Showing 3001 words to 6000 words out of 257873 words
nake naji zakayi magana ko kuwa" a fili kuma nace
"Afuwan, ganinka ne duk ya rikitani. Bari nayi maka packaging sauran se kaci idan ka koma"
"Haba dai, su Amir ba zasu ci ba? " Ya faɗa kamar gaske. Sena wuce shi kawai a raina ina gulmar halinsa. Ko pure water na bashi seya tafi da sauran balle abinci shine zece wani su Amir ba zasu ci ba. A fararen robobi na juye masa sauran abincin da banda wanda na ɗanɗana da ina girkin ban sake jinsa a baki na ba. Roba uku na masa ɗaya shinkafa ɗaya kaza se coslow a ɗayar lemon ma na juye masa a gorar Faro na haɗe masa komai cikin ledar dana ɗakko.
"Wannan halin naki yake tabbatar mun zaki kula da cikina idan mukayi aure, Allah dai yayi miki albarka ya barmu tare my Halims" ya faɗa sanda ya karɓi ledar. Muka jera yana mun surutu, seda na buɗe masa get ya fita da mashin na rufe kafin na fita na same shi ya ɗaure ledar yanda abin ciki ba zasu zube ba kafin ya hau mashin ɗin yana kallona yace
"Da yanzu zaki wuce gida se mu tafi na ɗana ki". Tunda yazo nake raya in masa magana akan da canza mashin ɗin da yayi dama gini ya cigaba ko yayi amfani kuɗin ya haɗa kayan saka ranar tunda dai tsohon nasan babu abinda yayi ai amma gudun kar yaga na shiga rayuwarsa yasa nayi shiru se nace
"To bari kawai nayiwa Anty Labiba sallama se mu tafi dama na gaji gashi kuma gobe ina da practical exam ina so nayi karatu" na juya cikin gidan.
Toshe kunne kawai nayi na haɗa kayana na gudu na bar mata wanke wanke ina tana faɗin zan sake zuwa ne na tafi, faɗan mu ba wani jimawa yake ba da kanta ma zata nemo ni musamman yanzu da yara zasuyi hutun makaranta ga tsohon ciki tana dashi dole ta nemo me tayata da kayaniyar yaran. Na ɗane tsuntsun soyayya ya lula damu muna tafe yana mun surutan da ba wani ji nake sosai ba saboda iska har muka isa sabon titi gidan mu. A bakin gate ya tsaya na sauka ya kalli ginin benen da ake ɗora mana da har an fara fenti yace
"Ashe aikin nan yayi nisa haka, wato mu talakawa ne muke jin garin nan masu kuɗi sha'aninku kawai kikeyi". Fuska ta ba yabo ba fallasa ban dai ce masa komai ba ya shiga laluben aljihu, harga Allah na saka ran tunda yace mun ya siyi mashin idan ya tashi zuwa ko 5k ce ze bani shiyasa ma banji komai ba na kashe kuɗin transport ɗina na sati da Abba ya bani nayi masa abinci ko be biyani duka ba a ƙalla zan rage wani abun musamman da yake ta koɗa daɗin abincin yana faɗin na cancanci tukuici ganin yana laluben Aljihun yasa nayi ɗan murmushi ina jira se naga ya zaro wayarsa ya buɗe kafin ya juyo yana cewa
"Bari in sake miki hoto wlh kin mun kyau yau ɗin nan irin sosai fa My Halims.
Takaici ya kamani amma haka na gyara ya shiga ɗauka na hoton seda aka kira sallah kafin yamun sallama ya burga mashin ɗinsa ya tafi na juya jiki ba ƙwari na shiga gida a raina ina ayyana ƙila se jibi da yace ze zo ko kuma ya mun transfer.
