Showing 156001 words to 159000 words out of 257873 words

Chapter 53 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

505

kai ba. Wlh Halima muddin baki yiwa kanki faɗa ba zaki kashe rayuwarki a banza ki ƙare a inda ba'a san mutunchinki ba. Yanzu ke ko dagaske kunyar yake ji idan yana sonki kuma yana darajaki da son cigaba da zama dake zai ɗauki tsayin lokacin nan ba tareda yabi ta kanki ba? Ki cigaba da mafarki kina yaudarar kanki, ko ki yarda ko karki yarda Halima Bilal baya sonki, idan ma a baya ya soki to yanzu bakya gabansa. Ya daɗe yana miki kora da hali wanda idan kina da tunani ya kamata ace tuntuni kin fahimci haka kin nemawa kanki mafita amma kin tsaya kina yaudarar kanki ke gaki uwar yan uzuri toh sai ki cigaba Allah ya bada sa'a". Bata bani damar sake cewa komai ba ta datse kiran.

Na tashi zaune ina sauke numfashi, ban san me yasa ba kowa ya kasa fahimtata. Waya ta ce tayi ƙara, na ɗauka Hansa'u ce dukda na san ko zata huce ba nan kusa ba sai dai sunan da na gani yana yawo akan screen ɗin ya saka gabana yankewa ya faɗi. Harta katse ina kallon screen ɗin wani kiran ya sake shigowa, bana so, hannuna kansa ya so yaƙi bani haɗin kai amma bisa tirsasawar zuciyata na amsa kiran. Ban ce komai ba na kara wayar a kunne na, daga can ɓangaren ina jin yanda ya sauke ajiyar zuciyar da na jita har cikin magudanar jinin jikina kafin cikin murya mai taushi haɗi da rauni ya furta

"Halims ashe zaki iya dogon fushi haka dani?". Kamata yayi ace naji haushin furucin sa domin ƙarara abinda yake nufi duk tsayin lokacin ni yake jira na kira shi Kenan shiyasa bai nemeni ba amma shirun na cigaba da yi ina saurarensa ya sake cewa

"Nayi kewarki adadin da baki ba zai iya furtawa ba dan Allah Halims ko mai zai sakw faruwa tsakaninmu a gaba ki hukuntani ta kowacce siga amma kada ki sake bari na, zan jure komai amma ba zan sakw iya jure rashin ji da ganinki a duniya ta ba wlh na azabtu wahalar da na sha a tsakanin lokacin nan kawai sai dai nayi fatan ta zame mun kankarar zunubi amma Halims kin sakani a wani yanayi da bana fatan na sake shiga irin sa".

Jin da nayi kamar wacce aka ɗauraqa fuka fukai ina shirin fara shawagi a sararin samaniya na sakw hawa gajimaren yaudarsa wanda sai nayi nisa ƙila ya sake girgijeni na faɗo na karye a in da ba zan ɗoru ba, tattaro duk wata jarumta haɗi da ƙarfin hali na nayi na ja masa tsaki mai ƙarfi kafin na zare wayar daga kunne na na kashe. Yanda kasan wacce ta sha tseren gudu haka na dafe ƙirji da hannu biyu ina sauke numfashi, na bi wayar da kallon jin kira ya sake shigowa har ya katse ya sake kira kafin ya dakata sai kuma ga saƙo sai a lokacin na ɗauke ta na buɗe na karanta.

"Na san kin huce, ina waje ki fito mu koma duniyarmu" abinda ya rubuta a ciki kenan. Kashe wayar nayi gaba ɗaya na kwanta lokaci ɗaya hawaye suka ɓalle mun. Ashe kallon wacce ta haukace a soyayya kawai Bilal yake mun yana ganin na manta ƙima da martabata a matsayina na mace shi yasa har yake tunanin bayan irin abinda ya faru tsakaninmu baya buƙatar wanke kansa ko rarrashina kai tsaye zan manta komai na sake komawa gareshi, lallai kuwa da na cika sakarya.

