Showing 45001 words to 48000 words out of 257873 words
aka sha ruwa ban ci dankali ko doya ba ji nake kamar ma ba azumi na kai ba. Dan ma lokaci ya ƙure ne dama so nayi ka bada kuɗin na bawa Anty Labiba su daga Jos ake kawo musu har can gida ma duk ita ake bawa ta siyo mana"
Se yayi gaba yana cewa
"Yayi kyau" na rakashi ina masa a dawo lafiya. Ni ban san wai ashe maganar dana faɗa tayi zafi ba, fitar sa babu daɗewa se ga Mu'azzam Abba ya aiko shi ya kawo mun gero da wake da sugar irin wanda yake rabon azumi harda madarar ruwa katan ɗaya da dankali cikin ƙaramin buhu. Sosai naji daɗin kayan, shikenan tun da ina da mai se na ringayin kunu da ƙosai ko ba yawa a bayar sadaka. A store na gyara komai na ajiye ina jiran Bilal ya dawo na gaya masa, ranar be shigo ba se ƙarfe tara ya dai kira ni sanda akayi sanarwar an ga wata yace tuwo zanyi abincin dare dashi yake so yayi sahur. A kwanakin in har ba yana gida ba daƙyar nake wuce isha'i ban fara bacci ba sedai idan ya dawo ya tashe ni, yau ɗin ma ina idar da sallah na kwanta a gurin bacci me daɗin gaske ya kwashe ni da bani na tashi farkawa ba se ƙarfe uku da wasu mintoci na dare shima fitsari ne ya matse ni.
Akan gado na hangi Bilal yayi ɗai ɗai yana bacci abun sa ni kuma ina ƙasa kan abin sallah. Se da nayo fitsarin kafin na fita falo jin ciki na kamar anyi yawa yunwa ta taso mun lokaci ɗaya. Ban gane kai ba se da na tashi da malmalar tuwo biyu tukun na ji dama dama. Se sannan na lura da kayan daya zube tsakiyar carpet, na kunna fitila me haske na shiga buɗe su. Har da nama da kifi da alama a ƙanƙara aka ciro su dan sun narke duk ruwan su malale mun a kan carpet ga kayan miya suma ciki akwai marasa kyau. Banji daɗi ba sam da abin da ya mun, jiya fa na shimfiɗa carpet ɗin bayan an dawo dashi daga wanki gashi me haske shine ze aje mun kaya akai su ɓata ga ƙarnin kifi da nama ni ban ma ce masa ya siyo mun kifi ba yama sani bana son ɗanyan kifi in dai ba cat fish ba ina da bushashshe da yawa dashi nake duk abin da naji ina so na kifi.
Ina mita ina kwashe kayan, duk abinda na lissafa masa ya siyo ɗin banda ƙwai. Naman na fara gyarawa na saka a freezer na juye kayan miya a kwandon su da sauran kayan tea da spices komai na ajiye sannan na juya kan kifin. Ina buɗe shi naji amai ya yunƙuro mun, kafin na janye shi gefe daga cikin sink ɗin aman ya ƙwace haka na ringa sheƙashi akan kifin kamar zan amayar da yan hanji, yanda ƙarnin yake dukan hanci na haka zuciyata take sake hautsinawa aman na sake taho mun. Se da nayi dabarar toshe hanci na da ɗankwalin kaina kafin na samu sassauci. Daƙyar ba samu ƙatuwar leda na tattare kifin daya sha wankan amai a ciki na sake zura shi cikin wata ledar, se da na masa leda uku sannan na ajiye a ƙasa na kwance robar morning fresh na zazzage cikin sink ɗin na ringa wanke gurin, ban ji kitchen ɗin ya mun dama dama ba se da na zazzage robar hypo daya siyo cikin kayan idan haka siddan ne yaci ace warin hypon kansa ya hau mun kai amma daɗin sa na ji na ware hanci na ringa shaƙa har seda ya maye gurbin ƙarnin dake yawo cikin hunhu na sannan na fara komawa cikin hayyaci na sosai.
A sharar baya naje na jefa ledar kifin sannan na dawo na sake gyara kitchen ɗin, seda naji an fara kiraye kirayen sallah sannan na fita na naɗe carpet shima dan ma kunna burner turaren wuta tun da na kwashe kayan dama. Ina kici kicin ɗaga carpet Bilal ya fito ɗaga ɗaki, kallo ɗaya na masa na maida kai na ɗaga carpet ɗin daƙyar ina nishi dan yana da girma da kuma nauyi. Be kula ni ba shima ya wuce kitchen, daga ciki ya ƙwala mun kira. Seda na zumɓuri baki kafin na amsa na bi bayansa. Yana tsaye gaban sink ya toshe hanci da hannun sa ya nuna mun robar hypo data morning fresh yace
"Meye haka?"
