Showing 168001 words to 171000 words out of 257873 words

Chapter 57 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

525

shiga yau sai dai ka shiga dan wlh ba zan kwana a hotel ba a gida na yi niyyar kwana tunda kuma ka kyautar mun da kayan gida ba tareda izini na ba sai ka kaini naka gidan ba wai matarka bata nan ba ko tana nan wlh ba abinda ya mun zafi a nan zan kwana dan dama da baka zo ba sai dai ka ganni a ƙofar gida kuma ko yanzu ka direni a nan ƙila sai na rigaka zuwa so baki alaikum ka wuce mu tafi dan ni a gajiye nake wanka nake so nayi na kwanta nayi bacci" ta bashi amsa itama.

Duk yanda ya so ya fahimtar da ita ta masa banza ƙarshe mayafinta taja ta rufe fuskarta kamar me bacci, ganin har ɗaya ta kusa suna gararanba akan titi bai kuma ga alamar zata canza ra'ayi ba ya saka kawai ya kama hanyar gida a ransa yana addu'ar Allah ya sa kowa yayi bacci har masu gadin layin. Ya da sauri ya kalli mirror jin ta ce
"Ga wata mota nan ma tun ɗazu take binka ƙila ma matar taka ce ko wani daya sanka" ta ƙarasa tana dariya. Kallon motar yayi dakyau, sai tayi masa kama da motar Suhaila matar Hafiz amma kuma number ta banbanta tata kamar ABJ wannan kuma ABC dukda dai bai tabbatar ba amma ya ƙarfafawa kansa hakan ne dan ba zai iya hasaso cewa Matar Hafiz ɗin ce ko kuma ma shine da kansa ba iya tashin hankalin da yake ciki yanzu ya ishe shi. Kamar me motar ya san me suke cewa kuwa yazo ya wuce su dama a junction suke ya ɗauki wata hanyar daban Bilal ya sauke ajiyar zuciya kafin ya balla mata harara ya cigaba da tuƙi.

Roƙonta ya ringayi akan ta rufe fuskarta sanda suka isa unguwar, duk wanda ya kalle shi dakyau sai ya fahimci bashi da gaskiya haka ya lallaɓa ya shige Allah ya taimake shi mutum ɗaya ne zaune sauran masu gadin duk sunyi bacci get ɗin kuma a buɗe yake dan haka bai ma taso ba tunda ya gane motar daga zaune ya masa sannu da zuwa ya wuce dama kuma windows ɗin motar tint ne ta gaba ne za'a iya ganin wanda yake ciki. Sai da ya shige da motar ya dawo ya kulle get kafin ya tsaya ya riƙe ƙugu yana sauke numfashi. Ta fashe da dariya bayan da ta fito daga motar tana cewa

"Wai yanzu duk tsoron kar yan unguwa su ganka ne yasa ka birkice haka amma baka tsoron Allah kake bajekolinka a hotel ko?"
"Dan Allah ki wuce ciki kum wlh tun kafin gari yayi haske zamu fita ba zaki zubar mun da mutunchi a unguwa ba dama duk sun tsaneni tunda Halima ta bar gidan nan" ya faɗa yana wucewa gaba bayan daya shiga ɗakin tsakar gida ya kunno Solar dan babu wuta tunda sha biyu ta wuce kuma ya san ba dawo da ita zasuyi ba. Bayan tafiyar Halima da aka fara rashin wuta ya haɗa ta babba har Ac take ɗauka. Kan kujera ta faɗa tana cewa

"Wash Allah, daɗi na da matar nan taka akwai tsafta ba wanda zaice falon me yara ne kamar na sabuwar amarya komai na nan da sabuntarsa"
"Basu daɗe ba ai bayan haihuwar Sharifa ta canza su" ya bata amsa yana ɗaukar remote ɗin Ac ya kunna. Ta miƙe tana ƙoƙarin cire doguwar rigar jikinta tace
"Dukda haka dai tana da tsafta gaskiya" sai ya wuce ɗaki yana cewa

