Showing 186001 words to 189000 words out of 257873 words
wannan lokacin na tonuwar asirinsa sai dai bai taɓa zaton zai riske shi ba saboda yanda yakeyin komai a tsare, a nasa wayon kuma ya zata zai iya yin komai har ya gama cikin sirri ba tareda wani ya san mai ya aikata a rayuwarsa ba.
Halima ce ta fara kawo masa cikas, da ace bata duba wayarsa a waccen ranar ba da duk haka bata faru ba amma ko da akayi hakan bai taɓa zaton cewa zata iya tona masa asiri ba.
Zuciyarsa ce ta raya masa
"Idan kai ne ka ganta a irin yanayin data kamaka jiya zaka iya cigaba da rufa mata asiri?"
Kai tsaye ya bawa kansa amsa da ba zai iya ba, ya sani idan da ace ita ce a matsayinsa tun a ranar data fara duba wayarsa daga lokacin dukkan wata alaƙa zata yanke a tsakaninsu baya jin kuma akwai wani abu da zai saka yayi dakon irin wannan baƙin cikin a zuciyarsa da sunan rufa mata asiri ba tareda ya amayar dashi tuntuni ba kuma ba wai dan baya son ta ba Aa, ya sani ba shi ba babu wani namiji da zai iya wannan juriyar sai dai matan daman kuma daban Allah yayi zuciyarsu ya hore mata ƙarfin da zata iya ɗaukar abubuwa da yawa ba kamar ta namiji ba.
Amma me yasa Halima ta zaɓi tozarta shi haka? Mai yasa bata fito kai tsaye ta faɗa masa rabuwa take so suyi ba ya bata takardarta tunda ko da yana son cigaba da zama da ita mutunchinsa da martabarsa ta fiye masa zama da itan amma ta zaɓi fallasa shi a gurin iyayenta?
Da sauri ya ɗauke ƙwallar da ta ziraro masa jin ana ƙwanƙwasa window motar, sai da ya dai daita kansa dukda ya san a kallo ɗaya tilas a fuskanci yanayin da yake ciki kafin ya tashi zaune ya ɗago kujerar sannan ya sauke window. Nasir ya gani tsaye, yayi masa murmushi ya ce
"Ranka ya daɗe; yau dai Allah yayi na ganka".
Murmushin yaƙe shima yayi ya ce
"Ko in ce yau na taki sa'a na ganka ba? Ka san zuwana nawa gidanka da shago bana tarar da kai? Ko ba'a faɗa maka?"
Zagayawa Nasir ɗin yayi ganin haka Bilal ya cire lock ɗin motar ya buɗe ya shiga ya zauna yana cewa
"Sau ɗaya dai Madam ta ce mun ka zo shago ma ina ga sau biyu Salman ya gaya mun kazo kuma duk idan aka sanar dani sai na kiraka a waya amma bata shiga, na ce mutumin ko amarya ce ta canza maka layi ne aka dena samunka"
Murmushin Bilal ya sakeyi kawai ba tareda ya ce komai ba sai Nasir ɗin ne ya sake cewa
"Toh ya al'amura? Ya amarya ta tare kuwa?"
"Bata tare ba weekend ɗin nan dai zata tare in sha Allah"
"Allah ya nuna mana, Maman Al'amin ba zatayi taro ba kenan dan banji Aisha tayi maganar ba" cewar Nasir. Bilal ya sake yin shiru sai dai kuma zuciyarsa ta raya masa shiru fa ba zai yi masa magani ba yana buƙatar wanda zai bashi shawarar yanda zai ji da al'amarin nan a kaf abokansa kuwa idan akwai wanda zai iya buɗewa cikinsa ba tareda wata fargaba ba toh Nasir ɗin ne.
