Showing 216001 words to 219000 words out of 257873 words
shi sai Jalilah da waɗanda suka siya a hannunsu ne kaɗai suka san da maganar ita kuma a hoto kawai ya tura mata su bata gansu a zahiri ba. Haka yayi ta kame kame daga ƙarshe ya watsar ya kama sabgoginsa tunda lissafin sa na farko ya wargatse ya sake dawo da Jalilar rayuwarsa sai dai ya jira kuma ya sake shiri.
BAYAN WATA BIYU
HALIMA
Na fara Bautar ƙasa na gadan-gadan, wani Private Research Center aka kai ni, mai gurin Abokin Uncle Mudassir ne na sha mamakin lokacin da naje gurin dan ban taɓa sanin wanzuwarsa a Kano ba. Guri ne mai ɗauke da Laboratories babu adadi ga kayayyakin aiki yyanda kasan a irin fina finan Turawan nan na Scientist haka da yawan ma'aikatan gurin duk fararen fata ne kaɗan ne baƙaƙe iri na.
Fara aiki na ya sa na yarda dagaske da aka ce zaman banza ne yake kashe zuciya har mutum yayi ta tunane-tunanen banza da wofi mai abunyi sau tari ya kan manta da duk wata matsala idan ba wacce ta shafi aiki ko sana'arsa ba. Toh nima hakan ce ta kasance dani domin ban rufa sati ba na fara ɗaukar saiti, na tattara duk wata damuwa na watsar na kama aiki na domin gani nayi tamkar ban taɓa zama a aji ba komai sai ya zamar mun baƙo a lab ɗin da aka kaini, da yake kuma har raina a shirye nake da na mayar da hankali na koyi abin sosai sai na ware duk wani test da akayi idan na koma gida zan zauna nayi Reserch a waya har sai na samu cikakkiyar fahimta akan abun, na ƙulla abota da ChatGPT, duk abinda ya shige mun dubu shi zan tambaya ya warware mun musamman da na gano yana jin hausa shikenan na samu abinyi ko Whatsapp sai in wuni na kwana ban leƙa ba ina can ina kwasar romon ilimi har na fara hasaso kaina na koma makaranta nan da wani ɗan lokaci nima na zama babbar Scientist tamkar mamallakin gurinmu dukda a hoto kawai na taɓa ganinsa sai dai ya burgeni, matashi don bai kai shekarun Uncle Mudassir ɗin ba ma idan kuma ba hoton ne ya mayar dashi yaro ba amma har mamakin irin abubuwan da yayi nayi wanda suke rubuce cikin tarihinsa da akayi bango guda a cikin reception ɗin gurin.
A cikin satin daya mutu na kammala iddar Bilal, mun rabu kenan ko in ce na cire duk wani sauran fata da nake dashi akan al'amura zasu iya canzawa ko da ace akwai sauran zama a tsakaninmu toh fa sabon lale ne, sabon nema, sabon ɗaurin aure wanda na tabbatar abu ne mai matuƙar wahala ace waliyyai na su sake karɓar maganar auren Bilal, sai dai ƙaddara mai girma irin wacce ta haɗa mu a baya wadda a yanzu ni da kaina bana fatan ta sake giftawa.
Aurensa ya zame mun darasi a rayuwa, banyi nadamar kasancewa tareda shi ba domin zaɓi na ne ba dole aka mun ba amma kuma na godewa Allah daya farkar dani a dai-dai lokacin da rayuwara take da sauran ma'anar da zan iya canza gobe na.
Tun ranar daya bani takardata ban sake haɗuwa da shi ba ko da a hanya haka bai sake nemana ba in banda text message daya turamun sau biyu akan cewar zai ƙwace yaransa shikenan bai kuma waiwayata ba ya tare da amaryarsa ya manta da ni da yaran da muka haifa tare.
