Showing 6001 words to 9000 words out of 257873 words

Chapter 3 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

454

nace masa eh". Yayi murmushi yace
"Karki damu Halims, in sha Allahu komi ya kusa zuwa ƙarshe kinji jinkirin kuma ze zama alkhairi".

Murmushi kawai nayi na miƙe ganin shima ya miƙe tsaye, muna tafe yana cigaba da surutansa ina binsa da toh har muka je get. Seya juya ya kalleni yana murmushi yace
"Halims menene?" Na buɗe ido na kalle shi nace "me ka gani?"
"Duk yanayinki ya canza mana ko akwai wani abu da baki gaya mun ba?" Ya ƙarasa yana jingina da ƙofa tareda langwaɓe kai yayi kalar dake sake wujijji gani cikin soyayyarsa. Sena sauke kaina ƙasa dan ma karya yaudare ni. Ya cigaba da cewa
"Kici gaba da yi mun addu'a kinji in sha Allah zan baki mamaki"
"Toh, Allah yasa" Na bashi amsa. Yaso ya sake jan hirar amma na bashi uzurin kaina namun ciwo ya tafi. Seda na tattare sauran snacks ɗin na kai kitchen kafin na samu Mama a falo suna kallo dasu Imam. Gefe na samu na zauna ina ɓata fuska sau ɗaya Mama ta tambayeni meya faru nace babu bata sake cemun komai ba.

Wayata dana saka caji ta shiga ƙara daga ringing tone ɗin na gane shine hakan yasa na zareta na wuce ɗaki. Sama sama na ringa amsa masa maganganun da duk kame kame yake can yace mun
"Seda naje aje mashin na shafa naji babu komai nace yau Halims tayi mantuwa"
"Mantuwar me?" Na tambayeshi se yayi yar dariya yace
"Baki packaging mun sauran snacks ɗina ba, sannan abincin ma an manta dashi". Dariya da mamaki ya bani lokaci ɗaya amma se kawai na bishi da cewa
"Kash aiko na manta"
"Ko na aiko a karɓa dan kin san da zan fita ma cewa Hajja nayi kar a ajiye mun abinci" ya sake faɗa, ban san lokacin da nace masa
"Ai kana tafiya su Imam suka cinye"
"Kai, harda girkin da kika mun?" ya faɗa se kawai nace masa
"Ni dama banyi maka girki ba ai iya snacks ɗin nayi" ga mamaki se ji nayi yace
"Toh shikenan Allah ya tashe mu lafiya" daga nan ya kashe wayar.
Mamaki sosai ya kamani, wato dama abinci ya biyo baya lallaima Bilal.

Mun saba a ƙalla koda yazo zance idan ya tafi kafin kwanciya bacci se munyi doguwar waya har se na fara bacci haka da Asuba shi ze tashe ni amma yau har na gama shirin tafiya makaranta banji wayarsa ba. Dake ban saba ba duk se abin ya dame ni na manta ma da fushin da na farayi hankali na ya sake tashi dana kira layinsa naji a kashe. Gaba ɗaya wunin ranar sururu nayi shi kowa ya ganni seya tambayi ko bani da lafiya ne haka dana dawo ƙarshe kawai nacewa Mama kaina ke ciwo na shige ɗaki naci gaba da kiran wayar Bilal amma har sannan ƙarfe biyar a kashe. Hansa'u na kira dan dama bata shiga makaranta ba ita bayan mun gaisa nace mata tazo dan Allah idan bata komai,
"Wlh lalle aka samun na ɗauka kema zaki zo ai ko kin fasa" ta bani amsa. Shaf na manta gobe za'a fara bikin Zainab dake tunda mukayi faɗa da Hansa'u ta ara ta yafa ni kuma da muka shirya banma bi takanta ba tunda tun asali dama ai shishshigi yasa ta shigarwa ƙawata faɗa bayan munfi kusa. Ko ankon dan dai mun rigada mun siya ne amma da bazan ba.