Numfashi ya sauke kafin ya tada motar yana cewa
"Dama nemanka nakeyi"
"Toh ai ga ni Allah ya sa kuɗi zaka bani" Nasir ya tsokane shi". Sai da suka fita daga unguwar ya samu guri ƙasan wata bishiya yayi parking ba tareda ya kashe motar ba, ya sakeyin shiru kusan minti goma Nasir dai baice komai ba sai wayarsa ya ciro ya shiga dannawa har saida Bilal ɗin ya mula dan kan sa kafin ya fara magana yana cewa
"Wani shirme na tafka Nasir gashi yanzu komai ya kwaɓe mun na rasa yanda zanyi". Tiryan tiryan kamar an matsi bakinsa ya shiga zayyanowa Nasir tun daga haɗuwarsa da Jalilah, irin mu'amalar da suka ƙulla har zuwa kama shi da Halima tayi da kuma zancen Zulaiha da zaman Haliman a gidansu zuwa abinda ya faru yau ɗin.
Motar tayi shiru tamkar babu wata halitta mai rai a ciki sai ƙarar Ac dake aiki da kuma gunjin inji, Nasir, mamaki ne ya kashe shi a zaune gaba ɗaya kalaman bakinsa suka tafi hutun wucin gadi duk wacce ya kamo da niyyar haɗa jimla sai ta zille dole yayi shiru kawai yana kallon Bilal ɗin yana sake bitar maganganun daya faɗa masa a ƙwaƙwalwarsa.
Sun kwashi minti kusan goma a haka kafin Nasir ɗin ya iya cewa
"Gaskiya kayi kuskure Abokina; mai ya shiga kanka wane irin tunani kakeyi da har ka jefa kanka a irin wannan halin?"
"Tsautsayi da ƙaddara" Bilal ya faɗa Nasir ya ce
"Da ƙwadayi da son zuciya ba? Wlh ko da na san halinka akan son abun duniya ban taɓa zaton zuciyarka zata iya kwaɗaita maka saɓon Allah a matsayin harkar samun kuɗi ba, Zina da aure? Abun yayi muni gaskiya"
"Ni fa ban aikata zina ba, duk na faɗa maka iya abinda nayi amma Allah ya sani ni ban taɓa shiga jikinta ba" Bilal ɗin ya faɗa cikin jin zafin maganar Nasir ɗin amma kuma ba yanda ya iya babu damar ya ce zai rama tunda laifinsa ne kuma neman mafita yakeyi yanzu.
"Dama akwai wani banbanci ne tsakanin abinda ka aikata? Ko da yake duk ba wannan ba yanzu ya rigada ya faru sai dai Allah ya kiyaye na gaba ni a cikin maganar nan gaba ɗaya ma ban fahimci mai kake so nayi maka ba" Nasir ya sake faɗa. Bilal ya taso cikin fushi ya ce
"Kamar ya baka fahimci abinda nake so ka mun ba? In gama buɗe maka cikina kaji komai sannan kce baka san ya zaka taimaka mun ba? Toh shawara nake so ka bani ta yanda zan shawo kan Halima tayi haƙuri dan ni dai ba zan iya sakinta ba"
Nasir ya zuba masa ido yana kallon sa na wani lokaci kafin ya ce
"Me ya sa ba zaka iya sakinta ba?"
"To akan me zan saketa? Tana so na nasan kuma ko yanzu tilasta mata akayi ba wai son ranta bane dan na san a ra'ayinta ba zata taɓa son rabuwa da ni ba" Bilal ya faɗa yana kumbura baki.
Nasir ya saki dariyar takaici kafin ya ce
"In dai saboda Son da take maka ne ina tayata roƙo ka dubi girman Allah ka sawwaƙe mata Bilal"
"Wace irin magana ce haka ni na ce maka bana sonta?" Bilal ɗin ya sake faɗa Nasir ya tare shi da cewa
"Ƙwarai kuwa baka son yarinyar nan; kai baka ma taɓa sonta ba. Tunda dai Allah ya sa ka samu wacce zuciyarka take so to ka rabu da ita haka taje, ka zauna da wacce kake so itama ƙila a gaba Allah ya bata wanda zai so ta kada ɗaukar haƙƙin yayi yawa. Ta yaya za'a yi ga rashin so sannan ka nemi dawo da ita rayuwarka dawwama tana kallonka baƙin cikin abinda ta ganka da idanuwanta kana aikatawa su kasheta tun kafin wa'adinta ya cika?
