Showing 114001 words to 117000 words out of 257873 words

Chapter 39 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

509

komai ba ƙarshe ya ɓige da nuna mun hotunan da ya yi a gurare cikin sabuwar wayar sa Iphone da ya siya. Sai da aka kira la'asar kafin ya ce mun zai tafi, ya ja ni jikin sa yana murmushin da ke wanke dukkan laifukan sa a gare ni ya ce

"Tun da na zo kike fushi kuma ko dai baki so dawowa ta bane?"
Gefe na ɗauke kai ba tare da na ce masa komai ba, ya juyo da fuskata ya haɗe bakin mu guri ɗaya.
Yanda kasan na rufe kaina da duka saboda takaicin yanda na kasa riƙe kaina a gaban Bilal. Da ya kira ni ma kasa amsa wayar na yi to na ce masa me bayan abin kunyar da na kusa tafkawa na je ina ta wani rawar jiki shi da yake namiji ma bai nuna min zumuɗin sa ba sai ni.

Kwanaki ukun da suka biyo baya kullum zai zo da daddare bayan magriba muyi hira har zuwa ƙarfe tara ko goma kafin ya tafi. Satin sa ɗaya da dawowa ya sake ce mun zai koma Abujan dama wai basu gama aikin ba kawai kewata ta saka ya zo. Dama Anty Labiba ta fara ƙananan maganganu akan ɗan abincin da yake ci idan ya zo abinda dama ko ya zo ko bai zo ba dole za'a dafa ba wai wani abu na daban na ke bashi ba da ta ke mita akai.
A haka muka cigaba da gungurawa har muka yi arba'in, a ranar kuma na tattara na koma gidana dan tun ana saura kwana uku aka je aka gyara mun Bilal ma ya dawo daga Abujar da na kasa gane abinda ya samu a can da ya tattare kusan sati uku tun da ya zo ya tafi bai sake dawowa sai yanzun.

Satin farko na dawowar mu zan saka shi a jere ranakun jin daɗi da kuma farin ciki a rayuwar aure na. Irin tarairaya da soyayyar da Bilal ya gwada mun ba ta nan kusa ba ce na kuma yarda da gasken da ya ce yayi kewata haka ne, ban san dalilin sa na ɓoye hakan a wancan zuwan da yayi ba amma dai duk wani haushin sa da nake ƙunshe da shi daga wancen lokacin sai da ya saka klin da hypo ya wanke fushin tas.

Kamar yanda aka ce yau da gobe bata bar komai ba tabbas haka ne domin kuwa yau na wayi gari babu ko ƙwayar hatsin da zan sarrafa mu ci a safiyar Talata. Tun dawowar mu nake tsammanin Bilal tun da ya san cewar komai na mu yayi ƙasa zaiyi ƙoƙarin ya siyo, kusan miya da soyayyen naman da na taho da su daga gida ne ma suka ɗan ja mu sati ɗayan ba tare da na buƙaci cefane na dole dole ba. Ruwan shayi na tafasa ma zuwa a flask nayi wanke wanke na gyara kitchen ɗin, indomie guda ɗaya da ta rage na tafasa na ci dan yunwa nake ji dagaske ba zan iya jira har sai ya tashi daga bacci kafin ya ƙaro wata na dafa mana ba dan dama na ɗauka guda biyu ce shiyasa ko da ya dawo jiya da dare bai shigo da komai ba ban wani damu ba.

Ina cikin shirya Al'amin Bilal ya shigo ɗakin yana hamma haɗi da shafa cikin sa, yanda yake yi ko bai yi magana ba na san yunwa nake ji, ya jefe ni da harar da ban tantance ta wasa ba ce ko ta gaske kafin ya ce
"Dariya ma kike yi mun ko?"
"Ni na isa? Ba dariya nake yi ba ka san dai haka fuska ta take dama" na faɗa ina miƙa masa Al'amin da na gama shiryawa. Ya karɓe shi ya zauna tare da shi a gefen gado ni kuma na wuce gaban wardrobe dan ciro kayan da zan saka.

"Badai baki ɗora abin karyawa ba?" Ya faɗa yana bi na da kallo. Sai da na ware doguwar rigar atamfar da na ciro kafin na kalle shi na ce
"Na dafa ruwan tea kai nake jira ka tashi ka siyo Madara da Milo tun da da sauran cake ɗin can sai a sha da shi dan na san babu lallai a samu burodi tun da rana ta fara yi goma yanzu".