"Abu na wanke" na bashi amsa ba tare da na kalle shi ba. Ga mamaki se ji nayi yace
"Baki da hankali Halima? Robar hypo ɗin kika ƙarar data abin wanke wanke kiji yanda warin ya cika ko ina yana neman bugar da mutane, me ma kika wanke?"
Baki na tunzura cikin shagwaɓa nace
"Ni fa ban ce ka siyo da kifi ba gashi nan ƙarnin sa duk ya hautsina mun ya saka ni amai" na ƙarasa ina toshe baki na dan sunan kifin dana faɗa yasa naji kamar lokacin nake shaƙar ƙarnin sa. Ji nayi dagaske amai na taho mun dan haka na ture shi daga jikin sink na shiga kwararawa. Yana tsaye har na gama na wanke fuskata na jingina da cabinet ina mayar da numfashi. Kamar ma abun be dame shi ba ba sannu balle yaji ba'asin aman kawai ya matsa gaban gas ya buɗe tukunyar miya, se ya juyo ya kalle ni yana nuna mun tukunyar yace
"Ina naman cikin miyar nan?"
"Na cinye" na bashi amsa ina barin kitchen ɗin dan aman da na sake yi duk ya taso mun da wasu ciwuka da ban gane musu ba. Ƙafafu na kamar ana sare su ji nake kamar zan faɗi. "Naya yanka biyar ɗin kika cinye ke kaɗai saboda ke kika siya?" Ya faɗa yana sakin murfin tukunyar, ta gefen ido na kalle shi cikin ƙunƙuni nace
"Ni dai kar ka fasa mun murfin tukunya" na ƙarasa ina ficewa daga kitchen ɗin. Ina kwanciya kan kujera ya iso kaina yana huci kamar wani kumurci yace
"Me kika ce?"
"Ni ba abin da nace dan Allah ka ƙyale ni naji da kaina" na faɗa ina riƙe ciki na da ya fara murɗa mun. Tsaye yayi yana kallo na ina murƙususu dan ciwo sosai ciki na ya tayar mun tun ina kan kujera se da na sauka ƙasa na durƙushe, ganin yanda nake juya kai ina kiran sunan Allah yasa ya rage tsayi yana tambayar menene, ban iya ce masa komai ba se ciki na dana nuna masa. Ɗaki ya wuce ina jin sa yana cewa
"Kin ci rabon ki da ba naki ba ai dole kiyi ciwon ciki" hawayen azaba haɗi da takaici suka zubo mun lokaci ɗaya. Saboda na ci nama shine ze zama sanadin ciwon ciki se kace wadda ta ci na sata ko Allah ya isa?
Farin magani ya dawo dashi a hannun sa ya durƙusa gaba na ya buɗe bayan ya jijjiga ya tsiyaya mun a murfi. Cikin ikon Allah ina shan maganin ciwon ya fara lafamun, a nan ƙasan tiles ɗin bacci ya kwashe ni, ban san ya Bilal ya ƙare da sahur ba ni dai na farka naga ga gari ya waye tangarau. Se da na watsa ruwa nayi sallah ina ji na duk ba yanda na saba ba. Jiki na ba ƙarfi sam ga marata dake murɗa lokaci lokaci se na kawo ko period ne yake shirin zuwar mun. Dana shiga wanka ma se da nayi amai dan haka na haƙura da zancen azumin ranar kawai. Har na shirya na sake fitowa falon banji motsin Bilal ba hakan yasa na fita na leƙa part ɗin sa, ta window falo na hango shi yana bacci akan kujera se na koma cikin gida kawai. Ina jin yunwa amma sam bana jin cin komai, a haka na ja Carpet ɗin dana naɗe na fita dashi na share wajen nayi mopping sannan na kwanta ina jin duniyar na hautsina mun.
Bilal be fito ba se gurin sha biyu saura lokacin har na gama murƙususun ciwo har ya sake ni na miƙe na shiga kitchen ina tafasa indomie da dafaffen ƙwai. Ina tsaye jikin cabinet ina jiran indomin ta ƙarasa na sauke ya shiga kitchen ɗin, muka haɗa ido se naga kamar harara ta yayi kafin ya mayar da idon sa kan bowl ɗin dana saka ƙwai biyun dana dafa ina jira su huce na ɓare. Gaban deep freezer ya wuce ya buɗe ya shiga ɗaga kayan ciki ni dai na wuce na kashe gas ganin indomin ta mun yanda nake so. A fusace ya ɗago ya kalle ni yace
"Ina kifin dana siyo jiya?"