Ko kusa ban taɓa kawo cewar ko da cewar baya sona na kuma yarda da hakan babu haufi amma kuma na ɗauka albarkacin zaman da mukayi na shekaru zan samu gurbin da zai ringa tunawa da ni a zuciyarsa har ya tuntuɓe ni, kai ko bai nemeni ba ya kamata ace ya nemi yaransa, ko da yake tun kafin ya sakeni ma zaman da mukayi bai taɓa waiwayarsu ba har gara ni a sanda ya so ya yaudareni ya sake mayar da rayuwata cikin uƙuba ya bibiyeni amma bai taɓa tambayar yaransa ba, bai san cin su ba, bai san shan su balle suturar su ba shi ba hatta da yan uwansa babu wanda har kawo yau yayi tunani ko karar dai dai da rana ɗaya yazo ya gansu ko ya kira yaji lafiyarsu sai Abubakar.
Shi kaɗai yake tuntuɓata duk kuma sanda ya zo Weekend sai yazo ya gansu ba kuma zai zo hannu haka ba idan ma bai kawo komai ba zai basu kuɗi ya ce a siya musu bayan shi hatta Anty Amina da nake zaton tana so na tun ranar da suka zo biko suka tafi ban sake jin ɗuriyarta ba balle kuma uwar gayyar Hajja a taƙaice dai sun barmun yaran kawai na kuma yi murna da hakan a kullum kuma ina addu'ar Allah ya raya min su suyi tsahon rai su kai lokacin moro naga yan uwan Bilal ɗin zasu zama ire iren marasa kunyar mutanen da nake samun labari da sai a lokacin da yara suka zama abin moro ne sannan zasu gwada iko akansu matsayin dangin mahaifinsu ko kuwa sun barsu har abada?
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 54*
Jinyar stitches ɗin Zulaiha ta saka Bilal baya fita ko ina idan ba masallaci ba, duk ayyukan gidan shi yakeyi, sannan ya kula da ita a ɗan taƙin lokacin kuma ya ɗan fara samun nutsuwa daga tsoron sababbin halayen da ya ringa gani a gurinta tun bayan da aka ɗaura musu aure. Ranar data kwana uku ƙanwar Ummansu Anty Habi taje gidan ta kai mata gamje gamjen magunguna da ta ce na Aljanun da suke shafarta ne. Shi ya ringa jigilar dafa mata na wanka safe yamma kuma ya hura mata coal tayi turare, maganin na sati ɗaya ne ranar data cika satin tana yi kuwa Aljanun suka tashi.
Lokacin ya fita siyo kayan miya ya dawo ya tarar da ita su Suby sun daddanneta tana wasu abubuwa suka ce masa wai a haka suka tarar da ita suma. Dukda dai yayi mamakin ta inda suka shiga gidan tunda ya rufe daya fita ita kuma sun ce sun sameta ta hau iskoki to waya buɗe musu ƙofar?
Haka ya fita can masallaci ya samo wanda zaiyi mata ruƙiyya, suka ringa kafa masa Sharuɗan kar a ringa ɓata mata rai, kar ayi mata faɗa da sauransu in ba haka ba zasu dawo daga haka dai suka fice sai kuma suka riƙe mata ƙafa, sati biyu taci tana jinya kafin ta ware gaba ɗaya suka durfafi sabuwar rayuwar amarci tunda ɗinki ma ya warke, duk yanda take ƙoƙarin dannewa kar tayi abinda zai sake jefa zargin wani abu a zuciyar Bilal ɗin ta kasa.
Ranar da suka sake gamuwa dukda shi ya fara nuna buƙatar abun amma tun kafin ayi nisa taga ya canza, karsashin daya fara da shi ya sakeshi sai ƙananan tsaki da ya ringa saki, bata damu ba ta cigaba da shafashi a ƙoƙarin mayar dashi kan network amma sai kawai ya tureta lokacin da wayar sa tayi ƙara. Abun ya mata ciwo matuƙa, tana sauraron wayar da yakeyi data gane da Hajja ne kuma masifa take masa dan sai bata haƙuri yakeyi kafin ya kashe bayan ya ce mata gashi nan zai zo gidan yanzu da yake da yamma ne.