"Ba laifi amma dai ni nake shara da mopping har wankin toilet duka" ta kuwa fashe da dariya tace
"Ashe boyi boyi ta mayar da kai sannu mijin tace".
Indomie ya dafa mata bayan tayi wanka ya ɗumama Shawarmar daya siyo ɗazu a microwave dama guda biyu ce ya dafa tea suka ci kafin ta kwanta a Asalin ɗakin Halima da tace gadon irin nata ne na gida dan haka nan zata kwanta kafin ma ya gama wanke kwanukan da suka ɓata ya tattare falon har tayi bacci. A falo ya kwanta bayan daya leƙa ta ya tarar tana bacci dan dama cike yake da taraddadin karta nemi suyi wani abu dan gaskiya ba zai iya ba gaba ɗaya yanzu haka ma a mugun tsorace yake ji yakeyi kamar wani zai iya shigowa ya tarar dasu yayi mamakin yanda yake ji ɗin dan ko kaɗan bayajin komai idan suka je can gidan ta ko da yake yan unguwar kallon ma'aurata suke musu irin kamar a wani garin suke zama sai hutu suke zuwa nan ɗin. Daƙyar bacci ya ɗauke shi yana yi yana farkawa gudun karsu makara gari yayi haske bai fita da ita daga unguwar ba.

HALIMA
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*


*PAGE 43*

HALIMA
Yanda naga rana haka naga dare, sai naji ashe ma jiya baccin daɗi nayi yaune nake ganin asalin baƙin dare. Sai da aka idar da sallar asuba kafin na samu bacci ya fizgeni, sai dai ban wani yi nisa ba na farka sakamakon kiran suna na da nake ta ji anayi.

Na tashi zaune daƙyar ina matse ido haɗi da dafe gefen kaina da nake ji kamar zai faɗo saboda ciwo. Mama na tsaye ta ce
"Hala kin manta abinda Abbanku ya faɗa miki shiyasa kika shantake kina bacci har ƙarfe tara".

Gabana ya yanke ya faɗi, mai take nufi? Takardar ya turo ta karɓa ko me?

Muryata bata ko fita sosai saboda uban kukan da nasha jiya ga bacci da ciwon kan da suka mun rubdugu na ce

"Dan girman Allah Mama ki bashi haƙuri"

"Kin yafe ba zakiyi bautar ƙasar ba kenan in je na gaya masa?" Ta katse ni. Na tabbatar har kunnuwanta ƙarar ajiyar zuciyar da nayi ya isa jin ba abinda nake tunani bane, ta ja tsaki ta fice daga ɗakin tana cewa

"Ki tashi ki shirya tun ranki bai sakw ɓaci ba dan wlh a cike yake dake kin kuma san dai bai iya fushi ba".

Ina wanka ina hasaso ta inda zan samu mafita cikin wannan tsaka mai wuya da Abba yake ƙoƙarin jefa ni. Yanzu shi ba bu ruwansa a ringa cewa aure na ya mutu kenan? Na tafi tunani dangi na uwa da uba babu wata bazawara kamata, yawanci ma har manyan mutuwa ce ta rabasu da mazajensu ba sakin aure na shikenan ni zan zama abar buga misali a dangi da unguwa, fatan da aka ringa mun zai tabbata na san ƙila labari na babu inda ba zai kai ba har Facebook da Whatsapp groups.

Kan toilet na zauna na sha kuka na godewa Allah kafin na fito na sake zama kan gado na rafka tagumi. Allah ya sani ina son Bilal, rabuwa dashi abu ne da ban taɓa hasasowa a nan kusa ba duk da abinda ya faru yayi silar zabtarewar sama da kaso hamsin na yanda nake jin sa a zuciyata amma in ce na dena son sa wannan ƙarya kawai nakeyi.

Hannu biyu na saka ina goge sababbin hawayen da suka ɓalle mun, da kaina kuma na shiga tugumar kaina anya kuwa nayiwa kaina adalci idan na cigaba da son Bilal?

