Showing 144001 words to 147000 words out of 257873 words

Chapter 49 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

495

har sai an ɗaura musu aure amma kuma duk ɗaya domin shigarta ne kawai bayayi bayaga wannan babu kalar abinda baya mata, haka suka dilmiya cikin ƙazamar rayuwar da suka zaɓawa kansu, ta sakar masa bakin aljihu tana jiƙa shi da kuɗaɗe wanda koda wani lokacin yaji rashin dacewar abinda sukeyi ya fara janye mata tunda ta fahimci shi ɗin masoyin kuɗi ne alert ɗaya zata masa ta girgizashi ba ma sai tace ya taho ba zai kama hanyar Abuja yaje gurinta ko kuma ita tazo Kano dan har gida ta siya da sunan sa akan idan sunyi aure zata zauna a ciki dan haka idan tazo can take sauka baki alaikum ba sai sunje hotel ba.

Haka suka cigaba da tafiya a sirrance dan daga shi har itan babu wanda yake so Hafiz yasan abinda yake tsakaninsu musamman Bilal dan hatta yan uwansa da duk sanda tazo Kano sai tayi nacin ya kaita su gaisa amma saidai yayi ta bata uzurin yau gobe a haka har ta gama kwanakinta ta wuce. Shammatar sa tayi ta kai kanta gurin Hajja ta kuwa yi mata shatara ta arziƙi ta gabatar mata da kanta a matsayin budurwarsa shikenan Hajjan ta gigice ta ringa faɗin ga arziƙin gaske ya tarar dasu har gida amma da yaje ya kwaso musu yar masu kuɗin cizo dan abinda Jalilan ta kai mata a zuwa ɗaya ya fi duk hidimar da Halima ta mata tun daga neman aurenta har zuwa yanzu.

Shikenan ta samu nayi kullum zancen ta yaushe zai tura ayi maganar aurensu ai yanzu ne zai yi mata yarinyar jinin larabawa wanke hannu ka taɓa ga tarin arziƙi kuma hannunta a buɗe dan ba'a rufa wata ba tareda tayowa Hajjan aike ba ta hannun sa wani sa'in kuma ta tasha zata turo musamman idan kayan amfani ne haka kwana bibbiyu zata kirata a waya su gaisa kati kuwa da data duk zalamar Fadila sai dai ta gaji ta ajewa Hajja wayar ta dan basa taɓa yankewa ita Jalilan ce ma ta saka aka buɗewa Hajja Whatsapp a sabuwar wayar data siya mata wai ai batayi tsufan da za'a ce ba zata riƙe babbar waya ba.

Haka nan suke, yana jin daɗin mu'amalar sa da Jalila domin kuwa ta sake masa kuɗi yanda ya kamata ba sai ya tambayeta ba yana zaune kawai zaiga alert kuma bata taɓa tura masa kuɗi kaɗan haka kyaututtuka kusan tun da suka fara mu'amala zai ce bai sakw siyan sutura ko wani takalmi ko agogo ko turare ba ita take siya masa kuma masu asalin tsada da kyau, bayan gidan da ta siya da sunan sa a yanzu haka ya mallaki filaye biyu Manya da gona itama babba y siya babu daɗewa saboda yana so ya fara noma.

Hatta wannan motar ita ta bashi kuɗi miliyan shida cis tace ya siyi mota, da farko cewa tayi ya zaɓi wacce yake so zata siya masa sai kuma yayi tunanin rana tsaka a ganshi da mota zai zama abin surutu wannan ya saka yace kawai ta bashi kuɗin ta kuma bashi sai ya raba biyu da niyyar ya siyi kamar ta 3m haka amma da yayiwa Hafiz magana shine ya cika masa yace ya ɗauki wannan ɗin a gurin siyar da motocinsu. A hakan ma ya sha surutu koma yace yana kan sha dan yanda yake dai da aikinsa kowa ya san an ɗan lokacin nan bai kai ya tara kuɗin siyan mota haka ba amma duk wanda ya cewa ubangidan sa ne ya bashi shikenan tunda da yawan abokanan sa sun san Hafiz ɗin sun kuma san yana da sararin da zai bashi fiye da ita ma shiyasa yayi dabarar jona shi cikin zancen motar tun farko.

