Showing 180001 words to 183000 words out of 257873 words

Chapter 61 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

470

yawa, Allah kaɗai ya san bayan ita mata nawa yake mu'amala da su ko ita Zulaihan ma ta sani ko kuma itama ninketa yayi yanda ya mun? Allah kaɗai ya sani.

Haka na kwana cikin alhini, tausayin kaina da yayana musamman Sharifa ya cika mun zuciya. Da naga kuka da tunani ba zasu kawo mun mafita ba sai na miƙe na ɗauro alwala na shiga jera nafiloli na mayar da hankali akan addu'ar kar Allah ya kama ni ko yayana akan laifin Bilal.

Allah shaida ban rage shi da komai da har zai fita ya nema a waje ba idan ma ban ishe shi ba bai taɓa faɗa mun ba na san Allah ba zai kamani da laifin haka ba.

Kafin wayewar gari na sake zugewa sai k ɗauka kwana nayi ina zawo tsabar yanda na zabge lokaci ɗaya.

Da Asuba bayan na idar da sallah ina zaune ina lazumi Mu'azzam ya shigo ɗakin, sai da gabana ya faɗi na ringa kallonsa har ya zaune gefen gado shima yana kallo na ya ce

"Abba ya tambayeni mai ya sameki bayan mun fita" cikin firgici na ce
"Sai ka ce masa me? Amma baka faɗa masa ba ko?"

Ya taɓe baki ya ce
"Ban faɗa masa ba, na ce masa ne zaki faɗa masa da kanki saboda kin san ni ban iya ƙarya ba idan na buɗe baki zan gaya masa gaskiya be kawai".

Tashin hankali na ya nunku ban san sanda na fashe da kuka ba na ce
"Amma baka kyauta mun ba akan me zaka haɗa ni da shi? Ba sai kawai ka ce masa babu komai ba kawai jini na ne yayi ƙasa?"

"Ke idan ya kiraki sai ki gaya masa" ya faɗa kafin ya sake cewa
"Ni ba wannan nw ya kawo ni yanzu ba, an jima ki shirya zamuje asibiti ayi miki test".

Ban kalle shi ba na ce
"Test ɗin me bayan likitan ya ce ba abinda zasu mun?"

"HIV test da na sauran STDs". Yanda kasan kiɗan mandiri haka zuciyata tayi wani diri, na kafe shi da ido, tsabar yanda abun ya dakeni na kasa cewa komai daƙyar na haɗa kalmomi na ce

"HIV kuma?"
"Eh, kin san sai ba'a raba yan bariki da ita dan haka tun da wuri gara a miki gwaji ki san makomarki" yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin.

Ji na ringayi kamar na hau rollercoaster, daƙyar na lallaɓa na koma kan gado na rufa da bargo saboda wani sanyi da naji yana shigata kamar zazzaɓi zai rufeni. Na ringa nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a zuci har ta fito fili, tsoro mai tsanani ya lulluɓe ni.

Duk tunanin da ya taho mun sai in kore shi na idan ta kasance aka mun test ya zama positive ya zanyi? Ban iya cin komai ba har ƙarfe goma ina kwance a ɗakin kafin Amirah da suka gama Exams jiya ta shigo ta ce wai Mu'azzam yana jirana. Haka na fita yanda kasan zautacciya, fuska jeme jeme baki a bushe Kai ba iya bakina ba komai na jikina ma ya bushe kamar wata tsohuwa haka na dawo a dare ɗaya.

