Showing 33001 words to 36000 words out of 257873 words

Chapter 12 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

471

kawo gara babu wanda ya sake zuwa se ranar dana yi kwana biyar ne Gwaggo Habi tazo mun sallama zata koma Birnin gwari.

Ranar da muka yi sati biyu tun safe ya ce mun zamu fita. Na ringa murna dan ji nake kamar na shekara a guri ɗaya, na ɗauka ma da wuri zamu fitan dan haka kafin azahar na gama girki na shirya se yace mun se da yamma. Tsaf muka shirya, tsakanin ni dashi se ka rasa tantance wanda auren yafi karɓa. Munyi kyau jikin mu ya murje muna ta ƙyallin amarci abun mu. Muna tsaye a bakin titi muna jiran abin hawa ya kalle ni yana murmushi yace
"Kin ga da ace Abba ya sako miki mota a kayan gara hankali kwance zamu fita muna yangar mu a titi".

Murmushi kawai nayi ba tare da nace masa komai ba, gidansu muka fara zuwa tamkar zasu cinye ni saboda ƙauna. A can mukayi sallar Magriba kafin muka wuce gidan mu Hajja nata mu tsaya mu ci tuwon dare yaƙi, a cikin dubu goman da Hansa'u ta cire mun na bata dubu biyar ta ringa murna kuwa. Har goma muna gidan mu saboda Abba be dawo da wuri ba. Na lura da yanda Mama take ta bi na da kallo kamar na canza mata, se da muka shiga ɗaki take tambaya ta komai lafiya dai nace mata ƙalau.
"Haka ake so aji, Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitina. Da go be su Imam suke cewa zasu zo amma tun da kun zo yau se su bari se wani sati" na mairairaice nace
"Haba Mama zuwan mu daban nasu daban ai, dama goben ya ce zeje wani ɗaurin aure jigawa nasan kuma zeyi yamma kinga sa tayani hira". Da zamu tafi Mama ta haɗa mun su kuka daddawa da kuɓewa wanda dama tace se daga baya za'a kawo harda dambun nama da kilishi. Abba ne ya ce Mu'azzam ya kaimu tun da dare yayi, naso ace mun biya gidan Anty Labiba amma tun kafin mu fita daga gida da na yiwa Bilal maganar cewa yayi ba yau ba, da muka fito kuma dare yayi shiyasa kawai na haƙura se wani lokacin. Da yake mun ci abinci wanka kawai mukayi muka kwanta rungume da juna kamar ko yaushe.

Washe gari da wuri ya shirya saboda ɗaurin abokinsa da yace tare sukayi karatun university. Khalil na da kirki sosai, tun daga Maiduguri ya zo mun biki kin ga ai ba naƙi zuwar masa ba nan dai da Jigawa" ya faɗa. Ina gyara masa zaman hularsa nace
"Ai kam dai ka kyauta, ba dan yanda kake ta nanata amincin ki dashi ba bazan yar da ka tafi wani guri yini guda ba tare da ni ba". Se da yaja hanci na ni kuma na shagwaɓe fuska kamar zanyi kuka se ya rungumeni yana cewa
"You have no idea on how much I'm going to miss you sugar, na faɗa miki kawai dan Khalil ne badan haka ba yau Sunday dai ɗaurin aure ko a ciki garin Kano ne se dai a mun haƙuri". Nema mukayi mu lalace a tsaye da soyayya se da wanda zasu tafi ya kira shi kafin ya sake ni duk ya kashe mun ya saka mun shauƙin son kasancewa tare dashi.

Se da na raka shi get ina masa addu'oi kafin na koma cikin gida, minti uku tsakani wayata ta shiga ƙara na amsa ganin shine yace
"Babe kin san guy ɗin nan wai motar sa babu mai se yanzu yake faɗa mun?" Nace
"Toh, Allah ma ya sa kun sani da wuri ai ba se da kuka hau hanya in da babu gidan man ba".

"Haka ne, amma yayi yawa ai, me yasa tun tuni be faɗa ba kawai yace mana za'a tafi a motar sa? Ai se yace dama zamu haɗa kuɗin mai kinga da se musan da lissafin sa" Ya sake faɗa. Se nayi murmushi nace
"To yanzu dear kwata kwata nawa ne zeyi muku full tank da kake wannan mitar, ka bad kuɗin a saka man ku tafi mana kaga fa lolaci yana ta ja kar ku makara kuma"

Ƙaramin tsaki yayi kafin yace
"Ni fa 2k kawai na fita da ita shima saboda ba'a son tafiya babu kuɗi. Kuma ATM ɗina jiya na manta shi hannun Abubakar dana bashi ya ciro kuɗi, amma bari mu dawo na gani na san bazan rasa yan canji dana bari a gida ba" daga nan ya kashe wayar. Tunanin kar su sake ɓata lokaci yasa kawai na cire dubu biyar cikin kuɗin da Abba ya bani jiya na riƙe a hannu na, ina jin tsayuwar mota na yafa mayafi na na fita muka ci karo a bakin get na miƙa mishi ina murmushi se ya karɓa tare da pecking goshi na ya juya yana ɗaga mun hannu.