"Ban gane na siyo Madara da Milo ba, kina nufin babu kayan shayi a gidan ko me?" Ya faɗa kusan cikin ɓacin rai, na dakata daga zuge zip ɗin rigar da nakeyi na ce
"Amma dai kai ne ƙarshen amfani da su jiya da dare tun kuma da zaka sha shayin sai da na gaya maka sauran kenan na juye a container baka kula ni ba".

"Kada ki gaya mun maganar banza Malama, kina nufin saboda na sha shayi da dare dan haka na sha rabo na ma safe ko me?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Hannu biyu na ɗaga na ce
"Mai da wuƙar ni ba haka nake nufi ba amma dai kayan tea sun ƙare, ni da wannan sutun ma da taimakawa kayi ka siyo dan yunwa nake ji sosai Indomin da na ci babu in da ta je mun".

Fita yayi ba tare da ya sake cewa komai ba, na cigaba da shiri na ina mitar yanzu kuma kayan shayi ne zasu haɗa husuma da safiyar Allah, shi dai baya raina abin magana dama.

Madara biyu Milo biyu ya siyo na sachet sai burodi babba guda ɗaya, na ringa kallon kayan sai dai gudun jan fitina ya sa ban ce komai ba na ɗora komai a try, sai da na ɗakko container sugar na ga shima ashe ya ƙare burbuɗi ne a ciki na tattara na kai masa falo in da yake zaune yana jira. Har muka gama karyawa babu wanda ya ce ƙala, yana gamawa ya wuce can part ɗin sa, ƙamshin turaren sa da na jiyo har cikin falo na ya sa na gane wanka ya yi zai fita, ina nan ina sauraren ya shigo na ji yanda za'ayi da girkin rana sai jin ƙarar rufe get na yi. Na tashi na fita da sauri amma ko ƙurarsa ban tarar ba sai ƙamshin sa da ya baza tsakar gidan.

Komawa na yi na ɗauki waya ta na shiga kiran sa, kira uku bai amsa ba haka na haƙura na ƙyale shi. Shiru shiru har sha biyu bai biyo kiran ba ga yunwa ta fara kawomun farmako dan Al'amin tsotso ne da shi ba na wasa ba, sha ɗaya idan ya yi sai na samu wani abun na cike gurbi. A can gidan Anty Labiba da yake ba na aikin komai sai dai na ci abinci na kwanta shi ya sa na cika na yi dam kamar ba jego nake yi ba yanzu kuwa daga dawowar mu sati guda har na fara jin ƙashin wuya na ya bayyana.

Ganin tunanin da tsammanin dawowar Bilal ba zasu kaini ko ina ba ya sa na zura Hijabi na na fita neman yaron da zan aika. Babu kowa a layin kasancewar rana ta take haka ta taka har bakin titi na yo cefane na da kaina. Sai bayan la'asar ya dawo na ringa kallon sa kawai yanda ya shigo babu ko tsinke a hannun sa sai fuska da ya haɗe kamar hadari amma da ya shiga kitchen ya fito sai naga ya ɗan saki fuskar ba kamar sanda ya shigo ba. Sai a lokacin ya ke ce mun wai ya ga missed calls ɗina me ya faru?

Takaici yanda ka san na rufe shi da duka kuma kamar wadda aka kullewa baki na kasa amayar masa da abinda ke cikin zuciya ta. Ban jinjinawa rashin ta idon sa na sai da ya tambaye ni ina abinci, haka na wuce na haɗa na kawo masa ya zauna ya hau ci na ringa kallon sa kawai har sai da ya gaji ya ce mun

"Wai kallon me kike mun haka ne ko so kike yi ki saka na ƙware?"

"Babu komai" na faɗa ina cigaba da kallon sa. Ya bata rai ya cigaba da cin abincin. Wayar sa da ya ajiye akan dining lokacin da zai shiga kitchen ta ɗauki ƙara, ban motsa na har sai da ya ce na miƙo masa ita kafin na tashi. Na ringa kallon sunan da ke yawo akan screen ɗin 'JALILA ABJ'.

A iya sani na Bilal ba shi da wata yar uwa ta kusa ko ta nesa mai irin wannan sunan, amma ko wanda baya son sa in har zai bayar da shaida akan sa kowa ya sani Bilal bashi da kule kulen yammata kuma nima zan shaidi hakan domin wayar sa ko password babu akai tun ina ɗauka na masa bincike ba tare da ya sani ba har na saki zuciya ta na yarda ni kaɗai nake da dashi dan haka ko yanzun abinda na bawa zuciya tabbaci akai shi ne Abokiyar aikin sa ce ba wata Mace daban ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 29*

Kafin na kai masa wayar ta yanke dan haka da na bashi ajiye ta ya yi ya cigaba da cin abincin ba tare da ya duba wanene ya kira ba. Duk yanda na so na mayar da hankali na kan Al'amin dake ƙananun rigima sai na kasa ƙarshe kawai na goya shi na yi tsaye ina kallon Bilal da ke cin abinci wayar sa na ƙara alamar shigowar wani kiran amma be amsa ba. Kamar me tsoron magana na ce masa
"Ana kiran ka a waya fa" ya ɗago ya kalle ni kafin ya ɗaga wayar ya karata a kunnen sa lokaci ɗaya yana miƙewa tsaye.