Matsalar daya fara fuskanta da Jalilan yanzu, a farkon tarayyarsu bata damu da Halima ba, ta gaya masa ita ko mata uku yake dasu bata da matsala zata shiga a ta huɗu amma kuma da tafiya ta fara nisa sai zance ya canza ta fara nuna masa ita fa ba zata iya haɗa shi da wata ba dan haka idan lokacin auren su yazo sai dai fa ya zaɓa ko ita ko Halima wanda wannan abunda ta ɓullo dashi yana daga dalilin daya saka neman nasu yin tsaho domin yace ba zai iya sakin Halima hakanan ba dan babu wani laifi da zai iya danganta cewa tayi masa da zai saketa akan hakan amma ta bashi lokaci zai ɓullo da hanyoyin da ita da kanta zata gaji ta nemi rabuwa dashi.

Sai dai fa a zuciyar sa kwata kwata ba son Jalila yakeyi ba kwaɗayin abun hannunta yakeyi. Dama a wannan tsukin yake tunanin samo hanyar rabuwa da ita cikin sauƙi domin har ransa bashi da burin aurenta, a lamarin aure yana buƙatar macen mai tarbiyya wacce zai faɗawa magana taji irin Halima ba wacce zata zama ita ce mijin shi kuma matar ba balle kuma ita da ya rigada ya san halinta kuma sun gama tambaɗewa ai babu zancen mutunchi ko zaman lafiya ma a tsakanin su idan su kayi aure.

Yana da burin ƙara aure nan kusa kuma ZULAIHA yake so ita ce zaɓin sa tun asali kuma ita zai aura kuma ko a yanzun rabin abinda yake samu daga gurin Jalila ita yakeyi wahaltawa yake kuma yi mata tanadin bayan auren su gashi yanzu garajen Halima na nema ya rusa masa lissafin daya shiryo.

Wayarsa dake ajiye gefe ta ɗauki ƙara abinda ya maido shi daga duniyar tunanin daya lula. Sunan DUNIYATA dake yawo akan screen ya saka shi sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗauki wayar ya amsa haɗi da sakata a speaker. Daga can tayi sallama cikin muryarta me sanyi da sautin shagwaɓa, amsa sai taci gaba da cewa
"Habibi lafiya kake kuwa yau kwana uku ina kiran wayarka sai dai tayi ta ƙara amma baka amsawa kuma baka biyo baya ba?" Ta ƙarasa kamar zatayi kuka. Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kafin ya ce

"Banida lafiya ne".
"Subhanallah, mai ya sameka?" Ta tambaya a ɗan rikice, sai ya sake yin ƙasa da murya kamar mara lafiyar gaske yace

"Zazzaɓi nakeyi da mura"
"Wayyo Allah ya baka lafiya Habibi ni dama na san sai dai ba lafiya ba shine kaɗai abinda zai saka ka kasa amsa kirana, to yanzu ya jikin naka? Amma dai da sauƙi ko kasha magani?" Ya amsa mata da
"Eh da sauƙi kuma nasha kada ki tayarda hankalinki dama yanzu nake so idan nayi wanka na kiraki nasan zaki damu kwana biyu baki jini ba".

"Wallahi ko na damu sosai tun waccen ranar da Umma tace mun kaje tareda Maman Al'amin na kira kace kana driving zaka kirani shikenan fa da na sake kira da daddare ka amsa bakayi magana ba har naji tsoro ko zuwan da kukayi da ita ya haifar da wata matsala ne yasa kake avoiding ɗina" tayi maganar kamar zatayi kuka, sai ya saki murmushi yace
"Wace matsala zuwan Halima zai haifar? Kin san dai yanda nake sonki ko duniya zata taru babu wanda ya isa ya shiga tsakanina dake ko?"

