Showing 117001 words to 120000 words out of 257873 words

Chapter 40 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

474

kanti na siyo abinda nake buƙata. Sai bayan na gama karyawa sannan na lura da dubu ɗayar dake ajiye kan dining da yar takarda a samanta na ɗauka na buɗe
"Ga kuɗin cefane nan" abinda ya rubuta a jiki kenan. Na ringa juya dubu ɗayar ina kallon ta a raina ina lissafa me zan siya da ita?

Cefanen yaushe ma yake nufi na rana kenan ko kuwa har da dare? Da yake na siyo Indomie da rana ita na dafa da ƙwai na ci duk da ba wani ji na yi na ƙoshi ba ni tunda na dawo gidan ma nake ji na kamar wacce ulcer ta kama komai na ci bana ƙoshi ga Al'amin da tsotso har na fara tunanin ko dai na haɗa masa da madara ko zan samu sauƙi.

A hanya bayan na dawo daga cefanen girkin dare wanda sai da na yi cikon dubu uku kafin na samu siyo abinda nake buƙata ina ƙoƙarin buɗe gida na jiyo Maman Yusuf na kiran sunana, sai da na zura ledar hannu na ciki na janyo ƙofar kafin na juya ina murmushi a raina ina addu'ar Allah ya sa bata ga kayan hannu na ba.
"Na aiko Khairat ta ce bakya nan sai Sunusi ya ce kin tafi cefane, maimakon ki bawa Sunusin ko kuma ki aiko nan ko Hauwa ce na turo miki ta yo miki cefanen shine zaki ringa fita da kanki Amarya? Haka jiya ma fa na ganki can bakin titi da tsakar rana har ina cewa mai kama da ke ce ashe dai ke ɗin ce dagaske ni na zata ma Oga ya koma Abujan ne shiyasa kike yawon cefane da kanki ashe yana gari" ta faɗa tana kallo na.

Na yi guntun murmushi na ce
"Aiken sauri ne kin san halin Sunusi kuma idan ka aike shi wani lokacin sai ka manta ma kafin ya dawo Hauwa kuma ai na ji randa kika shigo kin ce ta je gida an musu rasuwa ban san ta dawo ba ai".

Na ɗauka zata wuce amma ta tsaya da alama shiga take so tayi ba'a son raina ba na buɗe ƙofar muka shiga tare. Sai da na kai kayan kitchen kafin na dawo falo muka sake gaisawa ta ce
"Kiyi haƙuri kin sanni da shegen surutu da shiga abun da babu ruwana. Da safe Sunusi ya ce mun maigidan nan ya aike shi siyan ƙosai da Kunu, naga an kwana da wuta Amarya ga blander ki babu abinda bata niƙawa ɗan ƙosan da baifi kiyi na gwangwani biyu kuci har kuyi sadaka ba shine zaki bari a siyo muku a inda baku san tsaftar sa ba? Kunun ma ai gara ki siyo geron kiyi gasara tunda yana so, In da kin aiko ma ni ina da gasarar sai na baki ki dama".

"Ni ce nayi sha'awar kunu da ƙosan ma naga kuma kafin na yi zan ɓata lokaci" na faɗa ina murmushin yaƙe, tayi jumm kamar dai ba iya maganar da ta kawo ta ba kenan kafin kuma ta miƙe tana cewa
"Shikenan dai bari na je dama baya zan zagaya gidan Maman Anisa kin san yaronta da ya tafi makarantar Sojoji Aliyu shine ya faɗo daga sama suna training an dawo da shi gida jinya zan shiga duba shi".

"Ayya Allah ya bashi lafiya ya kiyaye gaba ayi masa sannu" na faɗa ina taka mata, a bakin ƙofa ta tsaya ta ce
"Da babu abinda zakiyi ma se mu je tare tunda ba zama zanyi ba nima"
"Eh wlh girki zan yi da munje taren na faɗa ina kallon Bilal dake tahowa daga ɗakin sa mamakin sanda ya dawo gidan ya kamani, ganin sa ya saka ta wuce ita ma ni kuma na koma ciki.

Tare muka shiga cikin falon ya dakatar da ni cikin ɗaga murya yace
"Daga yau na soke shigowar duk wata matar unguwar nan cikin gidan nan kema kuma na hana miki hulɗa da su tunda a gurin su kike koyon duk wani rashin mutunchin da kikeyi".

Nayi kasaƙe ina kallon sa kawai, wai nake koyon rashin mutunchi, ya cigaba da cewa
"Ita ga munafuka ta fito kai tsaye ta ce kina fita cefane za'a ce Mijinki baya kulawa dake shine take ta wani zagaye zagaye. Shi Mijin nasu da ya gina musu ƙaton gida ya basu motoci suke wani jin kansu waye bai san ɗan damfara bane ba? In sake ganin ta a gidan nan wlh sai na mata rashin mutunchi aikin banza kawai" fuuu ya fice.