"Ranki ya daɗe Hajjaju na" ya furta kalmar da naji ta dirar mun a ƙwaƙwalwa tamkar saukar aradu, ya gota ni ya shige kitchen yana murmushi ko na ce dariya ƙasa ƙasa. Ina nan tsaye kamar mutum mutumi ya fito fuskar nan kamar an masa bushara ya sake wuce ni ya koma kan kujera ua zauna ya cigaba da amsa wayar sa.

Gashi dai ina gurin kuma kallon sa nake yi amma ba zan iya cewa ga abinda yake faɗa ba dukda ba wai a hankali yake wayar ta yanda ba zan ji me yake cewa ɗin ba, Aa, gaba ɗaya kunnuwa nane suka toshe ko kuma ƙwaƙwalwa ta ce ta dena fassara saƙon murya oho, kiran suna na da ya yi da ƙarfi ya maido da ni hayyaci na. Na sauke ajiyar zuciya kafin a hankali na matsa kusa da shi ganin ya miƙo mun wayar sa.

Screen ɗin na fara kallo Jalila ɗin ce dai suke magana kuma har tsayin minti goma kenan minti na goma da yin mutuwar tsaye.
"Ina wuni Maman Al'amin" ta faɗa bayan da na yi sallama cikin muryar da banyi zaton ta ji ni ba. Na amsa da "lafiya lau". Da "Eh, A'a " na ringa amsa mata tambayoyin da ban ma san me take cewa ba har ta gaji ta mun sallama ta kashe wayar ba tare da na maidawa Bilal ba.
"A can head quarter ta ke tare muka yi workshop ɗin da na je da ita, ta damu kullum muka yi waya sai ta tambaye ni ke yau dai kun gaisa na huta" ya faɗa bayan da na miƙa masa wayar.

Na sauke numfashin da ban san dalilin yin sa ba haɗi da yin gajeran murmushin da iyakacin sa baki. Fita yayi ya barni. Ban san tsahon lokacin da na ɗauka a zaune ba ban kuma san tunanin me nake yi ba har aka kira sallar magriba kafin na iya tashi daga gurin da nake. Me ya sa ban tambaye shi matar aure ba ce ko budurwa ko ba komai na samu cikakkiyar nutsuwa daga tunane tunanen da zuciya ta take ta raya mun? Haka nan na yi sallah ina jiran ya dawo na ji cikakken bayani akan wacece JALILA? Daga muryar ta zan iya fasaltata a shekaru talatin zuwa sama daga kuma maganar ta na tabbatar yar gayu ce, har na fasaltata a idanuwa na irin matan Abuja jiki duk madarar nan. Wannan tunanin ya saka mun ƙunci da rashin nutsuwa a zuciya ta amma kuma duk yanda ma zaƙu ya dawo na yi masa tambayar sai na kasa lokacin da ya dawo.

Sai da aka yi isha'i ya sake shigowa falon lokacin ina cin sauran abincin da ya rage, ya zauna a kusa da ni fuska a sake ya ɗauki Al'amin ya fara masa wasa ni dai kallo ɗaya na masa na mayar da kai na cigaba da cin abincin da nake yi ina kokawa da zuciya ta dake azalzalata akan na tambaye shi wacece JALILA amma na kasa.
"Akwai sauran abincin ne?" Ya tambaye ni, ba tare da na yi magana ba na girgiza masa kai kawai, ya sake cewa

"Ba har dare kika yi girkin gaba ɗaya ba ko me?"
"Iya abin da na siyo kenan na dafa" na bashi amsa ba tare da na kalle shi ba, sai na ji ya ce
"Au, dama ba Gara aka kawi miki ba?". Na yi tsam kafin na waiwaya na kalle shi dan ban fahimci in da maganar sa ta dosa ba, wace Gara kuma yake magana akai?