[5/18, 13:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi.*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 2*
Washe gari daƙyar na yakice bacci nayi shirin makaranta, ina gama karatu Bilal ya kirani har gurin ƙarfe ɗaya muna hira kafin ya barni na kwanta dama ga gajiyar dana kwaso a makaranta jiyan na ɗora data girki sannan dana dawo gidan ma ban zauna ba na tarar anyi fenti a ɗakina gaba ɗaya an hargitsamun kaya seda na gyara su sannan na kwanta. Shaf na manta da munyi faɗa da Hansa'u jiya na zauna jiran zuwanta har ƙarfe tara seda na kirata sau biyu bata amsa ba wanda nasan ba halin ta bane da wuya na kirata a waya bata amsa ba sedai irin haka idan munyi faɗa. A fili nace
"Lallai, wai ita ta ɗauki abun har zuci ashe. Ni da ya kamata nayi fushi ta zagar mun Habibi banyi ba se ita? To ai shikenan" na ɗauki jakata da Lab coat na fito falo na tarar da Mama tana ware atamfofi. Sau biyu ina ce mata zan tafi tana mun Allah ya tsare hanya. Ɗari biyar ce a jakata, zata kaini ta dawo dani amma bani da canjin da zanci wani abu kuma yau ɗin wuni zamuyi se ƙarfe huɗu zuwa biyar zamu taso. Ganin na tsaya yasa ta tambayeni lafiya? Na shiga sosa kai, tsaki kawai Mama tayi ta buɗe POS ɗin ta dake gefe ta zaro dubu ɗaya ta miƙa mun tana cewa
"Banda shegen iyayinki me yasa baki zo kin masa abincin a nan ba?" Karɓa nayi tareda mata godiya na fita. Ina son Mama, bata zafafawa a lamuranta. Nasan ba wani son zancen aure na da Bilal take ba musamman yanda duk yan uwanta suke sukar abun amma tunda nida Abba muna son ita ma ta karɓa tana mana addu'a.
Seda muka fito break kafin muka tsaya da Hansa'u nace mata "wai saboda maganar jiya yasa baki biyo mun ba yau kuma na kiraki baki amsa ba?"
"In biyo miki kuma? Ina ce kikayi kowa tasa ta fishsheki babu kr babu ni akan Bilal iyayenki ne kawai na zaki bari ba. To tunda ni ba iyayenki bace ai gara na tattara tsumman rayuwata na baki guri tunda baki na baze iya shiru ba har idan naga abinda ba daidai ba se nayi magana" Hansa'u ta bani amsa, sena rungumeta ina cewa
"Haba ƙawata ki barni in kama wa? Ai kin san dai tsakani na dake ya wuce ƙawance kema yar uwata ce kina cikin waɗanda bazan rabu dasu ba ai" ta mun banza, dake nasan nice da laifi dukda naji haushin abinda ta faɗa akan Bilal amma kuma nima abinda na mata ya shallake wanda tamun hakan tasa na ringa bata haƙuri harta sakko muka tafi siyo fanke da lemo. Bayan mun zauna nace mata
"Amma tsakani da Hansy dole a ringa jin kanmu har idan zaki ringa taɓa mun Yarima. Ya kamata ki ringa mun kara, ko baki son Bilal darajar ƙaunar dake tsakani na dashi ai yaci ki mun kara. Bana so ki dena zaginsa a gabana idan ma zaki zage shi kiyi can a inda bazanji ba dan nima bazan miki kara ba sena rama masa"
"Ai shikenan, ni dai bazan zauna tare dake ina kallo kina ƙoƙarin jefa kanki a halaka kuma nayi shiru na barki ba dole in faɗa miki gaskiya ko ki ɗauka ko karki ɗauka ruwanki" ta bani amsa, a hasale nace