"Kina ina?" Na tambayeta ta bani amsa da tana gidansu Ummi me lalle se kawai na zura hijabi na Mama na mitar lallen se yamma sakaliya zan tafi me yasa bazan bari se da safe ba tunda bazani makaranta ba nace mata ai baƙi za'a mun ba ja ba. Naji daɗi da na samu Hansa'un ita kaɗai sauran duk an cire musu sun tafi kangon da za'ayi Hennah party, tas na kwashe yanda mukayi dashi jiya na gaya mata ta gama saurarona tayi shiru nace
"Baki ce komai ba"
"To me zance Halima? Ni da kika ce in cire baki na daga sabgarki da Bilal yanzu kuma in ce wani abu ki canza mun ma'ana?" Ta bani amsa. Se nayi tsaki nace
"Ke matsalarki ruƙo wlh ba komai ya rigada ya wuce ba kuma? Dan Allah ki bani shawara me ya kamata nayi? Wlh ji nake kamar nayi ta kurma ihu wlh ko abinci wlh daƙyar na iya shan tea ji nake komai ya tsaya mun"

"Lallai kinyi nisa to Allah ya taro ki" ta faɗa tana cire lallen hannunta. Zanyi magana wayata tayi ƙara, seda na sauke wawiyar ajiyar zuciya kafin na tashi daga kusa da ita inaji tana cewa
"Ai dama kin ƙarasa zubar da ajin ya taka wlh, ai dai Halima kin bada mata Allah ya yafe miki kawai".

Gefe can na koma na amsa, shiru nayi ina jinsa yayi sallama seda ya maimaita sau biyu kafin na amsa.
"Ina kika tafi?" Ya tambayeni kamar wani Babana. Na tura baki nace
"Gidan lalle"
"Ya miki kyau, to gani a ƙofar gida ya za'ayi yunwa nakeji na taso daga aiki naje gida kawai naga wai tuwo Hajja tayi da miyar kuka fa" ya faɗa. Sena rasa me zance masa ma, wato saboda anyi abinda baya ci a gidansu shiyasa ma ya kirani da haka nan ne baze kira ba yake nufi ko me?
"Hello" ya faɗa jin nayi shiru sena sauke ajiyar zuciya nace
"Ina zuwa toh" na miƙe ban ko cewa Hansa'u na tafi ba na wuce gida. Yana jingine jikin lifan ɗin sa kamar kullum cikin gayu irin na yan birni idan ka ganshi da yanayin shigarsa zaka ce ɗan wani hamshaƙin mai kuɗi ne. Wuce shi nayi na gida, ta ƙofar kitchen ta baya na shiga. Muma tuwon mukayi amma da lafiyayyar miyar ɗanyar kuɓewa data ji naman rago. Seda na ɗumama miyar kafin na zuba a flask na ƙulla manshanu a leda da yajin daddawa sannan na shirya komai cikin basket me murfi na haɗa masa da kwalin exotic ɗaya da robar ruwa. Ina zuge basket ɗin Mama ta shigo kitchen ɗin, kallo ɗaya tamun ta girgiza kai kawai ta fita nima sum sum na fice kamar wadda aka kama tayi sata, koda yake satar ma nayi ai.

Tabbacin abinda ya kawo sa kenan ina miƙa masa basket ɗin ya ɗora a gaban mashin ɗin ya hau ba tareda yace mun komai ba ya amsa key ya bar gurin, tsabar mamaki da al'ajabi kawai na bishi da kallo se naji zuciyata ta karye banma sani ba ashe hawaye sun ɓalle mun seda na fara ganin dishi dishi kafin na ankara.