Babu wanda ya tambayi ina zamuje muka kama hanya muka fita, can wani babban lab muka je, ikon Allah ne kawai ya kaini har aka gama running test ɗin result ya fito ban mutu a gurin ba saboda tsoro. A gurin ya buɗe ya gama dubawa kafin ya miƙo mun takardar ban karɓa ba na girgiza masa kai daƙyar na ce

"Akwai ko babu?"
"Babu" ya bani amsa, sai na ji kamar an kwarara mun ruwan ƙanƙara tun daga tsakiyar kaina har tafin ƙafata. Na ringa jera ajiyar zuciya tamkar jaririn da ya wuni ba tareda mahaifiyar sa ba, a hanya muna tafe babu mai cewa kowa komai sai da muka kusa isa gida ba tareda ya kalleni ba ya ce

"Wannan ba shi yake nufin shima bashi da wani ciwo ba, ta yuwu baki da haƙƙin sa shiyasa Allah ya tsare bai shafa miki ba dan haka ruwanki ki godewa Allah ruwanki ki butulce masa zaɓi ya rage naki yanzu.

Baƙuwar motar da na gani ya saka na fahimci anyi baƙi, bani da tabbacin gurin Abba aka zo tunda yana gida ko gurin Mama koma su waye bana buƙatar haɗuwa da su dan haka na shiga ta ƙofar kitchen na shige ɗaki ba tareda na bi ta falon ba. Wanka na farayi na ɗauro alwala na fito ina ji na kamar iska zata kwashe ni saboda rashin nauyi. Ina zama Amirah ta shigo wai na zo nayi baƙi,

"Ban santa ba" ta bani amsa bayan da na tambaye ta su waye baƙin? Suhaila ce ta zo mun, na ɓata rai a zuciyata ina cewa zuwan da mijinta yayi bai isa ba shine ya sake turota?

Ban fita ba bayan na shirya kwanciyata nayi sai da Zainab ta sake zuwa ta kirani kafin na yafa ƙaramin mayafin abayar da na saka na fita, ba yabo ba fallasa na ƙarasa na zauna a ƙasa na shiga gaisheta, ta amsa a sanyaye tana ƙare mun kallo, na sace kallon Mama dake danna wayarta kafin na mayar da kaina ƙasa ina juya zoben hannuna.

"Ashe kuma abinda ya faru kenan Halima? Dan Allah kuyi haƙuri, wlh ban sani ba sai da aka daɗe tukunna nauyi da kunya kuma suka hana in zo ko na kiraki saboda na san duk dalilin da zai saka ki baro ɗakinki ba ƙarami bane duba da tarin ƙaunar da kikewa Bilal.

Na yiwa Mamanku duk bayanin da yayi mun, na san bai zama lallai abinda ya faɗa mun gaskiya bane amma koma menene tone tone bashi da daɗi ayi haƙuri har idan da yuwuwar komawa kiyi haƙuri ki koma, amma idan kinga cewa da cutuwa a lamarin zamanku wlh bana goyon bayan kici gaba da haƙuri kiyi abinda kike ganin ya fi kwanta miki a zuciya" Anty Aminan ta faɗa.

Mama na sake kallo naga ta taɓe baki kafin ta miƙe ta bamu guri. Nayi shiru sai Anty Aminan ta sake cewa
"Na san kina haƙuri da shi harma da mu da mahaifiyarmu baki ɗaya amma ki sani Halima babu wani gidan aure da bashi da nasa kalar ƙalubalen kawai na wani ne ya fi wani da kuma yanda ma'auratan suka iya riƙe sirrin su shine banbanci amma duk inda aka zaga hakan take shiyasa zakiji hausawa suna cewa da sabon gini gara yaɓe".

Kai na girgiza hawaye ya kawo ido na na ce
"Bana zaton zan iya zake zaman aure da Bilal dukda ina son sa".


Kuji tsoron Allah masu fitar mun da littafi babu lallai na yafe haƙƙina wlh
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 46*

"Kar kice haka mana Halima. Ke da na san ki jaruma shine zaki bari daga sama wata ta zo ta ƙwace miki miji kuma ki sakar mata? Haba mana dan Allah karki bani kunya.

