta a cikin gidana se na mata abinda idan an ga dama a kaini kurkukun ƙasan ruwa" yanda yayi furucin ba ƙaramin tsorata nayi ba; jiki na ya ɗauki rawa kamar mazari a ƙwaƙwalwa ta so nake na tantance da gaske Bilal ne ko wani daban? Ko kuma ya fara watsa ƙwayoyin gusar da hankali ne bani da labari?
Ji nayi ciwon dake taso mun ma ya kama gaban sa, na yunƙura Amirah na riƙe dani tace
"Ni dama na daɗe ina zargin yana shaye shaye; daga yanda yake yi da idon sa baya ma iya buɗe su da kyau za'a gane. Kowa se da yace karki aure shi kika ƙi, gashi nan ashe mahaukaci kika aura bamu sani ba" ta ƙarasa tana fashewa da sabon kuka.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*Page