Murmushi mai sauti tayi daga can itama tace
"Haka ne, toh yanzu yaushe zaka zo?" Ya ɗan yi jimm kafin yace
"Ina da uzuri yau da yamma zan tafi Abuja idan na samu jirgi amma kwana biyu zanyi zuwa asabar da yamma ko lahadi da safe za dawo sai nazo". Shiru tayi bata ce komai ba, cikin kulawa yace

"Akwai wani abu ne?"
"Toh ai kana da uzuri kaga kuma ba zaka bari saboda ni ba" ta faɗa cikin rawar murya, sai yayi saurin miƙewa zaune daga kishingiɗen da yayi dan alamun kukan da yaji a muryarta lokaci ɗaya ya tayar masa da hankali yace

"Ki faɗa mun menene naji kamar zakiyi kuka ko kuɗi kike buƙata? Kayan abincin da aka kawo sun ƙare ne?"

Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kuka daga nan kuma ta kashe wayar gaba ɗaya. Ji yayi duniyar gaba ɗaya ta masa duhu hankalinsa ya tashi ba shiri ya tada mota ya cillata titi ya nufu gidan su Zulaihan dan jin ba'asin kukan da takeyi. Daya isa bai ko jira an masa iso ba bayan da yayi sallama ya faɗa gidan, suna zaune a ɗan ƙaramin falon su ita da ƙanwarta Jidda sai Ummansu jigum jigum ya samu guri shima ya zauna.

"Magana daka sani ce dai Bilalu ba wata ba, babu jimawa Yayan mahaifinsu ya fita daga gidan nan sai kaga irin cin mutunchi da tozarcin da yayi mata ya kuma yi rantsuwa akan ranar sadakar Arba'in ɗin Malam kowaccen su ta kawo miji a ɗaura mata aure idan kuma ba haka shi zai zaɓa musu wanda yaga dama ya ɗaura auren a ranar" Ummansu ta faɗa bayan da suka gaisa tayi maganar tana share hawaye da Hijabin jikinta.

Yayi shiru a ransa yana ayyana "wata sabuwa kenan". Duk sai ya rasa mai zai ce musu, ranar Arba'in ɗin Babansu nan da kwana Ashirin fa kenan ake nufi yanzu ta ina zai fara gyaro ɓarakarsu da Halima, Ya yakice Jalila, sannan a auri Zulaihan duka a kwana Ashirin?

Shirun da yayi ya saka Umman cewa
"Ai na san abu ne da kamar wuya amma shi kawun nasu ka sani mutum ne mai wuyar sha'ani babu yanda banyi akan na fahimtar dashi ba amma daga ƙarshe sai cin mutunchi ne ya biyo baya kuma na sanshi da magana ɗaya tunda yayi rantsuwa babu abinda zai saka ya karya ina ganin tunda abun ya kasance da haka sai dai ayi haƙuri kawai a karɓi ƙaddara a yanda tazo, kai ka haƙura ita kuma ta karɓi duk wanda Allah yasa ya zaɓa mata tunda ita Jiddah yaron da yake aurenta dama a shirye yake tana kiran sa ta gaya masa yace babu komai gobe iyayen sa zasuje ayi magana to ai kaga ba kamar kai ba da kake da uzuri kuyi haƙuri kawai".

Tashi Zulaihan tayi cikin kuka ta fice daga falon, Bilal ya bita da kallo yana haɗiye yawu daƙyar kafin ya mayar da kallonsa kan Umman tasu. Ya ma za'ayi ace ya haƙura da Zulaiha? Yarinyar da ya raini soyayyar ta a zuciyarsa tun bata kai munzalin data mallaki wani abu da zai kalla ya burgeshi har ya so ta saboda shi ba?