Na san abinda ya aikata miki dole kiji zafi ba ke ba hatta Hajja dake goyon bayansa a ko da yaushe a wannan karon tana adawa da auren nan dan wlh ba dan mun tausheta ba rantsuwa tayi akan sai ya saki yarinyar ba zata tare ba. Mu muka yi ta bata haƙuri saboda a ganina bai kamata ace a gyara ɓarna da ɓarna ba, ubangiji ya rigada ya ƙaddara matar sa ce sai ayi haƙuri baki ɗaya a karɓi hakan ta yuwu silar auren sai ki ga kina zaune ubangiji ya fitar miki da haƙƙin ki ya wanke ki a idon duk mai ganin laifinki" Anty Amina ta faɗa cikin tausasawa.

Murmushin takaici nayi ina share hawayen da suka ɓalle mun, kowa ɗauka yake saboda Bilal zai ƙara aure ne muka samu saɓani amma nayi mamakin yanda da ta tashi tahowa bikon bai faɗa mata gaskiya ba ta yanda zata fi sanin hanyar da zata bi gurin shawo kaina idan ma hakan mai yuwuwa ne. Ina jin ta ta cigaba da cewa

"Kiyi haƙuri Halima, kishiya da ciwo amma sau tari mace bata sanin matsayin ta a gurin namiji idan tana ita kaɗai sai ranar da ya kawo mata abokiyar zama a lokacin shi kansa zai banbance tsakanin aya da tsakuwa.

Balle Bilal Allah na tuba ni da ke mun san idan ba ke ɗin ba babu wata mace da zata iya jure halinsa suyi dogon zango yanda kikayi,

ni da ace kinyi shawara dani tun farko zan ce miki ki danne zuciyarki ka bashi lokaci kawai ki kuma zuba ido ki sha kallo zakiga zuwan da dawowar amma yanzun ma bata ɓaci ba hakan za'a yi kiyi haƙuri ki koma ɗakin ki tun kafin amarya ta tare balle ta samu lagonki ta fahimci kina kishi da ita".

Girgiza mata kai nayi na ce
"Ko da ina son Bilal ina kuma tsananin kishin sa hakan ba zai saka na bijirewa umarnin ubangiji na so kaina ba.

Ban ce banji zafin ƙarin auren sa ba amma wannan bai ko kama ƙafar abinda ya aikata mun da ya saka na nisance shi ba. Kuma zuwan ki da maganganunki sun sake tabbatar mun da bai yi nadama ba, ba kuma shi ya turo ki ba zuwan kanki ne kawai domin da ace yana buƙatar cigaba da zama dani ba zai rufe miki ainihin abinda ya haɗa mu ba ya faɗa miki ƙarya" na ƙarasa cikin kukan da ya ƙwace mun.

Tayi shiru jiki a sanyaye tana kallona kafin tayi ƙarfin halin cewa
"Menene gaskiyar abinda ya shiga tsakanin ku Halima? Ni dama jiki na ya bani ba gaskiya ya faɗa mun ba, na yarda da shi ne kawai saboda rantsuwar da ya mun ban kuma yi zaton lalacewar ta sa har ta kai ya ringa rantsuwa akan ƙarya ba".

Na miƙe tsaye ina goge fuskata na ce
"Kiyi haƙuri amma ba zan iya furta miki komai ba domin bai zama lallai ki yarda da ni ba ƙarshe ma zaku iya cewa sharri nayi wa ɗan uwanku". Miƙewar itama tayi ta ruƙo hannuna ta ce

"Ashe har yanzu kina kallo na kamar sauran Halima?" Na girgiza mata kai na ce

"Ko da ace kamar su kike kin mun alkhairin da ko me zaki mun zan ɗaga miki ƙafa. Maganar Bilal kuma mu barta kawai kiyi haƙuri, idan zuwan kanki ne ba zan iya sake koma masa ba, Idan ma kuma shi ya aiko ki ki faɗa masa; ko da ƙaddara ta kasance akwai sauran zama a tsakani na da shi ba zan koma ba har sai shi da bakinsa ya faɗa muku abinda ya aikata mun" daga haka na wuce ɗaki na barta a tsaye da alama ta rasa da kalmar da zata tsayar da ni.

Kan gado na faɗa na fashe da kuka bayan shigata ɗaki, Amirah dake shafa mai a gaban mirror ta waigo ta kalle ni ta ce
"Wai Yaya Halima ba zaki dangana ki dena wannan koke koken banzan ba?"