Babu wani abu da zan ɗorar a zamana dashi wanda zan dogara akansa har ya bani ƙwarin guiwar sake bashi dama a karo na biyu bayan abinda ya faru. Ya gwada mun halayen ni da kaina na yarda zuciyar dake cike da so ba zata aikata irin su ba abu mafi muni ya ci amanata a bayan ido na yana mu'amala da macen banza sannan ya tozartani akan hakan har mahaifiyata yayiwa zagi mafi muni kuma dukda haka nake jin zan iya yafe masa na cigaba da rayuwa dashi.

Ƙasa na durƙushe na sake fashewa da kuka ina nanata "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Tabbas ina cikin masifa ni kaina na sani ta yaya wanda ya aikata mun irin waɗannan zunuban zan cigaba da dakon soyayyar sa a raina?

Muryar Mama naji a kaina tana cewa
"Halima wai ba zaki ko duba ƙananun yayanki kiyi tunanin halin da zasu shiga idan babu ke ba kin dage lallai sai kin ja wa kanki ciwon da zai kashe ki ko?" Ta faɗa tana kallo na, ban ɗago ba sai kukan da na cigaba da yi, tayi ƙaramin tsaki ta ce

"Mu'azzam yana da uzuri kin zaka ya tsayar dashi ya ce ya kaiki idan ba zakije ba ki fita ki gayawa Abba ya sallame shi ya tafi sabgar sa dan Allah"

"Mama kin dena so na, kwata kwata yanzu kin dena damuwa da abinda ya shafe ni kenan idan ma na mutu yarana ne kaɗai suka rasa banda ke" na faɗa cikin kuka. Tayi ƙaramar dariya tana nufar ƙofa tace

"Mutum kuwa ya taɓa haifar ɗa a cikin sa yace ya dena sonsa Halima? Ke ɗin ce ai kin zama gomnati ba'a miki kutse yanda aka dama da nace yaranki kuma kinga ai su ke kaɗai gare su ni kuwa Alhamdulillahi ku huɗu Allah ya bani dama kuma daɗin haihuwar da yawa kenan idan wani bai faranta maka ba wani zai saka ka farinciki. Ni dai idan ba zakije ba kije ki faɗa masa dan Allah ya sallamar mun yaro ya tafi dan shi yana da abubuwan yi da zasu taimaki rayuwar sa".

Wato ni ce wadda bata da abinyi da zai taimaki rayuwata? Haka nan na haƙurtar da kaina na saka kaya ban ko nemi mai ba balle aje ga batun turare ko in yi kwalliya, sai sa na gama shiryawa kuma sannan na tuna ai Khaki ya kamata na saka kuma ban taho dasu ba suna can gidan Bilal.

Har raina naji daɗi dan dole ai yanzu a fasa fitar, falon na fito, ina buɗe ƙofa muka haɗa ido da Abba dake tsaye da alama kuma ni yake jira. Kamar munafuka sum sum na zube a ƙasa murya ba amo na shiga gaishe shi, bai amsa ba sai cewa da yayi cikin dakewa

"Tashi ku tafi".

Nayi diriri a tsugunne ina ji Mama na cewa
"Da dai ta karya ko?"
"Idan sun dawo sai ta karya yanzu Mudassir ya kirani mutumin yana ta masa waya".

"Sai ku wuce ku tafi ai" Mama ta faɗa, na miƙe kamar kazar da aka tsamo daga ruwan zafi na nufi ƙofa Abban ya dakatar dani yana cewa
"Ina uniform ɗin?"

"Suna can gidan ai" na bashi amsa ina kallon ƙasa. Da hannu ya mun alamar mu je, Mu'azzam yayi caraf ya ce
"Bafa zasu barta ta shiga a haka ba yanzu doka na aiki ko colored hijan ba'a shiga dashi secretariat balle taje musu da kayan gida, kalli shigar da ta yi ga fuskar ta duk a kumbure ɗauka za suyi ma mabaraciya ce".