[5/18, 13:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 3*
Ranar ina idar da sallar isha'i nayi bacci saboda ɓacin rai seda na farka da asuba sannan naga missed calls ɗin Bilal guda biyu ya kirani tun ƙarfe tara na dare. Duk yanda nake cike da haushin abinda yamun jiya amma haka nan zuciyar dake sonsa ta angiza ni nabi kiran nasa. Murya ƙasa ƙasa muka gaisa ya shaida mun yana masallaci idanya fita ze kirani. Ko yasan ina fushi dashi ne se gashi bayan ya fito masallacin ya kira mun daɗe muna hirar soyayya nan da nan kuma na ware daga fushin na manta da komai. Har Mama seda ta lura da sauyina kan yanda na kwanta jiya na tashi cikin walwala wunin ranar kuwa haka nayi shi ga farin cikin gobe juma'a zamu kammala jarabawa. Safiyar Juma'a tun ƙarfe shida na shirya cikin rigar da mukayi ta graduation. Nayi kyau matuƙa ina kallon kaina a mirror a raina ina yarda da maganar Bilal da yake yawan faɗin ni kyakykyawa ce dukda ba wai ina da irin shahararren kyau ɗin nan bane na fitar hayyaci komai nawa ya dace da zubin halittata I'm just too cute.

Nayi mamakin tarar da Bilal a ƙofar gidanmu ba dan dama yana kaini makaranta idan yana da lokaci amma dake munyi magana na tambayeshi ko zeje mun sign out yace aa shiyasa nayi mamaki dana ganshi jingine jikin mashin ɗinsa yana ta buga mun murmushi. Ina ganin Hansa'u sun taho da Zainab Amarya data rufe fuska da niƙan yau zamuyi final exam kuma yau ne kamun bikinta gobe ɗaurin aure na ɗane Lifan ina ɗaga musu hannu muka wuce. Bilal be tafi ba seda muka fito, shi ya fara mun signing a farar rigata ta sign out muka sha hotuna sannan ya tafi muka cigaba da budurinmu har zuwa ƙarfe sha biyu kafin muka wuce gida.

Jakata kawai na aje na ɗauki yan abubuwan da zanyi amfani dasu nayiwa Mama sallama muka wuce gidan kwalliya dan ma mun kama layi dama ƙawar mu ce me kwalliyar. Kusan mu bakwai mukaje, seda mukayi sallar azahar muka ci awara kafin aka farayi dake mutum biyu ne kafin karfe huɗu ya rage ni da Hansa'u kawai. Muna zaune saurayin Baby Isma'il ya kirata a lokacin ita akeyiwa kwalliyar dan haka ta saka wayar a speaker. Na taɓe baki jin muryar saurayin da take mana kuri dashi, daga muryarsa na hasaso garan ƙauye ne. Uzuri ta bashi akan ana mata make up ne yace
"Zakije kwalliya amma baki gaya mun ba?" Se ta bashi amsa da "kayi haƙuri, munyi magana jiya ai na gaya maka yau kamun Zainab ko ka manta"
"Anyi haka, yanzu a ina kuke kwalliyar na gani ko zan samu zuwa na kaiki gurin bikin?" Ya tambayeta ta gaya masa daga nan sukayi sallama bayan yace ze sako mata kuɗin kwalliyar yanzu. Suna aje wayar ko minti biyu ba'a yi ba wayarta tayi ƙara alamar shigar saƙo, Zulaiha dake ɗaukar hoto da wayar tayi ihu tana nuna tace
"Dubu hamsin ya tura miki" nan suka riki ce da ihu tace
"Duk kunci albarka ci zan biya muku harda amarya" dama kwalliyar tamu 2k ce ta amarya dubu biyar gaba ɗaya in akayi total kuɗin ya kama dubu goma sha uku kenan suka shiga mata godiya ban da ni da seda Hansa'u ta taɓa ni kafin nace nagode.

Ko a jiki na, ba rainawa nayi ba ko hassada nake mata Aa kawai tunda mukayi faɗa da Hansa'u suka bi bayanta shikenan nima naja baya dasu, badan itan bama yanke alaƙa zanyi dasu dan duk wanda ya nuna baya so na da Bilal babu ni babu shi balle kuma naga suna wani fariya akan su samarinsu masu kuɗi ko da zamu taho daga makaranta saurayin Zulaihan ne ya dawo damu tana ta wani kauɗi bayan idan da naga damar kula samari saboda abin hannunsu kaf cikinsu babu wadda ta isa ta goga kafaɗa dani ko a yanzu alhamdulillah babu abinda Abbana be tsare mun ba shiyasa wani abun hannun samari baya burgeni su suka dogara dashi da har suke kula mutanen da kana gani kasan badan so bane ba. Niko Allah ya rufa mun asiri na samu me sona ina sonsa zamu mori ƙuruciyarmu tare.