"Ba zan iya ba Amirah, duk yanda na so na bari tunanin dake cunkushe a ƙwaƙwalwata ba zasu barni ba. Ban taɓa zaton Bilal zai mun haka ba na kasa yarda mutumin da na so tamkar raina zai maida mun da irin sakayyar nan" na faɗa cikin kuka har raina kuma na ji wani sanyi na samun wanda zan tattauna yanda nake ji a zuciyata da shi.

Tunda Hansa'u ta fahimci ina shirin yafewa Bilal a faɗar ta shikenan ta fita a sabgata ta dena kirana kuma ko da ni na kirata ba zata amsa ba kamar ma blocking ɗina tayi dan baya bayan nan idan na kira kullum user busy ake ce mun. Mama da Abba kuwa sun zame mun kamar dodanni a yanzu, banda tsawa da hantara ba abinda yake shiga tsakaninmu, Anty Labiba da ta kasance abokiyar shawarata tun asali na ruguza alaƙar mu tunda na kafe akan auren Bilal, ita ɗin kuma bata da sauƙi ta kasa haƙuri ta rungume ni tamkar yanda sauran sukayi kafin yanzu komai ya lalace.

Tasowa tayi ta dawo kusa da ni ta zauna ta ce
"Kin aure shi cikin rashin sanin ainihin wanene shi, a yanzu da komai ya fito miki; idan kika sake biyewa So ba kuskure bane bane abinda zakiyi ganganci ne, kin kuma san duk abinda aka aikata shi bisa ganganci, idan aka samu akasi sakamakon sa ya kan zarce na kuskure.

Ya hanaki abinci kin ɗauke ido, ya zageki kin ɗauke ido, ya doke ki duka kin shanye saboda kina son sa kina kuma son kiyi zaman aure sannan bakya so waɗanda suka ce kar ki aure shi suyi miki dariya shiyasa kika haƙura kika zauna amma Yaya Halima har zuwa wane lokaci zuciyarki zata iya jurewa bayan kin san mijinki yana da wata alaƙa a waje irin wacce take tsakaninku ma'aurata?"

Da firgici haɗi da mamaki na kalleta, ta gyaɗa mun kai cikin tabbatarwa kafin na buɗe baki ta ce
"Kar ma ki ɓata lokaci gurin tambayata a ina na sani, kowa kallonki kawai yakeyi suga iya tsayin lokacin da zaki ɗauka kina rufa masa asiri.

Ba Jalilah sunanta ba? Har gidan da ta siya masa a Kano suke zuwa suna sheƙe ayar su a ciki an sani, mota da kuɗaɗe duk da yake facaka da su zuwa yanzu kowa ya san karuwanci yakeyi tana biyansa.

Ke ce kike ta nuƙu nuƙu da abu a rai yana neman kashe ki a zatonki kin ɓoye sirrinsa bakya so mutunchinsa ya zube bayan shi tuni ya daɗe da barbaɗar da mutunchi hotel hotel a gari, dan haka tun wuri idan ma zaki saki ranki ki saki, idan kin ce zaki koma masa babu mai miki dole ki rabu da shi amma kiwa kanki faɗa tun kafin duniya ta miki.

Kinga test ɗin da kuka je ɗazu? Toh Abba ne ya saka ya kaiki dan ina ji yana gayawa Mama idan kika dage sai kin koma to fa duk abinda ya je ya dawo ki kuka da kanki, waya sani ko an gaya masa yarinyar da yake neman bata da lafiya ne? Ke dai kawai ki godewa Allah bai shafa miki ciwo ba kuma kiyi ta kanki in kuma kin na ce toh sai in ce miki Allah ya bada sa'a".

Yanda kasan wata uwar mata haka Amiran ta zauna tana tsara zance, duk maganganun nata ba wani fahimtarta nayi ba hankali na ya tafi kan cewa da tayi kowa ya san abinda Bilal yake aikatawa. A hankali na ce mata

"Mu'azzam ne ya faɗa muku ko?"

