Showing 102001 words to 105000 words out of 257873 words
gaba da zama da shi zan wuce mata gaba na rabata da shi"
"Yanzu dai me kake nufi Abba?" Mama ta faɗa tana kallon sa, sai ya miƙe tsaye ya ce
"Ki cire idon ki da kuma kunnuwan ki akan abin da wani ko wata yake kawo miki akan Halima. Har idan ba ita ta zo ta faɗa mun matsala ba, a guri na lafiya lau ta ke zaune dan haka babu wata magana da zan saurara" yana gama faɗar haka ya shige ɗakin sa.
"To ke me ye naki a ciki Mama? Ai kamar yanda Abban ya faɗa ne, tun da dai ita bata ga aibun abin da ake mata ba ko ta kawo ƙorafi ba kin ga ai lafiya lau ne a gurin ta, sai ki bar ta ki ci gaba da yi mata addu'a kawai tun da haka ta zaɓawa kanta. Dan Allah yan da ya bar maganar ke ma ki shafe ta kamar bata faru ba. Idan da ta ji zafin abin da aka mata kafin ma ace ta tafi zata yankewa kanta hukunci amma an ce ta tafin ma taga guri ta zauna se mu cigaba da bin ta da addu'a Allah ya shiga lamarin ya kawo rangwame" amsar da Anty Labiba ta bawa Maman kenan bayan da ta kira ta ta na mata ƙorafin yanda Abba ya bagarar da maganar da Baba Jummai ta kawo akan Halima.
****************
Farar shinkafa na dafa tun da akwai sauran stew, sai da na gama jere abincin a dining kafin na tuna da ban yi wankan yamma ba shima Al'amin ba'a masa ba. Ganin Bilal be dawo ba har na gama se na fita na shiga kiciniyar hura wutar dan ma ita cen busasshe ne kuma garin akwai iska, ruwan ma kaɗan na saka dan ya yi saurin tafasa na koma ciki na zuba abinci na ci dan yunwa nake ji sosai, sai biyar da rabi sannan Bilal ya dawo lokacin har ruwa na ya tafa sa dan haka na kwantar masa da Al'amin na yi shirin wanka na fita. A bokiti na ringa ɗiba ina juyewa a babban bahon da ke cikin banɗakin tsakar gidan, wani ruwan da zan zuba a flask da na wankan Al'amin na ƙara sannan na shiga wankan a raina ina mitar Baba Jummai da take cewa zan ga idan tana da amfani a guri na ko kuma ba ta da shi yanzu da ta tafin menene ban yi ba? Girki ko kula da Al'amin ɗin ko kuma saka ruwan wankan? Wankan ma gashi zan yi da kaina dama ai na mugunta ta ke yi mun ta yi jibga mun ganye idan nayi magana ta balbale ni dama masifa wai so na ke ta ringa mun jiƙa jiƙa na lalace ace ita ta cuce ni.
Ina wannan mitar a raina na ciro ganyen da na bari a ruwa ya juƙu gashi da ma ya yi laushi da safe da muka yi wankan na ji ta na cewa se an ɗebo sabo da yamma, ba tare da na ko girgije shi ba na yi bismillah na lafta a gadon baya na. Lokaci ɗaya na fasa ihu saboda wani azababben zafi ya ziyar ci fatata take baya na ya ɗauki raɗaɗi na jefar da ganyen a gefe na shiga tsalle ina shafo guraren da nake jin zafin a jikin fata ta. Bilal dake zaune falo yana wa Al'amin wasa jin ihu na ya fito da gudu dai dai nan kuma aka buga gidan. Banɗakin ya shigo yana tambayar lafiya ba bakin magana sai kawai na fashe da kuka ina nuna masa bayana yanda ya rafka salati bayan da ya duba bayan ya sa na sake fashewa da wani kukan ya ce
"Gurin ya yi jaa, ƙonewa kika yi?"
Zani na na ja na ɗaura kawai na fito ina cigaba da kuka shi kuma ya tafi ya buɗe ƙofa da ake ta bugawa. Hajiya Inna ce Surukar Maman Yusuf, ina durƙusa gaban kujera ina kuka dan sosai baya na yake mun raɗaɗi suka shigo falon tare, wai ashe idan an kwashe ruwan ya kamata na bari ya ɗan sarara kuma se an girgije ganye kafin a fara bugawa tana ganin ganyen kuma ta ce ai dole na ƙone saboda ganye ya gama dafewa. Daga ƙarshe da towel ta mun wankan ni dai har dare baya na be dai na mun raɗaɗi ba.