Nayi kamar banji ba ina ɓare ƙwai na se da ya maimaita da lafazin daya fi na farko kauri kafin na dakata na juya gaba ɗaya ina kallon sa nace
"Na zuba shi a sink zan wanke ƙarnin sa ya tayar mun da zuciya kafin na kar ga matsawa amai ya ƙwace kuma babu yanda za ayi ya ciyu shi yasa na zubar dashi"
"Kika zubar saboda kin yi hauka ko me? Ce miki nayi sato shi nayi ko a ƙasa na tsunto da zaki yi amai akai ki zubar saboda baki san zafin kuɗi ba Halima?" Ya faɗa fuskar sa na amayar da fushin dake cikin zuciyar sa. Yaci gaba da cewa
"Tsabar baki da mutunchi baki san darajar kuɗi ba shine zakiyi amai akan abin da za a ci kuma ba kunya ba tsoron Allah kike gaya mun kin zubar kifin dubu biyun kina zuba mun a shara, to wlh idan kin saba ɓarnatar da abinci a gidan ku saboda sangarta ba a ce miki komai ni a nan ba zan ɗauka ba dan ba sato kuɗin nake ba da gumi na nake neman su. Kin haramta kifi kin zubar sannan kin mun asarar hypo roba guda da abun wanke wanke to wlh bazan ɗauka ba ki kuma kwana da sanin se kinyi nadamar abin da kika yi" ya ja tsaki kamar ze katse harshen sa kafin ya buga murfin freezer ya wuce ni yana cewa
"Aikin banza kawai mace babu abinda ta sani se taci ta kwanta ta ɓarnatar maka da abinci".
[5/18, 14:39] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*Page 13*
Kasaƙe nayi ina kallon sa har ya fice daga kitchen ɗin lokaci ɗaya jiki na yayi sanyi lanƙwas kamar an watsa mun ruwan sanyi. A hankali na ajiye bowl ɗin hannu na na dafe drawer baya na da hannu biyu jin jiri na neman ɗiba ta. "Sam wannan ba Bilal bane, ba halin sa bane akwai wani abu da yake damun sa tabbas" abin da na furta a fili kenan cikin son ƙarfafawa kaina guiwa da kuma bawa kaina tabbacin ba cikin sani Bilal yayi mun wannan tozarcin ba. Nafi minti biyar kafin na tattara ƙarfin daya rage mun na bi bayansa zuciyata na ƙarfafa ni da naje naji me ya same shi? A bakin ƙofar ɗakin na ci burki na kasa shiga saboda yanda zuciya ta take bugawa fat fat. Ba zan iya jurewa ya sake gaya mun wasu maganganun ba zuciya ta zata iya bugawa amma kuma ina da buƙatar sanin me yake damun sa? Waye ya tunzuro shi haka ko ma im ce wasu shaiɗanu ne suka shafe shi?.
Ina kama hannun ƙofar aka buɗe daga ciki, mukayi ido huɗu ya jefe ni da kallon da na kasa mantawa kafin ya ja tsaki kamar ze ture ni ya fice, daga in da nake na jiyo yanda ya buga ƙofar get. A nan gurin na sulale na zura kaina cikin cinyoyi na se dai hawaye ko ɗis be zubo mun ba zuciyata ce kaɗai take suya wani abu me ɗaci da maƙaƙi na yawo cikin maƙoshi na. Nafi minti ashirin a zaune a gurin kamar ma ba a duniyar nake ba, kalaman Bilal na mun amsa kuwwa tamkar a lokacin yake faɗa mun su. Jin ana kiran wayata a karo na uku yasa na yunƙura daƙyar na tashi, Mama ce take kira na, na san har idan na amsa tilas zata fahimci halin da nake ciki hakan yasa na mayar da wayar na ajiye na kwanta akan kujera.
A nan na wuni sur sallah kaɗai ke tayar dani gaba ɗaya ji nayi duniyar tayi mun duhu komai ya haɗe mun na kuma rasa ta ina zan fara gyarota, wa zan kira na faɗa masa matsala ta? Ban san me yasa sam naji na kasa kiran Anty Labiba ba dukda ita ta fara zuwar mun se kuma Hansa'u amma duk su biyu dana tuna basa son Bilal se naji be kamata na kai kuka na kan abin da ya shafe su gurin sa ba daga ƙarshe na yanke shawarar na shanye ɓacin raina ni kaɗai tun da dama cikin nasihohin da aka mun an jaddada mun muhimmancin riƙe sirrin gidan aure na.
Rashin cin abinci da ɓacin ran da nake ciki suka haifar mun da ciwon kai da ciwon ciki me tsanani. Shida saura Bilal ya dawo, sama sama nake jiyo muryar sa da alama waya yakeyi yana ta raha amma dana ɗaga kai bayan daya turo ƙofa ya shigo gani nayi ya haɗe rai tamkar be taɓa dariya a rayuwar sa ba. Tsayuwa yayi a kaina yana kallo na, nayi kamar bacci nakeyi ina jin sa ya saki tsaki kafin ya wuce yana ƙunƙuni se na bishi da kallo hawaye na gangarowa ta gefen ido na, kitchen ya shige, daga can naji ya fara kiran suna na ban amsa ba se gyara kwanciya da nayi na bada baya ina goge hawayen da suka ɓalle mun.