BILAL
Tsabar mamaki daskarewa yayi a tsaye lokacin da sautin tsakin Halima ya isa kunnuwansa. Ko a mafarki bai taɓa kawo haka ba, Halimar da ya sani bata taɓa yi masa ko kallon banza ba balle ta jefe shi da irin wannan tsaki da yake tafe da ma'anar tsana da kuma raini. Ya raya ya tafi kawai yabi unarnin Hajja ya rabu da ita amma kuma ya kasa dan idan ya ce baya son Halima ko kuma yana da burin rabuwa da ita shi kansa ya san ƙarya yakeyi, kai ko baya son ta a karon kanta zai so ta saboda zuri'ar dake tsakaninsa da ita ballantana kuma yana son Matar sa, a duniyar nan kuma ya sani bashi da kamarta domin ita ta so shi ba dan komai na sa ba ta juri duk wani wulaƙanci da tozarcinsa ba dan ta rasa yanda zatayi ba sannan ta rufa masa asiri ta haɗiyi baƙin cikin sa ita kaɗai domin ta kare masa martabar sa.

Amma a yanda ya san tana son sa bai zaci za taji muryarsa tayi masa shiru ba, yayi amfani da salon da ya san duk fushin da takeyi zai saka ta sakko amma a maimaikon haka sai tsaki ta biyo shi da shi.
"Ba ita kaɗai ba har mahaifiyar ta ka haɗa ka zaga" zuciyarsa ta raya masa. Ya runtse ido, wlh yayi nadamar furucinsa idan da yana kuma da halin dawo da abinda ya wuce da ya goge waccen ranar ko komai ba zai canzu ba kuwa da ya goge mummunan furucin da yayi shi da kansa ya san bai kyauta ba. Sake kiranta yayi har sau biyu amma bata ɗaga ba, yana tsayen motar Abba ta iso ƙofar gidan maigadi ya buɗe masa ya shiga ya san ya ganshi amma bai ko nuna alamar hakan wannan tasa ya koma cikin mota ya zauna ya tura mata saƙo, jiran minti goma sha biyar yayi kafin ya sake kiran layin amma rashin sa'a ya ji shi a kashe. Ba yanda ya iya yaja mota ya tafi a zuwan gobe zai dawo.

A karo na babu adadi Zulaiha ta sake kiransa, guri ya samu ya gangare ya kashe motar kafin ya kirata dan tun da yamma da sukayi waya ya ce mata idan ya fito zaije amma ya manta dalilin hankalinsa da gaba ɗaya ya tafi gurin Halima.

Kukan kissa ta fashe masa dashi bayan data amsa wayar nan da nan kuwa hankalinsa ya tashi ya shiga rarrashinta, sai da yayi kamar zai yi yaya kafin tayi shiru ta shiga jero masa ƙorafin shikenan daga an ɗaura musu aure yana ganin ta zama mallakinsa zai fara wulaƙanta ta dama ashe duk alƙawarin da ya mata a baya ba gaskiya bane yanzu ne zai bayyana mata asalin halinsa. Ya ringa rantse rantse akan ba haka bane tun safe yana office da gargaɗin da aka masa akan rashin zuwa aikin da bayayi.

"Amma na ɗauka kace can Headquartern ku na Abuja aka mayar da kai meye kuma haɗin ka da nan da har zasu baka query?" Ta faɗa, sai yayi shiru dan ya manta abinda ya gaya mata kenan ya koma Abuja da aiki data tambaye shi yawan zuwan da yakeyi. Sai ya ce

"Kin san wani aiki ne daban na samu a can ɗin kawai bana faɗa ne saboda ba na gomnati bane ba zanyi saurin sakin wannan aikin ba sai naga wancan ɗin ya gama dai dai ta shiyasa kawai nake cewa headquarter aka mayar dani". Hira suka cigaba bayan ya bata uzurin ba zai samu zuwa yau ɗin ba kamar yanda ya mata alƙawari da farko.