Ni na ce mata ba se an yiwa Al'amin wanka ba saboda yanayin garin akwai sanyi sanyi dama ba'a son raina ake masa wanka biyun ba se mura ta zo ta kama shi a barni da wahala, da zamu kwanta na goge masa jiki na saka masa kayan bacci kawai. Tsabar yanda yan ayyukan da na yi suka gajiyar da ni dan na kwana biyu ban ba ina kwanciya bacci ya kwashe ni. Cikin dare azababben kukan da Al'amin ya ke ya farkar da ni, na buɗe ido daƙyar ina kallon Bilal dake duƙe kai na ya na tashi na, daƙyar na yunƙura na zauna ido na ko buɗuwa da kyau ba sa yi ya miƙo mun Al'amin ɗin ya na cewa
"Wane irin bacci kike yi haka Halima sai kace wacce ta mutu kusan minti ashirin yaro a kusa da ke yana kuka amma baki farka ba".
Karɓar sa na yi na fara ƙoƙarin bashi nono amma yaƙi karɓa sai ƙara ware murya ya ke yana canyara kuka kamar wanda ake wa wani abu, tun ina lallashin sa daga zaune har na miƙe na fara jele a cikin ɗaki sai lokacin na ga ashe ƙarfe goma da rabi ma sannan ban fi awa ɗaya da kwanciya ba gaba ɗaya.
Tun Bilal na karɓar sa idan na gaji daga ƙarshe ya zare system ɗin sa daga jikin socket na ɗauka ɗaki zai kaita ya dawo shiru shiru ban ji shi ba lokacin sha biyu har ta gota na saka dogon Hijab na saɓa Al'amin a kafaɗa na bishi dan ba ze gudu ya barni ni kaɗai da rainon ɗan sa ba ga bacci da ke cin ido na kamar zan tuntsira, ina murɗa ƙofar falon na fahimci ya rufe ta da muƙulli. Bugun duniya kamar babu mai rai a ɗakin ga sauro na ta cizo na har na gaji na koma ciki ina kuka Al'amin na yi, ranar naga rayuwa ban samu sararin runtsawa ba sai ƙarfe huɗu da mintoci dan har an fara kiraye kirayen sallah a wasu masallatan.
Daƙyar na buɗe ido na da na ke jin sa kamar an watsa mun barkono, ƙwaƙwalwa ta har wani yaji yaji take mun tsabar bacci da gajiyar da ke tattare da ni. In da na kwantar da Al'amin na fara dubawa a zato na ko yanzun ma kukan yake ta yi ban ji ba irin na daren jiya amma na ganshi yana baccin sa lakadan kamar ba shi ya gama wujijjiga ni cikin dare ba. Ɗaya gefen na kalla in da Bilal ke tsaye fuska babu yabo babu fallasa, shi ya tashe ni kenan.
"Amma kin san yau Monday ko?" Ya faɗa yana kallo na. Rufe ido na nayi kafin na sake buɗewa ina ƙoƙarin tuna me za'a yi ranar Monday ɗin da yake tuna mun amma babu abin da ya zo mun a ƙwaƙwalwa ta. Ya yi tsaki ya ce
"Ki tashi ki samar mun abin da zan ci fita zan yi".
Kallon sa na yi kamar ban fahimci abin da yake nufi ba, in tashi na samar masa abin da zai ci sai ka ce bai san yanda na raba dare ina raino ba shi kuma ya kulle ƙofa ya sha baccin sa, ƙaramin tsaki na yi na juya ba tare da na bashi amsa ba na mayar da haƙarƙari na dan ni kam bacci na ke ji. Ban kai ga rufe ido na ba ya daka mun tsawar da na jita har tsakiyar kaina ta sake haɗe mun da gigitaccen kukan da Al'amin ya fasa da alama kuma tsawar Bilal ɗin ce ta tsorata shi shima.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 26*
Ko ba'a faɗa mun ba na san da wahala idan jini na bai hau ba, daƙyar na lallaɓa Al'amin ya yi shiru na goya shi kafin na fita samawa Bilal abin da zai ci. Bamu da komai da zai ciyu da safe ban da taliya. Ita na yi jollof da sauran miyar da ta rage na dafa masa baƙin shayi. Ya ringa kallon abincin kamar wanda na aje wa mugun abu kafin cikin faɗa faɗa ya shiga tambayar babu nama a gidan ne da zan dafa masa tsurar taliya ko me?