"Babu ruwan Yaya Mu'azzam, ita magana ai kamar tusa take in dai an yita a sannu zata isa ko ina. In miki mai gaba ɗaya, to hatta da cewa da Abba yayi kije ki ɗakko Uniform ɗin ki a gidan jiya yana sane yayi haka ne saboda ki tarar da abinda idan kina da hankali ba zaki ko sake kallon in da Bilal ya gifta ba, amma kika sake gwada masa ke ɗin fa kinyi nisa bakya jin kira.

To wlh tun wuri ki wa kanki faɗa dan Abba ya gama kaiwa bango da lamarinki, Sai kinji yanda ya yiwa yayansa tas tas duk da ya ce shi bai san komai ba.

Ita kuma wannan Anty Aminar raina miki wayau kawai tazo tayi dan na tabbata su dai sun san komai" Amiran ta sake faɗa daga haka ta tashi ta fara saka kayanta tana sake jaddada mun wai in wa kaina faɗa na san inda yake mun ciwo sai kace wata uwata.

Jiki na yayi laƙwas da jin maganarta. Ashe ni duk bonono nake wai rufe ƙofa da ɓarawo, ina nan ina fama da abu a ciki na ashe na bar baya ba zani kowa kallona kawai yakeyi. Yanzu ashe iyaye na sun ma san abinda ni ban sani ashe su har sun san yana kai mata gida kenan.

Kuma mai ciwo na sake fashewa da shi, na rasa gane wace irin ƙaddara ce take yawo da ni haka, ina jin zuciyata tamkar zata fashe saboda ƙunci da baƙin cikin halin da na tsinci Bilal a ciki amma kuma a wani ɓangare babu ko ɗigo na soyayyar sa daya ragu, ji nakeyi ma tamkar ana sake rura mun wutar ƙaunar sa a zuciyata. A fili na furta

"Ko sonka zai zama ajalina na haƙura da kai Bilal in sha Allahu na barka har abadah" na sake faɗawa kan gado na cigaba da kukan da babu abinda yake rage mun saik ƙarin zafin zuciya da yake saka mun. Ina tsaka da kukan Al'amin ya shigo, motsin buɗe ƙofar ya saka na ɗago muna haɗa ido wani sabon kukan tausayinsu ya ɓalle mun. Ganin ina kuka ya saka ya taho da gudu ya faɗa jikina yana cewa

"Mami menene? Momy ta ce baki da lafiya dubaki muka zo yi ko naje na kirata ina ne yake miki ciwo?"

Rungume shi na yi na cigaba da kuka, abinda nake gudu ya rigada ya faru. Bilal ya cuce ni ya cuci yarana ya ɓata musu suna ya kuma bar musu abin gori har duniya ta tashi. Sai da ya fara kukan shima kafin daƙyar na lallashi kaina nayi shiru, ina lallashin sa Anty Labiba ta shigo.

Ta zauna kan bedside drawer fuska a washe tana kallo na ta ce
"Ta Bilal bada kanki a sare ya jikin?" Ba tareda na kalleta ba na amsa da cewa
"Da sauƙi" na ɗora da gaisheta. Ta amsa ta ce

"Ashe kuma haka abu ya faru? Toh Allah ya kiyaye gaba ya sa ya zame miki kaffara". Na ɗaga kai na kalleta dan ban fahimci mai take nufi ba, maimakon ta ƙara mun bayani sai ta ce

"Na tambayi Mama yaushe za'a je kwaso kaya ta ce ke za'a tambaya, yaushe zamuje? Dan na ji an ce ranar asabar amarya zata tare ko kin bar musu kayan naki ne da su zata tare?"

Sai lokacin na ɗaga kai na kalleta kamar mai tsoron magana na ce
"Anty ya aiko da takardar ne?"

"Au jiyan haka kika fito ziƙau baki musu aika aika kin kuma karɓo tikitin yancin ki ba?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login