"Kuma dai? To sai ku bari sai gobe ai a cigita ko a cikin unguwa ai ba za'a rasa masu service ɗin ba su bata aron uniform ɗin kan ta ɗinka wani" Mama t faɗa, sanyi na ji har raina sai dai kuma murnata ta koma ciki jin Abba ya ce

"Tunda uniform ɗin makaranta ne da zaki ce ta aro? Su biya ta can gidan ta ɗakko ko babu muƙulli a hannunki?" Ya ƙarasa yana kallona. Yau ɗin ganinsa nake wani daban kamar ba Abba na mai yawan fara'a da wasa da dariya ba, da sauri na ɗaga masa kai alamar akwai kafin na juya cikin ɗaki na ɗakko muƙullin dan yana ajiye dama a kan mudubi.

Har muka isa layin gidan ci kanki Mu'azzam bai ce mun ba nima kuma tawa ta ishe ni tunda na haɗa kai da window ban ko motsa ba sai da naji ya tsaya na duba na ganmu a ƙofar gidan.

Karki ɓata mun lokaci Malama" ya faɗa yana wani ɓata rai kamar shine gaba dani, haka nan na ringa jin wani iri a jikina. Na kalli layin daga farko har ƙarshe ina tuna ranar da na bar gidan. Sammani mai gadin gidan Maman Yusuf ya taso da sauri gani na, dole na ƙago murmuyna ɗora akan fuskata sanda muke gaisawa ya ce

"Kin dawo Hajiya?"
"Abu nazo ɗauka dai amma dan Allah karka gayawa su Maman Yusuf na zo dan sauri nakeyi ba zan samu damar shigar musu ba" na bashi amsa. Yana shafa kai ya ce
"Ai bata nan ma Hajiyar tana Umarah, Amarya kuma ai ta bar gidan kin san Alhaji ya ƙara aure shine ta tayar da rigima har dai sai da ya saketa yau kwanata huɗu da tafiya ita Hajiya tana can Saudiyya ma duk bata san meya faru ba".

"Allah ya rufa asiri" na faɗa ina zura key a jikin ƙofa har cikin raina kuma banji daɗin sakin Maman Khadija da ya ce anyi ba, na tuna yanda suka ringa kirana a waya suna bani baki akan nayi haƙuri na dawo aure duk zaman haƙuri akeyi dan duk a zaton su da sauran yan unguwa sakina Bilal yayi ashe itama nata sakin na tafe.

Ganin motar sa ajiye ya saka nayi turus dan ban zaci zamu iya samunsa a gidan ba musamman tunda yau ɗin akwai aiki kuma lokaci ya fara ja dan sha ɗaya har ta gota. Ji nayi kamar an ƙara bugun da zuciyata take yi, na yi taku biyu da niyyar in basar amma naji ba zan iya ba. Komawa nayi waje, ba tareda na kullo ƙofar gidan ba na buɗe mota na shiga.

Mu'azzam ya kashe wayar da yake ansawa yana kallo na ya ce
"Har kin ɗakko?"
"Yana gidan ba zan iya shiga ba" na bashi amsa ina dafe ƙirji na da hannu biyu saboda yanda bugun da zuciyata yakeyi na ke jinsa kamar numfashi na zai ɗauke. Tsaki yayi ya kashe motar ya fita yana cewa

"Muje, dukanki zai ko me da zaki ce ba zaki iya shiga ba?"

Sai da ya shiga gidan kafin nayi ƙarfin halin bin bayan sa. Banyi mamakin ganin ƙofar falon a buɗe ba tunda ga motarsa a gida, babu kowa a ciki ko ina tsaf tsaf hakan kuma ba sabon abu bane a guri na tunda na san wanene Bilal gurin tsafta. Ɗaki na na wuce Mu'azzam kuma ya tsaya, nayi turus ganin kan gadon a hargitse alamar ba'a jima da tashi daga bacci ba ga kuma wani ƙamshi da nake jin kamar ma sanshi a wani guri.