"Auren Bilal ɗin ne kike kira da halaka Hansa'u? Wai me kike nufi da Bilal ne? Ki gaya mun me yake aikatawa da har kike kiran aurensa da jefa kai a halaka wane mugun hali yake dashi da ban sani ba?" Na ƙarasa ina miƙewa tsaye. Watsa hannu tayi tace
"Kin fini sanin halakar da nake nufi sedai idan kin so ne zakiwa maganata mummunar fassara. Akwai halakar duniya data wuce mace tayi rashin dacen mijin aure? Bilal be dace dake ba, kiso ko karki so sena faɗa ke kike sonsa amma shi ba sonki yake ba idan ma kuma yana sonki to akwai dalilinsa na hakan amma ba zaki fahimci abinda nake faɗa miki yanzu ba ba kuma na miki fatan kiyi nadamar kin jij maganar masu sonki a sanda komai ya lalace miki. Tun wuri ga maza fululu masu ƙaunar ki dagaske ki nemi mijin aure a cikinsu ina mai tabbatar miki har ba Allah ya ƙaddara ba Bilal ya samu wadda ta fiki sedai kiji wani zancen wlh" ta ƙarasa tana bari na a gurin. A maimakon sulhu se gashi mun sake tafka wani faɗan dan da aka tashi ban tafi ba seda na sameta na sake zazzaga mata rashin mutunchi na faɗa mata nasan baƙin ciki take mun ba wani abu da saboda na samu me so na zamuyi auren soyayya da ƙuruciyarmu ba irinta ba da zata auri tsoho sa'an Babanta shine take mun baƙin ciki. Kwaɗayin daya kaita ta amsa zata auri tsoho shi zesa ta haɗiyi baƙin cikinta ta kalle mu ni da Habibi na musha soyayya. A bakin titi na cimmata suna jiran Adaidaita da ƙawayenmu biyu Zainab da Hussaina duk yan unguwar mu ne tare muke tafiya dama. Hansa'u ta ringa kuka ko a jikina su biyun ma da suka shigar mata nayi musu tatas nayi tafiyata na barsu raina fes domin ba wanda ya isa ya taɓa Bilal na barshi, dama ta kama kanta ta fita a sabgata dashi se mu cigaba da lallaɓa zumunchin mu amma ta soka kanta a inda ba'a gayyaceta ba.
Dana koma gida tsaf na kwashe labari na bawa Bilal daya kirani, ga mamakina se yace wai ban kyauta ba me yasa zan mata haka ai kamata yayi naji uzurinta domin yanda muke da ita kowa yasan ba zata cutar dani ba
"Kenan ka yarda kana da mugun halin da har zata ringa faɗar irin Maganganun nan akanka?" Na tambayeshi, se yace
"No Halims ba haka bane. Abinda nake nufi da se ki mata uzuri ki bita a hankali kiji menene hujjojinta amma yanzu abinda kika mata gaskiya baki kyauta ba ai tsakaninku ya zarce haka gaskiya banji daɗi ba" ya ringa mun faɗa har naji haushi ma na kashe wayar.
Kwana biyu da suka biyo baya banje makaranta ba mun samu interval kafin mu fara theory parts na jarabawa. Tun a washe gari da Mama taga har yamma bance zanje gidansu Hansa'u ba ita kuma bata ga tazo ba ta tambayeni ko lafiya se kawai nace mata jiya da muka taho gadon ƙaya ta wuce gidan yayarsu. A washe garin ranar da rana Abba ya dawo daga Enugu sunje wani aiki da magriba bayan ya dawo daga masallaci ina ɗakina na idar da sallah na jiyo yana ƙwala mun kira, Abba bashi da faɗa daga sautin muryarsa na san akwai wani abu abinda ya fara zuwar mun ko zancen Bilal ze mun tunda yace kafin ya dawo musan abinda muke ciki.