Dake su Imam da Amirah harda Inayah d Amir ɗin Anty Labiba sun zo tare muka wuni muna ta sabgogi se la'asar Mu'azzam ya zo ya ɗauke su, na basu kilishin da na taho dashi jiya daga gida su kaiwa Anty Labiba tun da nasan tana so kuma Mu'azzam yace su ze fara saukewa a gida bayan sun tafi na hau gyaran gida kafin wani lokaci na gama komi nayi wanka, ina da miya dan haka couscous zan dafawa Bilal idan sun dawo.
Dab da sallar isha'i ya shigo gida, se da na haɗa masa ruwan wanka na fitar masa da duk abin da ze yi amfani dashi kafin na barshi a ɗaki na koma kitchen na ƙarasa haɗa abinci. Har da fruit salad nayi dan nasan shi daga zarar an ci abincin dare ze fara mitar bakin sa na masa motsi yana so yaci wani abu kuma ya gaji da cin kayan gara. Mun cin abincin yana mun hirar yanda ɗaurin aure ya kasance, ashe mota ce ta lalace musu a hanya shiyasa ma sukayi dare. Bayan mun gama na kwashe koma na kai kitchen sannan na dawo na zauna akan cinyarsa ina jan gashin gemun sa, ya ɗora kan sa a kan ciki na yana cewa
"Har yanzu baki fara jin komai a nan bane?" Dariya nayi na ture shi ina cewa
"Haba sarkin kazallaha, 2 weeks fa yau me zan fara ji?"
"Ki dai zauna wasa yarinya ni nasan na daɗe da yin aika aika". Haka muka ringa hira cikin nishaɗi haɗi da wasannin soyayya. Ƙarfe goma yace mun na kawo masa wani abun ya ɗan taɓa bakin sa na masa motsi, se na ɗakko fruit salad ɗin da na sakawa madarar gari da condensed gashi yayi sanyi gwanin daɗi na haɗo da ruwa.

Se da ya fara shan fruit salad ɗin kafin ya ce na kawo masa kilishi.
"Ai ko ɗazu na bawa su Inayah su kaiwa Anty Labiba na san ta da son kilishi" na bashi amsa, se naga ya dakata da abin da yakeyi ya wani kalle ni fuskar sa kamar da fushi yace
"Kilishin kika bayar? Da izinin wa? Wato ita gata sarkin son cin kilishi ni kuma da bansan daɗi ba shiyasa zaki ɗauke mun abu ki bayar na tare da nayi miki izini ba".

Mamaki maganganun sa suka bani, kilishin da a gidan mu aka bani dan nayi kyautar sa shine ze fara tada jijiyar wuya yana faɗar maganganu akai? Kai tsaye nace masa
"Yanzu saboda na bawa ƙanwar Mamana abu shine kake wannan faɗan? Kuma fa kilishin nan naga daga gidan mu na taho dashi, nawa ne meye laifi idan nayi kyaitar sa ga wanda naso?"
"Ni kike faɗawa haka Halima? Ni kike yiwa gori akan kilishi?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Tsayen na miƙe nima ina cewa
"Karka canza mun magana ni ba gori na maka ba kawai na tunatar da kai ne kuma ba da wata manufa nayi magana ta ba".

Ikon Allah, ƙaramar magana ta zama babba. Daga dai zancen kilishi kamar dai dama Bilal yana neman hanyar da ze tijara ni ne se gashi ya samu nan ya ringa fisaji yana rashin mutunchi da faɗar maganganu tamkar ba Bilal ɗina ba. Har yana cewa wai dama tun da muka yi aure ya lura na ke masa wani gani gani, duk abin da zan bashi se in bashi kaɗan, ko kuma idan ya ɗakko da kansa in ringa kallon sa wato taƙama ta daga gidan mu aka kawo shiyasa to daga yau baze sake cin komai daga abinda ya fito daga gidan mu ba balle na goranta masa, maganganu dai marasa daɗi marasa ma'ana ya zubar mun da fruit salad ɗin akan carpet yayi wucewar sa ɗaki yana ci gaba da tijara.