Tayi ƙwafa ta bishi da harara sanda ya shiga banɗaki, sai kuma ta tashi da sauri ta ɗakko Humrar kiranyenta ta shafa sannan ta ɗebi maƙale mata a hannunta ta koma ta zauna tana murmushin mugunta, Tunda ba zaiyi dan Allah ba toh kuwa zai yi dan dole.
Bilal kuwa daya shiga banɗakin sakin ruwa yayi akansa dukda garin da sanyi sanyi amma bai damu ba, duk da ya san gaskiyar abinda ya sameta amma kuma zuciyarsa ta kasa karɓar abun har yanzu. Yana son Zulaiha tamkar rai, amma da zarar ya tuna cewar bai sameta a Mace ba sai yaji duniya ta masa zafi, duk sanda buƙatuwar ta ta motsa masa kuma da zarar ya tuna abun sai ya ji komai ya mutu kamar dai yanzun a matse yake ya kuma yi ƙoƙari ya kawar da tunanin amma suna farawa abun ya zo masa take yaji komai ya mutu duk yanda ya so daya daure ko dan ganin kamar itama tana so ɗin amma ya kasa.
Wani tunanin ne ya sake gifta masa wai me yasa ita bata tsoronsa?
Kashe shower yayi ya zauna akan toilet yayi shiru kamar mai jira wani ya bashi amsar. Ya tafi tunanin farkon aurensu da Halima daƙyar sai ya matsa take iya kallonsa babu riga amma ita wannan haka take ƙure shi da ido kamar mayya har lashe baki takeyi idan da ya biye mata ma da tuni tun kafin ɗinkin nata ya warke ma zata bashi kanta kwata kwata babu kunya ko jin nauyinsa a tareda ita ko da kuwa tayi ƙoƙarin nuna hakan bai san mai yasa yake ganin kamar na ƙarya ne ba.
Ji yayi kansa na nema ya fara ciwo dole ya kore tunanin ya miƙe ya shiga wanka, sanda ya fito tana kwance akan Gadon amma ya san ba bacci takeyi ba tunda bai ji munshari ba, ya wuce gaban mirror zai ɗauki wayarsa ya bar mata ɗakin hancinsa ya fara shaƙo masa wani ƙamshi, kansa ya sara, kamar wanda aka ja da igiya haka ya tafi kamar kuma waccen ranar yau ɗin ma haka ya ringa aiki tun yana na jin daɗi har ya koma na wahala sai gashi yana kuka wiwi duk kuma yanda ya so ya bari abu ya gagara sai da ita da kanta ta gaji kafin ta yakiceshi daƙyar ta gudu banɗaki ta kulle ƙofa.
Bilal kuwa kwanciya yayi riƙe da ciki yana juyi cikin azaba, ya gaji amma kuma so yake yayi abun, daƙyar ya lallaɓa ya fice daga ɗakin ya koma nasa ya shiga wanka, sai da yayi kusan saɓi uku har cikin hancinsa ya wanke kafin ya daina jin ƙamshin turaren a hankali kuma nutsuwa ta fara saukar masa ya fita ya kwanta akan gado yana sauke ajiyar zuciya a jere. Gaskiya ba haka kawai ba akwai wani abu dan shi dai a rayuwarsa bai taɓa gamuwa da irin wannan bala'in ba. Sai gurin ƙarfe tara ya iya tashi yayi sallar magriba da Isha'i, yana zaune ya jiyo tana ƙwanƙwasa masa ƙofa haɗi da kiran sunansa kamar na zai tashi ba sai kuma ya miƙe yana rangaji yaje ya buɗe mata.
Sum sum ta wuce ta ajiye try ɗin data shiryo masa kayan abinci akai, ba tareda ta kalle shi ba ta miƙa masa wayarsa tana cewa
"Tun ɗazu ake kira" ya karɓa yana kallonta sai kuma ya ji tausayinta yana ratsashi babu dalili. Abincin data zuba masa ya jata jikinsa suka shiga ci, jollop ɗin shinkafa taji nama ga kuma peppered chicken daban a gefe da salad sai lemon exotic babban kwali mai sanyi sosai. Sai da ya kai geji kafin ya shiga tantance abincin. Ɗanɗanon da ƙamshi harda yanda aka shirya abincin ma bai yi kama da girkinta ba.