"Amma wlh banji daɗi ba na gama saka ran zan kwanta a jikinka na ɗan yi bacci irin na jiya" ta faɗa kai tsaye bayan da ta gama zagaye zagaye taga yana ta kaucew irin hirar da take so suyi. Shiru yayi kafin ya ce
"Nima na so haka amma na faɗa miki uzuri na". Shikenan ta ɓallo hira, ta kuma sake goge masa hadda domin yau ya gane ashe jiya ba komai ya gani ba. Duk yanda ya ringa danne maganar a ransa sai da ya amayar ya ce mata

"Wai Zully ina kika koyi waɗannan abubuwan?" Kuma wai sai a lokacin ne taji kunya ta ce masa
"Gurin ƙanwar Umma Anty Sadiya tunda Baba ya tsayar da ranar ɗaurin aurenmu ba na gaya maka na koma can gidan ba ita ce ta ringa koya mana".

Ji yayi maganar bata kama masa hankali ba amma kuma ta wani ɓangaren ya ɗan samu nutsuwa akan abunda yake masa yawo a rai sai ya ce
"Tayi ƙoƙari amma a ɗan lokacin nan Zullyn da na sani ko ido bata iya haɗawa dani tayi wannan gogewar lallai wannan Antyn tamu ba ƙaramar Malama bace"

"To kuma kunyar me zanji yanzu bayan na rigada na zama mallakinka ko so kake na tsaya wasa Maman Al'amin ta ƙwace mun kai?" Ta bashi amsa, a ransa ya ayyana
"Halima baiwar Allah ita kam bata wannan rashin kunyar a sunnance take tata". A fili kuma sai ya ce

"Kin san kuwa gwana ce a wannan fannin"
"Ai kuwa duk ƙwarewar ta zan nuna maka na fita" ta faɗa ya ce
"Anya kuwa?"
"Idan kana musu yanzu kazo ka ɗauke ni mu tafi gida wlh yau sai na goge maka hadda dama ni a matse nake".

Zuwa yanzu kam ko yaƙi Allah dole tsoron Zulaihan ya ɗarsu a ransa, budurqa fa wacce bata taɓa sanin namiji ba take irin wannan sakin zancen, tattara nutsuwar sa yayi guri guda zuciyarsa na bugawa ya ce
"Kina da hankali kuwa Zulaiha? Duk ina kunyarki da na sanki da ita a da zaki iya ringa furta waɗannan maganganun? Ko da an ɗaura mana aure har yanzu ba banbancin dake tsakanin da da yanzu fa kaɗan ne domin bamu rigada mun zama ɗaya ba ya kamata ace har yanzu kina jin nauyina"

"Yanzu saboda ina ƙoƙarin faranta maka shine har kake nema ka faɗa mun magana? A fakaice ba so kake kace mun yar iska ko mara tarbiyya kenan" ta faɗa cikin hasalar da bai taɓa saninta da ita ba, dake shima zuciyar sa a kusa take sai ya ce

"Ki bawa kanki amsa ya kamata budurwar da bata taɓa sanin namiji ba ta ringa irin wannan abinda kikeyi?"

"Zargina kake yi Bilal? Ƙazafin zina kake so kayi mun?" Ta faɗa cikin ɗaga murya kamar yana gabanta, sai kawai ya zare wayar daga kunennsa ya katse kiran haɗi da kasheta gaba ɗaya dan ya lura idan ya biye mata zasu iya yin ɓatacciya. Mamaki ya rufeshi yanda lokaci ɗaya halayen da bai santa da su ba suke fitowa ɗaya bayan ɗaya. Zulaihar da ko haɗa ido batayi dashi ko zai yi me kuwa kanta na ƙasa duk maganar da zasuyi har gara gara a waya ta kan ɗan sake dashi suyi hira har ta faɗa masa kalaman soyayya amma ko tsareta yayi a zahiri yace ta maimaita sai dai tayi kamar zata saka masa kuka ya haƙura ya ƙyaleta ladabi da biyya kuwa kamar zata kwanta masa idan ya faɗa mata magana ba zata tsallake ba yanda take gudun ɓacin ransa kuwa wani lokacin har ji yakeyi kamar abun yayi yawa ya zama kamar tsoronsa takeji amma yau ita ce ta kama sunan sa katsal abinda bata taɓa yi ba tana ɗaga masa murya kamar zata rufeshi da duka?