In dai shawara kake so na baka toh babu abinda zan ce maka bayan wannan ka rabu da Halima kuma shine mafitarka domin wlh idan ka sake yaudarar yarinyar nan ka maido da ita gidanka idan haƙƙinta ya tashi bibiyarka sai ka rasa inda zaka tsoma ranka kaji sanyi.
Akan me zaka ringa amfani da rauninta ka cutar da ita? Ni dai akanka na taɓa ganin inda soyayya ta zama laifi yarinyar nan ta nuna maka ƙauna ita da iyayenta sun maka halacci amma Bilal ka zaɓi saka musu ta hanyar azabtar da ita da tozartata wlh bana raba ɗaya biyu ko wannan masifar daka jefa kanka ba komai bane sila illah haƙƙin Halima kuma saboda bata da rabon cigaba da shan wahala shiyasa ubangiji ya janyeta ya kawo maka wacce zaku wanke allonku tare"
"Mai kake nufi?" Bilal ɗin ya tambaya, Nasir ya ce
"Nan gaba zaka fahimci abinda nake nufi, ni dai yanzu idan iya wannan ce maganar dama toh ka mayar dani in da ka ɗakko ni"
"Gaskiya ni ba zan iya sakinta ba, alfarma ɗaya nake so kayi mun yanzu. Ka kirata a waya ka ce kana so ku haɗu idan ta zo shikenan ka gama mun komai na san da zarar mun haɗu zan warware duk wata huɗuba da suka mata suke so su raba mu" Bilal ɗin ya marairaice yana faɗa. Nasir ya rasa me zai ce masa, ya ringa masa magiya daga ƙarshe ya ciro wayarsa daga aljihu ya miƙa masa yana cewa
"Gashi nan ka kirata da kanka dan wlh ba zaka sakani a ciki nima ta dena ganin mutunchi na ba".
Wayar ya karɓa y shigar da number Halima ya danna kira.
HALIMA
Ina kwance a ɗaki na tun bayan da na dawo daga kiran da Abba ya mun in da ya zayyana mun yanda sukayi da Yayan Bilal.
"Na faɗa masa ya aiko miki da takardar saki idan ba haka ba satin nan ya cinye basu kawo ba zan maka shi a kotu ne kawai" Abban ya faɗa. Baba Salahu wanda ban san tare sukayi zaman ba ya ce
"Na ce kabar maganar kotun nan Aminu, yanda arziƙi ya haɗa idan akayi haƙuri sai a rabu ta haka. Kuma ni sai nake ganin bai kamata ka matsanta ba domin bai zama lallai ita a ranta tana son rabuwar tasu ba"
Kallon Abban nayi in ga yanayinsa da yanda ya karɓi maganar Baba Salahun, ya kuwa lafta mun hararar da ta sa ma mayar da kaina ƙasa ba shiri dan ban zaci ni yake kallo ba. Baba Salahu ya sake cewa
"Ka dena hararta, ita ce mai zama da shi idan taga a hakan zata cigaba da haƙuri ai mu bisu da addu'a Allah ya shirye shi na san kuma tunda har haka ta faru in dai ba shaiɗan bane a tare da shi ai kunya kaɗai ta isa ta saka ya sauka daga layin banzan da ya hau tunda dama can ba halinsa bane"
"Yanzu Yaya idan ɗaya daga cikin yayanka ta zo da irin wannan matsalar irin hukuncin da zaka yanke mata kenan?" Abban ya faɗa cikin ɓacin rai yana kallon Yayan nasa, Baba Salahu ya ɗan yi jim kafin ya ce
"Karka canza mun magana Aminu. Ni bance abinda yayi dai dai bane abinda ya saka har kaji nayi wannan maganar kawai saboda na san halin Sadiya, ban manta irin dambaruwar da aka sha da ita ba babu yanda kowa bai yi akan ta haƙura da auren yaron nan ba amma ta kafe ina jiye maka tsoron ka takura a raba su daga baya kuma su koma au ɗinke ta hanyar da ba za'a so ba tunda dai tana son mijinta"