Ina fita naga Hansa'u a zaune, a raina nace lallai ma, ƙarata ta kawo ko me? Haka na samu guri na zauna nan kuwa Abba ya haɗa mu duk mu biyun ya mana kaca kaca kowa ya bata laifinta. A yanda yace tun da la'asar daya fita aka bashi labarin wai munyi faɗa a makaranta a raina na ringa tsinewa munafukai nasan kuma baze wuce Nasir ko Musan gidan inji ba sune yan unguwar mu kuma a gabansu mukayi faɗan shine ashe sunzo unguwa suna yawo damu, Abba ya mana kaca kaca yace kuma mu bawa juna haƙuri kuma idan ya sake jin irin haka ba faɗa ba seya haɗa mana harda duka mun san kuma ze aikata. Yana da sanyi da wasa da dariya amma fa kaifi ɗaya ne muddin yace zeyi abu zeyi dan haka muka masa alƙawarin haka ba zata sake faruwa ba. Washe gari kuwa da mukaje makaranta komai ya wuce, dukda dai Hansa'u na lura bata gama hucewa ba amma ni na sake gaba ɗaya ina ta janta har daga ƙarshe ta huce muka cigaba da sabgoginmu.
Ranar Asabar Bilal yace ze zo, tun haɗuwar mu a gidan Anty Labiba be samu ya dawo ba se waya mukeyi, sun sake komawa Abuja ance wannan watan in sha Allah albashinsu ze fara shiga harma za'a biya su na baya da basu samu ba. Naji daɗi sosai ko ba komai maganar aurenmu zata taso masu ganin ba aure na zeyi ba zasuji kunya. Allah ya sani ina son Bilal tamkar rai, yanayinsa da halayyar sa sun min a irin mijin da nake fatan aure na kuma faɗa na ƙara ciki wuya ko daɗi zan zauna dashi domin shi nake so ba wani abu ba duk wanda suke zuwa masu abin hannun da ake ganin sunfi dacewa dani ni basu gaba na shi ɗin shi nake so kuma ina ji a jikina gaba se mun zama abinda ba'ayi zato ba duk masu gulma se sunji kunya.
Kamar ko yaushe nayi masa snacks samosa da cake se dambun nama da Anty Hasiya ƙanwar Abbanmu ta kawo masa na ɗibar masa. Tsayin fara soyayyar mu Allah keda kullum amma duk sanda Bilal ze zo sena masa abinci ko wani abun taɓawa da zan bashi. Tun Mama na biye mun harta fita sabgata a cewarta abin nawa bana ƙare bane, harta kai shi ze faɗa mun abinda yake so ko in tambaye shi babu ko sisinsa haka zanyi yazo ya cinye har ya tafi da saura balle kuma da azumi gidanmu yake shan ruwa idan be zoba zan aika masa dashi haka in sallah tayi zan haɗa sha tara ta arziƙi a kaiwa Hajja mahaifiyarsa sannan in haɗa masa wanda zasu zo da abokanansa suci se an samu me mutunchin gaske ne cikinsu ze iya ɗaukar wani abu yace mun ga tukuici amma hakan ni sam baya damuna domin dan Allah nake masa kuma arziƙin so da ƙauna.
Seda a gama jere masa snacks ɗin da kunun aya me sanyi kafin na zauna muka gaisa muna kashe juna da murmushin ƙauna. Na cika masa kofi da kunun ayar yasha ya gode Allah yana kallona yace
"Wato Halims, bansan kalar murnar da zanyi ba ranar da aka ƙwala shelar ɗaurin aure na dake, ina ga se na hau kan hasumiyar masallaci tsabar murna" na ƙyalƙyale da dariya nace
"Ka dai rufa mana asiri kar ace ango ya karye a garin murnar aurensa" yace
"Allah Halims baki san yanda nake jinki a raina bane kedai kawai Allah ya kaimu ranar da zan nuna miki komai a aikace ba surutun da kike ɗauka wasa ba".