"Gaskiya akwai matsala" ya furta a fili kafin ya tayar da mota ya nufi gidan Hajja.

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 40*

Tunda yaga babur ɗin Kawu Sani a ƙofar gidan gabansa ya shiga faɗuwa domin ya san abinda akw ɓoyewa ya rigada ya bayyana. Sai dai kuma shima yana buƙatar hakan ko dan ya samu a wuce gurin Zulaiha ta tare amma kuma ya san da wahala su kwasheta da daɗi da Hajja. Tun daga tsakar gida yake jiyo maganganun Hajjan tamkar zata ari baki tsabar masifar da take zazzagawa, yana ɗaga labule suka haɗa ido kallon data jefa masa sai da yaji yan cikin sa sun juya, ta ce

"Yawwa gara da kazo, dama Bilal idan har ni na haifeka ba canza mun kai akayi a Asibiti ba, bana buƙatar jin kowacce magana daga bakinka a yanzu har sai bayan ka rubuta takardar saki yanzu an kaiwa waccen kaskar da kuka munafurceni aka ɗaura maka aure da ita." Sai kuma ta fashe da kuka tana cewa

"Allah ya isa tsakanina da kai Sani dan nasan wannan abun shirinka ne Bilal ba zai taɓa mun haka ba, dama shi ɗan uba duk in da yake ai ba zai taɓa sonka tsakani da Allah ba sai in yana da wata manufa, to ka sani haƙƙin marigayi ba zai barka ba wlh tallahi domin ya ƙaunace ka tsakani da Allah in ba an faɗa ba ma waye zai ce ba ciki ɗaya kuka fito dashi ba amma shine saboda zuciyarka cike take da mugun abu ka rasa kuma akan wa zaka juye shi sai akan ɗan da yafi so tir da kai Sani" ta sake rushewa da kuka harda fyace hanci.

Daƙyar ya ƙarasa cikin ya samu guri kusa da Kawu Sani da ya zabga tagumi yana kallon Hajja, murya a dace kamar wanda ya tashi daga ciwo ya ce

"Kiyi haƙuri Hajja amma babul laifin Kawu Sani a cikin maganar nan domin ni na saka shi ya nema mun aure ba wai gaban kansa yayi ba". Kamar an yi ruwan sama an ɗauke kuwa ta dakata da kukan da takeyi ta kafe shi da ido alamun sauraron ƙarin bayani, ƙasa yayi da kai kafin ya cigaba da cewa

"Hajja kin fi kowa sanin irin son da nake yiwa Zulaiha amma a haka na haƙura da ita saboda kin nuna bakya so a wancan lokacin, Hajja kin san yarinyar nan bakay buƙatar na sake gaya miki komai akanta aurenta tamkar jahadi ne zanyi saboda na taimaketa kuma idan kika duba tsahon lokacin da muka ɗauka tare tana jira na tun banyi aure ba har kuma nayi auren bata haƙura ba kuma yanzu nace na zan aureta ba ai zai zama kamar na yaudareta ne kuma dama ai Hajja munyi yarjejeniya dake na faɗa miki duk idan na samu dama a gaba zan aureta kuma baki ce ba haka ba".

Kukan da ya fi na farko Hajjan ta sake fashewa dashi shi kuma ya sake laƙwashe murya ya ce
"Hajja kin san bana miki musu duk abinda kika ce ko bana so ina yinsa, dan Allah zan roƙe ki ki mun wannan alfarmar ki barni da Zulaiha, ina sonta nayi miki alƙawari ko me kike so zanyi amma kiyi haƙuri dan Allah kada ki rabani da Zulaiha" ya ƙarasa yana zamowa gabanta ya dafa guiwarta hawayen da yake kokawa dasu suka gangaro akan kuncinsa.