Nayi murmushin takaici a fili na ce
"Ashe kasan mutane zasu ringa kallonka a matsayin wanda bai iya riƙe gidan nasa ba amma saboda rashin son gaskiya zaka ɓige da faɗan rashin dalili. Da ya dawo can falon sa ya ce na kai masa abinci na haɗa komai na kai masa bayan ya gama ya kira ni a waya ya ce na zo na kwashe kwanukan bayan na kwashe ya ce idan na kai su kitchen na je yana son magana da ni.

Kayan abinci ya nuna mun da ban san sanda ya shigo da su gidan ba, ya ce
"Gashi nan na siyo kafin ki cigaba da yi mun Gorin tunda na aureki abincin da kika zo da shi daga gidan ku kike ci". Ni dai na yi murmushi kawai yace na je na shirya na dawo yana jira na, na san me yake nufi.

Washe gari da safe sauran abincin dare na ɗumama muka karya da shi, mun tashi da walwala ba laifi saboda yanda daren jiyan ya kasance mana. Har ya gama shirin fita banga ya fito da kayan abincin ya kai su store ba dan haka na tuna masa, ina tsaye ya shiga kitchen ya fito da kwanuka na ringa kallon sa ina mamakin mai zaiyi ya wuce ya koma can ɗakin ba daɗewa ya ƙwala mun kira na je, ya nuna mun shinkafar daya auna cikin roba da ba zata wuce gwangwani uku ba sai mai da maggi, ya zaro ɗari biyar daga aljihun sa ya miƙa mun. Na ringa kallon kayan da kuɗin gaba ɗaya na rasa kalmar da zan yi amfani da ita gurin magana, shi kam ko a jikin sa ya ce

"Ki ɗauka zan rufe ƙofa sauri nake yi kada na makara". Haka na fito da kwanon shinkafa da mai da Maggi na guda biyar akai kamar wacce ta je roƙo maƙwafta. Na daɗe a zaune baƙin ƙofar falo na mamakin abun bai sake ni ba. Kenan awo Bilal zai ringa mun ko me? Ni bani da yancin da zan ɗibi abinci na dafa a cikin gida na sai iya abinda yaga dama ya ɗebo ya bani shi zanyi amfani da shi kenan?
Mai yake damun Bilal? Wai dama haka yake ko kuwa dai wani abun ne ya canza shi da ban sani ba?

Yini guda na kasa kataɓus duk in na kalli shinkafar sai na ji duniyar ta mun duhu wani abu ya tsaya mun a ƙahon zuci na ma kasa dafata balle na ci. Gashi na rasa wanda zan kira na samu sauƙin abinda nake ji a raina, wai wa zan ma zan iya gayawa wannan abun takaicin? Haka nan daga ƙarshe na ganin la'asar ta kawo kai na dafa masa da sauran cefanen da nake da shi amma ban iya ci ba cikin provision ɗin da na ɗan yi nayi ta dama Golden morn da cornflakes yini guda ina sha. Da yamma daya dawo ya taho da nama, kifi harda kayan miya. Haka ya zauna ya raba su ya ƙulla a ledoji ya zuba a frizeer tare da gaya mun tsahon lokacin da yake da yaƙinin zasu kai kafin su ƙare.

Tun daga sannan muka ɗoru akan sabon tsari, yawanci da safe zai siyo Lipton da sugar da buredi, wata rana in ya ga dama ya siyo madara da Milo ko ya siyo ƙwai. Su dankali, doya duk zai siyo ya ajiye sai dai irin ikon da yake gwadamun akan abinci ya saka lokuta da yawa nake haƙura da ko menene ya kawo sai dai na bar masa kayan sa ya ci.

Da rana kuma shi zai ɗiba mun iya abunda zan dafa cikina da nashi. Sau ɗaya na masa magana akan idan kuma muka yi baƙi fa? Yaya zanyi tunda kulle ɗakin yake yi? Bai bani amsa ba nima kuma ban sake tayar da zancen ba, sauƙin ta ban fiya yin baƙi daga ɓangare na ba, shima yan uwansan da suke zuwa a da yanzu duk sun ɗauke ƙafa Abubakar ne kaɗai zan ce har yanzu alaƙar mu take nan bai canza layi ba sai kuma Anty Amina ita kuma tsakanin mu gaisuwa a waya ne ko kuma idan mun haɗu a gidan Hajja.