Na sadda kai ƙasa ina murmushi kawai ba tareda na ce masa komai ba, ya fara cin samosa yana mun hira can yace "Albishirinki Halims" na ɗago na kalle shi tareda cewa
"Goro" ya karɓi kunun aya kafin yace
"Albashin mu ya fara shiga, an turo mana na wata uku jiya". Sosai naji farin cikin albishirin ɗin nada na gyara zama ina cewa "kai alhamdulillah naji daɗi sosai Allah yasa albarka" ya amsa da
"Amin" yana cigaba da cin kayan gabansa. Hira muka cigaba ina jira naji ya sako zancen aiko sa rana tunda salary ya fara shiga amma shiru hakan yasa nace masa
"Dama ko jiya Abba yake sake mun magana nace in sha Allah idan kazo zan gaya maka, to ashe ma jira ya ƙare tunda abinda muke tsammani ya iso".
Seya shafa kansa yace
"Eh wlh, ai Baba Malam ma yace kawunku na Galadanci ya masa magana akan akwai bikin da za'ayi acan gidan kakanninku so samu suna so a haɗa"
"Lah bikinsu Salina ya taso kenan" na katse shi se yace
"Ina ga su ɗin ne, yace wai wata shida suke so a saka wancan ɗin". Ɓata fuska nayi nace "har wata shida?" Seya kalleni yana cewa
"Yayi kaɗan ko?"
"Kaɗan ko dai yawa?" Na faɗa ina ɓoye fuskata. Na zata ze tsokaneni akan abinda na faɗa se naji yayi shiru dana ɗaga kai na kalleshi se naga yayi shiru yana kallon center table ɗin dake aje. Da yar damuwa nace
"Lafiya dai naji kayi shiru?" Ɗan murmushi yayi yace
"Babu komai, kawai ina tunanin yanda al'amura zasu kasance ne. Idan son samu ne ma ni nan da wata uku ma a kawoki gida na sedai uzururrukan da suke gabana bana tunanin a shekara ɗaya ma zan iya kammala su" ya faɗa kamar zeyi mun kuka.
Da sauri na kalleshi jin abinda ya faɗa, ya marairaice fuska yace
"Kin san nauyin da suke kaina Halims. Yanzu fa ba tareda anyi shawara dani ba aka saka bikinsu Fauziyyah yanzu haka a yanda akayi sa ranar saura wata biyu da sati uku bikin. Daƙyar fa na lallaɓa Baba Malam ɗin aka maida sa ranar wata shida a lissafi na idan akayi nata kinga na sallameta sannan na koma kan ginina na ƙarasa se azo ayi sa ranar mu idan na samu yanda nake so ma wata ɗaya ko biyu za'a saka shikenan".
Kallonsa kawai na ringayi na kasa cewa komai, ban ma gane kan lissafin da yake ba. An saka auren ƙanwar sa wata shida se anyi nata sannan azo a fara maganar namu a ƙalla dai shekara ɗaya zuwa da rabi yake sake nemowa akan shekara biyar ɗin da muka kwashe. Karo na farko da Bilal yayi wani abu da naji haushinsa har raina amma bance komai ba na sunkuyar da kai kawai ina jinsa yana cewa
"Kin san na gaya miki harda gadonta na haɗa nayi sponsoring karatu na in ba dan haka ba waye ze ɗora mun wahalar aurenta ace se na mata kayan ɗaki dole?"
"Zaka mata mana tunda ai bata da wani yayan da ze mata bayan kai. Kaine makwafin mahaifinta a yanzu" na faɗa murya a ciki, se yace
"Haka ne idan ina dashi zan mata amma a halin da nake ciki yanzu nima ai ban tsaya da ƙafata ba ga kuma tawa wahalar a gabana. Se yanzu nake dana sani lokacin da Alhaji Lawan yace muyi musanye na bashi kango na ya bani wani gida complete dana karɓa canjin nayi wani abu dasu ƙila da tuni yanzu mun haifi Nur da Nurain ko?" Ya ƙarasa da sigar tambaya. Ɗan murmushi kawai nayi yaci gaba da surutan da duk uzururrukan sa da basa ƙarewa ne kullum yana so yayi kaza da kaza kafin ayi waye da waye jin yanda nake amsa masa maganganun yasa yace mun
"Ko kin fara jin bacci ne naji kina amsawa daƙyar?" Se kawai