"Wace irin Gara kuma?" Na tambaye shi ganin ya tsare ni da ido, ya haɗe girar sama ya ce
"Gara kala nawa kika sani?" Nima haɗe tawa girar na yi na ce
"Nasan dai ana Garar aure ta al'ada, idan ita kake magana kuma an yi mun" na bashi amsa ina cigaba da cin abincin gabana. Sai ji na yi ya d
Sake cewa

"Kawai ki ce saboda mugun hali ku a gidan ku bakwa yin Garar haihuwa ko kuma kece ba za'a yi wa ba tun da ba'a sona?"

Mamaki, takaici da haushi duk suka kamani lokaci ɗaya. Bilal dai ba zai canza hali ba, sam bakin sa ba zai taɓa koyon tauna kalami kafin ya furta su ba. Gyara zama na yi na kalle shi da kyau na ce

"Muguntar ce ta saka aka baka aure na, duk a cikin muguntar aka cika maka gida da kayan ɗaki aka kuma haɗo ni da kayan abincin da har yau shekara biyu auren mu babu wata uku kake ci a cikin su ba. Sharaɗin ciyarwa akan Namiji ya ke ba Mace ba, haƙƙin ka ne da ka kawo mun abin da zan ci a cikin gidan nan ba wai ka zauna kana jiran a kawo daga gidan mu ba, baka ga duk ƙoƙarin da aka yi maka a baya ba ashe kai nan jira ma kake yi bayan Garar aure a sake lodo ta haihuwa a sake kawowa kenan? Sannu Bilal" Na faɗa ina tsare shi da ido.

"Gori zaki yi mun kenan?" Ya faɗa lokaci ɗaya fuskar sa na rinewa da ɓacin rai. Na ture kwanon gaba na na miƙe na ce
"Gaskiya ce kawai na faɗa ba gori na maka ba, na zata ai yau sabon muna da kayan abinci ya sa ka manta ka fita ba tare da ka bar mun abinda zan ci ba ashe kai duk a tunanin za'a kawo mun Gara daga gidan mu".

Ya mun kallon bani da lokacin ki a yanzu kafin yayi tashin Magajin Dagacin Ƙauye da Al'amin a hannun sa, na yi ta jira ya dawo ya rufe ni da masifar da ya saba amma shiru har na gama tunane tunane na bacci ya kwashe ni bai shigo ba balle ya dawo da Al'amin ɗin sai cikin dare na farka na ganshi a kusa da ni.
Bayan na yi fitsari na canza masa diaper muka sake komawa bacci. Gurin ƙarfe bakwai da rabi ina tsaka da mopping dan tun asuba da na tashi sallah shima Al'amin ya farka ya kuma ƙi komawa dan haka na goya shi kawai na shiga aika ce aika ce na naji ana buga get, Hijab na zura na fita, jin muryar Sunusi maigadin maƙwaftan mu ya saka na buɗe kofar.

Ya gaishe ni na amsa ina mamakin tsadadden warmer na da na gani a hannun sa, a iya tunani na ban tuna sanda na fitar da shi ba da har zai je hannun Sunusi. Miƙo mun ya yi da baƙar leda na karɓa ina masa kallon rashin fahimta ya ce
"Yallaɓai ne ya bani tun jiya da dare ya ce a siyo Ƙosai da Kunu".

A kan dining na ajiye kayan na buɗe Ƙosan da basu fi ƙwaya goma sha biyar ba na rufe, Kunun ma ƙulli biyu ne tsululu da shi da gani ma na masara ne ina jin ko ɗumin kirki babu sai wani ƙullin sugar abin dai kamar na rusa kuka saboda takaici. A gurin na barsu na cigaba da abinda nake yi ina jiyo motsin buɗe ƙofar sa lokacin ina mopping kan barander dan tun da ya dawo daga masallaci na jiyo shi yana share compound ɗin ya kuma wanke na ɗauka ma harda barander ya wanke sai da na fita karɓo ƙosan na ga gurin da datti shine na sake shareta na goge.

Fuska ba yabo ba fallasa ya tsaya yana kallo na, na gaishe shi daga in da nake tsaye ina ɗauraye mopper ya amsa kafin ya shige cikin falon. Sai da na shanya mopper na kwashe kayan wankin da na manta ban ɗauke ba jiya kafin na shiga falon nima.

"Ina abin karyawa?" Ya faɗa dai dai ina ƙoƙarin shigewa ɗaki na, na nuna masa kan dining ba tare da na ce komai ba na shige ɗakin, ban fito ba sai da na yi wanka na yiwa Al'amin na tarar ya bar mun Ƙosan guda bakwai sai ƙullin Kunu ɗaya, Hijabi kawai na saka na goya Al'amin bayan na juye Ƙosan a farar leda na fita da su na bawa wani Almajiri sannan na wuce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login