Kuka na zauna ina yi, ni banga abin laifi duk a cikin wannan abun ba, idan ma beji daɗin abin da nayi ba a zato na ai ba ta haka ya kamata ya nuna mun ba se muyi magana cikin lumana amma ya za'ayi ya fara faɗa har yana cewa baze sake cin abinda aka kawo daga gidan mu ba. Na zata daya shiga ɗakin ze fito ya lallashe ni tun da ya barni ina kuka amma har agogo ya buga ƙarfe sha biyu ina zaune ban sani ba, na share fuska ta na tashi a raina ina tuna nasihohin da Mama tayi mun akwai in da take cewa
"Karki kuskura kiyi kyauta da abun mijin ki ko da ƙwayar zarra ba tare da izinin sa ba, sata ce, har kuma be yafe miki ba Allah se ya kama ki" 'Amma kuma wannan ai ni aka bawa' na raya a zuciyata, 'ko da yake tunda an kawo gidan ina ganin ya zamu namu kenan ni dashi' wata zuciyar ta tunasar dani.

A hankali na tura ƙofar ɗakin da ya shiga, akan gado na hango shi yayi ɗai ɗai yana bacci abun sa, wani abu ya tsaya mun a rai. Wato ko a jikin sa bacci ma kwanta yana yi. Sabbin hawaye ne suka ɓalle mun, hakan nan na canza kaya na kwanta kusa dashi ina cigaba da ɗauke hawayen daya ƙi tsaya mun dan banyi zaton Bilal ze fara mun haka ba. Da asuba be tashe ni ba kamar yanda muka saba yayi ficewar sa masallaci daya dawo kuma ɗayan ɗakin ya shiga ya kwanta. Ban farka ba se kusan bakwai na safe saboda rashin kwantawa da wuri ga kuma ciwon kan da kuka da damuwar dana kwana dasu suka saka mun. Nayi mamakin ganin rana tarwai kuma babu Bilal a gefe na, haka dai na watsa ruwa nayi sallah bayan na gama addu'oi na na fita ganin baya falo se nayi tunanin to ko fita yayi?

Yan ayyukan da zanyi na fara na sake gyara falo na saka turare kafin na wuce kitchen na shiga fere doya. Har na gama haɗa abin karyawa be shigo ba, ɗaki na koma na ɗakko wayata na shiga kiran sa ga mamaki na se na jiyo ƙarar wayar daga ɗayan ɗaki na. Katsewa nayi na nufi ɗakin, na murɗa handle ɗin ƙofa naji shi a rufe da key, mamaki ya sake cika ni, a hankali na shiga ƙwanƙwasawa, nafi minti biyar a tsaye ina buga ƙofar amma ko motsi ban ji ba balle na saka ran ze buɗe mun.
[5/18, 13:09] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 10*
Ɗaki na koma dan bazan iya karyawa ni kaɗai ba na fara sabawa tun da mukayi aure da Bilal bamu taɓa raba kwano ba, yanzu bama na jin cin abincin raina duk babu daɗi. Tun ina sauraron jin ya buɗe ƙofa ya fito har bacci ya kwashe ni a kishingiɗen da nake. Ban farka ba se da naji ana ƙwala kiran sallar azahar, nasha mamakin irin baccin da nayi. Se da sake watsa ruwa saboda jiki na da naji duk ya ɗaure sannan nayi alwala na fito ina jina fayau ciki na a rarake. Sallar na farayi sannan na gyara fuskata na saka kaya dukda yanda nake jin yunwa dan Anty Labiba ta hora ni da kasancewa tsaf tsaf ko da yaushe. Daga yanayin falon na gane ya fito yayi abinda ze yi. Dana duba kan dining kwano kaɗai na tarar an cinye doya dana soya tas ga kuma cups biyu da aka sha tea, kwashe kwanukan na farayi na kai kitchen sannan na dafa indomie naci ina mamakin me yayi zafi haka ne da Bilal yake wannan abun?

Ranar haka na wuni ni kaɗai a gida, se da yamma ne ma maƙwafta na mutum huɗu suka shigo mun, biyu gidan su ɗaya matar wa da ƙani ne Hafsa Maman Salim da Amina ita amarya ce tsiran mu sati biyu kamar yanda suka ce gidansu shine a farkon layi se Zubaida Maman Yusuf da gidan ta ke kallon nawa da kuma Bintu ita ce muke katanga ɗaya. Har gab da kiran magriba muna ta hira kafin suka yi mun sallama suka tafi na rakasu na dawo na gyara gurin da muka ɓata. Zuwan su ya rage mun kewa ya kuma ɗauke mun hakankali daga damuwar in da Bilal ya tafi yini guda na kuma kira wayar sa sedai tayi ta ƙara baze amsa ba daga ƙarshe ma ya kashe ta gaba ɗaya.