Zulaiha bata iya girki ba bai kuma yi mamakin hakan ba domin ya fi kowa sanin daga gidan daya ɗakkota, yayi gyaran murya ya ce
"Daga ina aka kawo abinci?" Ta kalle shi a shagwaɓe ta ce
"Ni na girka mana" ɗan murmushi yayi ya ce
"Ai nasan bamu da ingredients ɗin da zakiyi irin wannan girkin, ya kamata ma a samo fridge gaskiya saboda ajiyar nama da kayan miya na gaji da siyan guntu guntun nan" daga haka ya ɗauki wayarsa ya shiga duba missed calls ita kuma ta kwashe kwanuka ta fita da su ranta ƙal.
Kiran Kamalu ya fara bi dukda yaga missed calls ɗin Hajja kusan guda goma, basu wani ja gaisuwa mai tsayi ba Kamalu ya ce masa
"An ce kayi ta zuwa nemana Allah ya sa lafiya dai"
"Eh wlh kuma nayi ta kiran layinka kullum a kashe, dama maganar shagunan nan ce na bawa lawyer na takardun ya duba amma ya ce fake ne" Bilal ya bashi amsa.
"Fake kuma?" Kamalu ya tambaya cikin mamaki Bilal ya amsa masa da
"Haka ya ce, nima nayi mamaki amma kuma dana haɗa su da wasu takardu na ga banbancin da ya ce akwai tsakaninsu da original ɗin".
"Gaskiya toh bansan a inda aka samu matsala ba dan kai shaida ne takardun nan hannu da hannu yanda aka bani su take na miƙa maka ban ko tafi dasu wani guri ba balle ace ni na canza su" Kamalu ya faɗa.
"Ai ba ina zarginka bane Alhaji Kamalu nima abun ya bani mamaki ne kaga kenan daga can gurinsu da suka siyar mana sune macutan, sun karɓi kuɗin mu ƙila zasu sake siyarwa da wasu kuma"
"Gaskiya a sanin da nayiwa Alhaji Balarabe ba zai taɓa yin haka ba, na fi shekara goma sha biyar muna harkar ƙasa da shi ba'a taɓa samun saɓani ba, amma abinda zai faru gobe idan Allah ya kaimu kazo office ka sameni sai muje gurinsa duk ma abinda ya faru sai a warware" Kamalu ya sake faɗa daga haka sukayi sallama.
Dukd dare ya farayi haka ya tafi gidan Hajja tareda Zulaiha, sai da ya tsaya a hanya yayi mata siyayyar toshiyar baki kafin suka isa gidan. Fadila na falo tana kallo ita da Abubakar shi kuma yana cin abinci suka shiga, ta gaishe shi ba tareda ta ko kalli Zulaihan ba Abubakar dai tamkar bai ji shigarsu ba sai da Bilal ɗin yayi masa magana kafin ya ɗaga kai tareda yi masa sannu a taƙaice ya cigaba da cin abincin sa.
Ɗaki ya wuce da Fadila ta ce masa Hajjan ta kwanta, ya zauna daga gefen ƙafarta yana gaisheta dan ba bacci takeyi ba kafin ta miƙe zaune fuska ba yabo ba fallasa ta ce
"Ashe kuma ka saki Halima"
Kai a ƙasa yana shafa ƙeya ya ce
"Kotu suka ce zasu kai ni Hajja ni kuma naji tsoro kar su fitar da waccen maganar shiyasa kawai na saketa".
"Ai shikenan, yanzu yaushe zaka karɓo yaran toh?" Hajja ta sake faɗa. Da sauri ya kalleta ya ce
"A karɓo yara kuma Hajja?"
"Da bar mata su zakayi shikenan an rabu kake nufi ko me?"
"Aa ba haka nake nufi ba, da niyyata dai a barsu su ƙara tasawa tunda yanzu idan an ɗakko su nan idan aka kawosu wahala zasu zamar miki" ya sake faɗa kai a ƙasa. Hajja dake kallonsa ta ce
"Au, ni kake zaton zan riƙe maka yaran ma kenan? Ita waccen ɗin daka auro menene amfanin ta? Da zuwa kawai tayi ta samu guri taci arziƙi kenan ko me?"