"Kayi haƙuri ka ajiye duk wani tunaninka ko shawara a yanzu, Halima yatace, da yardata ta aure shi a yanzu kuma da na hangi cutarwa a zamansu zan datse alaƙar dan haka kowa ya riƙe shawarar sa bana buƙatar su na rigada na yanke hukunci kuma ko mutuwa zatayi wlh sai sun rabu" Abban ya faɗa yana kallona. Hawayena suka ƙara gudu har sannan dai kaina yana ƙasa ban sake ɗagowa ba ya cigaba da cewa
"Kin ɗauka shirun da kikayi zai tabbata gaskiya ba zatayi halinta ba kenan? Tun zuwan da yaron nan abokinsa yayi da maganganun daya faɗa mun na saka mutane suka mun bincike na kuma ringa bibiyar duk wani motsinsa a sannu kuma na gane gaskiyar komai har abinda bai faɗa mun ba na gano da kaina dan shi da ya zo ce mun yayi kawai ko da ace kin nuna buƙatar komawa gidan Bilal mu hanaki saboda Bilal ɗin ba wanda muka sani a baya bane cigaban zamanki da shi kuma zai iya jefa ki cikin halin da zamu zo muna da na sani.
Ba sai na faɗa miki abinda na binciko ba dan kin rigani sanin wasu amma tunda naga har yanzu hankalinki bai tsaya guri ɗaya ba a hakan kike tunanin sake koma masa to babu wannan maganar, yanzun ma na kiraki ne dan kar idan yayi taurin kai na maka shi a kotu ki ce an tozarta uban yayanki, dan haka tun da girma da arziƙi ki faɗa masa ya sallameki".
Na ringa kallon Baba Salahu in ji ko zai sake magana amma bai ce komai ba da alama yaji gargaɗin Abban da ya ce baya buƙatar shawarar kowa. Haka na tashi ina share hawaye jiki ba ƙwari na koma ɗaki na kwanta na cigaba da sabuwar sana'ata.
Ƙarar wayata ta saka na waiwaya na kalli in da take, sunan Yaya Nasir da na gani ya saka na ɗakko ta amma kafin na amsa ta katse. Ajiyewa nayi ina tunanin ko me ya saka ya kirani sai Allah. Ƙila haƙuri zai bani ya ce in koma gidan Bilal ko kuma shima irin Hafiz ɗin ne cin dunduniyar Bilal zaiyi ya ce kar in koma?
Tambayar kaina na shigayi wai ma shi Hafiz meye ribarsa duk a cikin maganar nan? Yanzu ladan me ya samu daya zubarwa da Bilal mutunchi a gaban iyayena? Wani haushinsa ya kamani, wato shiyasa aka ce makashinka yana tareda kai yanzu idan ba halin ɗan adam na rashin tsoron Allah da munafunci ba ta yaya za'ayi abokinka ko ma in ce amininka ne zai kawo sukarka gidan surukai shi da ya kamata ace ko wani aibunka ya ji sai inda ƙarfinsa ya ƙare?
Kiran daya sake shigowa ya tsayar mun da tunani na ɗaga da sallama muryata a dashe saboda kukan da na sha. Daga can ɓangaren Bilal ya sauke numfashi tamkar jaririn daya yini yana kuka, na zare wayar daga kunnena ina kallon screen ɗin dan in tabbatar da waye ya kira amma naga number Nasir ɗin ce dai.
"Dan Allah karki kashe Halims" ya faɗa kamar ya san abinda nake shirin yi kenan. Na dakata da waya a kunne ba tareda na ce komai ba daga can ɓangaren ya marairaice ya ce
"Duk abinda aka faɗa miki ba gaskiya bane wlh so kawai sukayi su raba mu"
"Abban nawa ne yake ƙarya kenan?" Na faɗa cikin dasasshiyar murya, da sauri ya ce
"Aa wlh ba shi nake nufi ba su waɗanda suka faɗawa Abban nake magana ai kin sani dama duk ba ƙaunar ganinmu tare sukeyi ba dan Allah karki bari suyi galaba akanmu kinji my Halims na sani kina so na zaki mun uzuri duk abinda ya faru sharrin shaiɗan ne amma ina neman alfarma ki bani dama mu zauna in warware miki komai na san zaki fahimce ni daga nan sai kiyi mana alƙalanci".