"Wato baki ma ɗora mun abin shan ruwa ba ko? Na lura nema na kike yi da fiti na Halima. Iya asarar da kika mun bata ishe ki ha yanzu kuma hora ni kike so kiyi da yunwa ko? shikenan kiyi yanda kika so" ya faɗa ni dai ban juyo ba ya wuce ɗaki be ɗauki lokaci ba ya fito ya sake shiga kitchen ina jin sa yana haɗa tukwane yana gwarawa ƙarar tana shigar mun har tsakiyar kai. Ina kwance a gurin aka kira sallah na yunƙura na tashi da ƙyar ina dafe da kaina ga ciki na daya fara yamutsawa dalilin ƙamshin suyar ƙwai daya fara tasowa daga kitchen ɗin.
A hankali na kalli Bilal ya fito daga kitchen da plate me ɗauke da ƙwai da cup ɗin shayi. Kan center table ya ajiye su ya wuce cikin ɗaki, ganin ƙwan da ƙamshin daya sake kusanto ni ya hautsina mun zuciya. Da ƙarfin da ban san in da na same shi ba na miƙe muka ci karo a bakin ƙofa yana shirin fitowa ni kuma zan shiga ganin yanda na tafi zan kifa ya ruƙoni kafin na ƙwace aman da nake dannewa ya fi ƙarfi na na shiga kwarara masa a jiki. Irin kallon da yake mun kaɗai naji gara ya rufe ni da masifa ko ya doke ni yafi wannan kallon. A ƙasa na kwanta ina juyi cikin aman saboda wani irin yanayi da nake ji da bazan iya fasaltawa ba. Bansan ko imani ne ya shige shi tausayi na ya kama shi ba ya tsugunna dukda kallon da yake mun wanda daga baya na fahimci na ƙyamar ƙazantar aman da nayi ne be bar fuskar sa ba ya shiga kiran sunana yana tambayata menene. Da hannu na nuna masa kaina da ciki na, tashi yayi ya cire rigar jikin sa ya ajiye a gurin sannan ya ɗauke ni, se da ya ɗauraye mun jiki da ruwan ɗumin da nake jin kamar ruwan dalma yake watsamun take zazzaɓi ya rufe ni.
Yana tsaki kamar ze katse harshen sa ya gyara gurin aman tsaf ya goge ya fesa room freshener sannan ya ɗauraye kayan sa da nawa da suka ɓaci kafin ya gama bacci ya kwashe ni ban zan ya ya ƙare ba se cikin dare na farka yunwa na neman yin ajali na. A kan center table na samu sauran jallop ɗin shinkafa daya ci ya rage na cinye na haɗa da sauran wacce na gani a tukunya sannan na fara gane kaina. Ƙarfe uku da kwata lokacin, a falo nayi sallar magriba da isha'i da banyi ba ina lazumi Bilal ya fito daga ɗaya ɗakin. Kallo ɗaya ya mun ya wuce kitchen, zuciya ta ta shigan bugawa ina jira na ji ya fara masifar abincin da naci amma naji shiru se gashi ya fito da cup da ruwan zafi ya haɗa tea a kan dining ya zauna yasha da ƙaton bread ɗin sa bayan ya gama ya koma ɗaki ya canzo kayan jikin sa ba tare da yayi mun magana ba ya tayar da sallah nan kusa da in da nake.
Ina zaune gurin ya dawo daga sallar asuba, kan kujera ya kwanta ya harɗe hannunsa biyu bayan kansa yana kallon sama, na shafa addu'a na gyara zama ina kallon sa kamar me tsoro na shiga gaishe shi. Nayi mamakin yanda ya amsa ba yabo ba fallasa har ya tambaye ni jiki na na sanar masa babu abunda yake damu na a lokacin.
"Naga dankali da doya da wasu kaya a ɗakin can" ya faɗa bayan daya tashi zaune, kaina na ƙasa na ce
"Eh, Abba ne ya aiko da su shekaran jiya"
"Shine baki faɗa mun ba?" Ya faɗa cikin sautin daya fi na farko taushi. Se na ɗaga kai na kalle shi maganganun daya yaɓa mun jiya suka shiga dawo mun take ido na ya ciko da hawaye na sadda kaina ƙasa ba tare da nace komai ba.
"Zan kwanta, idan ƙarfe bakwai tayi ban farka ba ki tashe ni" ya faɗa yana komawa cikin kujerar ya