Haka na koma na ɗebo masa naman ina ajiyewa ya sake balbale ni da wata masifar wai ina kayan tea, na kalle shi kawai, sai ka ce ua siyo ya ajiye. Ciwon da kai na ya ke mun ba ze bar ni na yi doguwar magana ba Allah Allah kawai na ke yi ya fita na koma na kwanta amma naga alama shi jan magana ma yake so ya yi. Wucewa na yi na koma ɗaki na ba tare da na bashi amsar kayan shayin da ya buƙata ba, ban san ya ya ƙare ba dan bai biyo ni ba ina shiga na kwanta rubda ciki da Al'amin a baya na dan ba zan yi gangancin sauke shi ya farka na shiga uku ba. Allah ya taimake ni har ƙarfe goma muna bacci kafin ya farka, ba wai baccin ya ishe ni ba amma na rage, nauyin da kai na ya yi mun ma ya ragu.
Sauran taliyar na ɗumama na ci, babu wuta ni kuma gaskiya ba zan iya kunna ita ce ba, da ya ke garwar wankan ta mu irin wacce ake haɗawa da gwangwani ce mara nauyi sai kawai na ɗora ta akan gas, na sake goya Al'amin da yake ƙananun koke koke na shiga gyaran gidan ina gamawa ruwan ya tafasa. A bokiti na ɗiba da zummar na fara yi masa kafin nan sauran ya sarara sai na yi kar na sake ƙona kaina irin na jiya.
Duk abin da zan buƙata na ɗakko na ajiye zuciya ta cike da tsoro na zauna, a bokitin na surka ruwan na shimfiɗa towel a cikin bahon wankan yanda na ke ganin turawa a TikTok su na yi ba irin wankan da Baba Jummai ta ke yi masa ta cika baho da ruwa ta saka shi a ciki ba.
Cikin ikon Allah na masa wankan ba tare da na shaƙa masa sabulu ko ruwa a hanci ba abin da na ke tsoro, kafin na gama shirya shi ya koma bacci. Na yi hamdala, na juye sauran ruwan na yi wankan soso da sabulu kawai dan na aje wankan ganye gaskiya.
Na shirya daƙyar saboda wani irin ciwon baya da kwankwaso da suka tasar mun lokaci ɗaya kamar ba wanka na yi da ruwan zafi ba, saida na sha paracetamol sannan na kwanta baccin ni ma.
Bamu farka ba sai bayan azahar tukunna na kuma samu sauƙin gajiya da baccin da yake damuna har ciwo jikin duk na samu sauƙin su. Haka nan muka wuni ni da Al'amin mu kwanta can mu ta shi can muka sha hotuna abun mu, da yamma ma a Gas na sake ɗora ruwa na yi wanka na fesa kwalliya tun da gida ya zama namu daga ni sai miji na Baba Jummai ta tafi balle ta fara mun kwakwazo idan na yi kwalliya.
Cikin canjin hannu na na bawa almajiri ya yiwo mun cefane na yi masa sakwara da miyar agusi, a food processor na niƙa doyar tayi luƙai bayan na gama na gama komai na turare gidan da ƙamshi sannan na canzawa Al'amin kaya muka kame a falo abun mu muna jiran Dady. Sai da aka idar da sallar magriba ya shigo gidan, fuska ba yabo ba fallasa ya yi sallama na miƙe tare da Al'amin a kafaɗa ta na nufe shi ina masa sannu da zuwa. Takaddun hannun sa ya miƙa mun na karɓa shi kuma ya karɓi Al'amin ɗin na wuce ɗaki jiki a sanyaye na ajiye masa su.
Duk kwalliyar da na yi amma ko kyakkyawan kallo ban samu daga gare shi ba. Haka na wuce kitchen na ɗakko ruwa da lemo na fito, ban tarar da shi a falon ba na ajiye na leƙa ɗaki nan ma baya nan har can ɗakin sa na leƙa duk ban tarar da su ba. Tunanin ina suka shige na tsaya ina yi?
Daga tsakar gida na jiyo muryar sa da wani, na leƙa na gan su su uku sun nufo falon hakan ya sa na koma ciki da sauri na shiga ɗaki na lalubo mayafi. Mutum biyun duk ban san fuskar su ba yanayin su da harshen su ma kamar ba hausawa ba ko ma in ce ba Musulmai ba. Ya gabatar mun da su a matsayin abokanan aikin sa Patrick da Joshua sun zo ganin Al'amin.
Na haɗo ruwa da lemo na kawo musu, har zan tafi ɗaki kuma na fasa na koma kitchen ɗin na zubo nama na sake kai musu. Ban kawo komai a raina ba da irin kallon da naga Bilal ya yi mun na karɓi Al'amin da ya fara gungini nawuce ɗaki na bar su.