"Ba haka nake nufi ba Hajja" ya faɗa a hankali ta katseshi da cewa
"Ka saurareni da kyau dole ka karɓo yaran nan saboda ta hakane zaka ƙuntata mata da ita da iyayen nata kuma zamu samu damar jansu a ƙasa yanda muke so a dalilin yaran sannan itama wannan yar matsiyatan daka ɗakko ba zaman banza zatayi ba dole tayi maka wahalar yaya".
Shiru yayi ya kasa ce mata komai, Hajjan ce ta sake cewa
"Wai ina Hafizu ne kwana biyu?"
"Yayi tafiya ne kusan wata uku baya ƙasar" ya shata mata ƙarya, ta taɓe baki ta ce
"Yanzu saboda mugunta da hassada ƙiri ƙiri kaƙi kayi masa maganar Fadila ko? Tunda kai kayi mana baƙin ciki Allah ya kawo mana mai taimakonmu har gida amma ka kwaɓar da damar shine itama kake mata baƙin ciki karta samu in da zata huta har muma mu mora"
"Amma Hajja na gaya miki maganar nan ba mai yuwuwa ba ce ba, mutumin nan da matarsa yana sonta bai taɓa kallon Fadila a matsayin wacce zai iya so ba kina gani saboda rashin hankalinta ta ringa shige masa har sai da ya fahimci abinda take nufi in da yana ra'ayi ai da zai amsa amma daga haka mai ta janyo? Janye jikinsa yayi ya daina zuwa gidan nan kuma shine kike so ni na tallata masa ita gaskiya ba zan iya ba" ya bata amsa ba tareda ya kalleta ba.
Tayi ƙwafa ta ce
"Ai shikenan nan"
"Kiyi haƙuri idan na ɓata miki rai Hajja" ya sake faɗa cikin sigar rarrashi,
"Yanzu ita yaushe zata dawo ayi maganar auren?" Ta sake soko masa wata maganar, ya fahimci wa take nufi amma ya waske da tambayar wacece
"Ita shaiɗaniyar yarinyar nan mana" ta bashi amsa a fusace. Ya marairaice fuska ya ce
"Yanzu Hajja ko ni na dage zan aureta dan Allah sai ki barni nayi?"
"Akan mai zan hanaka? Dama ai abinda ya kamata kenan ko kuwa kana nufin taci banza ta lalataka sannan taƙi aurenka? Toh wlh ba zai yuwu ba" ta bashi amsa. Ya buɗe baki zai sake magana wayarsa ta shiga ƙara dan haka ya dakata ya zarota gabansa ya yanke ya faɗi ganin international number ko ba'a faɗa ba kuma ya san Jalilah ce.
Ji yayi zufa ta fara keto masa ya danna wayar a silent ya mayar da ita Aljihu ya miƙe yana kallon Hajja ya ce
"Bari naje Hajja sai gobe" ta amsa masa da
"Allah ya tashe mu lafiya" tana karantar sauyin da yayi lokaci ɗaya.
A falo Zulaiha kaɗai ya tarar tana ganinsa kuwa ta miƙe yayi gaba ta bi bayansa. Sai da suka zauna a mota kafin ta ce masa tana so taci Shawarma ta faɗa masa kuma ta inda take so. Ya kalleta da mamaki jin inda ta faɗo ɗin, kallon daya mata ya saka ta gane ta kwafsa dan haka tayi saurin cewa
"Saurayin Zahra ne yake siyo mata ya kai mata School, na taɓa ci sau biyu tayi mun daɗi sosai shiyasa na riƙe sunan gurin". Bai amsa mata ba suka tafi, tana ta sako masa hira dan ta kawar masa da tunani amma da Eh ko Uhm yake amsa mata kawai. ATM ɗin sa ya bata ya ce taje tayi order dukda yanda gurin yake cike da Maza amma yana buƙatar space ɗin ne saboda number ɗazu