A haka rayuwa ta buɗe sabon shafi, na yaye Al'amin na ɗauki cikin Sharifa. Tun ina ganin bazan iya jurewa ba har na haƙura na saba abin ma ya dena damuna musamman da hakan ya kasance silar dawowar nutsuwa da kuma walwala cikin zamantakewa ta da Bilal. Mun dena faɗa, soyayya da tattalin da nake kwaɗayin ina samun su da na zauna nayi tunani sai naga dama ita rayuwa bata taɓa zamowa mutum ɗari bisa ɗari yanda yake burin ta kasance masa.

Wasu matan sukan samu biyan buƙata na ababen more rayuwa amma kuma su rasa kula da farin ciki a gurin mazajen su. Wasu kuma su rasa wadata amma su samu farin cikin. Ni da na faɗa a tsaka tsaki domin dai ko da bana samun abinda na saba da shi ko nake so bai bar ni da yunwa ba. Sannan ina samun soyayya da tattalin da na tabbatar ba kowacce mace ke samun irin haka a gidan auren ta ba, amma duk da haka na sani Son da nake masa ne ya lulluɓe komai a ido na. Allah ya sani ina son Bilal son da ban san iyakar sa ba ba kuma na fatan ruyuwa babu shi dan nasan bazan iya ba.

Cikin kuɗin da nake dasu a hannu na da na account nake cira nayi duk abinda nake da buƙata wanda bai bani ba. Sau tari zuciya ta takan raya mun na siya abinda nake so na dafa na ci ni kaɗai idan baya nan amma sam na kasa yarda da hakan, ko gida na je na samo abu bazan iya ɓoye masa ba. Tunda kuma ya fahimci akwai kuɗi a hannu na ɗari biyar ɗin da ya fara bani a matsayin kuɗin cefane ma ya daina kwata kwata. A cewar sa babu abinda baya siyowa bai kuma taɓa tunanin abinda yake siyowar ko yake ɗibar mun baya isa ba. Zan dafa abinci da naman kaza ya ci har ya fini iko akai ba tare da ya tambaye ni a ina na samu kuɗin da na siyi kazar ba.

Bai taɓa gani na da wata sutura ko abin kwalliya wanda ba shi ya siya mun ba kuma ya tambaye ni a ina na samu, idan akwai abinda nake jin damuwa akai har ya jefa ni a tunani bai wuci yanda bai damu da komai ba har idan ba hurumin sa na shiga ba. Amma kuma daga ranar da ya faɗa mun wata magana, daga lokacin na fahimci kuskuren da mutane suke ta faɗin na yi akan auren Bilal, a ranar kuma na fara shakkun sahihancin ƙaunar da nake tunanin yana yi mun ya saka mun kokwanto akan aihinin manufar sa akan aure na.

Kuyi haƙuri, In sha Allahu daga yau har Friday zanyi post. Daga nan zamu tafi hutun azumi idan Allah ya saka mun kasance cikin waɗanda zasu gani.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 30*

Watan Al'amin goma sha takwas na yaye shi a kuma watan na samu wani cikin wanda ko kusa Bilal bai yi maraba da samuwar sa ba.
"Wai dama bakiyi komai na tsarin Iyali ba? Ni na zata hankalin ki zai baki da kiyi ba sai an tuna miki ba, kina kallon yanda abubuwa duke tafiya kuma kawai zaki kama ki wani sake yin ciki. To ni dai gaskiya ban so haka ba" Abun da ya faɗa kenan lokacin da na shaida masa ina da cikin.

Gaba ɗaya sai na rasa yanda zan fassara maganganun sa. Fassara ta kai tsaye dai na san yana nufin baya son cikin kenan sai dai nayi ƙoƙarin kyautata masa zato da bashi damar gyara maganar sa ta hanyar cewa

"Yanzu mai kake nufi kenan?"
"Duk yanda kika ɗauka haka nake nufi ni dai na faɗa miki ban so kika sake samun wani ciki yanzu ba. Kina sane tun ba yanzu ba na gaya miki a tsari na gaba ɗaya bana so yayana su haura guda uku, yanzu ƙasa da shekara huɗu kina shirin yin yaya biyu" ya yi tsaki haɗi da tashi ya bar mun ɗakin.

Ko a mafarki ban taɓa zaton Bilal zai ƙyamaci abinda ya fito daga guri na ba. Na jinjinawa ƙarfin halin sa da har ya iya runtse ido ya ke faɗar abinda ni da shi mun san ƙarya ne Bilal da yake cewa idan munyi aure duk shekara zan ringa haihu muyi dariya na ce Akuya yake so na zama kenan amma wai yau shine zai dubi tsabar ido na ya ce mun baya son cikin da yake jiki na.