Cikin kuka Hajjan ta shiga cewa
"Yanzu ita wannan yarinyar ya zakayi da ita?"
"Kada ki damu kanki da batun Jalilah Hajja"
"Ba maganar karna damu ba, wlh a kanta zan iya ɓata maka rai Bilal wlh" ta katseshi, sakw marairaicewa yayi ya ruƙo hannunta ya ce
"Haba Hajja yanzu har kin fi son wata bare a kaina kenan?"

"Kai da ka nuna mun iyakata Bilal da raina ban mutu ba ka zagaya ka ɗaura aure har kana da bakin cewa na fifita wani a kanka? Ai ko da bana so har idan dagaske kana martabani a matsayin uwarka ya kamata ka gaya mun, amma shikenan, dama gashinan ƙanin ubanka ya fara cewa ni mai son zuciya ce na saka ka auro waccen yarinyar ga yanda ake ciki yanzu ina so na sake turaka ka auro wata ba'a son ranka ba shiyasa ka zagaya kayi aure baka gaya mun ba, shikenan kaje ba zan hanaka ba amma ba'a son raina ba" ta miƙe tana kuka wiwiwi ta wuce ɗaki.

Gaba ɗaya ji yayi kansa ya kulle dan ko maganar da Kawu Sani ya shiga yi masa sauraronsa kawai yake amma baya gane komai cikin abinda yake faɗa, ƙarshe kawai ya miƙe ya fice daga falon. Auren da take so ta saka albarka a ciki ma ya ya ƙare balle wannan da tace bata so?

Kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya Hajja ta ɗauke masa wuta ko gidan yaje daga sallama bata sake ce masa komai duk kuma magiyar da zaiyi da bata haƙuri ba zata tanka masa ba abin sai ya zame masa goma da ashirin dan yanda ya tsammaci lamarin Halima zai zo masa da sauƙi sai kuma abun ya sha banban. Washe garin daya sake komawa da yamma haka nan ya ƙara ci kiranta a waya amma bata amsa ba daga ƙarshe ma ta kashe layin gaba ɗaya, ya tura mata text duka babu amsa haka ya haƙura ya tafi ga ta ɓangaren Zulaihan itama ba wani sauƙi, fushi ta ɗauka dashi tun akan zancen waccen daren shi ya ƙwafe yana jira ta kira ta bashi haƙuri irin yanda ya saba da Halima amma har aka kwana aka kusan wuni shiru bai ji ta ba.

Haka nan sonta dake azalzalar zuciyarsa ya tilasta masa kiranta kuma ko kafin su shirya sai da ta masa tatas ta amayar da duk abinda yake cikin ta kafin ta kammala da gargaɗi akan karya sake mata irin haka wai kuma abin takaici ba yanda ya iya ya bita da ban haƙuri shikenan suka shirya har a daren yaje gidansu kuma kamar yanda tace tunda ba'a masa gwaninta ta daina nuna masa kulawar hakan ce ta faru dan ƙin yarda ma tayi su zauna a mota sai a soro sukayi zancen.

HALIMA
Ba ƙaramin ƙarfin hali nayi gurin danne zuciyata naƙi amsa Bilal ba, so nakeyi na tabbatar da matsayina a gurin sa, ko da ya tafi zuwansa na farko na ringa ji kamar na kirawo shi na ce ya dawo amma da naga har dare ya tsala safiya tayi bai sake kirana ko tura mun sa saƙo ba sai ba raina kaina na kuma fara tausayin kaina akan igiyar zaton dana ƙulla na cewar Bilal ɗin dagaske yana ta tawa mutane kawai suke ganin ba haka ba. Na ji sanyi har raina daya sake dawowa sai dai kuma ban biyewa zuciyar da ta ringa azalzata akan na karɓi uzurin sa ba. Na tambayi kaina wane uzuri zan masa ne ma tunda shi dai bai furta ko nunawa a aikace cewa ya yarda yayi mun laifi ya kuma nemi da nayi haƙuri ba maimakon haka a kalaman da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login