A sanyaye yace
"Aa in sha Allahu Zulaiha rabona ce Umma, kawai dai nayi zaton zaiyi haƙuri tunda wata huɗu ya rage ta kammala karatunta sannan sai a taso da maganar aure amma tunda hakan ta kasance babu abinda zai gagara in Allah ya yarda zanje nima na samu nawa iyayen". Albarka ta ringa saka masa har ya tashi ya fita, a soro ya tarar da Zulaihan tana kuka nan ya tsaya ya ringa rarrashinta da faɗa mata kalamai masu daɗi bai bar gidan ba har saida fushinta ya yaye tayi dariya sannan suka fita tare ya siyo mata Ice cream da Shawarma ya mayar da ita gida nan ma ya daɗe suna hira kafin ya mata sallama ya wuce yana jin kaso tamanin na damuwar daya wayi gari da ita ya yaye.

Shekararsu kusan goma sha biyu tareda Zulaiha tun tana JSS1 lokacin da yayi TP a makarantar su a lokacin Allah ya haɗa jininsa da yarinyar saboda ƙoƙarinta har kuma bayan daya gama gama saboda ita yaci gaba da zuwa duk sanda ya samu lokaci kafin daga baya zumunchin su yayi nisa ya zama har gidansu yake zuwa a hankali ya zama kamar wani babban yayansu kasancewar su uku iyayensu suka haifa duka mata yayarta ɗaya sai ƙanwarta ɗaya. A sannu sannu shaƙuwar su ta fara rikiɗa zuwa soyayya duk kuwa da cewa Zulaihan bata da wata suffa ko dalili da zai saka ya sota kasancewar kowa ya sani shi mutum ne wanda tsarinsa na auren mace yar gayu ne kuma wayayyiya wadda ta fito daga babban gida ita kuma Zulaiha cikin suffofi ukun babu wadda ta mallaka.

Babanta Talaka ne liƙis wanda bai aje cin yau ba balle na gobe haka nan bata da wani kyau na azo a gani domin bata ko kai Halima ba balle ta kama ƙafar Jalila, tana dai da dirin jiki shima ba can ba, sanyinta da baiwar murya mai cike da shagwaɓa da Allah ya bata shine kaɗai abinda za'a iya cewa zai ja hankalin namiji gareta sai dai shi duk ba dan haka yake sonta ba gamon jininsu daga Allah ne.

Shi yayi ɗawainiyar karatunta tun daga junior secondary ya mayar da ita private daga ta gwamnati data fara har zuwa yanzu kuma da take ajin ƙarshe a Jami'a shi yake cigaba da ɗaukar nauyinta harda ƙanwarta Jidda, wata uku kenan daya siya musu wannan gidan da suke ciki watansu biyu da tareqa kuma a ciki mahaifinsu ya rasu.

Rashin samun haɗin kan Hajja ne ya hana shi ya auri Zulaihan tun bayan data kammala secondary domin Hajjan tace babu yanda za'ayi ya auro mata yar Allah baku mu samu, da wanne zaiji? Nauyinta dana yan uwansa ko kuwa na matarsa da danginta tunda kaf ahalinsu a binciken da aka mata an gaya mata babu mai samun cikakken ci uku a rana, ko hidimar da yakeyiwa su Zulaihan a lokacin a ɓoye yakeyi domin ya san muddin ta sani toh fa ba zata bari ba shiyasa ko da ta hana shi aurenta a lokacin bai matsa ba domin shi da kansa yana so ya aureta a sanda yake da damar bata kalar rayuwar da yake mafarkin sama mata saboda yanda yake tausayinta a ransa.

Yana son Halima har ransa saboda ita ɗin tsarinsa ce sannan kuma tana masa son da ya yarda da wahala ya samu qata mace da zata kwatanta masa irin sa sai dai kuma soyayyarta a zuciyar sa bata ko kama ƙafar yanda yake jin Zulaiha a ransa ba. Kusan kwatankwacin irin son da take masa ne shi kuma yakeyiwa Zulaiha har ga Allah kuma da ace ya samu irin damar da yake fata kafin ya aureta da Zulaihan zai aura ba ita ba. Sai dai a yanzu da al'amura suka kasance ba yanda ya so faruwarsu ba Allah ya ƙaddara ita Haliman ce matar sa ta farko ga kuma rabon da yake a tsakaninsu ya san ba zai samu matsala da ita ba idan ya auri Zulaihan daga baya. Toh amma yanzu komai ya lalace ya tashi daga yanda yayi hasashen faruwar sa kansa kuma ya kulle ya rasa ta ina zai fara gyarowa.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 37*