Tsaf muka gama kwalliyar mu, munyi kyau sosai aka mana hotuna kafin muka fita inda motar da ango ya turo ta ɗauki amarya ke jira. Saurayin Baby ya iso dan haka ta shiga motarsa Zulaiha ma saurayinta ne yazo ɗaukar ta se ni da Hansa'u ne muka shiga motar amarya muka tafi. Bayan an sauke mu kowacce seda saurayinta ya bata kuɗin da zatayi liƙi dashi har Hansa'u muna hanya da Alhaji Bala ya kirata seda yayo mata transfer kuɗi masu nauyi kan tayi kwalliya da liƙi haka akayi kamu aka tashi suna ta wanke amarya ni dai dana liƙa abinda na tanada dama na koma gefe na zauna seda aka tashi zamu tafi gida kafin har raina naji babu daɗi ganin still kowacce saurayinta ne ze maida gida suna ta zuzutun kwalliyar su. Kira uku nawa Bilal yace mun ze zo amma gashi har aka tashi shiru dana sake kiransa ma naji wayar a kashe. Wannan ya ɓata mun rai ban ko tsaya jira a gama watsewa ba nabi yan unguwar mu a Adaidaita muka tafi.

A ƙofar gida na tarar da Bilal tareda abokinsa Nura, duk da naji haushin ƙin zuwan da yayi gurin bikin amma ganin dana masa se naji zuciyata tayi sanyi. Light blue ɗin shadda ya saka data dace da atamfar ankon da mukayi me ruwan dark blue da ratsin fari da light blue ɗin. Na isa inda suke Ina haɗe fuska a son na nuna masa ɓacin raina amma na kasa musamman da Nura ya fara zolayarmu wai munyi too match dama mun haɗa baki ne amma gamu nan tamkar ranar auran mu. Haka na lalace a tsaye yana tsarani har seda Abba ya dawo kafin na wuce ciki su kuma suka tafi bayan sun gaisa dashi.

Ina tsaka da sallar magriba da isha'i da suka haɗe mun Amirah ta shiga ɗakin tana faɗin nazo inji Abba. Bayan na shafa addu'a na fita falo, Abba ma zaune yana kallon labaran ƙarfe tara. Seda aka tafi hutun rabin lokaci kafin ya juya kaina yana murmushi yace
"Hali dubu" haka yake tsokanata. Sunan babbar yayarsa ne kuma mafi soyuwa a gare shi cikin yan uwansa. Kwanana uku a duniya ta rasu seya haɗa soyayyar ta data kasancewata yar da ya fara samu duk yake mun.
Murmushi nayi kaina yana ƙasa na gaishe shi yana amsa yana tambayata biki kafin ya ɗora da cewa

"Yaya Salahu ya gaya mun sunyi magana da kawun Bilal yace ze kirashi duk yanda ake ciki ɗazu yake sake ce mun kimanin sati biyu kenan har yanzu beji daga gare su ba". Sena rasa abinda zance masa, ina ji yaci gaba da cewa
"Ɗazun har zan tsaya nayi masa magana da kaina se kuma sai nace bari na fara jin ta bakinki ko dai saƙon be iske shi ne". Daƙyar nace
"Eh Abba ya gaya masa. Dama maganar albashinsa da be fara samu bace ta dakatar dashi" se Abba yace
"Aa, har yanzu dama wannan matsalar bata kau ba? Na zata dana haɗashi da Malam Mansur yace mun an gyara komai tun last two or three months kenan da mukayi maganar.

"Eh Abba an gyara amma salaryn ne wai se wannan watan sannan suka sa masa na wata uku" na faɗa masa iya abinda na sani, se yayi shiru kafin yace
"Ikon Allah, to barka tunda an gyata ɗin. Yanzu ina kuka tsaya kenan a maganar?"