Bugun zuciya ta ne ya ƙaru sai dai ban bari tsoro da firgicin dake taso mun sunyi tasiri ba na wuce in da na ajiye ledar kayan tun ranar da na je camp na ɗauka na buɗe su har sun fara warin ajiya dama ga warin sabuntaka suna yi.

Kayan jikina na cire na saka KHAKIn, yanda ka san kyanwa haka nayi wata yar tsurut a cikinsu. Dama sunyi mun yawa tun ranar dana dawo na duba naga over size ne, nayi niyyar na bayar a rage mun sai dai kuma ban samu damar hakan ba abinda ya faru ya wakana. Cikin kayana na buɗe komai yana nan yanda na barshi na ɗakko Abayar da na tanada saboda fita da Khaki na saka sannan na ɗakko farin PLAIN VEIL cikin waɗanda na siya gurin *MARYAM ALL IN ONE EMPORIUM*. Hansa'u ce ta haɗa ni da ita lokacin da muka taɓa yin hira nace mata ina so na fara gwada kasuwanci tace mai zai hana na gwada siyar da mayafi musamman *PLAIN CHIFFON VEILS* da kasuwar su take ci a yanzu gurin yammata da matan aure. Shine ta bani number ta na siyi half dozen na amfani na kafin na samu kuɗi na saro wanda zan fara siyarwa.

Na yaba da kyawun yadikan da kuma quality domin idan ba an faɗa maka ba zaka iya ɗauka irin na Egypt ne. Abinda ya fi burgeni sauƙin farashinta domin har tambaya nayi naji yana ƙasa da na kasuwa kuma ya fi shi kyau ga colors irin wanda sai kayi zuwa nawa kasuwar ma baka samo su ba ƙarin daɗi tana delivery zuwa ko ina a faɗin Nigeria abinda kuma ka siya shi za'a kawo maka.
(Yar uwa mai neman sana'ar da zaki gwada kin san dai yanda kasuwar mayafai take ci a yanzu musamman PLAIN CHIFFON, ga in da zaki sara a ɗinkensu anyi packaging sai dai kawai ki tallata ki siyar ba ruwanki da wuni a sabon gari ko kwari gurin sarin mayafi.
Masu siyan ɗai ɗai muna maraba da ku muna da kowanne size daga smalla, medium har big bayan haka muna sa sauran kalolin luxury mayafai sai iya wanda kika zaɓa. Muna Kano muna aika kaya ko ina a faɗin ƙasar nan da yardar Allah a tuntuɓe mu kai tsaye akan *09064960666*).

Na ninke kayan dana cire na saka su a leda, already dama na siyi farin cambass shi na ɗakko kan shoe rag na saka dan waɗanda aka bani duk sunyi mun yawa. Wayata ta shiga ƙara na duba naga Mu'azzam ne na san zaice na daɗe dan haka ban ɗauka ba na fita daga ɗakin.

Yana ganin na ya juya fita dan dama tsaye yake a bakin kofa, na waiga ina kallon falon kamar bana so na fita daga cikin sa har hawaye ne ya tarar mun. A garin kalle kallen na hango can ƙasan kujera.

Ji nayi kamar an doka mun guduma a tsakiyar kaina, na saki ledar hannu na a ƙasa kafin na nufi gurin da sauri dan tabbatar da zahiri nake gani ko kuma gizo ido na yake yi mun?

Ɗauka nayi na shiga ƙare mata kallo tsabar yanda zuciyata take bugu tamkar zata fito ta baki, ko a lokacin da nake shayarwa duk yanda ƙirji na yake cika ban taɓa saka girman wannan size ɗin ba balle na yi tunanin ko tawa ce na, kai ni ban ma taɓa ganin irin design ɗin ba dan ko da nake a rikice tar na gane designer ce mai tsada ga kuma irin ƙamshin da na ringa ji a cikin ɗaki na nan a jikinata.

Sakinta nayi a ƙasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login