A haka na rainin cikin Sharifa cikin ƙunci da baƙin ciki domin kwata kwata Bilal canzamun yayi. Sai mu yini mu kwana bai ce mun komai. Da farko ya sakko lokacin da Mama ta ɗauki Al'amin ganin ina shan wahalar laulayi, watan sa biyu a can gidan kafin aka dawo da shi. Dawowar ta sa ma da farko farko bai wani nuna ɓacin rai ba sai bayan da siyayyar kayan ciye ciyen da aka haɗo shi da su ta ƙare ranar da na fara masa magana zai fita nace ya taho masa da ƙwai da Ceralac dan har sannan ita kaɗai yake yiwa shan ƙoshi sai kuma ƙwai haka ya rufe ido ya ringa zazzagamun masifa har yana faɗin idan da an san ba za'a iya riƙe yaron ba akan me za'a ɗauke shi aje a lalata shi da ciye ciyen banza?

Ba zai siyo ba, ai dama tun farko ni na koya masa shan cereal ɗin har kunu Hajja ta haɗo ta kawo amma naƙi bashi dan haka sai na cigaba shi baze iya ba. Ranar sai da na ji kamar na haɗa kaya na na bar masa gidan amma bazan iya ba. Ina son sa ina kuma son zama da shi. Nayi uzurin cewa cikin da na samu ba tare da shawarar sa bane ya ɓata masa rai na kuma ɗauki alƙawarin da zarar na haihu bazan fito daga labor room ba sai na yi family planning har idan hakan zai faranta masa rai.

A haka na haihu, na samu ya mace wadda ya bani zaɓin akan duk sunan da nake so in saka mata na kuma zaɓa mata SHARIFA. Sai ana gobe suna kafin ya bani dubu saba'in wai ko akwai abinda zan buƙata. Nayi murmushi kawai na karɓa. Ba abinda nake nema wanda bani da shi. A lokacin na godewa gatan da Anty Labiba ta mun na kwashe duk wani abu da muke da shi double lokacin haihuwar Al'amin ta ɓoye mun. Riguna kawai na kwalliyar mata na siya dan duk wani unisex muna da su. Ban yi taro ba, duk da yan uwan sa sun zo amma da suka ga babu kowa a gidan basu zauna ba suka tafi.

Haka na shiga rainon yara biyu sai kuma a lokacin kuma na fuskanci zaton da nake yi na zan iya ɗaukar nauyin kaina da abinda zan haifa ba tareda na damu da abinda Bilal zai yi mun ba ba mai yuwuwa bane.

Abban da yake bani kuɗin tun da na haifi Sharifa ya janye mun tallafi. Sai na yi zuwa biyar gida ba tare da ya bani ko sisi ba. Idan ma zai banin ya dena bani da yawa kamar da ƙarƙarin kyautar bata haura dubu goma ko ashirin saɓanin da da duk watan duniya sai ya tura mun dubu hamsin wanda ko Mama bata san da hakan ba kuma shi ya hana na faɗa mata. Sannan duk sanda naje gidan idan zan tafi zai bani na mota.

A sannu na fara gane ainihin abinda ake kira da yau da gobe bata bar komai ba, ga hidimar yara, ga damuwar Bilal da gaba ɗaya zaman mu ya canza salo. Duk ta inda nake zaton matsala nayi ƙoƙarin gyarawa amma tamkar ina sake rura wutar ne. Idan nayi abinci haka zai balbaleni da masifa ya ce na koyi mugunta wai yanzu sai na ringa abinci kamar wanda za'a bawa bayi ba taste babu komai. Akwai ranar da nayi tuwo da miyar kuka kamar yanda ya faɗa mun na yi kafin ya fita da ya dawo na kawo masa haka ya saka ƙafa ya ture kwanon miyar ya ringa sababi har da yi mun Allah ya isa akan ɓarnar abincin da nake masa kamar yanda ya ce. Abincin da ni da yaran sa muke ci amma shi ya ce ba daɗi baze iya ci ba, na rasa gane kan Bilal na kasa fahimtar inda ya saka gaba.

Duk yanda nake tunanin na samo bakin zaren shirin baya wuce na kwana biyu zuwa uku zai sake birkicewa. A sannu na fahimci hanya ɗaya ce take samar mun farin ciki tattare da Bilal shine samuwar kuɗi a hannu na. Idan ina da kuɗin da zan girka masa abinci mai daɗi a ci zamu ɗauki tsayin lokaci ba tare da kowa ya ji kanmu ba, daga sanda cefane ya canza na fara girka zallar abinda ya ajiye mana sai tashin hankali ya ce ina lalata masa abinci. Ma fahimci abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login