Shiru shiru ina jiran ya kira ni ya ce zasu tafi na ga har takwas ta yi babu alama sai ma tashar Ball da suka kunna, sakwarar da na yi bata da yawa sosai leda uku ce kawai amma akwai sauran doyar da na dafa na ga tayi yawa na saka a fridge, fito da ita na yi na mayar kan wuta ta sake tafasa kafin na niƙa ta na haɗa kayan abincin na jera musu akan dining. Daga yanda Bilal ya watso mun ido sanda na musu tayin abincin na san na kwafsa, ina kallo ya yi ƙwafa haɗi da ɗauke kai gefe. A raina na ce ikon Allah, ni a haka ma ina gudun ya ce ban karrama su ba shi yasa na ƙara yawan abincin amma naga alamar kamar laifi na yi a maimakon na yi gwaninta. Su da basu san dawar garin ba kamar dama jiran abincin suke suka tashi suka zubo, ina tsaye suka gama duk suka kwashe manyan naman cikin miyar haka dai na zubawa Bilal sauran na ɗakko ƙaramin try na ɗora masa akai na kai gaban sa na ajiye.
Indomie na koma na dafa na soya ƙwai kamar na san za'a yi haka da zan yi aiken na bada aka siyo mun na wuce ɗaki na ci. Ko sallama bamu yi da baƙin ba na dai ji sanda suke sallama da Bilal ɗin bai kira ni ba nima ban fita sai da ya kullo ƙofa ya dawo ya fara kwarara mun kira tun daga tsakar gida.
"Da izinin uban wa kika ɗauki abinci na kika basu?" Ya faɗa dai dai ina fitowa daga ɗaki. Shiru kawai na yi ina kallon sa dan ban san me ya kamata na ce masa ba, hakan ya sake harzuƙa shi kamar zai rufe ni da duka ya sake cewa
"Ina miki magana wato ga mahaukaci shi ne zaki mun shiru ko? Saboda baki da hankali baki san dai dai ba, nan yan uwa na jini na suka zo gidan nan ku ka hana su abinci amma yanzu wasu kattin banza ba dangin iya babu na Baba sun zo jikin ki na rawa kin ɗebo ruwa da lemo kin basu, bai ishe ki ba kin sake kawo musu nama sannan abincin baki ko bari ma na ga kalar abin da kika girka ba kin kawo musu tsabar kin mayar da ni banza shashasha sauran da suka rage zaki zuba ki kawo mun. Sai ki zo ki kwashe tsiyar ki dan ni ba mahaukaci ba ne da zaki bani sauran arna na ci. Wace tsiyar kika ga sun kawo mana balle ki ɗauki abinci na ki basu?"
Kallon sa kawai na ke yi yanda ya fitittike yana masifa sai kace wanda na aikatawa wani zunubi, daga na karrama baƙin sa shikenan cibi ya zama ƙari? Maganar sa ta ƙarshe ta saka na fahimci ainihin dalilin faɗan na sa, mamakin sa ya nunku a raina. Ban tsammaci a fili na furta
"Yanzu saboda basu kawo komai ba ne ya saka kake wannan masifar ashe" sai kuwa ya yo kaina yana cewa
"Kika zage ni sai na naɗa miki duka a cikin gidan nan Halima daga ni sai ke babu mai ƙwatar ki a hannu na". Da sauri na ja baya zuciya ta na bugawa da sauri. Da gaske na tsorata da yana yin sa, lokaci ɗaya idanun sa suka rikiɗa suka yi jaa. Ya nuna kan sa yana cewa
"Saboda ba su kawo ɗin ba ne, ai ni ba ɗan iska ba ne da zasu zo su cinye mun abinci su tashi ko kuwa kin ga gida na yayi miki kama da sansanin gajiyayyu da zan ringa ciyar da mutane kyauta?
Wannan ya zama karo na farko kuma na ƙarshe da wani ɗan iska ko yar iska zasu sake zuwa gidan nan ki ɗauki wani abu ki basu ba tare da izini ni na ba, idan kuma kin cika ke bakya jin magana ki sake" ya faɗa yana kaɗa yatsunsa biyu a fuskata.
Motsin da Al'amin ya yi ya sa na yi firgigit na kama jiki na guri ɗaya a tsorace kafin na fahimci shi ne na nutsu ina sauke ajiyar zuciya. Na kasa yarda lafiyar Bilal ƙalau, abin da ya faru yanzu ya saka mun kokwanto a zuciya ta, an ya kuwa Bilal baya shaye shaye? Gaskiya akwai abin da yake afawa a ɓoye da yake gotar masa da saitin kan sa dan dai abubuwa da yawa da yake