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 48*
Abinda ya fi tsaya mun a rai yanda duk sanda zamuyi magana sai ya ce ya san ina son sa, kenan shi baya so na kuma yana ɗaukata wawuya saboda ina sonsa dole na jure duk wani abu da zan fuskanta daga gare shi ko me?
"Dan Allah karki ce Aa Halims ki taimaka mu haɗu kada ki bari mahassada suyi galaba akanmu" ya sake faɗa cikin marairaice kamar zai fashe mun da kuka. Cikin dakiyar da na aro na azawa kaina na ce
"Ka sameni a gidan Anty Labiba bayan Magriba"
"Gidan Anty Labiba kuma?" Ya faɗa kamar a ɗan tsorace, a taƙaice na ce
"Idan ma ba zaka zo ba ai na tabbatar kaji saƙon Abba a gurin Kawun ka koh?"
"Haba Halims me yasa ki...." Ban tsaya sauraron mai zai ce ba na katse wayar na jefar da ita gefe na dafe ƙirji na da yake duka uku uku.
Siririn kuka na saki, ina jin yanda zuciyata take yamutsawa dalilin famin ciwon son da ya cika ta. Na jima ina kukan sai da aka fara kiraye kirayen la'asar kafin na tashi nayi sallah bayan na idar nayi wanka, ko mai ban shafa ba na zura doguwar rigar abaya na ɗaure kaina da ɗankwalinta na fita falo. Tunani nakeyi yanda Mama zata barni na bi Anty Labiban.
Mama kaɗai na tarar a falo tana shan fura Sharifa na kwance tayi matashi da cinyarta tana bacci na zauna kan kujera ina kalle kalle kafin na ce
"Sai ke kaɗai Mama?"
"Eh, Amirah sun fita da Zainab wai zasu karɓo awara a gidan Sahura ta bayar ayi musu" Maman ta bani amsa a sake yanda banyi zato ba ganin yanzu mun koma kamar wasu abokanan faɗa a gidan kullum cikin ɗaure mun fuska take.
"Anty Labiba fa?" Na sake tambayarta ta ce
"Tun ɗazu ta wuce dama wai hanya ce ta biyo da ita ba zama sukayi ba"
"Lah shine basu mun sallama ba na so fa in bita" na faɗa a sanyaye, na saci kallonta jin tayi shiru itama ni take kallo kamar me karantar gaskiyar dake bayan maganar da nayi sai kuma ta ce
"Kina gurin Abbanku ai sanda suka tafi, sai ki bari gobe in Allah ya kaimu ki je ai"
"Yau ɗin dai na so in je sai na kwana gobe na dawo" na sake faɗa, ga mamaki na sai na ji ta ce
"To sai ki shirya ai ki tafi yanzu tunda Magaji yana nan sai ya sauke ki". Ajiyar zuciya mai ɗan nauyi na sauke kafin na miƙe na wuce ɗaki. Kaya kala ɗaya na zuba a jaka sai ɗan abinda zan buƙata na undies na zura Hijabi na fito har sannan Mama na zaune ta bini da kallo bayan da na mata sallama. A compound muka haɗu da Abba da alama fita zaiyi, naji kamar na juya amma ya rigada ya ganni dole na ƙarasa na amsa masa tambayar da yake mun akan ina zanje.
Shi ya sauke a gidan Anty Labiban, kamar mai tunanin zan tafi wani gurin bai matsa ba sai da na shige gidan nayi murmushi kawai ina cewa "ko Abba ya zata guduwa zanyi ne ya kasa ya tsare".
Ban ɓoyewa Anty Labiba dalilin zuwana gidan ba, tayi shiru tana kallona kafin ta ce
"Wace shawara kika yankewa kanki Halima"
"Ban rigada na