"Yace zuwa ƙarshen watan nan zasu zo" na faɗa ya amsa mun da
"Toh Allah ya nuna mana. Yaya Salahu ya damu, kin san fa babu sanda zamu haɗu ba tareda yayi mun mitar ƙin aurar dake ba. Kullum se yace ga Bishira nan da yaya biyu bayan rana ɗaya aka haife ku"
"To ita Abba ai muna gama secondary aka mata aure bata cigaba da karatu ba" na faɗa cikin shagwaɓa yayi dariya yace
"Haka ne amma dai da kema anyi miki ta tatan da yanzu kin fara tara mana masu samu bari bari a gidan nan ai". Sena rufe fuska ta da hijabi ina cewa
"Haba Abba ni yar yarinya dani ai dama ban isa aure ba har yanzu"
"Baki isa aure ba amma kin iya dafawa gardi abinci" Mu'azzam daya shigo falon ya faɗa, na galla masa harara ina cewa
"Abba ka mana tsakani dashi"
"Se dai in ce ya dena tsokanarki amma babu batun na miki tsakani da ɗan uwanki" Abban ya faɗa nace
"To ka gaya masa ya fita daga sabgata"
"Gaskiya ce bakya so kuma se an faɗa, har gulmarki ake a unguwa da anga yara da kula za'a ce daga gidan nan ne" Mu'azzam ɗin ya sake faɗa kafin nace wani abu Abba yace
"Arziƙi ne ai kai baka san ladan ciyarwa ba ko?"
"Ciyar da mabuƙata ba. Kai kake bin bayanta Alhaji shiyasa kullum take sake shiga daji maimakon ta dawo hanya" Umma data fito daga ɗakinta ta faɗa sena miƙe na sulalae ɗaki na barsu inaji Abban na kareni yana faɗin ai ba laifi bane idan na bashi da babu ai ba za'a masa ba.

Washe gari akayi ɗaurin auran Zainab a ranar kuma muka rakata gidanta mw kyau acan sabuwar gandu. Mijinta matashin ɗan kasuwa ne yayi ƙoƙari sosai a gininsa iyayenta ma sunyi namijin ƙoƙari gurin yi mata kaya da suka sake ƙawata gidan muka fito munata santi da yiwa juna shaƙiyancin wacece next. Duk su uku da ranar su ni kaɗai ce amma dukda haka a jikina inajin sena rigasu amarcewa domin dai nasu samarin a yanda suke ko yau akace a fito ayi aure kowanne yana da abin yin auren amma sun tsaya suna jan lokaci har da Hansa'u da zataje a ta huɗu.

Kusan sati uku da suka biyo baya ina ta juya yanda zan sake ma Bilal magana ganin bamu daɗe dayi ba kuma ha uzurin daya bani se naji dama Abban ya amsa maganar da kansa kawai dan harga Allah yanzu dana gama makaranta bana komai hankalina ya fara komawa akan nima nayi aure na tafi nawa gidan. Safiyar litinin Anty Labiba ta haihu, ina bacci Mama ta tashe ni wai zamuje asibiti daga can kuma bayan an sallameta muka wuce gida Mama tace in zauna mata kwana biyu, ban so ba amma babu yanda na iya haka na tafi gida na haɗo kayan da zanyi amfani dasu na kira Bilal ya mayar dani.

Seda nayi mata sati biyu, dake morata takeyi bata damu da zaryar da Bilal ya ringayi ba kullum se yaje anan zeci abincin dare ko kuma yazo da yamma idan ya taso daga aiki mu ɗanyi hira ya karɓi abinci ya tafi, duk zuwan da yakeyi kuma sau ɗaya ya samu ya shiga ya yiwa Anty Labiba barka dan kusan duk sanda zezo tana da baƙi yan barka dake ta kwana biyu bata haihu ba tsakanin Amir da Inayah shekara ɗaya da rabi ita kuma ta bawa Sadis shekara biyu tun nan kuma seda ta shekara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login