HALIMA

Sati na biyu a Asibiti kafin aka sallameni zuwa lokacin kuma Alhamdulillah na samu sauƙi sosai ko in ce nayi matuƙar ƙoƙarin gurin yakice damuwar dake raina ko dan in samu na bar gadon Asibitin domin a zahiri basu da maganin matsalata kamar yanda kullum Dr yake nanata mun ni zan yiwa kaina maganin matsalata in cire koma menene na saka a raina yake neman halakani. Zama yayi ya mun karatun Yaya da ƙanwa kamar yanda ya ce,

"Ki dubi yanda hankalin iyayenki da yan uwanki duk ya tashi saboda ke, ki kalli yayanki da har yanzu basu san ina suka dosa a rayuwarsu ba idan kika bari damuwar wani can ta kasheki su kika yiwa asara domin tun kina raye dai kinga alamar cewa dake da babu a gurinda duk ɗaya tunda tun bayan da aka kawoki banga wani da aka nuna mun a matsayin shine mijin ki kuma nasan kina da aure dan haka kiwa kanki karatu Halima ki san mai ya kamace ki idan ma zaki mutu ki mutu akan abinda kike da daraja a gareshi".

Daga lokacin na fara ƙarfafar kaina domin dagaske na yarda idan na mutu iyayena da yayana suke kan gaba gurin asara yanda kuma suke zagaye dani kullum cikin nuna kulawarsu idan na cigaba da ɗaura musu damuwata na sani Allah zai iya kamani da haƙƙinsu. An sallameni da tarin gargaɗi akan abubuwan da zan kiyaye, muka koma gida na sake buɗe sabon babin zaman ɗaki domin bana son kowacce hayaniya yan dubiya da suke zirga zirga a gidan kuma takuramun sukeyi shiyasa na zaɓi da inyi zamana a ɗaki ko na samu damar yin tunanin da likita yace in daina amma ba zan iya ba ya zama tamkar mahaɗin rayuwata ne tunda ba zan iya buɗe baki in faɗawa kowa damuwata ba sai dai nayi ta tattaunata tsakanin ƙwaƙwalwata da Zuciyata.

Ranar da nayi kwana uku da fitowa daga Asibiti har lokacin tsakanina da Mama tsantsar kulawa ce tamkar zata mayar dani ciki ta sake haifoni haka take ji dani, duk sanda na kalleta tana mun hidima na tuna furucin Bilal sai naji wani abu tamkar dutse ya danne mun ƙirji. Kamar kullum bayan ta taimakamun nayi wanka na shirya ta fita ta dawo da try data ɗora mun breakfast, haka ta zauna tana tausata har saida naci da yawa kafin ta ɗauke ta sake dawowa da ruwa ta fito da magunguna na ta bani na sha sannan ta ɗakko mun wayata da jona mun a caji ta ajiye a kusada ni tana cewa

"Ga wayarki nan tayi caji sai ki kunna dan ƙila ana ta nemanki ba'a samu". Kaina yana ƙasa bance komai ba naja wayar na turata ƙasan filo, damuwa zan ƙarawa kaina idan na kunnata dan haka gara tayi ta zama a kashe kawai.
Ganin ta gyara zama tana kallona yasa naji zuciyata ta shiga bugawa da sauri dan na san da wahala idan ba zancen Bilal zata mun ba. A tsayin sati biyun da nayi a kwance ko bisa kuskure banji wani ya ambaci sunansa ba, na san kuma bai zo ba babu kuma wani nasa da yazo na san kuma dama babu yanda za'ayi su cigaba da yi mun shiru dole akwai lokacin da zasu tambayeni dalilin zuwana gida da kuma dalilin ciwo na amma bana zaton ina da amsar da zan bayar a nan kusa ko a gaba.

"Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login