Har nayi sallar isha'i babu shi babu dalilin sa, zuwa sannan hankali na ya tashi na fara tunanin ba lafiya ba. Ƙarfe tara na kira Mama ina kuka na gaya mata tun safe Bilal ya fita ina ta kiran sa kuma baya amsawa daga ƙarshe ma wayar a kashe take.

"To ban da shirme kuma kukan na menene? Ai lafiya ce take ɓuya. Ki kira Nasir ko wani cikin abokanan sa na gurin aiki kiji ko suna tare tun da hankalin ki be kwanta ba. Amma babu komai ma nasan tun da kina gida ma ai yana haka ku wuni ba kuyi magana ba se daga baya ya baki uzuri" abin da Mama ta faɗa kenan amma hakan be sa naji hankali na ya kwanta ba tun da ni dai tun da mukayi aure ko ƙofar gida ze fita se ya gaya mun. Layin ƙanin sa Abubakar na kira se dai shima na tarar a kashe wannan ya sake dugunzuma hankali na kawai na zauna na fashe da kuka na rashin madafa. Motsin buɗe ƙofa ya farkar dani firgigit daga baccin daya sure ni ba tare da na sani ba ina tsaka da kuka. Dishi dishi nake kallon sa ya tsaya shima yana kallo na kafin ya fara takowa cikin falon se na miƙe da sauri na nufe shi, tsayawa yayi na faɗa jikin sa tare da fashe wa da kuka ina cewa

"Ina ka tafi? Hankali na ya tashi ina ta kiran wayarka baka amsawa me yasa kayi mun haka?"

A dake cikin yanayin da banyi zato ba bayan ya janye ni daga jikin sa ya kalle ni yace
"Kin aike ni ne balle ki bi ba'asin in da na tsaya?"
Se na bishi da ido kawai na kasa cewa komai, ya yi tsaki tare da zagaye ni ya wuce ciki.

Kamar wata wawiya haka na rakashi da ido har ya shige cikin ɗaki tare da banko ƙofa. Tamkar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka naja ƙafafu na da suka yi sanyi na zauna kan kujera haɗi da zabga tagumi. So nake na tunano ta in da na kuskurewa Bilal, me nayi masa da yayi zafi haka? Ina nan zaune ya sake fitowa fuu ya shige kitchen ina jiyo shi yana birkita kwanuka kafin ya sake fitowa da kofin shayi a hannun sa se dublan a plate. Nan cikin falon ya zauna bayan daya kunna Tv ya shiga shan shayin sa, yanda yayi tamkar be san da wanzuwata a gurin ba yasa na fashe da kuka sosai har da shashsheƙa se gani nayi ya miƙe tsaye da kofin shayin sa da alama gurin ze bar mun. Bazan iya jurewa ba, ina buƙatar nasan takamaiman dalilin fushin da yake yi dani se na miƙe da sauri na isa gaban sa na durƙusa tare da riƙe ƙafar sa ina ci gaba da kukan nace

"Ka faɗa mun me nayi maka kake mun irin wannan horon Bilal?"
"Baki ma san me kika mun ba kenan?" Ya faɗa yana ɗage kai sama a ƙoƙarin hana tausayi na yin tasiri a zuciyar sa. Girgiza kai nayi ina ci gaba da kukan nace
"Wlh ban sani ba, ka taimaka ka gaya mun me na maka bazan iya cigaba da jure fushin ka irin haka ba"
"Shikenan tun da baki san me kika mun ba Halima, duk ranar da kika tuna se muyi maganar" ya faɗa yana janye ƙafar sa ya wuce cikin ɗaki se dai be kulle ƙofar ba a buɗe ya barta. Zuciya ta na raya mun na rabu dashi da kansa ze zo in da nake idan ya gama fushin amma zuciyar dake cike da so da begensa ta rinjaye ni haka na sake bin sa ɗaki ina kuka ina roƙon ya gaya mun abin da na masa amma se da mula dan kansa kafin ya maido mun da zancen kilishi"

"Kayi haƙuri, ban kawo hakan ze ɓata maka rai ba amma zan kiyaye haka ba zata sake faruwa ba a gaba" na faɗa ina goge hawaye. Duk da haka be wani sake mun koma yanda muke gaba ɗaya ba se da aka kwana biyu ranar laraba ya fita da yamma babu jimawa Mu'azzam ya zo ya kawo mun manya manyan kaji guda goma in ji Abba da ƙwai shima crate goma dake ya buɗe gidab gona ana kiwon kaji da kifi yanzun an fitar da layers ne da suka dena ƙwai shine aka kawo mun rabo na. Tuwo nayi niyyar yi ganin kajin yasa na fasa na haɗa lafiyayyen farfe su irin wanda Bilal ke so na kwaɓa fulawa na gasa bread dan na lura yanzu abin laifi baya yiwa Bilal yawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login